Page 6
*ABIN DA CIWO*
Na
©Rahma Kabir MrsMG.
Wattpad @rahmakabir
Page 6.
Sameeha tana shiga ɗakinta ta zauna a gefen gado tana cewa.
Ikram ku tashi ku koma falo da kallonku ina so na ɗan samu barci.
To anty amma har Yaya Hauwa ta tafi ne?
Eh 'yar aiki ta kawo mini gata can na bata ɗakin kusa da kitchen sam hankalina bai kwanta da yarinyar ba, gata dai 'yar kauye ce a yanayin shigarta amma alamu ya nuna idonta a buɗe yake.
Ai Wlh anty ke kika kyalesu amma da nice banga 'yar iskan da ta isa tayi mini haka ba, kuma umma sam bata bin bayanki ɗazun ina ji da kuna waya sai faɗa take yi miki. Allah shawarar da zan baki tana yin wata guda ki sallameta, in sunyi magana kice bata yi miki aiki mai kyau, kinga sai ki sa umma ta nima miki wata.
Hmmm umma cewa tayi wai ko marina Hauwa tayi karna rama na rabu da ita saboda sharri suke kokarin bina dashi, ni kam bazan ɗauka ba wlh, shiyasa ma ba zan sake faɗawa umma matsalata da su ba tunda ba bin bayana take yi ba. Ni ina ganin ɗiyar Inna Rukayya zan ɗauko kawai in sakata a makaranta tunda kinga su can ba wani karatu suke samu ba.
Shikenan ma ba ruwanki da wata 'yar aiki tunda aikin gidan ba wahala, na tsakar gida kyasa mai gadi da driver suna gyara miki.
Allah dai yasa mu dace.
Cewar Sameeha, Ikram ta amsa da amin kana ta tasa ƙeyar yaran suka fice daga ɗakin.
****
Najwa.
Har ta isa gida tana tunanin shawarar da Nafeesa ta bata akan ta haɗa kai da su Hauwa, sai dai ita tana ganin kamar ba zasu karɓeta ba ƙila suyi zargin ko Sameeha ce ta sakata, amma zata yi iya kokarinta ganin ta tusa kanta in dai zata samu cikar burinta, dan sai da Nafeesa ta ƙara hasko mata auren Aminu kafin ta ƙara jin kwarin guiwa, a yadda take jin zuciyarta tana bugawa so take ta ƙara tozali da shi taji muryansa ko hakan zai saka ta samu sukuni, sai dai ko taje gidan ba zata ganshi ba dan ta san zai yi tafiya kuma sai ya jima bai dawo ba kamar yadda Ikram ke fadya mata, koda ta isa gida ta samu inna ta tafi barkan da ta ce mata, dan haka ta kwanta a ɗaki tare da danna wayarta da take rakani kashi, taja guntun tsaki tana cewa.
'Yar wayar zamanin nan ma ta gaga in riƙe saboda duk samarin nawa talauci yayi musu kanta, haba wlh dole in sauya sheƙa nima in faso gari a dama dani, dan na gaji da wannan rayuwar maneji, yanzu da ace ina da babban waya ƙila in lalubashi a facebook in ga hotonsa ko ɗan chart in fara da shi.
Ta ƙare maganar tana jan guntun tsaki, sai ga kiran Zaidu ya shigo kamar ba zata ɗauka ba ta ɗaga kiran ta saka a kunne tana sallama, Zaidu ya amsa mata yana cewa.
Amaryata ya gajiyarki na jiya da fatan Sameeha bata gajiyar min dake sosai ba.
Hmmm ai gajiya tabi lafiya, kyawun gidanta ma ba zai sa naji na gaji ba dan Wlh Anty Sameeha ta dace da gidan duniya.
Gaskiya kam gidanta yayi kyau Allah ya bamu kuɗi masu albarka na gina miki kamar sa ko wanda ya fishi.
Ameen ya rabbi, dama ina shirin kiranka sai naka ya shigo.
Ok ina jinki me ya faru.?
Waya nake so Android wacce ake yayi na gaji da riƙe rakani kashin nan. Kaga ko da baka samu zuwa ba sai mu riƙa yin charting ko.
Hakane amma yanzu ina cikin uzuri sai in na gama da shagona In Sha Allah zan siya miki mai kyau, dama tuntuni nake tunanin yin haka.
Ai dama na san ba zaka siya mini ba sai dai kayita mini hanya hanya, in ba ta ƙuƙe mini ba ai da bazan tambayeka ba.
Sai kit ta kashe wayarta dan ta nuna masa taji haushi kuma da gaske haushin ta ji dan gabaɗaya ji tayi ta tsaneshi bata son ganinsa, Zaidu ya ƙara kiranta amma taƙi ɗauka har sai da yayi mata kira sama da uku tayi banza da shi, ya tura mata da sakon.
_Kiyi haƙuri zan shiga kasuwa yanzu in siyo miki koda second hand ne sai ki fara amfani da shi kan na samu kuɗi na siya miki sabuwa._
Data karanta ta ɗan saki murmushi sai ta ki bashi amsa akan bata sauko ba dan ta ƙara tunzurashi ya siyo mata ɗin, ta yatwine fuska.
Dama tuntuni haka nake maka da yanzu na dan samu abinda na sama a jikinka, Nafeesa tasha bani shawarar haka sai naƙi yarda ganin kar in fito da kwaɗayi ga samarina su raina mini wayo kuma suna yi mini kallon ustaziya mai hankali kar na zubar da kimata, amma yanzu ma duk zan yi maganinku na zubar daku gabaɗaya a kwandon shara, Saboda nayi mijin da ya kere sa'a zai fito mini da ajina sosai.
Tana gama faɗar haka ta miƙe ta fito dan ɗaura abincin rana tunda Inna tabar mata sallahu a gurin Yaya Sadik da ta samu a gidan.
***
Zaidu.
Yana zaune a ɗakin umma suka yi waya da Najwa, bayan ya gama tura mata sako ya duba umma yana cewa.
Wani lokacin yarinyar nan ina rasa inda tunaninta yake zuwa, gata da ilimi amma wani lokacin bata aiki da shi.
Meya faru kuma?
Ummu tace tana dubansa, sai ya bata labarin yadda suka yi yanzu, umma ta ce cikin faɗa.
Haba Zaidu ai tayi maka kawaici tunda sai yanzu take nuna maka tana son babbar waya, kuma ai ya kamata ka siya mata tunda ita ce ake yayi, ko Ikram baka ga wacce Saurayinta ya siya mata bane, in har kana so ka samu zuciyar Najwa dole sai kana kyautata mata, tunda 'yar uwarka ce ko ba soyayya kayi mata dan zumunci.
Amma umma nace mata ta bari na samu kuɗi yanzu ina fama da shagona ne.
Ka ɗauka cikin kuɗin ka siya mata mai saukin kuɗi itama ta shiga zamani a dama da ita, na tabbatar in kai ka fara siya mata waya a samarinta ka ciri tuta kuma zaka samu matsayi mai kyau, sannnan gidansu ma ba zasu hana ta riƙe wayar ba tunda kai na gidane ka bata wayar.
To shikenan umma zan duba na gani, amma naga tun yanzu kina goyon bayanta kar nan gaba tayi mini laifi na kawo kararta ki shigar mata.
Aiko kasan ko kaine da gaskiya ba zanbi bayanka ba dan yana da kyau in nuna kawaici, ba zan soka ba in ƙita dan na haifeka.
Amma ai wasu iyayen ko nasu keda laifi goyon bayansa suke yi.
To ni ba irin wannan iyayen bane ai kaso naka duniya ta ƙishi, kaƙi naka duniya ta soshi.
Wannan zancen haka yake ummanmu bari na fita na fara niman mata wayar kafin ta fashe dan fushi.
Ya faɗa yana 'yar dariya, umma dariyar tqyi tana a dawo lafiya Allah ya tsare ya amsa da amin ya wuce kasuwa.
Kamar yadda yayi mata alƙawari da yamma bayan sallar la'asar ya isa ƙofar gidansu ya aika mata yaro da wayar a cikin leda da karamar takada a ciki ya wuce. Najwa ce a tsakar gida yaron ya samu ya bata sakon yace inji Zaidu, ta amsa da sauri sai yaron ya fita, inna ta fito daga bayi tana cewa.
Me Zaidun ya aiko miki da shi?
Yanzu zan duba in gani.
Ta bata amsa tana zama a karamar kujera, ta buɗe ledan taga kwalin waya wato sabuwa ya siya mata kimanin na dubu hamsin da biyar, wani tsalle ta daka tana murna tare da cewa.
Inna waya toch ya siya mini wlh kin ganta sabuwa dal a kwali.
Allah yasa ba matsa masa kika yi ya siya miki ba dan nasan halinki.
Kai innata! wlh hakanan yaji ra'ayin kawo mini wata kila ya samu Kuɗi ne ko kin mance siyayyar daya yi mini shekaran jiya.
To Allah ya sanya alkhairi ya yi masa albarka. Amma ni nafi son ya turo ayi maganar auren nan zanfi samin natsuwa.
Inna tunda shi yace a bashi lokaci a jirashi, in kuma rabon wani ya ratsa ya yiwa kansa.
Me kike nufu da wannan maganar? Najwa ko dai yaudarar yaron nan kike ba sonsa kike yi ba kisa muji kunya?
Da bana sonsa inna ai bazan bari soyayyarmu tayi tsawo haka ba, kusan shekara guda fa muna tare.
Hmmm inna tace tayi bismillah ta fara alwalar sallar la'asar, Najwa kuwa ta miƙe ta shiga ɗaki ta saka wayar a caji cikin tsananin murna, ta duba takardan dake cikin ledan ta karanta sakon bada haƙuri ne, murmushi tayi tana mele baki, duk da wannan hidimar da yayi mata baisa ta sauko daga ƙudurinta ba dan gani take yi ma ta samu abinda zai sa ta samu kusanci da Aminu.
...
Ana gobe walima.
Najwa ta shirya tsaf ta tafi gidan Sameeha da nufin kwana zata yi, sai dai zuwanta da dalili saboda tana son ta samu number ɗin Aminu a wayar Sameeha, dan ta buɗe facebook tayi searching sunansa amma bata samu ba, ta san koda baya facebook to yana WhatsApp dan haka ta ke buƙatar number, saboda shawarar da suka yi kenan da Nafeesa a chat, dan tuni suka cigaba da tsare tsarensu ta online, sosai Nafeesa taji daɗin Wayar da Najwa ta samu dan ya ƙara musu kusanci da juna kuma zasu riƙa yin komai a waya ba lallai dole sai sun haɗu ba. Tana isa ta samu ana ta shirya kujeru a kasan kanofi da aka kafe su guda huɗu a tsakar gidan, tuni Sameeha ta saka aka samo mata hayarsu zuwa gobe zasu zo su kwashe, dan so take komai a yi shi cikin tsari, maganar abinci ma bayarwa tayi a yi musu bata so ta bawa Kowa aiki, tasa ayi waina da sinasir da miya, jelop din shinkafa da alale sai kaji guda talatin da aka gyaresu suna aikin suyansu ita da Ikram sai Mai aikinta, akwai rago da yaya Kamalu yace za a gasa shi a kawo musu goben, sai drinks kuma da ruwa gasu nan katam katam da yaya Kamalu ya kawo dan shine Aminu ya bawa kuɗin siyayya. Najwa tana shiga falon da sallama bata samu kowa ba dan duk suna kitchen, sai ta sauke idonta a kan katon hoton Aminu dake manne a bango ga kuma wanda suka ɗauka tare da Sameeha da kuma wanda suka ɗauka da yaran, sai ta sauke ajiyar zuciya a hankali tana cewa a zuciyarta.
'In Sha Allah saika zama mallakina sai na yi mulki a cikin zuciyarka.'
Sai ta wuce zuwa kitchen ta samesu sunata aikin suyan kaji, suka shiga murnan ganinta Ikram tana cewa.
Oyoyo matar babban yaya, ashe zaki zo?
Haba zan zo mana tunda ni nace zan zo ai. Ina yini anty Sameeha ya shirye shirye?
Lafiya lau Alhamdulillahi Najwa, yasu inna fatan kowa lafiya.
Lafiya lau sun ce a gaisheki. Inna tace ba zata samu zuwa ba saboda akwai suna a nan gida kawo.
Allah sarki nima badan taron nan ba da dani za ayi sunan, amma In Sha Allah zan je inyi musu barka.
Allah ya yarda, yanzu me zan tayaku dashi?
Zo ki karɓi suyarnan in je in watsa ruwa dan zafi nake ji.
Cewar Sameeha, Najwa tace to amma zata aje jaka ta dawo, sai ta fita ta shiga ɗakin Amrah ta aje jakarta ta cire hijab ta dawo ta amsa aikin, Sameeha ta tafi ɗaki ta barsu, Najwa ta kalli Ikram tana murmushi.
Bakuwa Anty tayi ne?
A'a Jamila ai 'yar aiki ce da su yaya Hauwa suka kawota.
Ashe har ta zo, 'yan mata sannunki.
Yauwa Jamila ta bata amsa a takaice, kiran daya shigo wayar Ikram ce yasa ta miƙe ta fita daga kitchen ɗin, a lokacin dabara ta faɗowa Najwa tace cikin jan Jamila da hira.
Sun barki kin ɗanɗana kazar kuwa?
Sun bani amma kin san kaza bata isata tunda gida babu maƙota sai ɗai ɗai.
Ɗauko ledan can ki ɗiba iya yadda kike so kije ɗakinki ki ɓoye kici abinki hankali kwance, nima kinga zan ɗiba kasona kafin su zo dan nasan halin Anty akwai rowar tsiya.
Jikin jamila yana rawa ta ɗauki baƙar leda ta ɗiba kazar iya son ranta ta fita da sauri ta shiga ɗakinta ta ɓoye kana ta dawo tana washe baki cike da mugun farin ciki.
Amma ke 'yar uwar mai gidan ce ko? Dan na kula danginsa basa shiri da anty.
Hmmm ni ƙanwarta ce amma babanta shine yayan mamana, sai dai ni ina zuwa ne saboda takurani da inna tayi, dan sam Anty Sameeha ba tada kirki.
Ai naga alama dan tunda na zo gidan nan take zuba mini dokoki ga shegen saka mini ido, abu kaɗan nayi suke kyarata ita da ƙanwarta, gaskiya naga ke kina da kirki ba halinku ɗaya ba.
Hmmm sai ma gobe zaki ga yadda zata yiwa 'yan uwan mijinta, sam basa jin daɗinta ni har tausayinsu nake.
Cewar Najwa tana taɓe baki, a zuciyarta kuma tana jin wani daɗi da farin ciki dan ta samu Jamila zata fara aika sakonta gurin su Hauwa, saboda ta san sun turota ne wu riƙa samun labarai a gurinta, kuma ga dukkan Alamu Jamila zata yi mata matuƙar amfani a cikin rawar da zata taka a gidan, muryar Jamila taji tana cewa a hankali dan kar ajita.
Kin san Allah na tsani matar nan addu'a nake Allah yasa Alhaji ya saketa ya auro mai mutunci.
Hmmm da nine 'yan uwansa sai na saka sun yi mata kishiya.
Cewar Najwa itama a hankali, Jamila ta saka dariya tana cewa.
Wlh kuwa da nayi murna naga ƙarshen ɗaga kai.
Jamila sunanki ko?
Eh.
Ina so za ki yi mini wani abu wanda zan biyaki da kuɗi mai tsoka amma ina so ya zama sirri a tsakaninmu, idan kika faɗawa wani wlh sai na saka an ɓatar dake dan mijin da zan aura soja ne kina yi mini ba daidai ba zan saka ya harbeki da bindigarsa.
Wlh zanyi miki kome kika so in dai zaki biya ni, amma dan Allah karki saka a harbeni.
Jamila ta faɗa tana zare ido, Najwa ta saka dariya tana cewa.
Ke wasa nake miki naga duk kin firgita ne, kawai dai zolayarki nayi, amma naga tamu ta zo ɗaya bani number ɗinki ko gaisawa mu riƙa yi.
Sai a lokacin Jamila ta samu kwanciyar hankali ta saki murmushi tana ce mata wayarta tana ɗaki anjima zata bata, Najwa tace to suka cigaba da aiki, sai dai ita Najwa da abinda take saƙawa a cikin zuciyarta, haka nan taji ta gwada Jamila dan ta hasko ƙila nan gaba tayi mata amfani, kuma ta kula yarinyar akwai wayo da son kuɗi, ta tabbatar da hakane su Hauwa suka yi amfani suka ja ra'ayinta ta zo aiki gidan, itama zata yi amfani da wannan damar wajen samun cikar burinta.