BAƘIN HAURE..........

Chapter 4

by @maidambu41

*BAƘIN HAURE....🐾🐾*


  {Greed for Money is the roots of all evils🫀}

 Arewabooks:maidambu41

Wattpad:Mai_Dambu

Mallakar:Mai_Dambu

      *004*

*Captain*

Juyawa yayi ya kalli Magaji Abba Chindo da yake mishi dariya, idan ya sake suka yi faɗa. Tow yau ba zai iya samun nutsuwa ba, don haka ya saki dan ƙaramin murmushi ya ce mishi. "Sai a ka yi rashin dace, ni mata-maza, bana haɗa jikina da yan maza, musamman waɗanda basu dauki aikata sabo illa ba." Daga haka ya juya abinshi, shiru wurin ya ɗauka, abin ya bawa Magaji Abba Chindo dariya, amma da ya nutsu sai ya fahimci da gaske Captain magana ya gaya mishi. Mikewa yayi zuwa ciki jirgin don da suna daga waje ne.

"Kai magana ka gaya min?"

Murmushi Captain ya yi sannan ya ce mishi.

"Kaga ni bana son tashin hankali, kayi hakuri ba magana na gaya maka ba." Kurawa juna ido suka yi, sannan ya fauce Map din hannun Captain ya yaga gida biyu.

"Naga yadda...!" Kafin ya rufe baki Captain ya zabga mishi marin da sai da ya daina gani. D'ago shi yayi ya ce mishi. "Kada ka sake wani yaji wannan labarin domin zai maka dariya, kada ka kuma aikata abin da kayi. Ni idan kaci zarafina zan yafe maka. Amma idan ka taba aikina zan baka sakamakon da yafi haka. " Wato marin nan, ya shiga Magaji domin kuwa hakorin shi na wannan bangaren har yana girgiza.

  Sauran matuka jirgin duk hankalinsu na kan aikinsu, babu ruwan su kuma haka da Captain yayi shi ne zaman lafiya, don haka, A hankali ya juya tare da fita daga dakin, Captain ya gyara takardan, bayan Mr Oke ya mika mishi salatep, ya gyara suna hira sama sama.


   Lokacin sallah yana yi suka fita baki ɗaya, musamman Domin a yi sallah wanda Captain ne ya jasu, sannan aka ɗauko abinci da wasu daga cikin sojojin suka dafa, mika mishi aka yi ya kalli agogon ya ce musu. " Na koshi!" Haka suka kyale shi, ya tashi tare da ɗaukar abin hango wasu abubuwan, yana me duba gabansu.

Komawa ciki yayi ya dauki wata waya,ya shiga duba sakon.

_Sir mutanen nan basa gudanar da kome sai dare yayi,hankalin kowa ya koma tsoron dare. Kada ku shigo da rana domin zasu gudu_ mai da wayar yayi ya ajiye, taya zai yi facing Commodore? Haka ya daure ya fita ya zauna a gabanshi.

  "Yallabai!" Cikin wani irin yanayi Commodore yake kallon Captain kamar ya shake dan banza amma yanzu ya fahimci gayen ya wuce tunaninshi. Mari daya yayi mishi, hakorinshi yake girgiza ina kuma da sun daku, tow kuwa kareraya shi zai yi ya tara dan iska a gefe kenan? "Meye?" "Inda zamu shiga basa kome da rana, sai dare."

"Tow me kake so nayi?" Ya faɗa yana nad'e hannunshi a kirji. "Ina ga a tsaya nan, sai mu duba nisan kafar ruwan, idan nisan ba yawa sai muyi musu shigar dare."

"A matsayinka na wa?" A hankali yayi kasa da kanshi kafin ya ce. "A matsayina na soja, kuma shugaban rukunin sojojin da suke aikin sirri, mataimakin ka. Na bada shawara kuma na fita." Ya faɗa yana me mikewa daga gaban Magaji ya nufi dakin iko. Jikin Magaji ne yayi sanyi, kudirinshi shine a kashe Captain a wannan lokacin, kuma ba zai fasa ba.

  Don haka ya mike tare da fito da sabon tsarin da ya sauya, a ka'idar zuwansu nan. Shi ne shi zai jagoranci wasu daga cikin Yaranshi su isa har inda ake zaton abin, amma son zuciya irin nashi, sai ya kalli Captain ya ce mishi. "Kai da team dinka zaku tafi inda ake badakalar, ni da team dina zamu zauna a nan. Domin ba za a rasa wanda zai iya kawo farmaki ba, idan kuma ba a samu ba kunyi nasara, ga fireworks sai ku sanar da mu."

"Amma Sir wannan abin babu tsari, taya kana shugaban sojojin kuma kace Captain zai jagoranci wasu daga cikin mu, kuma mutumin da bai tab'a rike bindiga ba, aikinshi kawai sanin meke faruwa."

"Shi namiji ne, idan har ya cika namiji ya jagorancin tafiyar."

"Na amince " ya faɗa tare da ware wasu daga team ɗinshi. "Zamu tafi in sha Allah hakkina ne, na bawa rayuwarku kariya,ku yarda da ni in sha Allah zan mai daku cikin iyalanku lafiya."

"Mun amince " suka fada, sannan ya shiga musu bayani tare da tara su a cikin wurin tukin jirgin, yana nuna musu yadda tafiyar zata kasance.

***

Addah


Kallon Addah mutumin yayi ya ce mata. "Ki kula da zuciyarki kada ki aikata abin da zai dame ki, ita yarinyar babu ruwanta." Kasa magana tayi can ta daure ta ce mishi.

"Yanzu haka 'yata zata kasance? Babu wani cigaban rayuwa sai ta karuwanci? Karshenta."

"Ba farinciki da nutsuwa ake nima ba?" Ya tambayeta yana gyara zaman wandonshi, domin yana matukar jin dadi Adda tana cikin mata na musamman da yake mu'amala da su. Murmushi yayi yana faɗin, " A gaskiya bakya tsufa " dauke kai tayi ta gyara jikinta, sannan ta dauki jakarta ta bar dakin, tana fita waje ta sauke ajiyar zuciya, tana jin wata iriyar tsanar Zahra. Duk inda zata aiki akan zahrah sai ta bada kanta bata san me yasa haka ba, yarinyar ta shiga ruyuwarta ita da take tutiyar ta samu hannun jari, ashe bala'i ta daukowa kanta.


   Hadiye bakinciki tayi ta shiga kasuwa tayi sayayya. Sannan ta dawo gida ta mikawa Ummi wata leda, ta ce mata. "Ki girka mata wake da hantar mu kai mata asibiti!" "Tow ai basu bamu kati ba" "eh idan kuka isa ku kira Zulaihah."

  "Hmmm!" Inji Munaisah, ta cigaba da gyaran farcenta, domin tana son zuwa saloon a mata fixing farce. "ina son zuwa saloon dai, domin farce na da kaina yayi datti." Da Ace Munaisah ta san halin da Adda take ciki ba zata fara fadar ita zata saloon ba, dauke idanun tai kanta ta wuce ɗakinta. Sai da tayi wanka ta cire roban condom din mata ta wurga cikin masai din, sannan ta wanke gabanta tass. Sannan ta gyara ta fito, Adda ta san darajar gyaran jiki, shi yasa take gyara jikinta. Duk da abin da take yi be dace ba, amma kuma ita ta dauki haka a matsayin wata hanya ta samun kudi cikin sauki,


Aiki take amma a zahirin gaskiya gangan jikinta ke jagorantar aikin, amma zuciyarta da kwakwalwarta basa bata haɗin kai, baki daya ta kashe rayuwarta domin yau ta samu riba, tana son ace yau ta zama wata hamshakiya, amma wani ikon Allah rayuwarta da na Yarta ne a lalace, wanda take ganin ta maida ita baya an gaya mata ba zata iya kome da ƙaddarar ta ba, "hmmm!" Ta fada tana kallon tilin kayan da ta sauke daga wardrobe ɗinta, tana mamakin me yasa meta da wannan aikin? Lallai ya kamata ta mike wannan lamarin sai kace an saka mata hannu. Jin muryar yan matan da suke mata aikin abinci suka shigo gidan yasakata mikewa


"Ina Zahrah take?" Jin murya Shamsiyah yasata fitowa daga cikin ɗakinta tana kallonsu. "Tana asibiti ba lafiya." Daga haka ta nuna musu kome da kome da ta sayo, sannan ta wuce ɗakinta ta kwashe kayan. Wurin karfe daya na rana Zulaihah ta kirata. "Wai Addah ba za a kawo mana abinci ba ne?" Runtse idanuwan ta tayi kafin ta lailayo wata uwar ashar ta maka mata, "babban.....,,, ubannki! Ba za a kawo ba kina da abinda zaki fada ne? Shegiya mara mutunci."

"Addah dubu dari aka baƙi, idan ba zaki d'aga kafa ba, ki dawo min da kudin mu maza, dawo da saba'in xan baki talatin din."

Kamar ta fasa ihu tayi shiru, kafin ta ce mata. "Bana son iskanci, nace ba za a kawo muku ba ne? An jima za a kawo muku." Ta fada a fusace, "Adda ihu kike mana fa?" Inji Zulaihah. "Yanzu don Allah na ce muku ba zan kawo ba ne, ku yi hakuri me da me kuke bukata?"

"Yawwa a hada mana da kofi biyu, kayan tea flask da kuma special abinci dare da rana. A kula da mu kamar baki Hajiya Addah."

"Shi kenan za a kawo muku." Wannan shine asalin dole kanwar naki. Haka suka kashe wayar, kowa najin babu dad'i ita Addah tana ganin kamar Zulaihah bata kyauta mata, ita kuma Zulaihah tana haka ne domin huce takaicin Mahaifiyarta.

***

 *Zahrah*

Ruwa aka sanya min, bayan an kara duba min ciwon, shi ne aka fito dani, yanzu dai sun saka min ruwa da wasu allurai. Ina jin wayar Zulaihah da Addah, a hankali barci yayi gaba da ni. Ban farka ba, sai wurin karfe uku, na samu Munaisah da Ummi suna hira sama-sama. Zulaihah bata dakin, kallonsu nayi kafin na ce musu. "Kunzo ne?" Domin ban kawo a raina zasu zo ba. Kallona suka yi kafin suka ce min. "Eh amma ke taya aka yi ana yin abun arziki ta kasa ke taya kika kare da gefen cikinki?" Shiru nayi ban ce musu kome ba, shigowar Zulaihah da Dr Umaima yasa ni kallonsu ina kakaro murmushi. Ganin su Ummi da Munaisah sai Dr ta kara yarda wani lokaci halittar kyau da hasken fata bala'i ne, domin kuwa Munaisah hancinta da huji, kunnenta kuwa har saman kunnen a makale suke da barima har da na gwal.

  Sannan ta kara kallonsu ganin yadda suke wani, iyayi yasa ta sha jinin jikinta waɗannan yan matan sun fini wayewa da gogewa a bariki, ni din kamar sabuwar yankar rake ce, shi yasa har nake gadon asibiti tow ko da ta koma gida ta ji kaninta yana bata labarin ai gida gida, Magaji Abba Chindo ya sa aka yi ta niman wata yarinya da ya dauko daga cikin gari. Kallona tayi tana mamakin anya ba ni ba ce? Duba min ciwon tayi tana faɗin. "Kin yi sallah kuwa?" Girgiza kai nayi. "me yasa kike wasa da sallah.". Kura mata idanu nayi kafin na bude baki ta daura da cewa. "Sallah tana kare mutum daga aikata alfasha, idan har kika kiyayye sallah, a duniyar nan babu wanda ya isa ya cutar da ke, sai dai abin da Allah ya rubuta xai same ki."

"Na gode zan kula, bana wasa da sallah amma daga faruwar wannan al'amarin nayi wasa da sallah har subhi da zuhur sun wuce ni"

  Murmushi tayi sannan ta juya tana kallon Zulaihah. "Idan kika hada mata tea, tayi sallah ko a zaune ne sai ta sha rabin kofi."

"Abinci fa, domin gashi an kawo." "Sai jibi saboda tumbin ta ya tabu, tasha tea din idan babu abinda ya faru, zata iya cin abincin."

"Shi kenan" ta faɗa tana hada tea din, sannan ta fita daga cikin ɗakin, haka Zulaihah ta rike ni har ban daki ta taimaka min nayi alola, sannan na dawo dakin na gabatar da subhi da zuhur, ina idarwa na amshi tea na sha, ciwon ciki ne ya sako ni gaba, kamar zan mutu kiranta Zuzu tayi suka shigo dakin. Wuce dani wurin scanning aka yi, aka min anan suka ga ɗinkin cikin bai yi da kyau ba, akwai buƙatar a sake min wani aikin yau. Alluran rage zafi tayi min, sannan suka wuce aka fara shirin, a lokacin Adda ta kira su Ummi tana faɗa akan me basu dawo ba, suka gaya mata ai aikin aka kuma shiga dani, babu shiri Addah ta nufo asibitin, domin abin ya bata tsoro kada garin niman duniyarta, na rasa rayuwata. Bata san amsar da zata bawa Shad'ari ba.


  Haka kuwa ta iso a gigice, tana tsaye har aka fito dani. A galabaice jikinta yayi matukar sanyi, ita tsoro take ji kada na mutu, haka suka bi ni har dakina, "Likita ya aikin?" "In sha Allah an dace, dama na farko munyi shi tare da bin raunin ne, amma na yanzu mun yi shi ne da bin duk inda yake ciwon."

"Hmm! Kuma nawa ake bukata? Domin akwai kudi a hannunsu." Kura mata idanu Umaima tayi kafin ta ce mata. "Allah sarki, ai Captain ya biya kome babu abinda ake bukata duk kudin da za a cire a insurance ɗinshi za a cira."

 "Kai madalla."

Murmushi Addah ta sake tana faɗin. "Don Allah ko zaki taya ni amsar kudin hannunsu, ki ce musu akwai wani abu da za a saya." "Hajiya anya kece kika haifi yaran nan?" "Kai haba daya Kyakyawar me dogon hanci da dogon gashi, ita ce na haifa. Ita kuma mara lafiyar da wancan me doguwar riga ruwan toka ubansu daya kanina ya haife su, ita kuma daya fara tas din can itama yar Kani nace, Zahrah ce ta dauki duhun fatar Uwarta ai kin gansu nan." Gaba Doctor Umaima tayi ta barta a nan tana surutu, haka kawai take jin Addah bata mata ba, Indai zaka kawo Yara ka daura su kan wani yanayi mara daɗi, meye ribarta? Itama Adda dakin da aka kwantar dani ta shigo, tana tsaye sai yamutsa fuska take tana faɗin. "Ita dai wannan shegiyar ta san hanyar b'adda kudi loko-loko, ban da iskanci da wulakancin taya zaki kare a gadon asibiti akan ciwon da bai taka kara ya karya ba, mtsew." Ta ja tsaki tana isa bakin gadon yarinyar nan yar bala'i, a ranta domin kuwa ta ga yadda ran kowa yake a b'ace idan ta cika mita kan yanayin da ake ciki.

   "Tow ai ku muje ko, tunda an yi aikin a sa'a" ta fada tana barin dakin, haka suka bi bayanta ban da Zulaihah da take zaune, ta saka ni a gaba tana kuka. "Ya Allah kai ka jarabce mu Ubangiji ka tashi kafadar Zahrah." Ta cigaba da kukanta, har aka yi sallar la'asar tayi sannan ta koma ta zauna. Shigowa Dr Umaima tayi tana faɗin. "Kuka ya isa haka, ki ci abinci."

"Ba zan iya ci ba, bayan Zahrah tana kwance."

Shiru suka yi, sannan Dr ta ce mata. "Matar nan Mamarki ce?" Rintse idanunta tayi tana jin kamar an watsa mata ruwan zafi a jikinta, don dai Allah ya ƙaddara zata zo a tsagin addah ne amma da ba zata tab'a yarda a ce Addah mahaifiyarta ce ba.

"Eh Mamata ce."

"Allah sarki naga kuna kama sosai."

"Eh haka mutane ke faɗa muna kama da Adda, shi yasa duk lokacin da wani ya ganni sai ya tambayeta ko ya tambaye ni."

Daga haka tayi shiru itama Dr Umaima bata zake sai ta san kome akanta ba, amma zucuyarta ta kwadaitu da son sanin wacece Ni?

 ★★

Tarkon makiya

  Bayan an yi sallar Isha, da ya jagorance su, yayi musu addu'a. Sannan ya mike tare da kallon sauran abokan shi da suke su bakwai ne, sauran kaso masu girman suna tare da Commodore Magaji Abba Chindo, murmushi yayi sannan ya dauko kayan aiki, yana kuma da kayan da zasu saka idan zasu faɗa cikin ruwa. "John ko zaka zauna anan ne naji kace matarka ta kusan haihuwa."

  Daukar kayanshi yayi yana sakawa, "Cab ai nayi Imani da Allah, amma gara na mutu a filin yaki da ace ina nan, ina jiran dawowarku." Ya fada yana saka rigar ruwanshi domin ana iska don har tana kad'a jirgin ruwansu. 

"Ammar kai ma ko zaka zauna ne, kace rabonka da Misau tun haihuwar Anam, saboda inda zamu mutanen suna dauke da miyagun makamai."

 "Hmm! Fatana kada Kasata ta mance da 'ya ta."

"Kana nufin zaka bi ni kenan!" Haka yayi ta rokonsu da su hakura da bin shi, amma ina baki daya suka nace, sai sun bishi anan ne suke ta hira da zasu tafi wurin karfe tara na dare, ya dauke su zuwa wurin Commodore. "Zamu tafi Sir! Dayawa sun daura hakkin kula da rayuwarsu akanka da kuma ni, Sir sun yarda da kai ne suka gwammaci su zauna da kai, Sir hakkin mu ne mu kare kasarmu da mutanen da suke karkashin kulawarmu. Please Sir gasu nan"

 Har ya gama maganar Magaji Abba Chindo,bai ce mishi cikanka ba domin kuwa baya fatan ya bude baki yayi magana, Babban burin shi Captain yana barin jirginsu yan tada kayar baya su yi musu daga-daga da namar su, shi yasa da ya ce ya tafi,ya fara bin sauran yana gaya musu ai fa Captain da suke ganin zasu bi, bai da lafiya da zaran an fara harbe-harbe cutarshi zata motsa. Muna cikin zamani ne da son kai yayi mana katutu, kowa son ranshi yake haka yasa baki daya suka janye bin bayan Captain.


  Kuma an gayawa Captain amma kuma bai ce kome ba, domin bai dauki haka a matsayin wani abu me muhimmanci ba. Yasan Commodore Magaji Abba Chindo yana jin haushinsa, amma kuma bai kawo a ranshi kiyayyar zata girmama haka ba, sai dai ya ce Allah ya kyauta.

Haka suka bar wurin da jirgin yake da wasu kananun jiragen ruwan, masu colour din navy blue. Haka suka shiga tafiya daidai an fara ruwan sama me karfin gaske.

 Haka suka yi ta tsala gudu, a nan Jirgin aikinsu, suna barin wurin aka shiga shagali da hidima, dama kafin dare sai da Commodore ya tura wasu matasan sojoji biyu suka kwasu musu yan mata, aka shiga shagali.

  Haka yasa yaki barin Captain zama domin, yasan matuƙar yana nan ba zai bari ayi shagalin ba, asalin sun manta da aiki suka zo yi, haka yasa suka yi ta shagali ga shi ana ta ruwa kamar da bakin kwarya.

 ---- A bangaren Captain da mutanen shi, ba karamin gudu suke ba, kasancewar takun yana jan jirginsu, karshe shi ya amshi tukin, ya kalli John ya ce mishi. "Da matukar hatsari fadawarku ruwan nan, a daidai wannan lokacin don haka tunda ana ruwa ku kashe fitilar goshinku, zamu isa har jikin jirgin."

"Ok Sir" shi ya fara kashe wutar nashi sauran mutane bakwan suka kashe nasu.


  A hankali suka yi ta tafiya, har suka isa wurin babban jirgin da yake dauke manya cantainers, zuwa kasashen waje. Tsayawa suka yi kusa da jirgin, sannan suka harba abin da zai rike su idan suka sauka daga cikin jirginsu. Hakance kuwa ta faru duk su bakwai suka shiga cikin ruwan bayan sun daure kugunsu da wata igiya, sannan suka fara hawa jikin jirgin har suka shiga saman jirgin.


   Babu kowa, Captain shi ya musu jagora, har cikin jirgin inda ya fahimci za a fara kwasar man saura wani lokaci kadan, don haka suka samu maboya suka boye, tare da samun bayanai akan kari. Sun kai wurin karfe sha biyu kafin aka fara aikin kawo danyen man fetur din, don haka sai da suka samu damar musu kawanya, kafin suka bude wuta a sama, dole yan daban suka yarda makamansu, domin abin ya basu mamaki, "dama sojojin da aka kaiwa hari daban ne da waɗannan sojojin?" Inji Shugaban yan daban. "Captain ka ji sun kai hari jirginmu.........

Waye zai mutu? Waye zai rayu follow my golden Pen.

#Thedambuje