BAƘIN HAURE..........

Chapter 5

by @maidambu41

*BAƘIN HAURE....🐾🐾*


  {Greed for Money is the roots of all evils🫀}

 Arewabooks:maidambu41

Wattpad:Mai_Dambu

Mallakar:Mai_Dambu

      *005*

"Captain mai zamu yi?" Shiru yayi yana kallon yan tadda daya bayan daya. "Sir me zamu yi?" A hankali ya saka hannunshi ya ballo tear gas, tare cilla musu, sannan suka ƙare fuskokin su, ai kuwa sai ga hayaki fuuuuu, haka yasa shi shiga cikin hayakin tare da kama su sannan suka daure su baki daya, kafin ya mike yana faɗin. "John zaka tsaya anan, kai dasu Ammar, duk wanda ya motsa ku sakar miishi wuta ko waye shi?" "Ok Sir!" Sai da ya karkasa su sannan ya sauko ruwa ya nufi inda jirginsu yaƙe na aiki. Sosai yayi shirin tunkarar asalin jirginsu da aka kaiwa hari.


   Koda ya isa ya samu babu kowa a cikin jirgin sai wasu mutane biyu, da suka jikata sosai. Durkusawa yayi a gabansu. "Me ya faru?" Cikin azaba da Harbin da aka mishi ya fara bashi labarin. "Muna cikin shagali bayan tafiyarku sai kawai muka kaji ƙaran harbi, ashe yan fashin tekun ne suka mana tarko." A hankali ya mike tsaye duk da ruwan da ake yi, dafe kanshi yayi ya koma cikin jirgin mutum daya ne a cikin matuƙan ya tsira shima yadda ya fada don ya shiga ban dakin kasa Allah ya kubutar dashi. "Yanzu ka juya da jirgin zuwa headquarter zan tawo da sauran mutanen." Ya fadi haka yana fita daga jirgin, a hannun dayan mutumin ya samu takarda. Amsa yayi yana dubawa,

*Mun ji labarin baka tab'a fita operation ka fadi ba, so wannan karon ka zo ka amshi yan uwanka sannan ka sakar min mutane na, ko na kashe Commodore.*

  "Zaku wuce headquarter zan tawo da wancan jirgin." Ya fita da sauri ya koma asalin jirgin yan fashin tekun, tsoron shi daya kada suma tarko aka musu. Koda ya isa ya same su, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya saka aka karkato kan jirgin, baki daya suka nufi headquarter ɗinsu,. Suna isa dama labarin ya isa an kaiwa jirginsu hari har an sace wasu sojojin. Yana isa da wadanda aka harba, asibiti aka wuce da su. Admiral da kanshi ya zo inda aka ajiye jirgin. A lokacin karfe biyu na dare, "Sir!" Ya sarawa Admiral. "Aiki yayi kyau, yanzu wani hali Magaji yake ciki tare da sauran abokan aikinku."

"Umarni nake jira mu sake sabon shiri." Captain ya faɗa yana sarawa. "Zan duba lamarin yau, amma tabbas dole a kai musu ɗauki." Mika mishi takardar da aka ajiye musu yayi. Shiru Admiral yayi yana kallon takardar. "zan tura yau kafin gobe zan nema maka _permission_ "

 "Ok Sir!" Ya sara mishi, sannan suka bar wurin aka wuce da mutanen da suka kamo, lokacin da ya shiga barrack din baki daya labarin ya karad'e cikin barrack din, waɗanda mazajensu suke hannun hankalinsu ya tashi, waɗanda mazajensu suke asibiti, a daren wasu suka yi ta wucewa, su kuma suna tafiya a mota. "Yallabai wannan abin da ya faru, da damu zai faru Allah ya tsare mu." Gyada kai yayi yana kallon hanya, kofar gidanshi aka sauke shi, kasancewar shi ne babba a cikinsu. Sai da ya fito ya ce musu. "Kada ku manta ku kula da kanku. Idan sun gama zamu tafi gobe ko jibi."

"Ok Sir!" Sannan ya ce musu. "Ku kula da iyalinku." Ya wuce ciki da sauri, yana shiga ya sauke ajiyar zuciya bayan ya shiga da sallama, a ka'idar wannan operation din ba a fita da waya, daga nesa ya hango wayarshi yana haske, a matuƙar gajiye ya isa wurin. *Brother* ya gani baro-baro a saman screen din wayar, a hankali yayi picking yana sakawa wayar a kunnen shi. "Baka yi barci ba?"

"Taya zan yi barci bayan wurinka na zo."

"Ka koma, ina da abinda zan yi nan da kwana biyar."

"Ai na gama nawa kawai, ka shirya." Brother ya gaya mishi. Dafe goshi yayi yana sosawa ya ce mishi. "Ka koma inda ka fito, don Allah." "Babu inda zan tafi." Yana fadar haka ya kashe wayar. Zama yayi jikinshi da matukar damuwa.


*Zahrah*

Muna kwance muka ji kar'ar motar daukar marasa lafiya. Kafin wani lokaci asibitin ya cika da hayaniyar mutane. Har kusan karfe hudu na asuba, can sai ga Dr Umaima ita da wasu Nurses su uku. "Baku yi barci ba?" Girgza kai nayi nace mata. "Eh Aunty, amma lafiya?" "Sojojin mu ne suka hadu da tsautsayi, Sisi kira mana Captain aikin nan ba zan yi ni daya, sannan ki haɗa da Mrs Kayode hutun ya ƙare." A hankali ta tawo kaina. "Nasan kuna da hankali, please ku kula da kanku sannan kada ku ce wani abu."

  Gyad'a kai nayi nace mata. "tow Aunty Umaimah." Fita suka yi, can kuwa muka kara jin hayaniyarsu ya karu, Zuzu kan duk abin da ake tana ta barci, sai da na gaji na tashi zaune ina yatsina fuska. 

Suna fita basu wani ɗauki wani lokaci ba, suka yi ta kiran wayar likitocinsu.

   Haka suka halarta kafin wani lokaci sun fara aiki, kafin karfe shida na safe, sun fito daga aikin. "Captain ko zaka kwanta ne?" Ta tambaye shi cikin kulawa, domin Allah ya jarabceta da kaunarshi, amma shi babu haka a ranshi. Gyada mata kai yayi, ko bude idanunshi baya iyawa balle yasan inda yake jefa kafarshi, haka ta juya itama ta bar sauran aikin a hannun Mrs Kayode ta tafi gida.

 Dama mun yi da Zuzu karfe shida zata wuce ko shida saura domin tun fitar Dr Umaima, itama ta farka ta leko mana abinda yake faruwa. Har tayo saurayi a cikin sojojin. Shi yace zai kai ta gida, muna idar da sallar asuba, ya zo suka tafi ni wani barci me karfi ya dauke ni. Ko don mun raba dare bamu yi barci ba ne. Haka nayi ta barci kamar me, yana shigowa ko don ya gaji ne, kawai yana shigowa ya kwanta. Tuni barci yayi gaba da shi, duk da yana son yin sallar asuba, amma ina barci me nauyi yayi gaba da shi.

 Wani ikon Allah dukkan mu biyu babu wanda ya fahimci halin da dayan mu yake ciki. Har wurin sha biyu lokacin Nurse tazo duba ni, anan ta same mu kwance ya tattara ni ya cusa cikin jikinshi ni kuma kamar mage na kwanta kwayam kamar mage, ko yanayin ba mamaki ko dumin da muka ji daga junanmu ya haifar mana da barci me nauyi, ganin haka ta juya tana me barin dakin, Dr Umaima ta kira ta gaya mata. Ai babu shiri sai gata a asibitin, tana isowa Zuzu tana isowa itama. Kallon juna suka yi, kafin Dr Umaima ta ɗan bata rai tana faɗin. "Ki jira ina zuwa."tana faɗin haka ta shigo, a hankali ta tashe shi, kaina yana kirjinshi, hannunshi dukkan biyu ya zagaye ni dasu. Sake tab'a shi tayi ya buɗe ido dakyar yana kallon ta. "Kafin ka dawo hankalinka ya kamata ka san inda kake." Kallonta yayi, sannan ya kalli inda nake kwance. Bai ga fuskata ba, amma baki daya yaji lissafinshi ya fara aiki kamar wanda ya aikata wani mugun aiki, ya ware manyan idanunshi ya kafeta da shi. "Su waye a waje?" Sanin ko ta fusata ba zai dame shi ba. Ta ce "babu sosai." A hankali ya zare jikinshi a nawa, kafin ya saka kafarshi cikin takalminshi, yana kallonta. "Baka duba ciwon ba, sau biyu aka yi aikin fa." Cikin kamewa da nuna kamar bai aikata kome ba, "Good!" Ya saka kai ya fita. "Karfe nawa?" Agogon hannunta ta kalla ta ce. "12:30" "innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un! Ban yi sallah asuba ba." "Sai dai sallah safe." Inji Dr Umaima. Da dan sauri ya bar ward din, dama dabi'arshi ce matukar yayi aikin dare tow ba makawa sai ya shiga daki daya yayi barci, a gidanshi baya iya barci kwana yake yana mafarki.

   Koda ya fita motarshi ya faɗa, da gudu yana shiga ya bata wuta, kan lokaci ya isa gidan, a kofar gidan ya taradda motar bmw, sai da ya tura motar gefen gidan,a kasar bishiyar lim, yayi parking da sauri ya fito tare da kallon inda motar take. Bai ga alamar da wani ba, haka ya wuce motar ba tare da ya kalli inda motar take ba, ya shiga kokarin buɗe kofar gidanshi, a hankali yaga kofar a buɗe yaƙe. "Emmanuel yazo aiki kenan?" Ya tambayi kanshi,cikin gidan ya shiga tare zubawa wanda yake zaune idanuwa. Dauke wuta yayi tabbas a duniya an rena shi. Wucewa yayi a gaggauce ya nufi dakinshi. "Na ga kayan jini, na san baka fara kisan kai ba, balle na ce ka fara amma na wanke Yaronka bai sani ba, domin ya same ni a kofar inajiranka."

  Bai ce mishi cikanka ba, ya wuce dakin yayi wanka da alola yazo ya gabatar da sallar asuba, sannan ya hada da zuhur. Shima bakon zuhur din yayi sannan ya wuce kitchen. Abinci ya dafa musu mai kyau sai kamshi yake, a hankali ya nufi falo da abincin, ya ajiye nashi sannan ya wuce da na Captain ɗin ya ajiye mishi a gabanshi. "Kaci nasan kana nan kana wasa da cikinka, ga aikinka aikin hatsari ne." "Me yasa baka jin magana?" Ya tambaye shi yana kallonshi. "Ni kuma? Ai idan akwai mara yafiya da rashin jin magana kai ne dai baka jin shi, kai a dadin ranka ne ka bar mahaifiyarmu tana kuka tana gayawa Allah yaushe zaka dawo gare ta? Ya Majeed duk abinda ya wuce ya wuce, a barshi ya wuce ban ga amfanin datse alaƙar da kayi ba."

"Aryan ka koma kace baka ganni ba."

"Zan koma amma ka sani na gama abin da ya kawo ni, gashi ka duba."

Ya ajiye mishi takardar izinin tafiya da Captain Majeed Mamman Ba'are, kuma Doctor a wani bangaren. 

"Akan me zaka min haka?" "Muna da Kyakyawar alaƙar kasuwanci da kamfanonin mu da mahukuntan Nigeria, don haka kai tsaye daga sama na liko da kai kasa, don haka sun baka hutun wata guda."

   "Kasan hatsarin da abokan aikina suke ciki?" Ya fada a fusace, "bai kai hatsarin da BA'ARE GOLDEN EMPIRES yake ciki ba, sai ka zab'a saura kwana uku zaben, su kuma abokanka, zai dauki sati kafin su fito domin sun bada zabin a sake musu kayansu ko su kashe su. Na gama hada maka kayanka." Ya fada yana ƙoƙarin barin dakin yana faɗin. "Akan shegen aikin da albashinsa bai wuce a sayawa karen gidan mu abinci ba, kazo zaka kare rayuwarka akanshi."

   Shiru yayi yana kallon abincin, tabbas abubuwa dayawa sun faru. Amma kuma ba zai tab'a yarda ya rike musu kome ba, zai dawo bakin aikinshi. Kamshin abincin yasa shi jin wani irin yunwa, da sauri ya fara ci, shigowar Aryan Ba'are yasa shi d'ago kai yana kallon shi, zama yayi a gaban Aryan Mamman Ba'are, murmushi suka yiwa juna, zama yayi ya juye abincin kan na Captain Majeed, suka fara ci hawaye na zuba daga idanun Aryan Mamman Ba'are, diban abincin yayi a cokali ya mikawa Majeed din, amsa yayi yana kallon shi, "kayi hakuri saura kwana huɗu ne ba uku ba, na fahimci yadda kake son aikinka." "Ba kome." Ya diba shima ya bawa Aryan Mamman Ba'are, amsa yayi yana ci, d'aga kai Captain yayi yana maida kwallarshi. "Kayi hakuri!" "Ai ba fushi nake ba, kawai dukiyar wancan mutumin ne bana son alaƙa da shi, don Allah ka."

"Ba dukiyar shi bane yanzu, dukiyarmu ce wanda naka da kaki amfani da shi yafi karfin tunanin kowa. Duk hannun jarinka sun fi na kowa yawa,.kaga yawan kudinka."

 A hankali ya bude baki zai magana Aryan Mamman Ba'are ya cusa mishi abincin a baki, dole ya ci. "Maganar aurenka ma Hajiya tana son lallai ka koma ayi maganar aurenka."

   "Ni bana son." Tura mishi abincin yaƙe yana murmushi, karfi da yaji Aryan ya hana shi magana, kuma yayi shiru ya ci abincin tass, sannan ya bude mishi ruwa ya sha, sannan ya mike yana kallon shi. "Me ya faru? Naga jini a zanin gado da sauransu."

"Ba kome fa."

"Nasan baka fara bin mata ba, amma wannan sarkar fa." Shiru yayi yana kallon Aryan. "Ban san me ya faru ba, kawai dai."

"Amma kuma." Girgza kai yayi, Aryan ya san halin ba zai tab'a magana ba.

 A hankali ya mike ya dauki wayarshi, ya kira Admiral. Sun jima suna magana, sannan ya koma cikin dakinshi can sai gashi dauke da kayan aiki. "Zan tafi kwana biyu in sha Allah zan yi."

"Nayi alkawarin maida mata kai gida, zan zauna har zuwa ranar."

  "Shi kenan!" Ya faɗa ya fita daga cikin gidan.

*Asibitin!*

 Wato yana tashi daga gadon, ina bude kanana idanuwa na da suke cike da barci. "tashi" inji Zuzu. "Ke wani irin dumi naji, shi yasa nayi ta barci." Murmushi tayi min sannan ta ce. "Zahrah kin san dumin da kika ji?" Girgiza kai nayi ina kallonta, dariya tayi min sannan ta ce min. "Dumin wani Kyakkyawan soja kika ji, ke dama ana samun Kyawawa ne a sojoji?" "Ke!" Na ware idanuna, ina shafa jikina. "Da fatan bai min kome ba?" Na fada ina zare idanu. "Namiji fa?" Gimtse fuska tayi tana hararata, "Sai hakuri domin ya b'arar miki da darajarki sai dai mu taru mu kwashe." "Ke Zulai!" Na san a duniya ta tsani na kirata da Zulai tun muna yara, don haka ina cewa zulai ta ce. "Zan ci mutuncinki banza babu abinda yayi miki."

"Allah ya huci zuciyarki." Daga haka na rufe bakina. Ban daki ta shiga ta haɗa min ruwan zafi,.na shiga na kama ruwa sannan na fito da alola.

 Abin sallah ta shimfida min nayi sallar, asuba da zuhur ina istigfari,domin nayi laifi me girma na wasa da sallah, koda na idar addu'a nayi sosai sannan na tashi zuwa bakin gadon. A hankali nake jin wani irin kamshi yana tashi me matukar dad'i da sanyi, ware ido nayi ina kallon Zuzu. "Zuzu kamshi me nake ji?" Kamshi kuma?" Gyad'a kai nayi ina kallonta. Itama ni take kallo, dube dube muka shiga yi, a hankali Zuzu ta d'aga pillow da yake gadon, wani ƙaramin hanky ne yake wannan azabebben kamshi.

"Mtsew ji abin da yake kamshi." Na ja tsaki, ina kokarin gyara zama, fari ne kal a hankali na warware. Gefen zanen wani babban gida ne kamar masarauta gashi nan kamar castle. An rubuta BGE. 

  "Mene ne ma'anar wanan kalamar?" Na tambayi Zuzu. "Adda mai tuwo tuwo!" Ta fada min hankalinta kwance. "Amma dai ke dai anyi yar banzar Y'a."

"Tow shi kenan sunanshi Fadimah Zahrah Buba Shad'ari." "Bana son b.... uba." "Na waye? Nawa ko naki ko najin dadin bakinki?" Abinci ta saka min kaɗan, duk da dama aikin ai ba wani aiki na tashin hankali ba ne, a hankali nake kurbar shayi, ina kallonta. "Zuzu!" "Na'am!" Ta amsa tana kallona. "Kinyi alƙawari ba zamu tab'a cutar da juna ba?" Na mika mata hannuna, "Me yasa kika bukaci haka?" Ta tambaye ni, murmushi nayi ina kai abinci bakina, a hankali na d'ago kai ina kallonta. "Ban sani ba, amma kuma nasan dai wata rana zamu iya cin amanar juna."

 Amsar kofin hannu na tayi da plate ɗin,ta ajiye, a duk lokacin da tayi haka nasan me take nufi. "kin san an min aiki." Na faɗa idanuna rau-rau. "Mtsew! Kin ci sa'ar ciwon jikinki da kin sha mamaki."


 Dariya nayi mata, sannan na cigaba da karyawa ta, har na gama ta balla min maganin da na gani ta Ciro a lock din gadon ta mika min. Da ruwan tea na sha ina son tmbayarta Addah amma nasan halinta bai zama dole ta bani amsa ba.

"Ya Addah take?"

"Lafiya lau!" Kallon fuskarta nayi naga kamar a dakile. "Wani abu ya faru ne?" "A'a." Ta fada tana leka wayarta, kawai na sha jinin jikina haka kawai Zuzu ba zata sauya ba. Sai na share kawai ban ce mata kome ba.

Tuna abin da ya faru a komawarta gida yasa baki daya, ranta ya kara b'aci da maganar Zahrh

 Lokacin da ta koma gida, ta samu Addah tayi bakon wani mutum, tunda ta gansu a dakin Addah tasan mutumin ba na alkhairi ba ne, duk da ba yau din ya fara zuwa ba, sai dai kuma zuwan shi na yau kamar niman shi aka yi, shi din d'an bori ne. Haka yayi ta tsalle yana ihu, kafin can ya fara gyatsa. Ya fashe da dariya, yana nuna Addah da hannu. "Tabbas baki da arziki a jikinta a yanzu, sai gaba zaki ci arzikinta sama da yadda kika zata. Ƙaddara ta hadata da shi, maza ki nisanta ta daga wannan duniyar zuwa wata duniyar, domin kuwa kika sake suka kuma haduwa ba zaki kara morarta ba har abada."

"Nazimu ya zanyi? Ita Zulaihah bata da gobe ne?" Ta faɗa a hankali. Gyatsa ya sake yana dariya. "Gobenta yana manne da yarinyar da take asibiti." A dame ta kalli Nazimu ta ce mishi. "sauran yan matan fa?" "Hmmmm! Itace inuwarsu."

"Babu yadda za ayi a mallake min ita?" Shafa gemunshi yayi ya ce mata."ba zan iya wannan aikin ba,lokaci na zuba da zaki amfana da rashin haka, idan aka mallaka miki ita ba zaki tab'a samun biyan bukata ba."

    "Nazimu kace na dauketa daga nan?" Gyad'a kai yayi yana gyatsa. "In sha Allah wani sati zamu wuce Taraba!"

"Dakyau. Ki nisantatta da nan domin zai bincikota."yana gama fadar haka ya fara kwara amai, nan Addah ta fito ta gaya musu zasu tafi Taraba, shiru kowa yayi a cikinsu. "Addah kinsan muna zuwa za a fara maganar munki aure fa."

"Ba zamu wuce kwanaki uku ba, tunda zamu bi motar dauko shanu ne,iya kwanakin da zamu yi uku ne, idan kuma kuna son zama anan shi kenan "

"A'a zan tafi naga Yakumbo na kwana biyu ban ganta ba."inji Ummi,

"Nima zan je na ga Nenne na!......

#Thedambuje