Mutum Mugu Ne

40

by @azizat

*MUTUM.....Mugu ne*

©AzizatHamza2019

                     40


An ci kuma an sha, duk yadda Zaytunah ta so a saka kiɗa ba hali saboda strict warning Sajid ya bawa organizers ɗin event ɗin akan banda kiɗa. Hoto kam an ɗauka kamar ba gobe.

Tunda Nadia ta ja ta suka fita ta samu waje ta rakuɓe tana tunanin yadda za ta cigaba da zaman gidan Uncle Sajid musamman da ya bayyana mata cewa Zaytunah ko ta halin ƙaƙa bata son zamanta a gidan, ko dai ta cewa Uncle Saj ta fasa zaman ne za ta koma Lagos.

  Muryan Yassar ya katseta da cewa "ashe nan kika ɓuya muna ta nemanki ayi hoto" Naziha ta ƙaƙaro murmushi tace " Yas I'm not in the mood for pictures today" 

" ai ba ki isa ba, ki zo kawai mu je ko na ɗaukeki da kaina" ganin zai takura ma ta ya sa ta tashi ta bishi

Hoto ake ta yi a wajen Azra na ganinta ta taho da gudu ta jata cikin hoton da ake shirin ɗauka yanzun wanda ya ƙunshi su Alhaji a ciki, suna haɗa ido da Zaytunah ta mata kallon 'bar nan wajen'. Duk wani motsinta yana kallo haka nan itama Nadia ke bin duk wani movement ɗin idonsa, zuciyarta ya cika da farinciki ganin hasashenta zai iya zama gaskiya, haka dai aka yi taro aka watse aka maida kowa gida, suna cikin dawowan farko dan haka tana shiga ɗakin Saratu ta faɗa kan gado tana maida numfashi, har yanzun mamakin faɗan da uncle Saj ya mata take yi dan har yanzu ba ta ga laifinta cikin abinda ya faru ba.

Zuwa yammacin ranan gidan ya ragu dan wasu sun wuce destination ɗinsu wasu kuma sai washe gari da safe za su tafi. Wanda za su tsaya har Monday su Alhaji ne da Nadia masu bin jirgi.

***

Cikin study ɗinsa ta shiga ta miƙa ma sa mug ɗauke da coffee da ta haɗa ma sa.

" Thank you auta" ya faɗi ya na ƙurɓan coffee ɗin.

"Ya Saj ni dai ka bani kwangilar haɗa lefe idan lokaci ya yi"

cikin rashin fahimta ya ce " I don't understand "

" kai yaya, kuma ni ɗin taka ma ɓoyemin za ka yi, to ni dai na gane komai kuma na yi booking tun yanzu ni zan haɗa maka lefe"

" kin fara shirmenki ko, who told you I'm getting married, ko lefen Nurain ki ke booking tun yanzu"

Ta ja kujera ta zauna suna kallon juna ta ce " joke apart Yaya, i'm very serious, ko dai har yanzu tsoron Zaytunah ne zai hana ka ƙarin aure" bai ce komai ba ya cigaba da kurɓan coffee kawai dan yasan ta da cracking silly jokes

" Yaya, Ziha is a perfect match for you, i'm glad you finally fall in love"

Maganar da ta yi ya sa shi ƙwarewa "this is ridiculus Nadia, ki bar irin wannan wasan ya isa haka"

Ta yi dariya sannan ta ce "Yaya, what do you think happened in the morning?, ka ganta jikin wani hankalinka ya tashi har da yi mata tsawa, ban san ka da tsawa ba Yaya, amma da safe kishi ya saka ka yin hakan. Just admit it Yaya, kana son Naziha, i can see it in your eyes"

Tsaki ya ja sannan ya ce ma ta ta ishe shi ta je ta kwanta. Ba ta musa ba ta fita daga ɗakin tana Murmushi. Tunda ta fita ya kasa taɓuka aikin komai, tambayar kansa ya ke, ta ya ma za ace zai so yarinya kamar Ziha wanda idan da ya yi aure da wuri ma da yana da 'ya ko ɗan da ya girmeta a shekaru.

Ganin gaba ɗaya ta rikita masa tunani sai ya miƙe ya tattare wajen kawai ya kashe wutan ɗakin ya fita. Bai samu Zaytunah a ɗakinsa ba ya san ƙila ta yi bacci dan tun da Isha da aka zauna ana ɗan taɓa hira ya lura sai hamma take akai-akai. . Bacci ne ya ƙaurace ma sa lokacin da ya gama shirin bacci ya kwanta, maganar Nadia ce dai ta kuma tsaya masa a rai. Yai ta juya maganar ƙarshe ya haƙura, ya jima kafin bacci ya sace shi.

***

Washegari Bayan an karya duk sauran masu tafiya a ranan suka wuce, gidan ya yi saƙayau. A wannan lokacin ne kuma ana zaune a falon Sajid Nadia ta shigo da maganar Ziha cikin hira tace "Ɗan tsoho wannan yarinya da ta taimaka wa Yaya Saj da jikokin ka ya kamata a mata ko 'yar ƙaramar kyauta ce, ai za ta ji daɗi" zuciyar Zaytunah ya tafaso tana son yin magana amma ba hali Alhaji sirikinta ne gashi tun rigimar da su ka yi ranar sunan Azra da Nadia ta ke shakkan Nadia, dan Nadia macece mai kaifin baki idan ta yanka ma ka wata maganar sai ka yi kuka tsabar takaici.

"Ayya! ita ce yarinyar da a ka yi hoto da ita ko, ƙawar Azra" Nadia ta amsa da eh

Nan ya ce Yassar ya kirawo ta, Yassar ya sauko ƙasa ya isa ƙofar ɗakin Ziha ya ƙwanƙwasa ya ji shiru sai ya yi ƙoƙarin buɗewa ya ji a rufe. Saratu da fitowarta kenan daga kitchen ta ce "'yan biyu" dan ba ta iya banbance su. "Naziha tana ɗakina barin kira ma ka ita" yana tsaye ya na danna waya ta fito.

"Ya a ka yi ne manya"

" mi yasa ba ki koma ɗakin ki ba tunda yanzu baƙi sun tafi?" Ta yi saurin cewa "Lah i like the new room, yanzu ina da abokiyar hira i'm not alone kamar da" ya girgiza kai ya ce "liar, Aunt Zayt ce ta kulle ɗakin ko?" Ba ta amsa ma sa ba ta sunkuyar da kai. Ya ce " anyways Alhaji na kiran ki" ta kalle shi da mamaki, ta san mutum ɗaya ake kira da Alhaji a gidan nan wato Mahaifin Sajid. " stop staring at me, ki zo mu je" da sauri ta ce barin sa hijab ya ɗaga kafaɗa alaman ko oho. Ƙaton hijab ta saka ta bi bayanshi. Yau ne ranar farko da ta haura sama tun zuwanta gidan, gaskiya falon Sajid ya fi na ƙasa haɗuwa duk da kuwa na ƙasan ya fishi girma. Da ƙyar ta ƙarasa wajen da su ke zaune saboda kunya. Godiya Alhaji ya ma ta daga nan ya ba ta kyautar gona. Ummi kuma ta ba ta kyautar ɗan kunnen gold. Rasa bakin godiya ma ta yi saboda abinda ba ta taɓa tsammani bane suka ma ta.

Tayi mamakin generosity na ahalin Sajid gaba ɗayansu.

Haka ranar ta kasance cike da farin ciki da walwala saboda ba a gida ma suka wuni ba Nadia ta fita da su yawo cikin gari. Sajid dama tun safe ba ya gidan sai dare ya dawo. Lokacin suma ba su jima da dawowa ba.

"Hajiya Zaytunah ko za ki iya ba da key ɗin ɗakin Naziha, na ga kamar ba kya son zamanta a ɗakin" Nadia ta yi maganar ba tareda ta kalli inda Zaytunan ke zaune ba. Wani dim zuciyarta yai dan kowa ya ji maganar da Nadian ta yi a falon. Suna haɗa ido da Sajid ya ma ta kallon mi ke faruwa? Ta ɗan gyara zama tace "Lah Nadia ni mantawa ma na yi tunda su Siddiqa su ka maida min key ɗin ban bata ba"

Nadia ta ce "to maza a ɗauko dan yarinya za ta kwana a ɗakinta yau, suna zama ɗaki ɗaya da mai aikinku ai sai a ɗauka babu ɗaki a gidan ne"

Zaytunah ta tashi cike da ɓacin rai ta wuce ɗaki ta je ta ɗauko key ɗin yayinda zuciyarta ke ayyana ma ta irin abinda za ta yi wa Naziha idan ta sauka ƙasa. Da ƙarfi ta buga ɗakin Saratu wanda tuni ta yi bacci Ziha ma har ta kwanta amma ba ta yi nisa da bacci ba, jin bugun ƙofa ba kakkautawa ya sa ta tashi da sauri ta zo ta buɗe " Anty la......." ba ta ƙarasa ba ta ji saukar mari a fiskarta, Zaytunah ta hankaɗata ta shigo ɗakin ta jawo kanta ta na ranƙwasanta haɗe da murɗe ɗaya da ga cikin kunnenta " dan ubanki har kina da hurumin da za ki haɗa ni da ƙanwar mijina saboda ke jaka ce, wallahi I will show you hell in this house"

Saratu da ba ta jima da farkawa ba saboda maganan Zaytunah ta shiga ba ta haƙuri. Zaytunah ta hankaɗa Ziha ta faɗi ƙasa ta tsifta ma ta yawu a jiki ta ce "banza, karuwa kawai, to sai kin bar gidan nan dan ubanki" tana faɗin haka ta cilla ma ta key ɗin ɗakin ta fice.

Duk yadda Saratu ta daure sai da itama ta zubda ƙwalla gashi ba wanda ya ji su saboda duk suna sama. Ta taimaka wa Ziha ta tashi ta haɗa ma ta ruwan zafi ta shiga ta yi wanka. Sai da ta sha kuka acikin banɗakin sannan ta samu ta yi wankan ta fito. Ta chanja kaya ta kwanta Saratu ta shiga ba ta haƙuri. "kar ki damu Baaba, komai mai wucewa ne"

Safiyar Monday an tashi busy yau Sajid zai fara aiki ga shi su Alhaji za su tafi dan haka tunda wuri Saratu ta fita kitchen dan fara aiki kafin Zaytunah ta sauko. Tana cikin gyara kitchen ɗin Nadia ta shigo, cikin fara'a da raha suka gaisa ta ce " yau ni zan yi abin kari tunda kin san daga yau kafin a sake haɗuwa haka sai an kwana biyu" Saratu ta amsa da hakane.

Lokacin da Ziha ta shigo kitchen ɗin Nadia ta so gane wani abu ya faru amma Ziha ta nuna ma ta ba komai. Su uku suka haɗa abin karin, ƙarfe bakwai da kwata sun kammala komai.

Su Alhaji ne suka fara wucewa saboda su jirgin ƙarfe goma na safe za su bi,  yayinda Nadia kuma sai ƙarfe sha ɗayan dare tukunna. Dan haka ranar wuni suka yi ana hira har da ƙarɓan numbar Ziha, da rana ma ita ta yi girki suka zuba na Sajid a warmers suka nufi asibiti su huɗu banda 'yan biyu dan su ma sun tafi na su wajen.

Ya ji daɗin kawo abincin da Nadia ta yi.

" yaya yaushe Naziha za ta fara aiki anan dan ka san su Azra sun kusa komawa school she'll be lonely at home"

" next week, she'll be working at the pharmacy section. Sannan still na enrolling ɗinta computer training za ta dinga zuwa ƙarfe biyu zuwa biyar"

" Oh that's nice, ba ri na wuce gida, na ga akwai aiki a gabanka"

"Thanks Auta"


Tunda Nadia ta tafi abubuwa suka lalace, matuƙar Zaytunah tana gidan to Ziha na ɗaki, in ka ga ta fita to Yassar ne ya ja ta suka fita. Kasancewa Sajid ma idan ya fita sai dare ya ke dawowa shi ya sa bai ankara da abinda ke faruwa ba.

***

"I'm serious Sady, wallahi ni da gidana amma yanzu in dai na shiga na ga wannan baƙar yarinyar sai hankalina ya tashi"

Sady ta yi murmushi ta ce " babe ga shi kin hana in zo gidanki ai da na ga ya yarinyar ta ke"

" babe kin san my one har yanzu bai dawo dai-dai ba idan ya ganki a gidansa he'll be very furious"

Sady ta ɓata rai tace " amma ai ba lokacin da yake nan zan zo ba sai ya tafi asibiti or better still idan ya tafi Lagos"

"Oh no! ba za ki gane bane kawai, ki bari idan na fitar da tsinanniyar yarinyar nan daga gidana zan saita my one, then you can come visit me"

"shikenan Zaytunah, amma ban ji daɗi ba"

"haba tawan in dai yarinyar nan kike son gani za ki ganta"

......safiyar Sunday Uncle Saj ya bawa Ziha sabuwar laptop tareda gaya ma ta driver zai zo ya ɗauketa daga asibiti ƙarfe ɗaya saboda ƙarfe biyu ne za'a dinga training ɗin. Bayan ta ma sa godiya ya ce " Ziha you'll work at the pharmacy, aikin da za ki yi a wajen ba mai wahala bane, kuma na amince ki yi aikin ne saboda ki samu experience na aiki, and ba na son ki shiga harkan mutane, just do your job and go"  ta amsa da cewa " nagode Uncle Insha Allah zan bi duk dokokin da ka tsara min"

" very good then"

Duk wannan abinda ake yi Zaytunah na kwance a ɗaki tana bacci saboda sunday ne Sajid ba zai fita aiki ba, shi yasa tunda ta yi sallar Asuba ta koma bacci.

Daga baya Sajid ke gaya ma ta tsarin da ya yiwa Ziha as usual sai da ta yi 'yan guna-guni. Hakan bai dame shi ba saboda ya saba da halinta.

***


.......BAUCHI.....

Sakamakon gwajin da aka ma ta ta miƙa masa a tunaninta wannan labari zai sa shi farinciki sai dai ga mamakinta yana gama karanta takardar ya ce "Alhamdulillah, Allah ya saukeki lafiya"

"Yaya sai yaushe za ka kwantar da hankalinka da abinda ya faru, Aarif yana buƙatanka, ni ma haka, you have to stop worrying too much about Nazira, all you can do for her is prayers" ta tashi ta shige ɗakinta saboda ta ji haushin abin ya yi, ta ɗauka labarin cikinta zai sa shi farinciki ko da na yau ne kaɗai, amma sai bai nuna excitement ɗinshi akai ba.

Ya jima a zaune a falon yana tunani kafin shima ya shiga ɗaki, ganin bai ganta a nasa ɗakin ba sai ya leƙa ɗakinta. Ya sameta ta kwanta kan gado ta lulluɓe duk jikinta, ya zauna gefen gadon ya ce "Fatima, ki yi haƙuri dan Allah"

Ta buɗe fiskarta ta kalleshi ta ce cikin muryan kuka " Allah babu adalci cikin wannan lamarin, ni da Arif duk muna da haƙƙi akanka, dan Nazira ta zaɓi ta bijire maka ba shi zai sa ka share mu ba, nuna mana kake kaman we did not exist at all" ta ƙarasa maganar tana goge hawaye.

"Ki yi haƙuri da ni ki tayani da addu'a Fatima, ina cikin ƙunci"

Ta taso ta rungumeshi tana ɗan shafa bayansa a hankali dama kullum aikinta ne lallashinsa tunda Nazira ta tafi.

........

"Inna kinga ni ba ruwana idan aka shigo aka mi ki koran walaƙanci dan na riga na sayar da gidan nan, yanzu da ki ka ganni na zo ɗiban duk wasu kayana masu amfani ne, sauran zan zub dasu wa Almajirai"

Laure ta cigaba da magiya tana roƙon 'yarta ka ce ita Shamsiyyar ce ta haifi Lauren.

"ki ji tausayina Shamsiyya, idan ba za ki bar ni anan ba, ki tafi da ni zan biki Abujan"

Shamsiyya ta yi tsaki "Allah ya kiyaye, ni dai kin ga tafiyata" ta cilla mata dubu goma ta ja akwatinta ta kai waje inda mai mota ke jiranta, ta dawo ta rufe ƙofar gidan ta wuce ta bar Laure da ihu.

Tunda Shamsiyya ta tafi Laure ta yi zaman dirshan a ƙofar gidan tana tunanin abin yi, ƙarshe ta yanke hukuncin zuwa wajen Boka ta nemi magani ko Sulaiman zai yafe mata ya maida ta ɗakinta dan nan ne rufin asirinta yanzu.

To idan ta ce wajen Boka zata, bata san ina za ta samu wanda zai mata aiki mai kyau ba. Ƙarshe ta yanke shawaran neman wani Boka da suka taɓa zuwa da Inna Hansai lokacin tana da rai, ta yafa ɗan gyalenta mai kama da tsummokara ta ɗauki kuɗin da Shamsiyya ta ba ta ta yi gaba.

Wajen ƙauyene tukuf, ba tayi tunanin zata iya gane wajen ba sai ga shi ta iso, da kwatance aka nuna mata gidan. Da ta isa gidan sai ta samu wasu mata su biyu na fitowa daga gidan ta ƙarasa wajensu tana f " sannunku, kun samu ganin Malam kuwa? Na ga kaman ranku a ɓace ya ke"

Ɗaya daga ciki ta yi tsaki ta ce " wai ashe ya mutu tun wata biyu da suka wuce "

Laure ta dafe ƙirjinta ta ce " na shiga uku, yanzu ina zan samu wanda zai min aiki da gaggawa haka"

Ɗayar ta ce " ai bashi kaɗai bane ya iya aiki, idan akwai mai zuwa Gombe akwai wanda aka taɓa min kwatance acan wai ya iya aiki"

Laure ta langwaɓe kai ta ce " bani da kuɗin mota ne da na je"

"Kar ki damu da mota na zo" in ji matar farko.

Dukkansu suka ɗunguma zuwa wajen motar Hajiya Ladi, ta ja su sai Gombe. Wani ƙauye can ta wajen Tula suka nufa, basu isa ƙauyen ba sai wajen ƙarfe bakwai na dare. Aka musu kwatance suka shiga cikin dajin da ƙafa saboda mota ba ta shiga, su uku suna tafiya kowa da abinda ke tafe da ita. Sun yi tafiya kusan minti ishirin kafin suka isa gidan Boka Tuyaaya, daga nesa suka hango hayaƙi ya turnuƙe ilahirin gidan amma zuciyarsu wasai suka ƙarasa bukkar. Hajiya Ladi ce ta fara kutsa kai cikin gidan ta ci karo da wata mata zaune akan tabarma ta zuba tagumi, da gani kuɗi sun zauna mata dan kayan jikinta kaɗai ya isa ya tabbatar maka da hakan.

Ta gaisheta sai a sannan ta ɗago ta kalleta. "Dan Allah Boka Tuyaaya muke tambaya" inji Hajiya Ladi su Laure suma sun ƙarasa shigowa lokacin. Matar ta ɗan yatsina fiska tace " tun ɗazu ya shiga ɗakin tsafi yana min aiki har yanzu bai fito ba, ku zauna ku jira shi" suka samu ɗan nesa da ita suka zauna suna jiran tsammani.

Kusan minti goma da zamansu suka ji ihu daga ta ciki, gaba ɗaya suka tashi tsaye lokaci guda suna kallon juna, jin ihun ya yi yawa sai Laure ta ce "kai Jama'a anya lafiya"

Bilkisu da suka zo tare wanda duk cikinsu ita ce mai ƙaranci shekaru ta ce " ko dai zamu shiga mu duba ne, dan ihun wahala ne wannan" matar da suka samu a wajen ta ce ba zasu shiga ba, ai Boka ya bata umarnin ta jirashi anan ne.

Kafin su ƙara wani maganar Boka ya fito agigice yana sunbatu duk jikinsa tabo sai sose-sose yake. Lokacin da aka sake shaɗa Boka sai ya sake ƙwalla ihu wayyo. Jin ƙaran saukar bulala kuma basu ga bulalar da mai dukan ba

yasa dukkansu suka fice daga gidan a gigice ko takalmi ba su tsaya ɗauka ba. Cikin gudu suma suka fara jin saukar bulala ajikinsu ta ko'ina, nan suka shiga ihu suna bada haƙuri, ba su fasa gudun ba dan tunaninsu gudun shine mafita. Abu da duhu suka ranta cikin jeji ba tareda ko kallon gabansu ba.

Da safe mutane suka tsinci gawar Hajiya Ladi a bakin titi jikinta duk tabon duka, Bilkisu kuwa suma ta yi amma ba ta mutu ba, aka shiga jejin duba sauran saboda bayan farfaɗowan Bilkisun ta sanar dasu abinda ya faru. Gawar Madam Binta suka tsinta itama a yashe bayan mummunan raunika da taji, gidan Boka kuma ya ƙone ƙurmus ganin basu ga gawansa ba suka tabbatar dashi gidan ya ƙone. Ba a samu gawar Laure ba sai washe gari har ta fara wari aka damƙawa jami'an tsaro sai dai ganin yadda gawar ta lalace yasa kawai suka ce a bunneta bayan an ɗauki hoton gawan. Yaɗa hoton gawan Hajiya Ladi, Madam Binta da Laure ya sa 'yanuwansu suka san miya faru. Cikinsu Laure ce kaɗai ba wanda ya nemi ƙarin bayani akanta har yanzu.

***

Bayan sati ɗaya.....

Anty Zahra na chatting a whatsapp sai ga shi a wani group an turo hotunan gawan su Laure tareda bayanin abinda ya faru. Da farko ta gane gawan Laure sai dai bata san inda ta wayi matar ba. Ta jima tana tunanin inda ta san fiskar, amma ba ta tuno ba har Abba ya shigo ya sameta a haka. Bayan ta ƙarɓi jakarsa ta kawo mishi ruwa ya sha ta ke nuna masa hotunan da aka turo ta ƙara da cewa " ni kan dear kamar na san ɗaya daga cikin matan nan, amma na rasa a ina" ta nuna hoton gawar Laure.

"Haƙiƙa Allah ba azzalumin bayinsa ba ne, ga shi tun daga duniya Allah ya nuna mata sakayya" inji Abba da ya gane fuskar Laure sarai

"Yaya ka santa ne?"

" Lauratu ce, yayar Umminsu Nazira"

Anty Zahra ta riƙe baki tana maimaita Hasbunallahu wa ni'imal wakeel

.......