41
by @azizat
*MUTUM.....Mugu ne*
41
..........ABUJA........
"My one gatan da ka ke nuna wa yarinyar nan yayi yawa fah, gani za ta dinga yi kamar a sama muke samun kuɗin ba aikinshi ake yi ba. Wannan asibitin ya ci ma ka kuɗi dayawa ga shi this year stock market ya crash and things are not stable since then. Imagine ka sai ma ta waya irin tawa ga expensive laptop, paid for her computer training, feeding her, you even gave her a job, haba My one ko 'yar da haifa albarka" Zaytunah ta faɗa yayinda take taya shi saka kaya. Ko uffan bai ce ba ya wuce gaban mirror ya ɗau comb ya fara taje gashin kansa.
Ta ɗau turare ta fara fesa ma sa still ta cigaba da ƙorafinta " ni ba abinda ya fi ɗaga min hankali kamar yadda mutane za su dinga ganinta da daraja kamar ita ma wata ce bayan ba ta inda mu ka haɗa dangi"
Hannunta ya riƙe ya kalli cikin idonta ya ce " Wow! I'm impress Zaytunah, har kin san na kashe kuɗi wajen ginin asibitin nan, and stock market ya crash which of course i lost millions. But then abu ɗaya na ke buƙata a wajen ki ba damuwa da kashe-kashen kuɗin da na ke yi ba. Zaman lafiya da kwanciyar hankali shi nake buƙata, idan ki ka ban wannan ya fi min komai. Naziha is like Azra to me, so ko ma mi na mata ba damuwarki bane, infact i'm sponsoring her education daga farko har ƙarshe, bayan nan kuma idan ta tashi aure ni zan mata duk abinda uba ke wa 'yarsa a lokacin aure"
"Allah ya kiyaye" ta faɗi tana haɗa rai can cikin zuciyarta kuma tana faɗin "kafin watan nan ya ƙare ma za ta bar min gida balle har ka samu daman sponsoring karatunta"
Ya kissing goshinta ya ce " sai na dawo, take the kids to school on time kin san za su yi rigimar ni zan kaisu tunda yau za su koma"
Bai jira mai zata ce ba dan yanayin fiskarta kaɗai ya nuna masa ranta ya ɓaci ya fice da ga ɗakin. Ɗauke da briefcase ɗinsa ya sauko ƙasa dama ya riga ya karya.
Ganin Saratu na shirya breakfast ɗin yara a dining ya ce "Ziha ta shirya ne?" " yanzu ta shiga ɗaki za ta shirya sai dai ba ta karya ba" ya ce "ki haɗa mata abincin ta tafi dashi, ta sameni a waje"
Tunda Saratu ta shigo ta ce mata uncle Sajid na jiranta a waje ta fara shiryawa da sauri sauri. Dama tun da asuba Zaytunah ta shiga kitchen ta shirya wa Sajid breakfast ɗinsa shi kaɗai dama idan ta yi hakan Saratu ce za ta yiwa yara breakfast. Shi yasa ma da Zihar ta fito ta ga Saratu na aiki a kitchen ta tsaya ta tayata.
Wani Abaya ta saka fari ƙal mai adon wasu ƙananun stones kalar golden ta wajen wuya da hannu. Ta rolling gyalen da yake golden shima, ta saka flat shoe baƙi sannan ta riƙe baƙar purse ta fito ta karɓi ƙaramin basket a hannun Saratu ta fita da sauri. Tun daga nesa ta lura da kallon da yake mata wannan ya sa ta rage sauri ta sunkuyar da kai, yana jingine jikin mota cikin baƙin Dolce and Gabbana suit. "Good morning Uncle"
"kin daina saka hijabi ne yanzu?" Ya faɗi ba tareda ya amsa gaisuwarta ba.
Ta ɗan ɗago ta kalleshi suka haɗa ido ta yi saurin sauke idonta, har ga Allah tun a da ma ta fi saka gyale musamman idan ta saka gown tun tana Kano ma haka take.
Rasa mi za ta ce masa ta yi kawai ta juya da nufin ta je ta sako hijabin ta ji yace "zo ki shiga mota".
'Ya Ilahi, ba dai Uncle yayi fishi ba' ta dawo ta shiga motar, sai da ta shiga sannan shima ya shiga motan driver ya ja motan suka fice daga gidan. Tana ɗan murza yatsunta a hankali yayin da ƙanshin turarenshi mai sanyi ke shiga jikinta a hankali. Kamar ba zata ce komai ba sai kuma ta daure tace "Uncle I'm sorry, tunda na zo nake ɓata ma ka rai, I'm very sorry"
Ajiye wayarsa ya yi ya juyo ya kalleta ya ce " Ziha ke amanata ce, all I'm doing is for your best interest, ba wai ina son takura mi ki bane"
Har suka isa asibitin ba wanda ya sake magana.
Haɗata yayi da wani staff ɗinsa ya wuce nashi office ɗin saboda surgery da za su fara ƙarfe bakwai da rabi na safe, kuma bakwai ta riga ta yi.
Ta ji daɗin fara aiki da pharmacist ɗin mai suna Amber Steven, budurwace amma za ta kai 34yrs haka.
Bayan sun fito daga surgery ɗin, yana zaune a office kiran abokinshi Alhaji Isa ya shigo "mutumina ka turo min adress ɗin asibitinka, yanzu haka ina Cikin Abuja"
"Ok" kawai ya ce ya katse kiran. Kusan 45mins sai ga Alhaji Isa ya shigo office ɗinsa. Yana ganin sa ya tashi da sauri ya miƙa masa hannu suka yi musabaha dukkansu suna murmushi. Bayan an gaisa Sajid ya masa jagora dan ya ga asibitin nashi.
Alhaji Isa ya masa addu'ar samun Alkhairi.
Alhaji Isa abokin Sajid ne sosai, lokacin da ya ke intern ɗinsa a John Hopkins hospital suka haɗu ya kawo mahaifiyarsa za a mata aiki, ganin su 'yan Nigeria ne yasa suka saba sosai har aka sallame su basu bar zumunci ba, duk sanda Sajid ya je Nigeria sai ya je Kano wajensa haka shima idan harkokinsa suka shigo dashi ƙasar America sai ya nemi Sajid ɗin, har zuwa lokacin da Sajid ɗin ya dawo Nigeria gaba ɗaya, ya zo bikin buɗe gidan Sajid ɗin, amma bai samu ya zo buɗe asibitin ba saboda ba ya ƙasar a lokacin amma yana shigowa Nigeria washegari ya shigo Abuja ganin asibiti.
Suna zama ya miƙa masa wata envelop wanda da ka gani kasan na Invitation ne. Sajid ya buɗe envelop ɗin ya fito da Invitation card ɗin da ke ciki yana karantawa, ganin sunan Alhaji Isa da Asma'u ya sa shi kallon Alhaji Isa da sauri ya ce "ba dai ƙara aure za ka yi ba?"
Dariya Alhaji Isa yai sannan yace "Abokina ai na gaya maka sai na cika huɗun nan, toh gashi nan ka gani"
Sajid ya girgiza kai ya ce "Alhaji yaushe ka aurar da 'yarka da har za ka ƙara aure?, matarka ta uku ma ai bai kai shekara uku da ka aureta ba ko?"
" Sajid kenan, ni fa ba Pastor ba ne kamar ka mai auren zobe, ni raya sunna zan yi na cika mata huɗu cas"
Sajid yai ƙaramar ajiyar zuciya yace. "well, ra'ayinka kenan. Amma bazawara ce itama ko?"
Alhaji Isa yai ƙaramar dariya ya ce " ai abinda yasa na auri bazawara wancan karan saboda taimaka wa yaran ɗanuwana ne kar suyi nisa da mu. Wacce zan aura yanzu budurwa ce. Infact yarinya ce ƙarama, bana ta cika shekara shatara"
Sajid ya zaro ido yana faɗin " haba Alhaji! at your age kana auren yarinya irin haka, 'yarka ta fari fa ta girmeta sosai, gaskiya ba girmanka bane at 51yrs Alhaji, da dai ka nemi wacce ta girma"
" toh anzo wajen Angon Zaytunah, ka ga Sajid ɗan shekara ashirin da biyar nake ganin kaina tunda na fara neman yarinyar nan, so bar maganan shekaru"
Ran Sajid a ɓace yace "ka bani mamaki, Alhaji ko za ka auri budurwa ka auri matured girl mana ba yarinya ƙarama da yaranka uku ma duk sun girmeta ba..." bai ƙarasa maganar ba wayar Alhajin ta fara ringing , " yawwa Alhamdulillah ba ri ka ji soyayyar yarinya" ya faɗi gameda ɗaukan kiran ya sa a handsfree
" Baby nah ya hanya, fatan ka isa lafiya?" Alhaji ya karairaya murya yana kashe wa Sajid ido ya ce " princess na iso lafiya, wallahi har na fara missing ɗinki"
" ni ma na yi missing ɗinka sosai baby, dan Allah ka dawo da wuri banda tafiyar dare"
" kar ki damu my princess zan dawo da wuri, zan kira ki anjima muna tare da Sajid yanzu"
" Lah baby dama a wajensa ka ke, ka bawa Uncle Sajid ɗin mu gaisa"
Alhaji ya miƙawa Sajid waya. Sajid wanda tunda suka fara wayar yake mamakin wannan al'amari, 'yar shekara shatara za ta auri ɗan shekara hamsin da ɗaya. Ko da ya ke yaran yanzu sun ɓaci da son kuɗi, yanzu haka dan kuɗin Alhaji Isa ta amince da auren.
Da ƙyar ya ƙarɓi wayar suka gaisa sannan ya miƙa masa.
"Yanzu dai ka gamsu da cewa ba auren dole za a ma ta ba ko?"
Sajid ya girgiza kai kawai ya cigaba da kallon katin, can ya ɗago ya kalli Alhaji Isa ya ce "zanje Lagos ranar Alhamis, I don't think I will be able to make it to the wedding"
"Wallahi baka isa ba, duk yadda za ka squeezing schedule ɗinka ka yi, amma ba zan ɗaga maka ƙafa ba"
" well I will try" but ban yi alkawari ba"
Dariya Alhaji Isa yayi yace "ko kai fa, ni fa fatana gareka kafin shekaran nan ya ƙare ka ƙara mata kaman biyu haka, ka ga kaima ka fita sahun masu auren zobe, kai ko ɗaya ma"
" Ba ni da wannan ra'ayin Alhaji"
Alhaji Isa dai dariya kawai yayi......
Ƙarfe shida Ziha ta iso cikin gidan gaba ɗaya, a gajiye take ga cikinta da ke ciwo, ta ajiye purse ɗinta ta kwanta kan gado tana tunanin yadda lokaci guda rayuwarta ya chanja, mutanen da ta haɗu dasu wajen training ganin irin kayan jikinta, wayanta da kuma motar da aka kawota ciki yasa suke ma ta kallon babbar yarinya, Lizzy har tambayarta ta yi wai ita 'yar gidan waye? Ita dai murmushi kawai ta yi ta share tambayar.
Tana wanka ta jiyo muryan Azra tana ƙwala sunanta tana faɗin "Nazzy my Mom is calling you"
Innalillahi ta fara maimaitawa a zuciyarta tareda saurin ƙarasa wankan ta fito, a gurguje ta saka doguwar rigan bacci pink ta fito, a falo ta sameta tana zaune ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya. Nesa da ita Ziha ta tsugunna tace "Anty ga ni"
Harara ta watsa mata kafin ta fara faɗa " saboda samun wuri da kika yi My one zai tafi wajen aiki kema ki saka ɗuwaiwanki a mota ku tafi tare kaman tsarinki ne shi, to wallahi ahir ɗinki ki sake zama cikin motar da mijina ya zauna, idan hakan ta faru ki kuka da kanki, kuma ba ki da matsayin da za a dinga zuba miki abinci kina tafiya da shi, matuƙar ba za ki iya karyawa a gida ba ya wuce ki kenan sannan..." sai kuma ta yi shiru jin tsayuwar mota a cikin compound ɗin ta san tabbas Sajid ne.
" tashi ki ban waje, mayya kawai" ta faɗi tana jan tsaki. Ziha ta tashi da sauri ta shige ɗakinta fitowar da ba ta sake yi ba kenan.
Ƙarfe sha ɗaya na dare ciwon cikinta ya yi tsanani gashi ba magani a ɗakinta ta duba ko ina babu ganin abin na shirin fin ƙarfinta sai ta fito daga ɗaki tana daddafa gini ta shiga ƙwanƙwasa ɗakinsu Yassar. Yassar ya yi bacci, Yamin kuma yana kallo a laptop, jin ƙwanƙwasa ƙofar da ake yi yayi yawa yasa shi tashi da sauri ya zo ya buɗe ya kalli Ziha tsaye murya na rawa tace "please Yassar ka taimaka min da pain reliever idan kuna da shi" kafin ya ba ta amsa ta ɗan yi nishi tareda ƙara matsa pillow da ta riƙe a cikin ta
" what is wrong with you Naziha, should I call Uncle?" Ta girgiza kai tana faɗin "just help me with paracetamol, please" ya juya ya shiga dubawa bai samu ba dan haka ya ɗau waya ya kira Sajid. Sajid na zaune a study room yana yin aiki a computer kiran Yamin ya shigo, ganin Yamin ne ya ɗauki kiran da sauri yana faɗin " Yamin lafiya?"
" Uncle Saj please ka sauko, Naziha is sick" ya ajiye wayar
Da sauri Sajid ya fito daga ɗakin, stairs ɗinma biyu biyu yake takawa.
A bakin ƙofar ɗakinsu Yamin ya ganta ta tsugunna sai murƙususu ta ke yi shi kuma Yamin ya tsugunna gefenta yana mata sannu.
Yana isowa Yamin ya miƙe ya ce "yawwa Uncle wai vikinta ke ciwo" bai ce komai ba yasa hannu ya ɗauketa ya nufi ɗakinta Yamin ya bi bayan shi, ya shimfiɗata kan gado har lokacin tana riƙe da pillow. Ya kalleta ya ce " Is it your period?" Ta gyaɗa ma sa kai
Ruwan zafi yace Yamin ya kawo masa da ƙaramin towel, kafin ya dawo ya ɗauke pillow da ta riƙe ya sa hannunsa yana ɗan danna ma ta cikinta zuwa wajen maranta. " akwai maganin da ki ke sha ne?" Ya tambayeta
"Yes, amma ya ƙare"
Yadda maranta ya riƙe lokaci guda ta tashi ta kwantar da kanta kan cinyar Sajid tana juyi. Ya ɗan riƙeta da kyau yana mata sannu. Yamin ya kawo ruwan zafi da ƙaramin towel Sajid ya ce mi shi ya haura sama ya ɗauko first aid kit a falonsa ya fita da sauri.
Gyara mata kwanciya yayi ya sa hannu a hankali ya fara ɗaga rigar sama, ta yi saurin riƙe hannunsa duk da yanayin da ta ke ciki amma ta san matsa mata ciki zai yi kuma kunyar sa ta ke ji saboda wutan ɗakin a kunne ya ke gashi doguwar riga ne kaɗai ba wando ta ciki.
Ya janye hannun ta ya cigaba da ɗaga rigan har ya kai dai dai ƙirjinta. Ta rufe idonta dan ba za ta iya haɗa ido da shi ba. Ya ɗau towel ɗin ya saka cikin ruwan zafi Ya fitar dashi ya matse ya fara danna mata ciki da shi. A haka Yamin ya kawo mishi kit ɗin ya ƙarɓa ya ce ya je ya haɗa ma ta tea marar sugar ya kuma kawo mata ruwan da za ta sha magani. Ya cigaba da danna ma ta ciki zuwa wajen maranta.
Yamin ya kawo tea mai kauri da ruwa Sajid ya ƙarɓa ya ce ta tashi ta sha tea ɗin amma kunya ya hanata ko motsawa.
"Uncle is there something else i can do for you?" Sai lokacin ya tuna Yamin yana tsaye kansu gashi Ziha is almost half naked, yayi saurin jan bargo ya rufe ma ta cinyoyinta ya ce " it's late Yamin, go and sleep"
Yamin ya ɗan yi murmushin gefen baki sannan ya fita bayan ya yiwa Ziha Allah ya ƙara sauƙi.
Duk yadda ta ke jin kunyarsa haka ta daure ta ƙarɓi tea ɗin ta sha rabin mug tana ajiyewa ya ce sai ta shanye tas. Haka ta shanye sannan ya ba ta diclofenac ta sha. Ya ci gaba da danna ma ta ciki har ruwan yai sanyi. Zuwa lokacin kuma ta ɗan ji relief. Kusan ƙarfe sha biyu da rabi bacci ya ɗauketa bayan ta gama juye juye da murƙususu a jikin Sajid.
Bayan ya gyara mata kwanciya ya tattare wajen ya jima tsaye a kanta yana ganin yadda ta ke bacci so peacefully, ya ɗan sunkuyo dai dai fiskarta ya tofa mata addu'a sannan ya kissing goshinta ya ce "good night" ya kashe mata wutan ɗakin ya fita.
Haka kawai ya ke hawan stairs ɗin yana murmushi. Zaytunah ta jima da bacci dan haka shima shirin baccin yayi ya kwanta.
Washegari.....
Har ga Allah yayi mamakin baccinsa na jiya, mafarkin Ziha ya yi har ba ya ma son tuno abin da ya faru cikin mafarkin saboda abin kunya yayi a mafarkin.
Dawowarshi daga Sallar asuba Zaytunah ta tare shi da buƙatar ta, yayi ƙoƙarin kauce mata amma ya kasa Saboda shima ɗin mafarkin Ziha da ya yi ya tada masa sha'awa.
Zuciya dai idan ta yi niyyan sarrafa kanta ba yadda mutum ya iya. A zahiri tareda Zaytunah yake amma zuciyarsa Ziha ta ke bayyana masa duk yadda ya ke ƙoƙarin ture hotonta da zuciyarsa ke hasko masa ya kasa...
" My one, I believe kai ma ka yi missing ɗina sosai, why don't we go for vacation ko da na sati ɗaya ne, ba sai mun fita waje ba, we can go to Lagos or Portharcort just the two of us ko ya"?
Ya cigaba da gyara tie ɗinsa yana faɗin "Ba ni da time Zaytunah ban jima da buɗe asibiti ba ga kuma kamfanin su Yamin"
" i know, but you've been busy this days we only make love every two days, sai dai idan ni na takura and it's not fair"
" zan je Lagos gobe ki shirya min jaka"
Ta zagayo ta rungumeshi ta baya ta ce "My one ka tafi da ni mana"
" Zayty, it's a two days business trip, zuwa da ke will be a distraction"
" kai dai kawai ka ce ba ka so naje, Wallahi I'm not going to distract you, I swear"
" stay with the kids then"
Tare suka sauko ƙasa suka samu yaran sun jima da fara cin abinci. Zaytunah ta yi serving ɗinsa ya fara ci. Ya kalli Yamin ya ce " Naziha ta karya ne?"
"no uncle, ɗazu mun dubata tana bacci sai muka ƙyaleta" ya amsa ma sa
" make sure idan ta tashi ta ci abinci sosai, and she should stay at home" Yamin ya amsa masa da toh.
Yau dole sai da yaran suka takura ya kaisu makaranta kafin ya wuce Asibiti, ya makara amma dai ba shi da surgery yau.
Sai ƙarfe goma Ziha ta tashi ciwon ya lafa mata kaɗan. Ta yi wanka ta shirya ta fito falon shiru ba kowa, ta ƙwanƙwasa ƙofar su Yassar ta ji shiru dan haka ta wuce ɗakin Saratu a kishingiɗe ta same ta akan gado, suka gaisa ta tambayeta ko su Yassar sun fita ne.
" 'yan biyu na buga ball a waje" ta amsa ma ta. Kitchen ta shiga ta haɗa tea ta fito ta sha dan bata da appetite na cin abinci dama idan tana period ba ta cika cin abinci ba. Da ta gama ta fita wajen compound ɗin gidan. Kayan da su ka saka iri ɗaya ne dan haka ba ta banbancesu ba, sai da Yassar ya hangota ya ƙwalla kiran sunanta ta gane shi saboda Yassar ne mai iya magana da ƙarfi haka, ya taho wajenta da gudu "Pretty ya jikin ki, sorry i was not there for you last night"
Ta ɗan kalli gefen da Yamin ke tsaye ta ce "Wallahi I taught it was you" ta ƙarasa wajen Yamin ta masa godiya. "actually you should thank Uncle Saj, he's the one that did all the work" ta yi murmushi ta ce " I'll call him up"
"Oh lalala! Pretty it's glaring already" Yassar ya faɗi yana dariya
Ta ɗan harare shi ta ce " what's glaring"
"the affection between you two" ta kai masa naushi ya goce yana dariya...
***
Karanta text ɗinta da Sajid ya yi ya sa shi yin murmushi babu shiri, gaba ɗaya sai ya tsinci kanshi cikin farinciki. Bai san dalili ba amma every single thing about her amuses him. " Naziha" ya kira sunanta a fili.
Ƙarfe ɗaya da kwata dreban Sajid ya zo ɗaukanta, a hankali ta fito goye da jakar laptop ɗinta tana sauri. Turus ta tsaya ganin Zaytunah na magana da dreban, da alama yanzu shigowar ta gidan.
Kasa ƙarasawa ta yi, ta tsaya tana jiran su gama magana. Tafiyar ƙasaita Zaytunah ta tako har wajen da ta tsaya ta ce "daga yau na kashe ɗaukan ki da ake yi a mota, ki nemi wani means na tafiya, amma ba da motan mijina ba" ta bangajeta ta wuce.
Allah ya sa akwai kuɗi a hannunta, ko ta kan driver ba ta bi ba ta fice daga gidan. Ba ta ji haushi ba dan ta saba da gorin Zaytunah yanzu.
Washegari da sassafe Sajid ya wuce Airport Zaytunah ne ma ta tuƙa shi, sai da jirginsu ya tashi ta bar wajen.
Kamar yadda Zaytunah ta riga ta faɗa mata, lokacin da ta shirya ba ta tsaya duba driver ba ta fita ta hau mota ta wuce Asibiti.
Ta na shiga cikin farfajiyan Asibitin ta haɗu da Dr Jamal wanda shima fitowarsa daga mota kenan. Yana ganinta ya washe baki yana faɗin "Good Morning beautiful" ta ɗan haɗe rai ta ce "Good Morning sir" haka ya dinga janta da hira har suka shiga, shi kaɗai ya ke zancensa bata sa masa baki ba. Sai da ya rakata har pharmacy section kafin ya wuce office ɗinsa duk yadda ya so ta bashi numbarta ta ƙi.
Daga asibiti ma taxi ta shiga ta wuce makaranta.
Lokacin da ta shigo gida ta haɗu da 'yanbiyu suna kallo a falo.
" Pretty, duk motocin da ke gidan nan da kuma two drivers amma sai kin shiga taxi, that's an insult to Uncle Saj" Yassar ya faɗa yana kai lomar dambun nama da ya cika spoon ɗin hannunsa.
Ta gyaɗa kai kawai ta wuce ɗaki, dan gaba ɗaya a gajiye ta ke ga shi tana so ta gyara jikin ta.
" Uncle Saj will surely be mad idan ya sani"
Yamin ya yi murmushi ya ce " he'll be mad kam, amma tana masa murmushi shikenan"
Yassar ya ɗan langwaɓe kai ya ce "kasan Allah Yassar sai da na ga hoton nan na amince 100% da maganarka, the picture says everything, you can really find true love at any age. Poor Uncle Saj yana sonta sosai amma bai gane hakan ba har yanzu"
"Shhhhh ka rufa mana asiri kar Aunt Zayt ta ji zancen nan, saboda za a yi yaƙi"
"Ba ƙaramin yaƙi za a yi ba kam" Yassar ya faɗa yana chanja tashar da su ke kallo
*
Zuciyarta bugawa ya fara yi da sauri sauri jin hiransu Yamin da ta yi. Tana son saukowa, amma gaba ɗaya jikinta yayi laushi duk wasu gaɓɓanta sun sake, Wani hoto su ke nufi? Sajid is in love with who? Shine abinda ta ke tambayar kanta. Da ƙyar ta iya saita kan ta ta ƙarasa saukowa falon fiskarta ɗauke da murmushi wanda bai kai zuci ba...