GUGUWA BIYU

GUGUWA BIYU

by @109696625203084497219

*GUGUWA BIYU*



*Aysha D Fulani*




*BABI NA GOMA*



بِسْمِ اللّٰهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ








Hannu biyu tasa ta amsa tai godiya ta juya a hanyar makaranta ta buɗe jakarta ta jefah ciki ba tare da ta buɗe taga me ta bata.

Kamar kullum ma yau karfe biyu aka tashe su, tattara komai nata tayi ta kama hanyar gida tana shiga ta iske Amie a falo tana zaune tana kallo, gaisheta tai ta shiga ɗaki ta sillo wanka cikin jallabiya mai gajeren hannu karamin hijabi ta saka ta gyara dakin tunda yau Alhamis babu islamiyya hakan ya sa ta dawo wurin Amie ta zauna gefenta.

A zabure ta mike da tuno kyautar Bilkisu da sauri ta shiga daki ta sanya hannu cikin jakar ta lalubo bakar ledar, wurin Amie ta dawo sai binta da ido Amie take tundaga zaman ta zuwa tashi ta. Gaban Amie ta dire ledar tana fadin "Kinga Amie ɗazun zan fita makaranta Anty Bilkisu ta kirani ta ban wannan ledar wai ga tsarabata da Abba ya kawo".


Girgiza kai Amie tayi ta dauki ledar ta buɗe, biskit ne sai dangin su chocule, murmushi mai kama da yaƙe tayi ta mika mata tana fadin "Ai kin gode sosai, Allah ya bata lada, daga yanzu kuma ko mai zata baki ki gaya mun sannan idan ta baki kudi kadda ki sake ki amsa komai ƙankantarsa kije ki adana waɗanan din akwai wasu a gaban madubin dakin ki da na ajiye miki sunanan sai ki hada".

"Toh Amie".

Miƙewa tai ta koma ɗakin ta ajiye a gurin da taga Amie ta ajiye mata saura, madafah ta nufah ta zubo abinci ta koma falo, tana zaune Abba ya dawo ta gaida shi ta koma daki.


Yau ta kasance Juma'a mai gajeren lokaci inji malam Bahaushe, da sallama ta shigo cikin gidan a tsanake take tafiya har ta karaso bakin kofar ɗakinsu sallama tayi aka amsa daga ciki bakin kofar ta kare ma kallo taga bakin takalma hakan yasa ta kusa kai kanta a kasa ta karasa shiga, a hankali ta ɗago ta sauke idonta akan mutane hudu da ke zaune a falo duk matane ƴan mata biyu sai iyaye biyu gaishe su tayi ta wuce ɗaki, don bata ga Amie a falon ba sai dai tajiyo muryarta a cikin ɗakin.

Wanka tai ta kwanta bacci mai nauyi ya dauketa don a gajiye ta dawo, kiran da Amie ke mata ne ya tada ita daga bacci da take amsawa tayi ta mike ta shiga bayi ta dauraye idonta ta fito falo.

Zama tai a kasa kusa da Amie "Kin ko ci abinci bayan kin dawo don Ni dai na san kin shigo amma dagana ban sake saki a idona ba".

"Wallahi bacci ne ya kwashe ni, bakin har sun tafi kenan".

"Eh ƙawaye na ne da yaransu, debo abinci kizo muyi wata magana".

Zama tai ta fara cin abincin, "kina jina?".

"Gobe zanje Abuja amma a gobe zan dawo in Sha Allah Yayata ce babu lafiya kuma abun ya yi ƙamari har an tafi asibiti gobe zamu Ni da Abba gobe zamu don nasan tunda yana gari bazai bari mu kwana ba, banda kina da islamiyya gobe da dake zamuje sai dai abin da zan gaya miki shine ki kulah da kanki don Allah zuwa yamma zamu dawo in Sha Allah".

Girgiza kai tayi tana duban Amie cike da tausayawa take fadin"Ubangiji Allah ya bata lafiya, Allah ya saukaka mata Allah ya kaiku lafiya ya dawo da ku lafiya, don Allah a gaidasu Amie na".

Ameen ya Allah sallamar Abba ce ta ɗakile hirar ta su, miƙewa tai ta koma ɗaki ta cigaba da cin abinci da take ci.


Karfe takwas na safe Aysha ta fito daga cikin ɗakinta cikin shirin tafiya islamiyya, Amie ta gani tsaye tana gyara zaman mayafinta."Ba dai har kin kamallah shiri ba Amie".

"Aikuwa dai na kamallah tafiya ta rage tunda kema kin gama mu tafi sai mu sauke ki, don Allah ki kulah da gidanan da kyau kinji in sha Allah da wuri zan dawo".


Hon din Abba ne ya katse musu hirarsu, da sauri Amie ta zura takalma ta na fadin "Muje kinga ya kamallah".


"Inallalilahi wa'inna alaihi raji'un!". Amie ta furta a kasan zuciya, lokaci guda takaici yakamata ganin Bilkisu tsaye jikin motar Abba, tsaki ta sake ja a karo na biyu cikin zuciya take addu'ar Allah yasa Abba bai sanar ma Bilkisu da zancen tafiyarsu, idan ko ya gaya mata tasan sai dai tsarewa Allah Ubangiji da karfin addu'a ne zai taimaƙeta yau.


Bakin motar ta kasara tana fadin "Ayi hakuri Abba munfito".


Juyawa tai tana amsa gaisuwar da Bilkisu take mata "Wallahi kuwa jikin ne babu dadi nima kiran sauri akai mun akan rashin lafiyar nata amma in sha Allah muna hanya yau". Shiga cikin mota tai don batason doguwar hirar da Bilkisu ke ƙoƙarin janta dashi, tana koyi tana fadin aikuwa da nasan da wannan batu ai da tun jiya na shirya ni ma na biku amma in sha Allah idan zaku koma sai muje tare don Allah a gaishe mun da'ita da jiki".


"Zataji" Amie ta fada ta janyo murfin motar ta rufe. Takaicin duniya ya isheta don har ga Allah bataso Bilkisu ta san da zancen tafiyar ta ba, addu'ar neman tsarin ta dinga ma Aysha a bakin kofar makaranta suka sauke ta Amie ta sake jamata kunne akan ta kulah da kanta sosai.


Bangaren Bilkisu ko yau take sallah a wurinta cike da murna ta shige ɗaki ta dauki wayarta kiran layin ƙawarta tayi, ring ɗaya zuwa na biyu ta dauka. "Ya ake ciki".

Maryam ta furta bayan ta daga wayar, cike da zumudi Bilkisu ta shiga koro mata bayanin yadda abu ke faruwa.


A jiyar zuciya Maryam ta sauke tana fadin "Dadina dake gaggawa ƙawata wallahi ki iya takunki ki bi komai sannu,amma fah dama ce ta sake mu akwai wani magani da na amso wurin Malam idan ki ka bata da kanta zata kawo kanta kuma amma cikin abinci zaki saka mata indai taci zance ya kare bari nazo na kawo miki sai kiyi amfani da shi, kin san dai abin da na gaya miki kadda kiyi abin da zai zo ya lalata duk wani shiri naki idan har zaki bi shawarata to kadda ki soma nuna zalamarki yanzu kiyi hakuri jan yarinyar nan ya kamata kiyi a jiki, kinga uwar ɗakinta batanan ki zauna ki shirya mata girki mai rai da lafiya, sannan kije ɗakin ki zauna ki dinga janta da hira ki bari sai ta saki jiki dake sosai sannan zaki fidda bukatar, amma fah shawara kadda kiyi abin da _Allura zata tono garma_ gara kizama _ _Mage mai kwanciyar daukar rai_ ko kuma kizama _koren maciji mai sajewa da koriyar ciyawa_ ki zauna kiyi tinani kin san cewa kishiyar ki tasan komai tana kauda kai ne kawai don bata cika shiga sabgar da babu ruwanta ba, don Allah kiyi komai da natsuwa kadda azo garin neman gira a rasa idanun, maganinan yana da kyau shine zai jawo mana ita ta shigo hannu cikin ruwan sanyi".


A ziyar zuciya mai karfi ta sauke tana jinjina lamarin, hakika a yau taso cimma burinta amma Maryam ta tuna mata cewa Karfe baya jin dokan komai sai na ɗan uwansa karfe, lumshe ido tai tana sake gyaran zaman wayar a kunnenta cikin sanyin muryar take fadin "In Sha Allah Maryam zanyi duk yadda ki ka ce wallahi kwakwalwata ce ke doɗewa akan dukkan lamarin da ya shafi yarinyar nan na rasa ina zan saka rayuwata a duk sanda na ganta jikina har rawa yake yi in rasa inda zan saka kaina, neman natsuwa nake in rasa, Maryam Allah ya sani ban taba shiga iftilan rayuwa irin na wannan karan ba, amma fah muddin nayi iya yina wallahi gagarumin asiri zan mata ta na canza mata akalar ta, ta bar gidan idan yaso na siya mata wani gidan ta zauna chan".


"Kiyi Hakuri dai muyi yadda nace mubi komai a sannu don cikar muradi". Maryam ta fada ta jan numfashi.


"In sh Allah". Bilkisu ta furta ta katse wayar ba don ranta yaso ba. Jingina tai da kujera tana jinjina lamarin Aysha dafe kanta tayi tana fadin "Tabbas yarinyar nan ta sani gaba, anya ba hakkin y'ay'an jama'a bane yake bibiyata". Sake shigewa cikin kujarar tayi ta lumshe ido tana tuno rayuwarta tabaya.

WACECE BILKISU

Bilkisu haifaffiyar garin Kaduna ce chan cikin anguwar masu hannu da shuni, mahaifinta hamshaƙin mai kudi ta bangare biyu kasuwanci da kuma fannin boko, su biyar iyayensu suka haifah hudu maza sai Bilkisu itace mace ƙwaya ɗaya kuma itace ta uku,kasancewar ta mace ƙwaya ɗaya yasa mahaifinta ke matukar ji da'ita duk abin da take buƙata take ake nemo shi, babban gida garesu wanda ke dauke da yaltatun ɗakuna, dakin Bilkisu babbane wanda ke nesa ƙadan da na mahaifiyarta ɗakine da aka yalwatashi da kayan alatu.


Zaune Bilkisu take tana yawata a cikin shafin Facebook na yanar gizo, cikin group dinsu ta tsunduma taji suna magana akan wani littafi wanda ya shahara ƴan matan ciki sai fadin albarkatun bakinsu suke akan marubuciyar sunata yabanta.


Har cikin ranta taji littafin ya yi mata sauka tai a facebook din ta dawo kan babban shafin bincike na waya wato (Google) kai tsaye sunan book din ta rubuta aiko bai bata lokaci ba sunan ya bayyana, kishingiɗa tai ta soma karantawa sakin wayar tai da sauri ganin abin da ya nemi ya zautar mata da ƙwaƙwalwa, yadda ake gudanar da rayuwar auratayya ake fadi a shafin data buɗo, jiki na bari ta rarimi wayar ta cigaba da karantawa wani irin yanayi taji yana shiga jikinta, gaba ɗaya yanayinta ya soma sauyawa matse jikinta take a jikin filo ta manne wayar da filon tana hasaso irin dadin da ma'aurantan keji saboda babu abin da marubuciyar ta boye komai sai da ta bayyana.

Buɗe wayar tayi ta dinga maimaita wurin sai da taji wani abu mai kama da ruwa yana fita daga jikinta sannan ta cigaba da karantawa, tsaki taja ganin labarin bai kai karshe ba. Nanauyar ajiyar zuciya ta sauke tunowa da marubuciyar ta ajiye number ta a farkon labari da sauri ta suri wayar ta dauki number matar ta ajiye ta a jerin lambobin wayarta.

What app takoma ta lalubo matar don tayi gargaɗi akan banda kira sai dai mutum ya yi sako ta chan WhatsApp din, hannunta na bari tai ma matar sallama, ba'a wani dau lokaci ba sai ga shi an mata reply da sauri ta kora matar bayanin cewa tana son littafi ba ta ɓata lokaci ba tai mata bayanin yadda farashinsa yake biya tai ta turo mata.


Cike da jin ɗadi ta sake komawa cikin karatun yinin ranar Bilkisu a ɗaki tayi shi kuma dama gashi gidan babu kowa, tas ta kamallah karatun a chan kasa taga marubuciyar tayi tallah wani littafi wanda yai mugun daukar hankalinta duk tunaninta iya kar fina-finan batsa ake fiddawa ashe akwai masu rubutawa ma.


Ba ta ɓata lokaci ba taje ta sake siyanan litattafai matar, cikin kwanaki ƙalilan Bilkisu ta zama shahararrin fans din matar duk littafin ta idan ya fito sai ta siya.


Karatunta ya bunƙasa ta inda ta cigaba da bibiyar marubuta masu irin wannan rubutun cikin hakane tai karo da wata marubuciya da take rubutu akan Lesbian (ƴan maɗigo) Ubangiji yai mana tsari dasu alfarmar Allah da Manzonsa, Allahuma Ameen.


Ganin free page yai mata dadi ya sa ta siya cike da jin dadi ta soma karanta littafin, ganin yadda ƴan matan ciki ke biya maƙansu buƙata ya sa itama ta fara kwatanta yadda suke yi abu kamar wasa ya zama gaske gaba ɗaya kwakwalwata ta juye a gun karatu a duk sanda za dauki waya sai ta aikata makamancin abin da taga anayi a cikin littafin.


Abu kamar wasa ya fara bunƙasa duk inda Bilkisu taga ƴar uwarta mace sai taji tanaso ta aikata abin da take karantawa, duk inda taje ta zauna kusa da ƴar uwarta mace sai ta dinga taɓata cikin ranta tana tuno yadda ake jin ɗadi a cikin littafi.


Cikin karo da wani sabon update na wata marubuciya ya sake birkita ma Bilkisu tunani, gaba ɗaya ta rasa ina zata sa kanta gaba ɗaya zuciyarta ta gama ƙawata mata yadda abin yake a zahiri, kasa zuwa makaranta tai ranar saboda muddin taje tasan duk wacce tai karo da'ita zata iya aikata komai. Zaune take a falo kusa da Umman su, mai aikinsu ce tashigo ta zube gabanta tana fadin Hajiya karama na gama dafah miki indomi lumshe ido tai a lokacin da tai tozali da albarkatun kirjin Larai, wacce ta ɗade tana kwaɗayi hannunta ne ya soma ƙaiƙayi ji take tamkar takai hannu kan zammamar rigar dake wuyan Larai ta tabo abin da ke mata tozali.


Jin Larai na sake maimaita mata sakon don a tunaninta bataji abin da tace ba, buɗe ido tai tace kawo munan inci tunda kin gama na gode sosai.


Shigowa tai ta dire mata kwanon abinci a gabanta ta juya ta fita, kura ma bayanta ido tai tana ayyana yadda za tayi ta shako kan Larai ba tare da kowa yasan mai ake ciki ba, sallamar mahaifinta ne ya dawo da'ita dogon tunanin data tafi amsa sallamar tayi ta dauki kwanon ta soma cin abincin.


Jin Abbansu na sanar ma Ummanta rasuwar kawunanshi hakan yai matukar yi mata dadi ko babu komai zata samu dama ko sau ɗaya ce akan Larai, tsam ta ajiye tunaninta gefe ta juya inda tajiyo mahaifinta ke fadin sai ku shirya gobe muje muyi gaisuwa zuwa jibi sai mu dawo.


"Wayyoo Abba Allah ya jiƙansa da Rahman amma ni sai ana gobe addu'ar bakwai zanje inyi kwana biyu, lokacin hutun mako ne kaga yau saboda banjin dadi ban leƙa makaranta ba kuma gobe ina son zuwa"


Bai ja ba, ya ce "Allah ya nuna mana, Ubangiji ya kara lafiya ".


Dadi fal ranta za'a bar mata gida taci karanta babu babbaka, murnar da take ce ta koma ciki don gaba ɗaya kuma ta rasa wacce hanya zata bi ta shawo kan Laira, shiru tai cen ta tuno da maganin bacci lumshe ido tai tana jin dadi






COMMENT FISABILLILAHI