Chapter 9
by @maidambu41
*BAƘIN HAURE....🐾🐾*
{Greed for Money is the roots of all evils🫀}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu
*009*
Tamke fuska yayi yana kallonta, domin ba zai tab'a mantawa da izayar da matar nan ta bashi ba, cikin muryar shi mara daɗi ya ce mata. "Nana kin ajiye ni ne da zan zo na duba ki?" Shiru tayi tana kallonshi kamar zata mutu, idan ta ga yana nuna mata kiyayya haka. "Alhaji ina laifin Nana don ta damu da kai?" Mikewa yayi bai basu amsa ba, musamman ita Hajiya Hadiza da ya tsani ta mishi magana.
"Kyale shi ai Uwarshi tana gani yake wulakantani." Murmushi Hajiya tayi tana faɗin. "kin sha gaya min idan kina magana da ahalinki na daina shiga cikin maganar, kuskure ne don na zab'i yin shiru akan na magantu?"
Cikin borin kunya ta ce mata. "Hmmm! Haka dai kika ce, amma ni yaushe na ce ki daina shiga cikin ahalina. Yanzu dai nazo ne maganar kamfanonin nan, da fatan dai ba za a cire min hannun jarina ba ko?"
"Ni babu ruwana ki same shi." "Tow ta nan kika bullo min Sa'adatu?" A gajiye da halin Nana Hajiya ta ce mata. "Nana meye nawa a cikin wannan lamarin? Yaran nan jikokin ki ne, sannan kuma."
"Kawai dai ki ce mana Yaranki sun fi karfinki, amma taya akan wannan yar maganar zaki ce wai babu ruwanki salon munafurci da nunawa kamar ba ruwanki." Inji Hadiza Abdul Majid ba'are, "Hadiza kin ga babu ruwanki da sha'aninmu, tsakanin Nana da Jikokin ta gata ga su ina ruwana?"
Ta fada tana kallonsu, kwana biyu da suka wuce har cikin gidan suka biyo ta suka ci mata mutunci har da mata gorin a caca aka aurota, haka duk bai isa ba Nana ta gaya mata cewa ta zuba idanu tayi kallo hatta wannan gidan da take ciki sai ta fice daga cikinshi, sai gashi Allah ya raba gardama ya kawo mata shi cikin sauki, don haka ba zata lamunci rainin hankali ba. "Hmm! Nana tashi muje!" Inji Hadiza, haka suka fito a harabar gidan suka same su, a ran Hajiya Hadiza ta ce. *Shaidanun biyu* kallon Nana Aryan yayi, ita hankalinta yana kan hannun Captain yana goge wata sabuwar bindiga. "Captain ni dai ka nima min lasisin rike bindiga!" "Munafiki algungumi uban me zaka yi da bindiga?" Juyawa yayi ya kalli Nana. "Hajjaju laifin me na miki? Uwar Mamman Ba'are!" Ya tambaye ta, yana wasa da katon lion dog ɗinshi. "Uwarka Sa'adatu gata can a sama." Juyawa yayi ya sumbaci hannun shi ya wurga mata. "Ta iya haihuwa tunda ta haifi Abdul Majid Mamman Ba'are, ta haifi Aryan Mamman Ba'are ba, Uwar Jamilah da Aneesah, Babar Amaan Mamman Ba'are, akwai saura ne?" Ya tambaye ta, cike da takaici ta ce mishi. "munafikin banza." "Da nayi miki me?" "Kai dai wutarka dabance." Sam baya son hayaniya, don haka ya d'anna kunamar ya sake harbi a iska, shiru wurin ya dauka. Musamman Hajiya Nana da ta ji kamar zuciyarta ya harba, kafin su farga daga ita har yarta sun gudu baka ganin alamarsu, sojojin da aka bawa Captain ɗin suka shigo a guje. "Sir!" Murmushi yayi ya musu alamar su tafi da hannunshi.
Kar'ar harbin Majid Mamman Ba'are, ya karad'e ilahirin gidan baki daya, wanda yasa kowa ya sha jinin jikinshi, lallai Majid ya iso, Gidan Alhaji Kamilu Abdul Majid ba'are, kuwa tab'e baki yayi ya ce. "Kowa ya sayi rariya yasan zata yi yoyo, ai na gaya musu, babu ruwansu da Yaran Sa'adatu amma suka ki, gashi nan sun takalo mana jaraba." Ya fada yana shan tea a hankali, "ni kuwa sai nake ganin kamar da gayya aka takalota."
Kallon Matarshi yayi, kafin ya ce mata. "eh da gayya ce mana, tayi abu ko Yaranta suyi su zama masu laifi ake so." "Amma me yasa suke haka ne?" "Saboda dukiyar Mamman ya raba biyu ya basu rabi, rabi aka yi rabon gado da ita."
"Allah ya kyauta!"
"Kin yi waya da Maisarah?" "Eh mun yi waya, amma tace min idan suka samu hutu zata zo." Shiru yayi yana kara jin ba dad'i. Kowa a duniya yana farinciki da nutsuwa idan yana tare da ahalinshi, amma shi a nashi ɓangaren dole ya hakura da Maisarah ta koma wurin dangin Mamanta da suke labenon, tunda a can ya auro ta,kuma ba karamin son Yaransu suke ba. Sai dai tun bayan Mutuwar Mamman Ba'are yarinyar taki zama a wurinshi. "Ina Jamal?" " Ya tafi wurin kallo!."
Gidan Hajiya Tani.
Cikin matsanancin b'acin rai take kallon Sajjid Mamman Ba'are, "kasan yadda na ɓata lokaci akan ka samu damar shiga cikin dukiyar Mamman Ba'are?" Girgiza kai yayi yana durkushe a gabanta. "Kiyi hakuri Hajiya!" "Idan ka kuma bani hakuri sai na tsine maka." Ta fada ranta yana suya, "sai da na gaya maka ba zan dauki kuskure ba, kace babu matsala Amaan zai bamu hadin kai, amma sai gashi daga kai har shi kun fad'i." Kasa magana yayi domin yana matukar tsoron kada yayi magana ta tsine mishi.
"Yanzu kana da hanyar da zaka iya dawo min da asarar da nayi?" Girgiza kai yayi, tayi kwafa sannan tacigaba da cewa. "Dake kai lissafinka baya ja, shine ka bude shegen bakinka zaka mishi barazana da rayuwarshi!" "Na tuba Hajiya!" Ɗaukar glass cup tayi ta jefe shi sai da ya tasa mishi goshi, jini ya shiga zuba a Kyakyawar fuskarshi.
"Ka sake bani hakuri sai na illataka!" Jini da yake zuba yasa shi rike wurin. "Ɓace min da gani." Mikewa yayi ya nufi dakinshi,ya shiga kallon kanshi a mirror din dakinshi. Wayarshi ce tayi ƙara. Dauka yayi ya ce. "Na'am!" Cizon fatar bakinshi yayi ya ce. "Ban san asara ba, kayan nan Libya zaa shiga da su, ka gayawa Guru ya binciko min duk inda Jaguwa yake a tsakanin sahara da dazuzzukar Kamaru da Nijeriya, idan kuka sake na fita farauta ba zai muku kyau ba." Ya kashe wayar yana me jifa da ita, asara biyu yayi yau baki daya bai tab'a shiga damuwa irin ta yau ba, ban daki ya wuce ya wanke fuskarshi da jikinshi, sannan ya bude first aid kit ya gyara goshinsa. Yana gamawa ya fito yana tsane jikinshi, ya ji harbin bindigar Majid. Datse fatar bakinshi yayi da hakorinshi sai da ya fara jini.
Ya sake bakinshi a hankali, yana jin Idanunshi yana cika da kwalla. Idan yana raye sai ya ga bayan Majid, ya raya a ranshi yana me kara tabbatarwa kanshi, sannan ya shirya cikin kananun kaya, ya dauki madubi ya saka domin ta rufe mishi inda aka jefe shi. A falon ya sami Hajiya Fauziya, tana kasa da murya ta ce. "Wato ban san yadda aka yi wancan dan iskan Yaron ya dawo ba, amma tabbas ita Uwarshi abin ya mata dad'i." "Zan fita." Dauke kai tayi tana faɗin. "Hm!" Daga haka ta juya ga Hajiya Fauziya. "Me kika ce?" Cikin tuntuben harshe ta ce mata. "Naga alamar babu nasara." A fusace Hajiya Tani ta watsa mata harara. "Kika ce me?" Hadiye yawu tayi ta ce mata. "Dama nace wannan karon mun fadi ya zamu yi?" Tab'e baki tayi tana faɗin. "Ya kuwa zamu yi? Ku je kuyi shawarar makomarku bamu ba."
A zunkud'e tace mata. "Ban gane ba?" Gyara zama Hajiya Tani tayi ta ce mata. "Dama da an samu nasara kamar yadda na gaya miki, kina da kaso saba'in cikin dari, ni zan tashi da talatin kuma gashi ya dawo." Cikin tsannanin takaici Hajiya Fauziya ta sauke kanta kasa, "Ban san ta inda aka samu matsalar nan ba, amma tabbas akwai wani abu."
"Idan ma akwai ya dace ki sani kece me yara mata baki daya, gara Rabi tana da Lukman, Harirah tana da Sharif ke fa? Babu ko daya sai Yara mata, kuma kin san koda yau gwanjon kayan ba'are aka yi kasonku bai wuce kason Aryan ba, kai ina ba ma zai kai kason Aryan ba. Duk da yadda muka yi dake na cewa zaki tsayawa Sajjid a wurin sai gashi har aka tashi baki yi kome ba, yanzu zaki zo kice min wani abu." Tana gama fadar haka, ta mike tana me barin Hajiya Fauziya a wurin. A hankali ta fita ta bar gidan, tana me jin takaici me yasa Majid ya dawo daidai wannan lokacin.
Alhaji Haladu.
Tunda ya shiga yake safa da marwa, kana ganinshi kasan lissafi ya kwace masa. Matarshi kuma me bashi shawara ta musamman ta zauna tana kallonshi. "Abban Afiyyah ban ga dalilin d'aga hankalin nan naka ba, ai ja da baya sai raggo, taya zamu zuba idanu Sa'adatu ta ci bulus bayan ka manta a caca aka ciyo ta."
Cikin takaici ya zuba mata idanu, ya ce mata "taya zan manta bayan dan uwana ya ciyo ta ne a caca,a lokacin da yake ƙishirwar d'a namiji a lokacin ya saka kudinshi aka ci kawunta."
Murmushi tayi tana kara jin haka shine abinda take bukata,bata kaunar Sa'adatu ta cigaba, amma dole haka zata hakura.
Shigowar Hajiya Fauziya kamar an watsota daga sama, yasa baki dayansu suka razana. "Ke lafiya?" "Ina lafiya kuwa." Ta fada tana gyara zama, "ya zamu yi Haladu?" Gyara zama yayi ya ce mata. "ya kuwa zamu ban da mu nime wata hanyar?"
"Kamar ya wata hanyar?"
Gyara zama yayi yana faɗin. "Dole zamu marawa Tani baya, sai mu san me za ayi kuma."
"Kana ganin marawa Tani baya shine mafita?" Inji Hajiya Turai Matarshi. "Eh mana shine mafita, domin ita ba zata watsar da ra'ayinmu ba"
Dariya tayi tana faɗin. "Lallai fa, tow Tani itama hanyar niman shiga take kan dukiyar Yaran Sa'adatu, idan kuka mara mata baya zata iya juya muku baya, idan kuka nime naku na kanku kowa zai kasance a ankare. "
Shiru suka yi kafin kuma suka ce mata. "Bamu fahimci inda kika dosa ba?" A hankali ta gyara zamanta ta warware musu fahimtarta, sannan ta kara musu kwarin gwiwa da cewa dole su kasance masu mika kai domin idan baka iya kama barawo ba tow shi zai kama ka."
Nan suka yi na'am da shawara ta, har Hajiya Fauziya ta fita, Hajiya Turai ta cewa Mijinta. "Bari na gaya maka gaskiya, matar nan munafuka ce ka sani nima kuma na sani, so abin da zan gaya maka. Zata tafi wurin Hajiya Tani da zancen nan, kai ka fara kiran tani ka gaya mata abin da ka yanke. Sai na gaya maka yadda zamu yi"
Ai kuwa kamar yadda ta fada haka ya kira Tani, ya gaya mata kome da kuma yankar bayan da Hajiya Fauziya ta mata, sannan suka dauki laifin kacokan suka daura mata, ita ce ta kawo musu zancen a shiga malamai. Jin shi Hajiya Tani take, sai da ya gama ta ce mishi. "Zan duba al'amarin"
Ta kashe wayar, murmushi Hajiya Turai tayi ta ce mishi. "Ka shirya zuwa bayan Magariba ka tafi gidan Hajiya Sa'adatu ka yi sulhu da ita. Idan ta lalace maka anan a can zaka fita"
Kurawa Matarshi idanu yayi tunda yake bai tab'a zata shaidaniya ce har haka ba. Take ya sake murmushi yana faɗin. "Lallai Hajiya ke duniya ce."
Murmushi tayi tana faɗin "taya ba zan kasance haka ba, ina tare da dai ga makiya sun rufa maka baya ta ko ina, ai lahu a gare ni na tsaya maka, don haka kada ka ji kome mijina."
***
Wurin karfe biyar na yamma Hajiya Sa'adatu tana kan abin sallah, tana lazimi Nabeeha matar Aryan ta shigo hannunta dauke da katon tire, bayan ta Aryan ne dauke da Kwando, "Assalamu alaikum Barka da maraice Hajajju." Sallamewa tayi tana kallonsu fuskarta dauke da murmushi ta ce musu. "Amin wa'alaikumus Salam, barkanku mutanen kirki." Gyara zama tayi tana faɗin. "Nawa ne ko na Hammanku?" Dariya sukayi. "Hajiya naki da nashi ne, muka ce bari a kawo mishi, duk da ban gaya mata da wuri ba." " Hajiya kinji ba yaki gaya min zai tawo da hamma kawai sai gashi nan yazo da zancen akwai bako." Nabeeha ta faɗa tana tura baki. "Baka kyauta ba, maza jeka dakinshi ka taso min shi."
"Tow Hajiya." Haka ya fita zuwa dakin Majid din da yake kwance, ya lullube kanshi da mayafi, dakin ya bada wani irin duhu. Kunna wutar dakin Aryan yayi, ya hango shi zaune ya jingina da allon gadon. Amma kanshi a lullube yake. "Baka da lafiya ne?" Janye lulluben yayi yana kallon Aryan. Dauke kai yayi yana me sake lullube kanshi. "Kazo falon Hajiya da yake sama Please."
"Me zan yi?" A yanayin rayuwarshi matukar ba'a wurin aiki ba,baka tab'a ganin fara'arshi, tashi yayi ya sauka daga gadon ya nufi ban daki. Sai da ya gama uzurinshi ya fito ya saka hula a kanshi ya fita. Zuwa falon hajiya domin sun fito daga ɗakinta, yana shiga ya same su a kan kafet sun baza abinci. "Matar Aryan ce ta maka abinci."
"Nagode sosai!" Ya fada yana gyara zamanshi a kafet ɗin, Aryan ya zuba mishi yana jan shi da hira. "Amma shirun da Hajiya Tani tayi babu magana a kasa?" "Allah yana sane kuma yafi mu sanin abinda yake zukatansu."
Inji Hajiya, tana cin abincin itama don ta lura Majid yaki cin ko loma daya ne, har yau yana shakkar cin abincin kowa, domin rufawa rayuwarshi asiri yasa ban da girkin Hajiya kai ko tea bai yadda ya ci wani abu daga wani wurin ba. Shi yasa a duniyarshi yake shakkar kaidin mace. Saboda kaf duniya babu wanda yasan cewa sanadin jinyar Mahaifinsu guba ce. A hankali ya tura abincin yana murmushi. "Bana son abincin da aka saka citta da tarfarnuwa, domin ina da allergy."
Sanin ba zai ci bane Aryan yayi maza y kare dan uwanshi. "Wayyo kayi hakuri, na manta na gayawa pretty baka cin citta da tarfarnuwa." Murmushi yayi ya mike, karshe abincin da bai ci ba kenan. Kuma ai Hajiya tasan ba zai ci ba. Ita tana ganin har yau Majid bai warke ba, pretend yake kamar mai lafiya amma a zahirin gaskiya bai da lafiya. Shi yasa take son yayi aure ko zai samu wacce zata jure matsalarshi,
"Kiyi hakuri haka yake, baya cin citta da tarfarnuwa ne, tun yana Yaro." Itama Hajiya ta fadi haka, shi kuwa gogan naku yana shiga dakin drower yaja ya Ciro kudi me yawan gaske, ya fito daga dakinshi kenan suka hadu da Amaan Mamman Ba'are,. Kallon kallo suka yiwa juna kafin kowa ya kame kanshi, akwai wannan rigimar na sako da sako, amma ita Hajiya bata taɓa kawowa al'amarin zai lalace har girman yaranta ba, a zahirin gaskiya tsanar da Amaan yakewa Majid tayi yawa da har sai da kowa yayi magana. Wani irin tsana ce irin na matukar na samu dama sai naga bayanka. Amma a bangaren Majid babu wannan tsanar kawai shi mutum ne da yasan ciwon kanshi da darajar kanshi,. Sannan bai kullaci Amaan har haka ba. Kamar yadda shi ya kullace shi, reni ne baya so kuma ya fahimci Amaan yana da reni da son abin duniya.
Kiyayyar tasu ta faro ne daga lokacin da Alhaji Mamman Ba'are, ya bar wasiyya akan cirewa kuri'arshi ya gadarwa Majid, sannan ko a halin jinya yadda Alhaji Mamman Ba'are yake ta rokon a nimo mishi Majid ya roke shi gafara kada ya mutu da hakkinshi ya kara tunzura dayawan mutanen dake jikinshi, bawan Allah nan har ya mutu da rokon a kira mishi Majid, don Allah ya yafe mishi.
Duk da akwai hakkin iyaye akan Yaransu, haka akwai hakkin Yara akan iyayensu, wannan al'amarin ya tab'a zuciyar kowa na jikin Mamman Ba'are musamman Hajiya Nana wacce idan taji yana cewa Majid ba zaka zo ba, Majid kana ina ne? Majid zan mutu ban ga fuskarka ba. Majid nasan na cuce ka, Majid kazo. Shi yasa bayan kome da ya warewa Majid, akwai wasu takardun da ya bawa abokinshi. Wanda babu wanda ya sani daga Hajiya sai Abokinshi Alhaji Abubakar Abzin, shima shahararren dan kasuwa ne da yake garin marad'i, kuma wani ikon Allah Alhaji Abubakar Abzin bai tab'a takowa zuwa Niamey ba, idan abubuwa suka shiga gaban Hajiya wurinshi take zuwa. Yanzu ma tunaninta kafin hutun Majid ya ƙare zata kai shi garin marad'i, su gana.
Wannan shine shirinta.
Sai da Majid ya jira Amaan ya shiga dakin, sannan shima ya shiga ya mikawa Hajiya kudin tare da mata magana da idanu, ta bawa Nabeeha. "Barka Hammayo." Inji Salaha matar Amaan, "Barka!" Ya fada a hankali, idan baka saka kunne ba, ba zaka ji me yace ba. Shigowar yara uku suna ihu, yasa shi juyawa. Sai wani guda daya da yake bakin kofar shiga falon Hajiya. "Appa kaga Shuraim ya dake mu ko?" Yaran suka nufi wurin Amaan, mikewa Amaan yayi tare da nufar Shuraim ɗin. Shima Aryan har zai mike Majid ya kalle shi, a fusace ya koma ya zauna yana kwafa. "Kai wato munafurcin da ka gada daga wurin wancan dan iskan Yaron shine zaka fara." Ya rike kunnen Yaron. Amadadin yaron ya fasa ihu, sai ga Amaan yana fasa ihu, babu wanda ya san me ya faru, sai yaron ne kawai ya san me ya faru. Daukarshi Majid yayi suka fita. "Daada taka mishi kafa kayi ko?" Ya rad'a mishi a kunne. "A'a" "Daada Allah yana kona me karya inji Ummina." Dakinshi ya shiga da shi, ya Ciro katon kwalin chocolate, ya mika mishi sannan ya kara dauko dayar ya ce mishi. "muje!" Haka ya riko hannunshi har falon Hajiya suka koma, zama yayi ya kira sauran Yaran, Yaran Amaan dake duk mata ne, tasowa suka yi duk da harara su da Amaan yake, haka suka tawo wurin Majid ya ajiye su a gefensu. Sannna ya mikawa yar karamar yar Aryan hannu da sauri ta taso. Ya ajiye ta" Kai Ayyan ka sammata a naka, Anum da Widad zan basu anan."
"A baco na Yaya!" Injin yarinyar. "Bushrah!" Babanta ya daka mata tsawa. D'ago kai Majid yayi ya watsa mishi harara. "Tow shi kenan tunda baki son na Yaya Anum a san mata?" Gyada kai tayi, ya bude musu kwalin ya ciro chocolate din ta ce mishi. "Dada a bacon na Anunu." Ta maida hannunta baya. Hajiya kuwa me zata yi ban da dariya ta ce mishi. " Ai yadda ka bawa sa'anta kwali itama haka zaka dauko mata kwali domin bata yarda a raba kansu da yan uwanta."
"Uwata taso muje." Ya dauki su Anum ya zaunar dasu a saman kujerar ya dauki Bushrah har dakinshi ya dauko mata nata, tun da ya bata, ta fara bashi labarin da Allah ya gani bai fahimci Yaren ba, har suka isa falon, bashi labarin take.
"Ja'ira mara kunya, dole ki bashi labari anya takwara haka zamu yi dake."
"Jiya babu luwana dake, ban baki cokulet dina ba " ta zauna ta yaga kwalin. Ya zube dukka. "Dada ashe min!" Wato ya kwashe mata, "abawa jiya." Ai kuwa Hajiya ta wafta ta ce. "Sai dai kada abawa gobe, amma jiya kan zan sha."
Haka aka yi ta hira har wani lokaci kafin lokacin magariba tayi duk suka tashi zuwa Masallaci..
*Sansanin gudun hijira*
300₦
#thedambuje