KUDRAT

C

by @kwalisa

Sosai suka Sha fira sannan ta kashe wayar ta kwanta ba ita ta farka ba sai wajen sallah asuba ta farka sai da ta Yi, wanka sannan ta daura alawa dan zumudi sai da tafara shiryawa tsaf da Ita sannan ta yi sallah tana kammallawa ta zauna zaman jiransa wajen karfe 7h30 ya kira ta yana waje cike da farinciki ta mike ta kara yin wanken turare sannan ta fito Mummy ta tarar a waje nan ta gaida Ita cikin rashin son fitar ta ce'' Kudrat har kin shirya ne?"

E'ee yana kofa yanzun ya kirani.''

Tom dan Allah badan ni ba duk inda zaki kasance karki yarda da namiji ya yi maki dadin baki da sunnan yana bukatarki ki rike darajarki da kimarki ki kama kanki da mutumcinki karki yarda karatun iskancinsa ya yi, tasiri kanki .''

Insha Allah Mummy bazan taba baki kunya ba .''

A dawo lafiya ta yi, mata Ita kuma ta fice tana fita ya mata alama da ta shigo ciki Babu musu ta shiga hanya duka sun yi tafiya mai nisan gaske sannan suka iso wani katon gidan gonarsa nan ya yi parking waje ya fito kai tsaye ciki ya shiga ya jima sosai sannan ya fito ya yi, mata iso amma taki fitowa daga motar zagayowa ya yi, inda take ya bude marfin ya ce'' Allah Amarya ta Idan baki fito ba Allah daukarki zan yi.''Jin abin da ya furta'' ya kara tsoratar da ita hakan ya sa cikin sanyin jiki tafito da kyar take daga kafa kamar wacce kwai ya fashe ma a jiki tafiya suka dan yi kafin su iso wata yar karamar rumfa irin ta shakatawa fleurs zagaye da wajen sanyin da ya ziyarce ta ne ya sakata lumshe idanu tsabar ratsa wajen da aka yi ya yi,matikar burge ta ga jeu da lumi猫re sai aiki suke ganin ta yi, tsaye ya saka shi kama hannunta suka karisa ciki day daga cikin kujerun dake wajen ya yi, mata masauki sannan shima ya zauna wacce take fuskantarta ya kama hannunta day yana massage din sa a hankali ya ce''........''

Hannun ta da ya kama yana massage din sa a hankali ya ce'' bana kawo ki nan dan na lalata maki rayuwa ba Kudrat na kawo ki nan dan muyi fira ta fahimta ki natsu kisan ma'anarta Kudrat tun daga ranar da Allah ya sa na daura idanuna kanki naji sonki ya darsarmin a zuciya hakan ya sa nake kula da ke saboda karki kulla wani saurayi ni dai ina da mata da yara uku Kuma ina da babban dalili wanda ya sa nake nemanki da aure dan Allah ki taimaka ki bani dukan wata kulawa saboda na rage zafin radadin da nake dauka a ko wace rana.''

Tom ina matarka?" da kake son nina baka kulawa .''

Kedai ina da dalili Kuma nasan zaki sanshi nan bada jimawa wata kila ranar ba zata yi mana amfani ba .''

Har zata yi magana ya daura yatsansa saman lips din ta ya ce'' banison tambaya amarya ta .''

Murmushi kawai ta yi, shi Kuma ya dauko pomme din dake ajiye ya bata a baki da kamar ba zaka karba Kuma sai ta amsa haka ya din ga jubga mata fruit har sai da ta koshi sannan ya kira mai gadi nan ya bada umarni ayi masa leda uku ta fruit Babu musu ya tafi tsaye ya mike tare da zagayowa inda take ya tara mata hannu ta daura kan nashi ya mikar da ita tare da rumgume ta a jikinsa sannan ya kai bakinsa dai dai kunnanta ya ce'' I love you so much amarya ta pls give me your lips .''

Babu musu ya dago da kanta shi Kuma ya karfe Bakinta nan ya shiga kissing din ta ya dauki 15mnt sannan ya janye bakinsa suka hada ido tare da sakarma juna murmushi '' nan mai gadi ya yi,masu sallama ya tafi ya karfi ledar sannan suka yi Shirin tafiya sai da suka wuce office ya kammalla abin da zai yi zuwa yamma liss suka baro wajen sai da ya biya da Ita ya siya mata ice cream da chocolate sannan suka kama hanya a kofar gidansu ya sauke ta nan ya mika mata fruit din Leda biyu sai da cr猫me din sannan suka yi sallama ta shige gida shima ya yi tafiyarsa yana ji duk rabin damuwarsa ta tafi ''Da sallama ta shigo gidan Mummy na ganinta ta sauke ajiyar zuciya ta ce'' Kudrat har kin dawo ?"

E'ee Mummy wallahi duk na gaji sosai aikin office ba wasa ba kin ga Alhaji ya ce nima zai dauke ni aiki mu din ga tafiya tare .''

Tun da Kudrat ta shigo Mummy ke kare mata kallo ganin babu abin da take tunani ya sa ta biye mata suka fara taba fira Abba da shigowarsa kenan da wani masifar gudu ya shigo kamar wanda aka koro ya damki ledar ya ce'' sannu da zuwa yar Albarka har kin dawo wace tsaraba kika kawo min ne.''

Sai da ta tsoro hannunta dafe da kirji ta ce'' ba komai Abba kawai fruit ne sai da muka biya sayan Ice cream .''Amma dai Malam anyi abin kunya gaskiya ka din ga rike girmanka.''

Nabi girman ba wando ina ruwanki ina magana da yarinya ta zaki sakamana baki .''Ganin haka ya sa Kudrat mikewa ta shige daki tana takaicin hali Irin na Mahaifinta .''





















WASHEGARI 

Kamar kullum sai da ta yi, wanka ta shirya ta yi sallah lokacin da Alhaji ya zo jiya yazo ya dauke ta suka tafi gidan gonarsa kamar kullum a gyare yake sai kamshi da yake fitarwa suna shiga kujerar da ta zauna ya zauna saman cinyoyinsa ya kama Bakinta sai da ya gama tsotse sa sannan ya dawo da idanunsa ya Sauke cikin nata ya ce'' jiya nayi missing din ki amarya ta ina jin dadin a duk lokacin da muke a tare .''

Wai ni Kam Haske na in tambaye ka ?"

Yess zaki iya tambaya ta amarya ta kuma insha Allah zan Baki amsa .''

Me ya sa kake son Sha min baki ne ?"

Saboda ina son haka kissing yana masifar birgeni a rayuwa ta dan yanda na damu da shi ko sex banaso haka.''

Sai da ta Kuma kura masa idanunta masu haske da sheki da kashe zuciyar masoyi ta ce'' me ya sa ba zaka tafi wajen matarka kayi mata hakan ba ?"

Amarya ta ko aikin jarida kika fara bansani ba hmm matata bata bukatar hakan koda na nufe ta zata ce bataso.''Ina aikin jarida ne bisa abin da nake so a rayuwa ta tom ka tambaye ta dalilin da yasa Bata so.''

E'ee ce min tayi bataso dan bata iya ba .''Har zata yi magana ya ce'' banason bincike insha Allahu idan mun yi aure zaki fahimci duk abin da kike son sani a kanta.''

Tom shikenan haskena na daina.''

Amarya ta ina son gobe insha Allah na taci wajen Abba muyi maganar aurenmu dan gaskiya na matsu na mallake ki tun kafin na bar maku garinku.''

Garinmu Kuma ka tafi ina Haske na.''Kwaida maganar ya yi ta hanyar cewa amincewarki nake nema kin ga cikin satin nan musha bikin aurenmu ko.''

Kanta ta tusa cikin kirjinsa tsabar kunya sai murmushi da take saki ta ce'' Babu abin da nake buri na kasance da shi a inuwa day da shi sai kai haske na ina masifar sonka ni kaina bansan adadinsa ba bare har fatar bakina ta isar da sakon da nake fada .''

Hannayensa ya saka tare da kara matse ta a jikinsa ya ce'' dagaske kina sona Amarya ta kuma zaki kasance ni har abada ki kula dani da dukan soyayyar da nake bukata a gare ki .''

Insha Allah indai muna tare ba zaka taba maraicin farinciki ba zan yi iyakacin kokarina ganin na wanzar da shi a fuskarka ka kasance cikin Jin Dadi .''

Abin break din da ya tawo da shine suka fara ci suna fira har suka kammalla suka sha zamansu sai da suka gama shan love dinsu Sannan suka fito zuwa office .''

Tun daga wanan ranar kullum sai Alhaji yazo daukar Kudrat saboda aiki da ya sama mata a ma'aikatarsa sai lokacin da suka so firansu su tafi gidan gonarsa sosai magana ta yi, zurfi dan manya sun shiga lamarinsu duk da day bangaren hankalinsa a tashe yake a gidansa amma a duk sanda suka hadu da Kudrat takan wanke masa zuciya ya dawo farinciki ranar da bazan taba mancewa a rayuwa ta saboda ita ce mafarin tabon da ya lake mata a zuciya farinciki ya dauke daga kan fuskarta ranar da Alhaji Hafiz ya zo gidansu tana fitowa suka gaisa ya ce'' Kudrat ina son magana dake idan ba damuwa .''Ba damuwa zamu iya yi.''

Ki bani lokaci mu tafi gidan gona zamu fi Jin dadin firan.''

Babu musu ta amince suka tafi tsan suna isowa ya zauna tare da janyota ya daura ta kan day cinyarsa ta sunkuyar da kai shi Kuma ya dan sunkuya yana kallonta cikin tsananin rudi da tashin hankali ya ce'' Kudrat !! Kala yanda ya ambaci sunnanta ya daki zuciyarta take gabanta ya fara dukan tara tara Sannan ya ci gaba da fadin'' amarya ta tafiya zan yi gashi burinmu bai cika ba bare na gani kalar farincikin da zaki bani .''

Idanunta da suka kawo ruwa ta zuba masa dan a halin yanzu yanda take ji ba zata taba rabuwa ko tsawon 1mnt ba tare da suna tare da a hankali ta furta'' ina zaka tafi haskena.''

Zan yi tafiyar da babu ranar dawowa Amma ki sani a duk inda nake ko zan kasance kina cikin zuciya ta Sannan idan kin tuna dani ki man fatan alkairi ki kasance cikin farinciki Abar kauna ta.''

Haske na gaskiya a yanda nake ji a halin yanzu bazan iya bari ka tafi ka barni ba bazan iya jurar rashinka a kusa dani ba ka tafi dani duk inda zaka tafi haske na karka horana ta hanyar yin nesa dani .''

Badan son raina zan tafi ba karki damu gobe Idan an daura aure daga baya zan turo maku da visa keda uwar gida kuzo tare kin ji ni dai abin da nake so gare ki shine kice kina sona .''

Shiru ta yi, masa shi kuma ya dago da fuskarta ya hade bakinsu yau da wani sabon salon kissing ya zo mata dan har breast din ta sai da ya yi wasa da su cike da tausaya ma Kansa ya dago da idanunsa da suka cika da hawaye kawai ya fashe mata da kuka kamar wani karamin yaro sosai ya kara karya mata zuciya ta ce'' haske na ina zaka tafi ka barni cikin damuwa .''

Bani ne nake son tafiya ba dole ce tasa hakan ki tayani da addu'a kawai a duk halin da zan kasance ya zamar min mai sauki ne .''

Haka ya din ga yi mata sambatu marasa kan gado wunin ranar a gidan gona suna kare sa sai kusan mangariba Sannan ya dauko ta ya maido gida duk ransu a jagule bude marfin motar ta yi, ta fito har ta kai kofar gidansu ta jiyo da karfi ta nufo sa da gudu ta bude inda yake zaune ta fada jikinsa ta shiga raira masa kuka shima hawayen da yake dannewa ba suka fara gangarowa ya daura hannunsa kan saman kanta yana shafawa ta ce'' idan ka tafi kayi alkawarin zaka turo mana da visa haske na.''

Tom zan turo idan lokacinku ya yi, na tafiya zamu hade da juna karki damu yanzu zan tafi ne saboda koda na tafi da ku ba zan baku lokacina ba Kuma banison ranku ya yi ta baci a kaina .''

Haske na zan zauna indai a kusanka ne nasan ko baka bani lokacinka ba zan din ga ganinka cikin koshin lafiya kuma zan ji dadi hakan.''

Dan dago da fuskanta ya yi, ya ce'' kina son na kasance cikin farinciki amarya ta.''Jinjina masa kai ta Yi, ya ce'' tom ki man fatan alkairi Sannan koda wane lokaci ki din ga tunawa dani a cikin sallah ki ki man addu'a zan ji dadi inda kin tuna dani ki saki kyawatacen murmushi ki tuna Kalmar ina sonki amarya ta zaki ji natsuwa da kauna ta suna kara shigarki .''

Ajiyar zuciya ta sauke abin da bata taba yi ba yau sai gashi da kanta ta hade bakinsu ta bashi hadin kai wajen maida martani sosai yaji dadin haka sun dan jima kadan Sannan ta janye bakinta ta ce'' ina sonka ! Ina sonka ! Ina sonka haske na Idan ka tafi kenan ai zaka din ga kirana ko.''

Kalmar dana jima ina son naji ta daga bakinki a dai dai lokacin da bana tunanin zaka yi mana amfani kika furta min ita amma naji dadi Kuma zan dinga alfahari da hakan a duk sanda na tuna da hakan zan yi kokari idan na shiga garin na kira ki amarya ta.''

Mikewa ta yi, daga zaunan da take a jikinsa ta dube sa sosai yanda ya kara baki mai kyau da daukar hankali fuskarsa har wani sheki take kamar wanda ya yi gyara jiki muryansa ta kara dadi sosai murmushinsa shi kansa abin sone murmushi mai ciwo tayi, sannan ta ce'' Haske na sai watarana .''

Tana gama fadan haka ya shige gida a guje cike da sanyi haka ya fara jan motar da karfin hali ya bar kofar gidansu .''

Tana shigowa ta fada jikin Mummy dake nemanta ta rasa inda tatafi ,ganin yarta cikin wani hali ya Saka ta furta'' na shiga uku Kudrat ina kika tafi ne? Kuma lafiya kika shigo gida kina kuka.''

Mummy shine rayuwa ta tazo karshe zan rasa farin cikina a kusa dani Mummyna me yasa sai a lokacin da nake jin shine mahadin numfashina tafiya zata zo masa dan Allah kice masa ya tafi tare da ni karya tafi ya barni .''

Ganin inda maganarta ta dosa ya sa Mummy janyota jikinta ta ce'' Kudrat hakuri zaki Alhaji Hafiz insha Allah naki ne dama nasan za'ayi hakan shi yasa koda Abbanki yazo min da maganar nace shi Alhaji ya Sanar dake ki dauki dangana da hakuri duk hakan zai zama labari................''


**

Ruwa masu matikar sanyin da aka watsa mata ne ya sakata dawowa daga duniyar tunanin da take firgigite ta kara matsewa jikin bango dan yanzu kam gani take karshenta ne yazo saboda Ajmal ya rikice baya da hankali bare digon Imani tsawar da ya daka mata ce ya Sakata dawowa dai dai saboda mugun tsoronsa da ya shige ta shi kuma ya ce'' wace shegiya ce tazo min gida?"Kayi hakuri ba zata kuma zuwa ba kuskure ne pls kayi hakuri karka kasheni dan Allah.'''

Abin matse kaya Idan an shanya ya dauko tare da matsa mata shi a ciki da mugun karfi ta fasa kara tana rufe idanu tsabar azaba ta ce'' dan Allah ka cire min da zafi yau kwana na uku babu komai a cikina ina bukatar ruwa makoshina ya bushe dan Allah Idan nasha sai kayi man duk abin da kake so.''

Yana jin haka ya nufi kofa fita jim kadan ya dawo dauke da plate a hannunsa da ruwa daura mata shi gabanta har zata matso ya dauki abincin ya zubar a kasa ruwan ma ya tarare mata a jiki haka take tara bakinta har yan kadan suka shiga tana kuka haka take kallon wanan ruwan a jikinta gasu da mugu mugun sanyi jikinta har rawan sanyi yake shi kuma ya kece da dariya ya ce'' gobe ma na sake ganin wata yar iska gidana zaki ga abin da zai faru .''

Zuwa yanzu Kudrat ganinta kawai yake amma bata Jin sa saboda jikinta da ya dauki zazafi sai rawan sanyi yake duk ta fita hayacinta shi Kuma ya ci gaba da fadin'' ni yau tafiya zan yi, yau din nan Sannan na kuskura na gani wata a gidan nan sai ranki ya yi mugun baci .''

Bata ce da shi komai ba sai kallo da take binsa da shi hannayenta ya kwance mata Sannan ya dauki jakarsa ya fice tare da yi ma dakin key ,tana ganin fitarsa tsabar hannayenta sun yi sanyi dan bata iya motsin kirki da su haka ta kwanta rufda ciki ta din ga cin abincin a haka tana matsar kwalla sai da taji cikinta ya dauka Sannan baccin wahala ya yi, gaba da ita sai da ta yi,kusan sati rabonta da shi ga jikinta ya kara tsananta ta yanke shawaran kiran Fareeha ta labarta mata cike da dakiya Fareeha ta zo gidan kai tsaye ciki ta shiga tafara duduba dakin da Kudrat take tana shiga cikin tashin hankali ta karisa wajenta tare da nufa wandrof ta dauko mata kaya tare da sakamata ta rumgume wasu zafafan hawaye suka zubo mata ta ce'' kudrat kece kika koma haka innalillahi gaskiya akwaye matsala bara na kira Mummy.''

Da sauri Kudrat ta rike mata hannu tana girgiza mata kai alamar A'aa duk yanda Fareeha taso kiransu amma fa firr Kudrat taki yarda hakan ya sa ta dauke ta suka tafi asubiti suna isowa ganin halinda take ciki na neman taimako ya sa aka karfe ta cikin gaggawa suka shiga da ita ciki doctor sun jima a dakin kafin ya fito Fareeha ta bi bayansa suna shiga ya rufe da masifar fada ta inda yake shiga batanan yake fita ba sai da ya dasa aya sannan ta ce'' kayi hakuri doctor me yake damunta .''

Mtsss kuna shirin kashe yar mutane shine kike son sanin abin da yake damunta tom yarinyar tana dauke da ciki wata uku amma na bayan mahaifane yanzu dole za'a cire mata shi kuma kasanta ya bude kwarai dan sai ta samu dumkin ciki da waje Idan ba haka ba zata hadu da matsala wajen har yoyan fitsari zai iya kamata ga ciwon zuciya da take dauke da shi gaskiya an cutar da yarinyar nan sosai .''

Da sauri ta dafe kirjinta ta ce'' innalillahi wa inna'ilaihin raji'un doctor duk Kudrat ce take dauke da wanan matsalolin wa'iyazubillahi Amma wanan mutuman anyi bakin mugu azzalumi.''

Doctor yanzu menene abin yi dan Allah kar mu rasa ta ?"

Aiki zamu yi dan ceto ranta sannan dole sai an bata kulawa ta musanman tun da har opration da dinkin Hq sai ta samu sannan a kula da maganinta na ciwon zuciyar.''Ba damuwa doctor Dan Allah ayi mana .''

Miko mata wata farar takarda ya yi, ta karfa tare da cikewa nan ta wuce wajen biyan kudi ta bada kudaden take aka shigar da ita dakin da za'ayi mata aiki nan Fareeha take zaune har Allah ya sa suka fito da ita mikewa ta yi,ta sha gaban doctor ta ce'' ya ake ciki doctor ?"

Normal mun kammalla aikinmu lafiya saura naku dan Allah a kula da ita sosai saboda yarinyar tana Shan wahala kiga yanayin fatarta duk a farfashe ga tabon ciwo wani saman wani harta fuskarta duk tabon ciwo ne aiko bayu ba zasu samu irin wanan wulakancin ba .''

Ayi hakuri doctor insha Allah zamu kara kiyayewa zan iya ganinta .''

E'ee tana dakin wutu sai de kar a takura mata da hayaniya saboda tana bukatar wutu ga alluran da muka yi mata na barci Kuma .''

Yana gama fadan haka ta Yi, masa godiya ta wuce tsaf ta karema Kudrat kallo sam kaminta duk sun sauya saboda kumbrin da fuskarta ta yi, duk fuskar a gurje sai kace wacce wuta ta kone ta yi, baki sosai ta rame ta kanjame abar tausayi sosai Fareeha tasha kuka har ta gode ma Allah .''

Haka Fareeha take kula da ita har suka yi sati a asubiti nan aka sallama su suka koma gida nan ta ci gaba da kula da ita hakan ya sa natsuwarta da kuzarinta suka dawo domin yanzu Babu abin da take yi sai zama ta wuta dumkin Hq din ta ya warke sosai sauran op茅ration din kawai ya rage kuma shima saura kadan ya karisa warkewa haka suke rayuwarsu cikin farinciki har sai da suka yi sati biyu suna tsaka da fira suka ji shigowar mota Idan hankalinsu yafi dubu duk ya watse nan ta boye Fareeha bayan labule a lokacin ya shigo da sallama a bakinsa .''

Cikin rashin natsuwa gabanta har dukan tara tara yake ta amsa ta ce'' sannu da dawowa .''

Maimakon ya amsa ya ce'' keda uwar wace a gidan nan sannan wanene ya kwance ki.''

Wayun wahala ta hadiya take idanunta suka kawo ruwa tayi daki da gudu tana bashi hakuri,bayanta yabi da sauri kafin ya karisa shigowa Fareeha ta falfala da gudun bala'i ta bar gidan bayanta ya bi amma har ta shige mota ta gudu ,kwafa ya yi, ya ce'' yar banza da kin tsaya wallahi sai na ci uwarki .''

Yana gama fadan haka ya shige dakin da dake nan ya hau dukanta kamar an Aiko shi har ball ya yi, da ita saitin fashin (op茅ration) da aka yi mata wata gigitaciyar kara tafasa dukanta yake kamar wanda ya samu wata jaka yana gama dukanta ya fita ya kwashe dukannin abincin gidan ya fitar da shi daga gidan Sannan ya kashe wutar gidan baki day gashi ya kulle ta a daki ya sa kai ya bar gidan baki day dama an kuma tura su mission ya biyo daukar abu ne kuma ya tattara ya bar kasar baki day .''

KUDRAT kuwa duk a tunaninta wuta yan nepa duka dauke tana nan kwance da kyar take tashi tayi sallah wunin ranar babu komai a cikinta sai ruwa mikewa ta yi ta dawo kan bed ta kwanta kanta na kallon plafond tana zubar da hawaye Sannan ta koma duniyar tunaninta .''

**********

Sosai Mummy take rarashin kudrat har ta samu ta yi,shiru da kyar ta samu ta tsakura abinci ta ci kadan tun da ta shiga daki bata fito ba.''

Tun da sasafe tana gama sallah ta shirya tana jiran kiran Alhaji amma shiru kuma Idan ta kira sa wayarsa a kashe hakan ya yi, mugun taga mata hankali fitowa ta yi, ba tare da sanin kowa ba ta shiga neman Alhaji duk inda tasan zata same sa amma shiru haka ta din ga zarya gidan gonarsa ta wuni tana jiransa shiru office din sa ma haka sai da tayi tsawon sati tana jigilar nemansa amma bata samunsa haka ta dawo gida ta zauna kullum kuka duk ta rame batason cin abinci Mummy ta yi fadan har ta gaji watarana tana zaune ta yi nisa cikin tunaninta ta tuna da inda suka fara haduwa da sauri ta mike tsaye kamar wacce aka tsikara da allura ta fito Mummy na magana amma ta yi mata banza tana fitowa kai tsaye wajen da suka fara haduwa ta nufi da kafafu ta tafi kamar yanda duk yawon da ta Yi,tsawon satin da suka wuce a kawa ta yi su gashi wajen da mugun nisa cikin ikon Allah ta iso wajen lokacin duk suna za zaune tana ganin Alhaji Bashir babban aminsa ta fashe da kuka da sauri ya mike ya nufo inda take cike da tashin hankali ya ce'' Kudrat lafiya kike kuka? Me ya faru ne ?"

Ina Haske na? Ina ya tafi ya barni cikin wahalaliyar soyayyarsa ya san zai gujeni ya barni na fada cikin tafkin so dan Allah ka fadin ya min adalci kenan shi kuma haka kalar ta shi soyayyar take .''

Fizgar da iska ya yi, ya ce'' mu tafi mota na kai ki inda zaki same sa Sannan nayi maki bayani.''Tafiya ya fara yi tabi bayansa har suka iso bakin motar ta bude ta shiga shima hakan nan ya yi,ma mota key suna cikin tafiya ya ce'' Kudrat a rayuwa Alhaji Hafiz babu wata mace da ya taba gani ko ya furta Kalmar yana sonta da bakinsa bayan ke yana matikar sonki kuma yana burin ki zama mallakinsa amma sai de kaddara ta riga fata dole ku rumgume hakuri daga shi har ke.''Bangane me hakan yake nufi ba ?"

Alhaji Hafiz yana da ciwon zuciya mai mugun tsanani Kuma ba kowa bace mafarin hakan illa matarsa bata da kirki ko kadan sannan bata ki ta kashe sa ba saboda haushinsa da take ji shi Kuma Mahaifinta ya bashi amanarta lokacin da zai mutu saboda ya toshe duk wata faraka da take son aikatawa saboda bata jin magana ko kadan tun yana boye damuwarsa har ta fito Fili tun da ya lura kece farincikinsa hakan ya sa yake zama tare da ke amma kina sake matarsa tana maki warwara domin yana tunkarar gidan zai hadu da tashin hankali da masifu kala daban daban tafiyar da ya yi sati day da suka wuce ya tafi asubiti ne da iPhone kula da lafiyarsa amma ciwon ya yi tsananin na ban mamaki yanzu haka yana gida an sallamo sa da asubiti amma abin ba sauki sai wajen Allah .''

A dai dai nan suka iso gidan yana gama parking suka fito kai tsaye bangaren Alhaji Hafiz suka nufa da sallama suka shiga tana ganinsa gashi a kwance idanunsa kawai ke motsi a jikinsa ba tare da ta kula da kowa ba ta fada jikinsa ta kankame sa ta fashe da kuka, hannunsa ya daura saman kanta yana shafawa cikin kuka ta ce'' Haske me kake yi haka?" Me kake shirin aikatawa ne ?" Kana tunanin hakan da kayi shine masalaha a gareni ka guje ka tafi ka barni me ya sa baka fadamin halin da kake ciki ba amma ka zafi ka boye min so kake ka mutu ka barni cikin tashin hankali dama irin wanan tafiyar ce kake tunanin kayi me ya sa zaka yi min haka.''Cikin wata zazakar murya ya ce'' amarya ta yanzu miye amfanin fadamaki dubi duk yanda kika tashi hankalinki banason saka ki cikin damuwa .''

Kenan kaso kawai naji labari marar dadi haske dan Allah karka min haka karka datse alakar dake tsakaninmu tun yanzu kazo mu rayuwa da juna nayi maka alkawarin zan kula da kai bazan barka ka kuka ba pls dan Allah ka tashi mu tafi lambun soyayyarmu Haske .''

Hawayen da yake boyewa ne suka gangaro masa ya ce''lokaci ya kure mana Amarya dan Allah kice kina sona sannan a ko wane hali zan kasance cikin zuciyarki sannan najin dadin ganinki domin idanuna sun yi missing kyakyawar fuskarki ba dama bare na tafi ganinki kunuwana sun yi kewar muryanki amma yanzu alhamdulilah zan ji dadi tun da gani a tare da ke ina sonki ki kula min da kanki sannan ki kasance cikin farinciki Abar kauna ta sai watarana.''

Cikin kuka mai tafiyar da zuciyar mai saurare ta ce'' Ina sonka ! Ina sonka! Ina sonka Haske dan Allah karka tafi ka barni ina da bukatarka a kusa gareni karka min haka .''

Jin hannunsa ya sauka daga kanta ya sakata dagowa da sauri tana kallonsa ganin ba ita yake kallo ba ya saka ta girgiza shi tana kiransa amma shiru wata uwar kara ta fasa ta ce'' innalillahi ya zaka yi man haka dan Allah ka tashi kace masu bacci kake karsu rabani da kai haske na taya zan kasance cikin farinciki bayan baka kusa na ka tashi karka tafi ka barni haske na gani nice kudrat din ka wacce kake ma lakani da amaryanka ka tashi a domin mu cika burinmu bani bukatar sai watarananka Haske na.''

Duk wanda yake dakin hawaye ne ke tsiyaya daga idanunsa tsabar tausayin kudrat ganin tana ta sambatu marasa kan gado ya saka Yayar Alhaji da kanwarsa suka kamata amma tana zillewa tana fadamawa jikinsa da kyar Alhaji Bashir da sayyad babban yaya gidansu Alhaji Hafiz suka kamata suka fita da ita waje nan Alhaji Bashir ya shiga motar ya jata zuwa gida haka suka dawo nan aka dauki gawar Alhaji Hafiz aka suturta aka kaishi gidansa na gaskiya wanda duk me rai sai ya dandana zafin mutuwa.''

Suna isowa gidan ya fito da ita cikin rarashi suka shigo gidan jikin Mummy ta fada taci gaba da kukanta tana fadin'' Mummy shikenan rabuwarmu ta har abada ta zo Alhaji ya tafi ya barni bazan sake ganinsa ko jin muryansa ba Mummy ki taimaka ki tasheni daga baccin da nake kuce min ba gaskiya bane mafarki ne Mummy .''Sosai suke rarashinta hade da nasiha har ta hakura ta daina kuka Alhaji Bashir ya yi tafiyarsa suna nan zaune ita da Mummy zazafi mai mugun zafi ya kamata nan Mummy ta bata Koko tasha kadan ta bata magani amma maimakon zazafin ya rage sai ma karuwa da ya yi, nan Mummy ta kira Abba suka wuce asubiti sai da ta yi, kwana uku batasan inda kanta yake ba ranar da ta bude idanu ta ce'' Mummyna !! Haske na baizo ya duba ni ba ?"

Kudrat ki dauki hakuri da dangana ki karfe kaddara da Allah ya daura maki Alhaji Hafiz yanzu babu shi ki taya sa da addu'a ya samu ya yi kwancinsa cikin sallama soyayyar da zaki nuna masa ita ce addu'a dukan mai rai sai ya dandana zafin mutuwa ki daure.''

Sosai Mummy ta yi mata nasiha mai ratsa zuciya tana zubar da hawaye haka ta shawo kan yarinyarta dan hakuri ta yi, amma tun daga wanan lokacin ta daura aure da damuwa bata sauraran ko wane saurayi ganin zaman ba dadi ya sakata komawa makarantar islamiya a nan ne suka hadu da su Fareeha da Nawal suka samu shakuwa sosai har suka san rayuwarta ta baya sun tausaya mata sosai duk da halinsu ya sha Banban da juna musanman Nawal dake da son kwadiya da buri dan ko saurayi bata kulawa indai baya da kudi ,Fareeha da kudrat kuwa babu ruwansu da wanan burinsu kawai su samu miji na gari .''

Bayan rasuwar Alhaji da wasu yan watanni Kaninsa ya zo gidansu kudrat ya sa aka yi masa sallama da Abba yana fitowa suka gaisa ya ce'' dama maganar gidan nan ne ke tafe dani dama Alhaji Hafiz ya fadamaka ba gidansa bane na gado ne dan haka ina son ka tattara ka bar gidan nan saboda zamu yi rabonsa .''

Dadam dam gaban Abba ya buga ya ce'' yanzu yaro inda mun bar nan ina zamu tafi dan Allah kayi hakuri ku barmu mu zauna muci gaba da biyan kudin haya dan girman Allah .''

Tom Naji dama zafi biyu nazo maka shi Idan ka amince gidan nan zai zama naka .''

Ina jinka yaro fadi ina ji.''Naga kana da yarinya a gidan nan ko.?"

E'ee Alhaji wani abin tayi.''

A'aa zan hada ta da yarona da yake tsan kasashen waje yana karatun aikin soja sannan mun dauke maku komai idan ka amince shikenan zan bar maka wanan gidan saboda dama ni za'a mallaka ma shi.''

Washe baki ya yi, ya ce'' wanan ai ba komai bane Alhaji amma gaskiya zaka bani wani abun saboda kyautar yarinya da gida musanman kyakyawar yarinya kamar Kudrat kaga ai ba karamar kadara bace .''Tom zan daura maka da 10million sannan mun dauke maka kayan daki da duk abin da kasan nauyi ne a kanka kawai amarya zaku wanke a kai ma yarona sannan Babu ruwanka da lamarin yara a barsu su shana suci soyayyarsu .''

Jikinsa na rawa ya ce'' na amince amma ka bani takardun gidan da kudin na rike a hannuna tare da shedu gudun karta je ta dawo .''Duk wanan ba matsala bace yanzu ga kudin zuwa gobe zan zo da shedu take a daura auren .''Wani tsalen dadi ya buga ya ce'' ba damuwa Allah ya nuna mana goben lafiya .''

Sallama suka yi ya yi tafiyarsa shi kuma ya shige gida ko zama bai karisa yi ba ya fara bama Mummy labari da sauri ta mike tsaye ta ce'' Malam gaskiya ba wanan maganar a janye ta haka kawai saboda kwadayi da son abin duniya zai sa ka sayar min da yarinya tom ai ba sasakota aka yi daga ice ba macece kamar kowa idan aure yake son hadawa da yaronsa me ya sa ba zai turo sa yazo ya ga yarinyar ba kawai dan kaja mana tozarci da kaskanci wajen yaron nan.''

Shima tsaye ya mike ya ce'' idan akwaye uban da ya isa gani dan iska billahil'azim koki yarda ko akasin haka sai na aurar da yarinyar nan saboda diya ta ko daga gidanku kika zo da ita ne kuma kije ki bata sako ta zamana cikin shirin gobe idan an daura aure zata tare nan da sati day idan baki Sanar da ita ba naki auren ne zai lalace ba nata ba .''

Yana gama fadan haka ya shige daki ya bar Mummy sake da baki tana mamakinsa  

Jiki ba kwari Mummy ta fara daga kafafunta ta nufi dakin Kudrat dake kwance tayi lumtsudum cikin tunanin a hankali Mummy ta zauna kusa da ita ta ce'' kudrat magana nazo muyi ki tsaya ki natsu ki fuskanci inda ta magana ta ta dosa Kudrat Abbanki ya bada ke insha Allah zuwa gobe za'a daura aurenki da wani soja Kuma cikin sati mai zuwa zaki tare.''

Kamar an kwada mata guduma haka taji kanta ya yi,wata iriyar sarawa zuciyarta tafara lugude kamar zata faso kirjinta ta fito ta ce'' Mummy aure Kuma ? Waye zai aureni ? Gaskiya Mummy bani sonshi kuma bazan iya zama da shi a matsayin mijina ba Mummy musali Koda na amince wane zama kike tunanin zamu yi bansan shi ba haka zalika shima baisan ya kammanina yake ba yanzu auren yanzu akwaye soyayya da fahimantar juna ya aka kaya bare Kuma ni duk ban hada su a nawa auren ba Mummy ki fadama Abba dan Allah karya min wanan auren na yi alkawarin zan kawo wanda zan aura.''Har Mummy zata yi, magana suka ji shigowar Abba yana fadin''idan kin iska shege nake kaji man rashin kunya ni zaki bama kunya a bainar jama'a kudrat tom bara kiji nine na haifeki ba kece kika haifeni ba idan kuma kece uban tom kiyi man musu kuma ki sani aure sai an daura shi ko kina so ko baki so ke koda gawarki ce sai an kai gidansa sannan a wuce gidan gaskiyarki dake kuma wallahi na kuskura naji wata matsala ta faru daga fangaranki ki sani ni ba Mahaifinki bane kije ki nemi wani uban muddin kika batawa mijinki Koda na second 1 ne.''

Tun da Abba yafara magana daga Mummy har kudrat kukan takaici suke suna mamakin halin Abba cike da tausayin kanta ta ce'' kayi hakuri Abba insha Allah bazan taba baka kunya ba na aminci kayi min fatan alkairi da zaman lafiya .''

Allah ya maki albarka '' kawai ya furta ya yi, tafiyarsa nan ta fada jikinta tana kuka mai tsuma zuciya sosai Mummy ta bata hakuri tare da yi mata nasiha mai ratsa zuciya nan taji zuciyarta ta dan yi sanyi sannan Mummy ta bar dakin washegari ne take Sanar da su Fareeha da Nawal sosai suka taya ta jimami .''


WANAN KENEN 

Jin shiru ba'a maido wutar ba ya sakata dauko wayarta ta kunna haske tana kuka sallah kawai ke tada ta har dare babu wuta hakan ya yi matikar tsorata ta gashi baya gidan saboda taji karar get da zai fita ga zufa ta da take shararawa kamar ana zuba mata ruwan pompo a haka bacci ya dauke ta kamar kullum lokacin da ta saba tashi lokacin ta farka ta nufi toilet ta daura alwala ta gabatar da sallah ta zauna tana karatun kur'ani har sai da ta gani gari ya fara haske Sannan ta bude Window din dakin iska na dan shigo mata a takaice haka Kudrat take rayuwa babu komai a cikin sai ruwa tun tana da karfi a jikinta har tafara liliss kullum ruwa take rayuwa da su a cikinta ga opration din ta yafara zubar da ruwa sai de ta rinka tsanza kaya tana kuka tsabar azabar yunwa da zafin da Fashin nan yake mata sai de ta kaima Allah kukanta a haka har ta yi wata biyu zuwa lokacin Babu ko numfashi a tare da ita shima sai da ya kara da sati daya ranar da ya shigo gidan ya kunna wutar sannan ya nufo dakinta tana daga kwance idanunta a rufe kamar mai bacci ga wajen riganta a jike da jini wajen da jinin yake bi ya daga rigan da sauri ya sake ta yana kauda kansa hade da toshe hancinsa wani irin bugawa da karfi gabansa ya yi,ya daura hannu wajen wudojin hancinta amma shiru bata numfashi sake kallon fuskarta ya yi, yana tunanin murmushinta lokacin da take kuka yar shagwafar da tayi masa da lokacin da take basa hakuri ba zata iya cika tanki ba kiranta sunnanta ya fara yi yana jijiga ta amma shiru bata motsi wani tausayinta da kaunarta suka fara ziyartar zuciyarsa ya fadi kasa dirshen ya shiga zubar da kwalla yana fadin'' Kudrat ya zaki yi man haka?" Dan Allah ki tashi karki tafi ki barni a cikin wanan duniyar tamu nine mijinki ina sonki bazan iya jurar rashinki a kusa dani ba dan Allah Karki mutu yanzu ki tashi muyi rayuwa kamar ko wane miji da mata nasan ba abu ne mai sauki ba ki yafe min amma nasan na aikata babbar kuskure a gare ki kudrat karki man haka pls .''

Ko ci kanka bata ce masa bare ya sama ran zata daga koda hannunta ne '' da sauri ya mike tsaye ya sungume ta tare da fitowa waje da ita kai tsaye ciki motarsa ya nasa ta ya bude get a gaggauce ya rufe gidan Sannan ya dauki hannu da gudun bala'i ya nufi asubiti da ita .'

Fareeha da karyo kwana da motarta Kenan ta gani yaja motar da karfi ya sa tabi bayansa dan haka kawai ta dinga Jin faduwar gaba bata tsaya wani bata lokaci ba ta kira Mummy da Abba nan take shaida masu halin da Ake ciki har suka iso asubitin ta Sanar da su asubitin da suka zo sannan ta katse kiran ta yi parking tafito a guje ........''

Bayansa tabi lokacin har an karfe Kudrat an shige daki ita ko kallon inda yake Fareeha bata yi ta nemi guri nesa da shi ta zauna'' tun da aka shiga da Kudrat babu wanda yafito daga cikin likitocin sai da suka shafe awanni sannan doctor Irfan ya fito ransa a matikar bace ya ce'' waye ya kawo Kudrat ?"

Da sauri Fareeha da Ajmal suka karisa wajensa ba tare da ya tanka su ba ya wuce office dinsa nan suka bi bayansa da karfi ya naushi table ya cen'' wanan wane irin dabbanci ne so kuke ku kashe yarinyar mutane da kiriciyarta ku lalata mata ita tom ku je ku shirya party ku gayyaci gari gari kuyi murna burinku ya ci a karshe kun barta a kwance rai a hannun Allah da mutuwa me zaku ce iyeehh Amma baku da kirki ko kadan.''

Ajiyar zuciya Fareeha ta Sauke cike da nauyin baki dan da kyar maganar ta fito ta ce'' doctor me ya sa mu Kudrat dan Allah karka ce min ta mutu .''

Aikinmu ya dawo ya baya operation din da yake jikin ya lalace ya rufe har tsanwa ya fara sai fitar da jini yake ga ruwa da baku yi saurin kawo ta hakan zai iya infect din wajen a karshe Cancer ta shiga ciki ga bugun zuciyarta ya kara hahauwa yanzu sai addu'a kawai saboda numfashinta yanzu da kyar muka samu ya dawo yarinyar tana wahala sosai idan bakukaunarta ku rabu ita mana ko dole ne zaman zaku kashe ta a banza wofi kawai.''

Sosai jikin Ajmal ya mutu murus ya kasa furta komai sai idanunta da suka ciciko da ruwa yana mai nadamar halinda ya jefa ta tirr da halinsa da kyar ya dago da jajayen idanunsa ya cen'' doctor dan Allah ka taimake ta karka bari ta mutu yanzu me ya dace ayi mata ina son ganinta dan Allah.''

Tun da an cuceta ba dole a damu da rashan lafiyarta ba mtsss yanzu dole sai an kwance dumkin Operation din mun tada fatar sama wacce ta lalace sannan mu bude ciki mu wanke sa a fitar da gubataciyar fitar ciki da ruwan da suka taru a ciki mu karkare tsanwan ( green) din da ya yi a dumke sannan mu fara duba rauni da sauran lafiyar jikinta kuma aikine bana kankanan kudi ba sai kun ware 2million saboda kayan da zamu yi aiki da su da kuma doctor din da zamu gayyato.''

Iska mai zafi Fareeha ta fizgar sannan ta ce'' doctor Inde kawata zata samu lafiya na yarda ayi mata aiki yanzu zan in Nemo kudin ka bani awa guda dan Allah karki bari rayuwarta ta salwanta a kan burin wani banza sakarai marar mutumci da baisan darajar dan Adam ba mai yanke zumunci wanda shine sanadin duk wanan abun da ya same ta tirr da halinka wallahi tallahi mudun kudrat ta bar duniya n'a rantse da Allah kaima sai ka bakun ce ba zamu taba yafe ma ba Kuma ka rubuta takardar sakinta yanzu iyayenta zasu zo ka mika a hannunsu dan auren da suka yi mata badan basu sonta ko sun gaji da ciyar da ita jamais Kuma ina ta ma badan tana sonka ta aure ka ba halisa ma karfinta akafi tayi biyayya saboda ita din yar halak ce kuma ta nuna ma iyayenta Kalar soyayya da biyayyar da take masu tun da har ka mayar da ita haka kai Kuma ko yanzu munsan su waye masu tarbiya tsakanin kai da jakan iyayenka dan yarinya kawai mtssss .''

Ke wacece da zaki tsare ni kamar uwata kina fadamin maganar da kika dama mata tawa ce Kuma na rantse da Allah ni zan biya kudin aikinta dan doctor yayi kuskuren karfen kudinki sai na sare masa hannaye dan haka kai bani takarda in cike aje a fara Aiki.''

Aikin banza zaka yi wahalar banza ne dan kudrat koda bala'i kake kwana ba zata taba komawa asararen gidanka ba .''

Tana gama fadan haka ta nufi kofa buda kofar da zata yi suka ci karo da su Mummy dake jikin kofa tana sauraran duk Abu da suke fada ajiyar zuciya Fareeha taja tare da jan hannun Mummy suka zauna day daga cikin kujerun dake wajen hawayene suka gangaro ma Mummy ta ce'' Fareeha dama kinsan kudrat bata cikin natsuwa kuka zuba idanu kika kyale mu.''Mummy kiyi hakuri Kudrat ce take hanani wanan ma na Sanar da kune saboda karya kashe mana ita saboda mu muna kaunarta kuma burinmu farincikinta da tana sane ba zata bari na kira ku ba amma wanan shine na karshe domin ta faru ta kare Mummy Koda kudrat zata koma hannun wantsan shedanin dan Allah ku gasa masa aya a hannu saboda ya san darajarta da kimarta wanda ko gobe ba zai yi sha'awar yi ma wata ya mace ba ku tada masa hankali a rasa gane kansa tamkar mahaukaci ko dan shaye shaye wallahi Mummy Idan kin ga kudrat ba zaki taba gane ta .''

Sosai suka firanta bisa lamarin kudrat a lokacin tuni har na shiga da kudrat dakin da za'ayi mata aiki addu'a kawai suke Allah ya sa a gama aikin lafiya shi Kuma dan iskan sai zagaye zagaye yake daga zarar ya dubi Mummy zata watsa mata harara ta daure fuska kamar wacce bata taba sanin yanda ake dariya ba duk ya kasa sakewa sai Kaf kafta idanu yake saboda yanda yake hango tashin hankalin tsana daga cikin idanunta ganin haka ya nufi wajen Abba nan ya nemi magana da shi suna fitowa ya ce'' Abba dan Allah kuyi hakuri bisa wanan lamarin da ya faru ina son Kudrat wallahi har inde zata koma nayi maka alkawarin babban gida da mota ta 30million na buda maka shago sannan na baka jari Inde kudrat zata koma gidana.''

Da Abba ransa a matikar bace yake amma jin abin da Ajmal ya fada ya Saka shi washe baki ya ce'' Ah haba wai Allah yaro irin wanan abin arziki haka karka damu insha Allah kudrat zata koma gidanka amma yanzu ka bama mahaifiyarka dama ta sauko daga dokin zuciyar da ta hawo daga baya sai mu gyara komai sannan a halin yanzu zata zauna tare da mu a gida saboda ta samu jinya mai kyau idan ta warware a baka matarka .''

Tom shikenan tun da tare zaku tafi gaskiya bazan bari matata ta zauna a gidanku ba saboda ta saba rayuwa cikin daula da A.C dan haka zan baku gidan da zaku zauna saboda aji dadin kula min da ita.''

Tom ba damuwa yaro a da sharadi duk son kudina da son tara abin duniya bana ciki da a tozarta min yarinya wallahi Allah zan baka dama ta karshe idan ka kuskura Kudrat ta bata ranta saboda kai tun bata kai ga zubar da hawaye ba dolenka ko waye ya maka tsaye sai ka rabu da yarinyarta sannan na kaika kara kotu dan mutumci na yafi man kudi kaji na fadamaka saboda haka a kiyaye dan ka bar ganin ka saye ni da dukiya hakan ba zai hana na shuka maka rashin mutumci kuma naci kudinka sun ciyu dan ban takura ka nace dole sai ka bani ba .''Insha Allahu Abba hakan ba zai sake faruwa ba wallahi yanzu har ga Allah ina kaunarta dan zan iya sadaukar da komai na jikina ko na dukiya ta ko wani abu mai matikar mahimanci a gareni tsanma kuskure ne Kuma Allah ya riga da ya tsara hakan saboda shine kaddara mu .''Tom ka bani lokaci har mu dai dai ta da uwar yarinyar okay.''

Jinjina masa kai ya yi sannan suka dawo ciki lokacin suka tarar da Fareeha tana magana da Doctor ya basu umarni zasu iya shiga su duba ta .''

A tare suka nufi dakin da take kwance gatanan kamar ta dadafa ta ta bude idanu tana kwance a natse hankali kwance sai sharar baccinta take ..

Suna shiga dakin Mummy ta dubi yarinyarta tsaf wani kulutun bakinciki da tashin hankali suka ziyarce ta ganin yarinyarta son kowa kin wanda ya rasa yarinyar da Koda kudinka sai da rabonka yarinya kamar ita ce ta zauna ta tsara kanta tsabar kyau gata a kwance baiwa marar galihu tafi fuskarta kyau kallo fara mai kyau duk ta yi baki ta kode yar duma duma gashi ta dawo kamar karan tsintsiya innalillahi ta furta ta ce'' na shiga uku na bani ni Aminatu yanzu Kudrat dina ce haka wallahi dani kadai na shigo dakin nan bazan ce yarinya ta bace wanan gaskiya an cuce ni kuma bazan yafe ba hukuma ce zata raba mu da mutume na rantse har ga Allah ko idan kuma anfi karfinmu saboda dukiya zan kai karar mutume kotun ubangiji wacce babu cin hanci bare zalumci .''

Tun da Mummy ta budi baki tana magana Ajmal yafara jikewa da zufa kasa zama ya yi bare tsaye ya fita daga asubitin yana mai nadamar abin da ya aikata .''

Haka su Mummy suke zaune da Kudrat har tsawon sati day bata farka ba sannan Fareeha ita ce ke daukar nauyin kawo masu abinci duk da Ajmal yana yi Abba kadai ke cin abin da ya kawo amma ban da Mummy da ko kallo bai ishe ta ba sai de ta saka yarinyarta a gaba tayi ta kallo tana tausaya ma rayuwarta sannan Nawal kullum tana asubitin sai dare take komawa gida sai de suyi jimami da jajanta ma juna kullum sai de doctor su shigo su duba Kudrat su fita .''

Yau tun da sasafe Ajmal yazo asubitin nan ya tarar da Mummy kan sallaya babu kowa a dakin ganinsa ta hade rai ya gaishe ta amma bata amsa ba sai ma tambayar data jefo masa ta ce'' Malam lafiya? Me kake nema a wajen nan? Ko ka bamu ajiya ne ?"

Ajiyar zuciya y Sauke ya durkusa har kasa yana sosa keya ya ce'' kiyi hakuri Mummy dan......''

Da sauri ta daga masa hannu ta ce'' point d'interrogation karka kuma kirani da Mummy saboda bani da wanan matsayin a gare ka ka manta lokacin da ka kirani ka ci man mutumci nasan da ni mahaifiyarka ce ba zaka min wanan zagin cin kashin ba dan haka kirani Aminatu kawai dan bana bukatar darajawa daga Wajenka Kuma daga yau karna kuskura na sake ganinka a asubitin nan da sunnan Kudrat kazo dubawa .''

Mummy kaddara ce ta riga fata dan Allah karku raba anta da jini wallahi a yanzu kudrat ta zama wani bangare daga jikina ne bazan iya rayuwa babu ita ba ku duba girman Allah karku datse alakar dake tsakaninmu da ita.''

Kasan da Allah kake azabtar min da yarinya kodan ka same ta a bagass shine kake tozarta ta baka San mahimancinta ba in banda kaddara da rabon da ya ratsa tsakaninku miye hadinka kudrat da kai.''

Wane irin rabo Mummy ?"

Tirr tambaya ta ma kake ko ? Cikin da ka dirka mata saboda tsabar azaba da kake gana mata ya shige bayan mahaifa sannan aikin da aka yi mata ka lalata shi gashinan ya dawo baya sai ka zuba ruwa a kasa kasha dan farinciki.''

Wata sabuwar nadama ta kuma riskenshi yanzu dama kudrat tana dauke da jininsa a jikinta amma ya yi sanadiyar lalacewarsa innalillahi dafe kansa ya yi da mugun karfi saboda sarawar da kansa ya yi masa sannan ya mike ya fita waje yana Jin dacin abin da ya mata gaskiya bai yi mata adalci ba dan yanzu haushin kansa yake ji.''

Hawaye ne suka gangaro mata daga kwancen da take dan tun lokacin da ya shigo Allah ya sa ta farka amma bata bude idanunta ba motsin da tayi da hannu ne ya kada karfen dake kusanta har ya ankarar da Mummy da sauri ta mike tsaye ta nufi inda take tana kiran sunnanta ganin hawaye na fitowa daga idanunta ta ce'' Kudrat sannu kinji Allah ya kare min ke ki hakuri insha Allah ba zaki koma gidan wantsan dan iskan yaron ba .''

Sai a lokacin ta bude idanunta tarrr tana ganin buji buji ta ce'' Mummyna kece ?" Da sauri ta yunkura ta rumgume ta tana kuka ta ci gaba da fadin'' Mummy ashe zan sake ganinka a rayuwa ta na zata na rasaki Kamar yanda na rasa haske na Mummy nayi kewarki sosai Mummy dan karki Kuma tafiya ki barni dan Allah Mummyna.''

Dadafa bayanta ta shiga yi tana sumbatar goshinta wata soyayyar uwa da yar ta mamaye mata zuciya ita ma yarona ta fashe da kuka ta ce''Kudrat bazan kuma barinki cikin wanan halin ba ina matikar kaunarki da farincikinki ko duniya zata kiki ni bazan guje ki ba insha Allah bazan barki a hannun wanan mugun ba .''Sosai suka sha kuka har suka gode ma Allah sannan Kudrat ta ce'' Mummy dan Allah Karki barni a hannun wanan mugun azalumin wallahi kasheni zai yi Mummy dan Allah Karki maidani gidansa .''

Insha Allah domin farincikinki shine nawa kudrat koda kaddara zata mayar dake insha Allah sai na kwatar maki yancinki saboda ya san mahimanci a rayuwa ba wai ya din ga wofantar dake ba sannan zai maki riko na ban mamaki .''

Ni dai banison in koma gidansa Mummyna wallahi daya kasheni a wulakance kwara na mutu yanzu haka Haskena yana tsan yana jirana dan ya ci gaba da bani farinciki mu tashi daga inda muka tsaya kullum a cikin bacci sai nayi mafarkinsa Mummy.''

Insha Allah ba zaki mutu a wulakance ba saboda wani Sha ka tafin namiji marar mutumci kema kina da gata koba kudi a gare mu muna da yanci da daraja .''

Mummy me yasa kaddara ta take zuwa min a haka yaushe nima zan kasance cikin farinciki yaushe zan ji dadi nayi rayuwa tamkar wata sakakiyar tsutsuwa Mummy gaskiya ni bazan taba komawa gidansa ba sai de Abba ya tsine man.''

Tirr zubar da wanan yawun Kudrat kisa Allah a lamarinki domin duk wanda ya bi shi ba zai tafe ba ki hakuri ki dauki dangana nice Mahaifiyarki sannan an daina zalumtarki nayi shiru sai inda karfina ya kare a kanki kin ji yarinyar kirki yanzu ki daina wanan maganar kin ga baki da lafiya bara na hada maki tea kisha daga baya sai kice abinci saboda kwanakin da kika yi sun daure maki ciki sai da abu mai zafi saboda kar cikin ya daure .''

Janyeta daga jikinta ta yi, da taimakonta ta mikar da ita suka nufi toilet ta wanke Bakinta da fuskarta sannan suka dawo dakin ta zaunar da kan gadon ta fita ta Sanar da doctor a tare suka shigo nan ya duba ta yaga bata da matsalar komai sai ma tsokanarta da yake tana dariya ya dan jima kadan Sannan ya fita nan Mummy ta mika mata tea din ta karfe saboda wata wulwuleliyar yunwa take ji tana gama shan tea din kamar ta kara tsokano yunwar har jikinta ke rawa ta ce'' Mummy ki bani abinci naci yunwa nake ji .''

Da sauri Mummy ta mike ta mika mata ta saka hannu tafara cin abincin hannu baka hannun kwarya haka ta din ga ci sai da aka yi mata plate uku sannan ta dawo hayacinta natsuwarta ta kuma dawowa mata wani farinciki ya fara mamaye zuciyarta musanman idan ta tuna da nishadin da Doctor ya bata sai ta saki murmushi ana haka ne suka dan taba fira Fareeha da Nawal suka shiga suna ganinta cikin farinciki suka nufe ta da gudu tare da rumgume ta cike da Jin dadi ita ma rumgume su ta ce'' kawayena barkanmu da sake haduwa hmm kaga su Nawal anyi bulbul bani sirrin me kika ci.''Hmmm kaji ki da tsokana daga tashinki lanle mai hali baya barin halinsa .''

Me za'a fasa ai yanzu ji nake nama fiki lafiya dan na samu sauki.''

Tom tashi mu tsale mu gani wa zai yi saurin gajiya .''

Ok dan kamani in tashi sai mu fara.'''

Dariya duk suka saka sannan Fareeha ta ce'' wacce za'a kama ta mike tsaye ita ce zata yi tsale kawai kin yarda mun fiki karfi .''

Uhmm Mummy kina jinsu ko .''Rabu da su ai suma sunsan kece da karfin yanzu.''

Gwalo ta yi,masu sannan suka dan Kai mata dukan wasa tana dariya ta ce'' Haba dai irin wanan dukan karku karisa ni.''

Haba mu mun Isa kisa haskenki ya dawo mana matsayin fatalwa .''

Sosai suke shan firan nishadi dan su burinsu bai wuce tayi ta dariya ba saboda suna son gusar mata da damuwar dake cin ranta sallah kawai take tashinsu bayan sallah la'asar ne Abba da Ajmal suka shiga ai Kamar anyi wuta an dauke ta hade rai tare da kawar da kai gefe dan bata bukatar sake ganin wanan azalumar fuskar saboda tsanarsa da ta darsarmata a yanzu , cikin kunya ya ce'' Sannu da jiki Kudrat ashe kin farka.''

Bata jiyo da fuskarta ba haka ma bata amsa masa ba sai ma kara hade fuskar da tayi,ganin hakan ya Saka shi hadiyar yawu masu mugun daci saboda yanayinta ya nuna yanzu baya gabanta saboda yanda ta karfe sa .............''