ABIN DA CIWO

11

by @rahmakabir13

*ABIN DA CIWO*


Na

©Rahma Kabir MrsMG.

Wattpad @rahmakabir


Page 11.


Ikram tana isa falon ta miƙawa Sameeha wayarta tace cikin rawar murya.


Anty kinga an samu wanda ya ɗauki video ɗinmu na rikicin jiya sun yaɗa a social media har da tagging fuskarki da aro ana cewa ke ce matar da kike yiwa dangin mijinki wulaƙanci dan sun zo gidanki walima. Kalla dai ki gani.


Hannun Sameeha yana rawa ta amsa ta shiga kallo zuciyarta ta gama tsinkewa sai hawaye ya soma zarya a kuncinta, har ta gama kallo ta miƙawa Ikram wayar tana share hawaye tana cewa.


Sharrin su Hauwa ne dan a cikinsu aka samu shaiɗanin daya ɗauka ya yaɗa domin su zubar mini da mutunci a idon duniya, kuma duk wanda ya zageni Allah ya isa dan bazan yafe ba.


Amma wlh mutanen nan basu da kirki rashin imaninsu har ya kai su yaɗa video irin wannan dan suci mutuncinki, sauƙin abin hoton fuskarmu bai fito sosai ba saboda daga nesa aka ɗauka.


Koma waye yayi mana haka to yama kansa kuma...


Bata gama magana ba wayarta ta shiga ƙara taga Zaidu ne, tana ɗauka shima maganar video yayi mata, nan ta fashe masa da kuka ya dinga bata haƙuri yace tabarwa Allah duk wanda yayi mata haka sai Allah ya saka mata, haka suka aje wayar, a takaice haka ta dinga amsa wayar mutane wanda suka gani duk dai haƙuri suka bata, dan har Yaya Kamalu ya kirata yace zasu ɗauki mataki. Cikin damuwa ta kira Aminu yana ɗauka ta bashi labari yace cikin fada.


Na gaji da abinda su Hauwa suke yi mini yanzu, su rasa abinda zasu saka mini da shi sai suci mutuncinki, ai bake suka tozarta ba ni suka tozarta, kiyi haƙuri zan ɗauki mataki.


Yana kaiwa nan a maganarsa sai ya kashe wayarsa, ya duba agogo yaga ƙarfe sha biyu saura sai ya kira wani da yake aiki a gurin jirgin ƙasa yace zai tura masa kuɗi ya siya masa ticket na ƙarfe biyu zai je Kaduna da yake yanzu sau biyu jirgin ke zuwa Kaduna daga takwsa na safe sai kuma biyun rana, yana gama wayar sai ya shiga toilet dan ya watsa ruwa ya fito ya shirya.


Sameeha kuwa saboda damunta da aka yi da kira dan duk wanda yaga videon sai ya kirata, ya sata kashe wayarta gabaɗaya, tayi kuka harta gode Allah Ikram sai bata haƙuri take yi, umma ma ta kira a wayar Ikram ta bata haƙuri tace dama dole rayuwa tana tafiya da ƙalubale dan haka jarabawa ce sai ta ɗaure zata ci, kuma matakin nasara yana tare da yin haƙuri, maganganu ta gaya mata masu daɗi da ya sakata samun natsuwa. Da aka kira sallar azahar ne suka shiga ɗaki dan gabatar da sallah.


****


Najwa.


Lokacin data kira Hauwa tana tare da Nafeesa dan rubuta mata maganganun tayi a takarda wanda zara faɗawa Hauwa kuma itama ta ƙara da nata, sun haɗu a islamiyya ne wanda dama tun jiya suka shirya zata kira Hauwa ta shinfiɗa mata karyan maganganu da zai sa ta samu shiga a gurinta, wani aji suka shiga da ba a amfani da shi wanda empty yake ko kujeru babu, a nan ta saka katin data siya ta kira Hauwa kuma tayi sa a ta ɗauka, shine ta samu damar faɗa mata maganganun da suka ƙara hautsina Hauwa ta dinga sakin magana, lokacin da ta gama wayar ta saki shewa cike da tsantsar farin ciki Nafeesa ma tana dariya ta miƙa mata hannu suka tafa tace.


Ƙawata saura kiris ki samu Aminu a hannunki domin kayanki ya tsinke a gidin gaba, dan naga kin zurata ta hau ta zauna har da cewa ai babu haramci dan kin auresa, ga dukkan alamu ta yaba da ke Najwa kinga sauran aiki ita zata ƙarasa miki, yanzu abu na gaba shine ki riƙa kai mata ziyara akai akai kina riƙe ɗan tsaraba, ke ko omo ne ki kai mata, wlh zaki ƙara shiga zuciyarta sosai taji duk duniya babu wacce ta dace da kaninta sai ke.


Bari kawai Feena har wani gumi nake ji saboda tsabar farin ciki da nake ciki, kuma wlh ban taɓa tunanin maganar dana faɗa zai yi tasiri a zuciyarta ba, ko da yake me niman kuka ne aka jifeshi da kashi. Ai in zani gidan sai kin ƙara bani haske akan maganganun da zan je mata dashi, sannan san siya wani abu na kai mata, amma kawata ya zanyi da Zaidu.?


Cewar Najwa tana riƙe haɓa, Nafeesa ta kalleta tayi 'yar dariya.


Malama ta inda aka hau tanan ake sauka, ki cika masa iska ya ƙara gaba dan kuwa bakin rijiya ba gurin wasan yaro bane, a yanzu akwai tazara a tsakaninku ke ba matar yaro ba ce. Kuma ni kin san tunanina nafi son 'yar uwarsa ta fita daga gidan kafin ki shiga ta yadda zaki sakata ki wala ba ruwanki da matsalar kishiya, dan kin san fa zaku buga da ita tunda aure ne na cin amana za kiyi, to gwara ayi mata me gabaɗaya ta ƙara gaba kema ki zuba naki 'ya'yan ki cike gida Hajiyata.


Itama Hauwa baki ji abinda tace bane, so suke ta bar gidan fa, dan haka dole ne zan ƙara iza wutar ƙiyayyarsu akanta yadda zasu haɗo mata bama-bamai tayi checking out wlh ta bani guri.


Sai suka tafa suna dariya daga haka suka fito daga ajin suka wuce asalin ajinsu suka shiga, a yanzu tunda ta sakawa kanta masifar soyaygar cin amana ko haddar bata iya haɗawa ta kai, ta shiriri ce ko da tazo sai dai taga ana kaiwa, amma ita tunanin Aminu data kwallafawa ranta ya hanata ta yi bitar karatun balle ta yi yunkurin kai haddar, Nafeesa dai tana kai nata tunda ita ba tada wata damuwa dan kuwa tana da wanda zata aura, jira ake ya fito daga short service daya shiga na NDA ayi bikinsu.


Bayan an tashi daga makaranta ne, Najwa tana cikin napep zata gida sai wayar Ikram ta shigo tana kiranta, ta ɗauka da sauri dan tasan wani labarin zata samu, nan Ikram take faɗa mata an samu shaiɗanin daya ɗauki videon faɗarsu ta jiya an yaɗa a special media wanda har hakan yasa Aminu zai zo kaduna saboda zai yi magana da 'yan uwansa, ya jawa su Hauwa layi da iyalinsa dan yasan duk sharrinsu ne suka yi haka. Najwa jin Aminu zai shigo gari yasa ta ji wani farin cikin ya lulluɓe bargon zuciyarta tana sakin murmushin ba zata, tace cikin zaƙuwa.


Aiko gani nan zuwa yanzun muka tashi a makaranta, ashe sharrin da suka kuma jifanta da shi kenan, amma naji daɗi da Aminu zai zo ya ci musu, ai gwara ya nuna musu yana son matarsa.


Ke dai bari wlh abin da ciwo, mutane sai kiranta suke yi suna jajantawa, in dai haka ake dangin miji to Allah ya wadaransu ya rabamu da sharrinsu muma ba muyi aure ba.


Ameen 'yar uwa ina tafe In Sha Allah yanzu.


Yauwa gwara ki zo dama zan miki maganar yaya Zaidu, haba Najwa ya kike so ki watsa mana ƙasa a ido, karki yi mana haka mana, muna farin ciki zumunci zai tkara ƙarfi.


Ke ni rabani da wani maganar yaya Zaidu wlh ni tuni na canja sheƙa bana yayinta dan wuciyar rakumi yayi nesa da ƙasa, na samu wanda zai saka ni a farin ciki kamar yadda Anty Sameeha take cikin daula dumu dumu har kuma ku zo kuci arziki.


Ahaf ai dama na faɗa, wahalar da kansa yake dan nasan halinki da shegen kwaɗayi da buri, to wlh ɓata masa lokaci da kika yi Allah ya isansa shegiya mayyar kuɗi.


Cewar Ikram tana kaiwa nan ta kashe wayarta cike da takaicin Najwa tare da ƙudurta zagin da zata yi mata in ta ƙaraso, dan sai ta yi mata wankin babbar bargo, Ita kuma Najwa dariya ta saki tana jin daɗin ta samu hanyar da zata aika sakonta ga Zaidu cikin sauki, dan dama tun da ta rabu da Nafeesa take tunanin yadda zata yarda kwallon mangoro ta huta da ƙuda, sai gashi Allah ya kawo mata hanya mafi sauƙi da zata isar da saƙonta. Ba ƙaramin alfahari da Nafeesa take yi ba tare da farin cikin zamowarta aminiyarta, ashe can da kanta a murfi yafe sai yanzu da Nafeesa ta wayar mata da kai ta gane da ta tafkawa kanta babban kuskure ta cucu kanta abanza, dan bata ganin zata tsinci wani abin arziki a aurenta da Zaidu, dan shima cima zaune ne bai koshi ba balle ya kosar da ita. Ta sauke ajiyar zuciya ta cewa mai napep ya wuce da ita unguwar dosa 'yan majalisu zata ƙara masa kuɗinsa, mai napep yace to kana suka cigaba da tafiya ita kuma ta kira wayar Hauwa, bata ɗauka ba sai ta tura mata da saƙo kamar haka.


_Yaya Hauwa an samu wani ya ɗauki video ɗin faɗarku na jiya ya saka a social media ana ta zagin Sameeha, yanzu haka Aminu yana hanyar zuwa Kaduna da yace kune kuka yiwa matarsa haka kuma zai ja muku layi a tsakaninku, dan haka sai ki shirya maganar da zaki yi dasu, yanzu Ikram ta kira ni take faɗa mini shiyasa na Kira in sanar dake._


Sai ta tura mata, tana sakin wani shu'umin murmushi dan bata taɓa zaton videon zai yi mata aiki ba har haka, sai gashi ya jawo mata masoyinta zata samu damar yin rozali da shi, ita kuwa babu abinda zata sakawa Nafeesa dashi face Addu'ar gamawa lafiya dan gabaɗaya duk wannan shirinta ne, kai ilimi akwai daɗi dole ne itama in tayi aure ta koma makarantar boko ta ƙara wayewa dan akwai bambanci sosai da wayewar boko da ta islamiya, gashi dai in ilimin addini ne tafi Nafeesa amma kuma ita ta fita wayewa saboda tayi boko sama da secondary. Da tunani barkatai suka isa gidan Sameeha lokacin karfe biyu saura.


Lokacin da Hauwa ta idar da sallah ta ɗauki wayarta taga miscall din Najwa sai ta duba sakon data tura mata, tana gama karantawa ta miƙe a zabure tana salati, tare da sanyawa Najwa albarka dan tasan in ba ita ba babu yadda zata san da wannan ƙulli da aka shirya musu, ga babu kowa a godan balle ta tambaya ko sunga videon ko tasa su bincika mata a facebook, kiran Laure tayi a waya bugu ɗaya ta ɗauka ta shelenta mata sakon Najwa, Laure ta saki murmushin takaici.


Yo ke ce baki sani ba amma tun ɗazu Sa'a ta nuna mini a wayarta, yanzun nan Alhasan ya gama balbalin bala'i a gidanmu ya fita, yace kuma Aminu yana hanya in ya ƙaraso zasu kira ki kizo ayi wacce za a yi.


Wlh ya zo ɗin gabaɗayansu ina dai-dai dasu, akan Sameeha babu wanda ya isa ya faɗa mini magana inyi shuru in kyalesu, idan ta gama dasu to ni bata gama dani ba kuma wlh zanyi maganin Aminu na yiwa rufkar hanci.


Hmmm dama ina shirin in kiraki in faɗa miki sai ga kiranki, amma wannan yarinya ta zame mana babban CID, ke ni banga amfanin wannan 'yar aiki Jamila ba wlh, tunda har yau ba wani labari data kawo mana mai daɗi irin wannan.


Saki layinta Laure, ni dai wannan yarinya zan tsaya tsayin daka sai ta auri Aminu dan wlh itace ta dace da shi, ba ƙaramin biyayya zata yi mana ba, zan shiga in fita har sai hakkarmu ta cimm ruwa koda kuwa kuɗina zai ƙare. Jamila kuma akwai lokacin da zata yi mana amfani.


Hmmm Allah ya kaimu anjima muga wainar da za a kashe.


Ameen, a tsakanin ni dasu shege ka fasa, ke ni duk wanda ya ɗauki video nan Allah yayi masa abarka, ai ba sharri aka mata ba halinta ne aka bayyanawa duniya, kuma kaɗan ma ta gani, In Sha Allah sai Aminu yayi mata saki uku ta fita daga gidan cikin damuwa da dana sani.


Allah ya amsa bakinki Hauwa.


Hauwa tace Amin ta kashe wayar da har mtn sunyi mata warning kuɗinta saura minti ɗaya ya ƙare, Hauwa ta cigaba da zagaye ɗakinta tana cizon yatsa da gyada kai, tare da ayyana irin bala'in da zata sauke sumu in dai suka kawo mata wargi, dan wlh ba zata taɓa yarda a yi mata cin kashi ba a dalilin Sameeha, ƙaramar hauka zata yi musu ayi uwar watsi.


*Afwan biki muke ta fama da shi.*