DUBA da WURI

Chapter B

by @kwalisa

TSOHUWA MAI DUBA DA WURI ...4

Jumi ta fashimci tusa ta riga ta karewa bodari. Don haka bata da mafita face mika kai bori ya hau. Amma tabbas ita kam ta yi imani ba zata mika kai haka salin aslin ba. A cikin abu biyu za a yi daya ko ita ko a Alhaji Bilya.

Tasha jin labarin matayen da aka yi mu su auren dole,wasu suka shiga yawon duniya,wa su suka kashe kansu,wa su kuma mazajen suka kashe.

Ita kam ba zata shiga duniya ba, amma tabbas zata yi kisa. Wata kila lokaci yayi da mata da 'ya 'yan Alhaji Bilya za su wataya suma su yi wadaka da kudi son ransu.

Matanki da Jumi ta dauka na kawo karshen matsolon attajiri Alhaji Bilya.


Mu huta nan muga shin zata aiwatar da burinta.

M.Kwalisa


TSOHUWA MAI DUBA DA WURI....5

***

Biki yana kara karatowa, ba wani tartibin abu da Jumi ta cimma,duk wata kawarta idan ta ji labari sai mamaki ya kamata ya za a yi macce 'yar kwalisa kamar jumi ta auri matsolo kazamani mai kudi kamar Alhaji. 

Kawayenta na kusa suka yi ta zuwa domin jin tabbacin maganar.

"Da gaske ne nan da kwana uku za a dauran aure". Tace wa kawarta.

" Amma kinsa ko shinkafa 'yar gwamnati ba a ci a gidansa sai mai tsakuwa? Ba a shan shayi a gidansa sai koko,ko dumamen tuwo. Nama kuwa sai na suna idan aka masa haihuwa". Jumi ta zuba tagumi.

"Duka nasan da haka".

" Amma kika yadda za ki aure shi?" Ta girgiza kai.

"Bani na yadda zan aure shi ba,kaddara tace ta zo a haka". Kawarta ta dubeta.

" Sai ki sauya kaddara taki...." Jumi ta zabura da sauri kamar an tsira mata allura,kawarta ta bita da ido bata katse mata hanzari ba,ta dauki Riga abaya ta zumbula ta yafa wani dan mayafi ta dubi kawarta.

"Zan fita".

" Zuwa ina?"

Ta soma tafiya "Wajen da zan sauya kaddara ta,kinsa zomo baya kamuwa daga zaune" Ta fice daga dakin.


Tana fitowa kofar gida suka yi karo da wani matashi,mai ruwan barayin wayar salula.

"Kece Jumi?" Ya tambayeta.

"Eh ni ce..." Bata karasa magana ba sai taji saukar mari har sai data ga wasu taurari.

"Wallahi kika sake kika auri Babanmu sai na kashe ki,shegiya mayya kudi" Iyakacin abinda taji kenan kafin ta wartsake daga marin da ya yi mata har ya bar wajen kamar aljani.

"Kan ubanan kayyasa, yaro bai san wata ba sai ya takata,tabbas yau ka tsokano tsuliyar dodo" Ta fada cikin fusata cikin azama ta nufi gidan tsohuwa mai duba da wuri.


Ta shiga dakin tsohuwa a fusace kamar kububuwa,fuska a murtuke. Tsohuwa ta dauko wuri ta karkada ta watsa,tace mata.

"Dauki daya" Jumi ta dauka.

"Takadirin yaro kema ya mareki...ai shi ne yake hana matan babansa zaman aure".


Yanzu aka soma

M.Kwalisa