INTERVIEW WITH WRITER'S

Ayshercool

by @halimahz

Aisha Adam marubuciya me sauƙin hali da nagarta, Sha'awarta na son rubutu ya fara ne tun tana da ƙarancin shekaru.

________________________________________


ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH.


TAMBAYA: Menene cikakken sunan marubuciya da tarihin rayuwa a taƙaice?

AMSA: Sunana Aisha Adam wadda aka fi sani da Ayshercool, Ni haifaffiyar garin kano ce, ƙaramar hukumar gwale, na yi makaranta daga Nursery zuwa high institution, yanzu ina aikin gwamnati, ina rubutu ina taɓa kasuwanci.


TAMBAYA: A wacce shekara kika fara rubutu?

AMSA: Na fara rubutu a 2019.


TAMBAYA: A matsayin me kika ɗauka rubutunki?

AMSA: Abubuwa da dama, kamar hanyar tura saƙona kai tsaye, wato faɗakarwa, nishaɗi a karan kaina, da kuma sana'a.


TAMBAYA: Daga 2019 zuwa shekaran 2024 da mu ke ciki a yanzu. Adadin littafai nawa kika rubuta? Kuma a cikin su wanne ya zama Bakandamiya? Sannan menene jigonsa?

AMSA: Na rubuta litattafai bakwai, mun rubuta ɗaya mu uku, Ruɗin ƙuruciya ne bakandamiyata, saboda a ganina wani muhimmin jigo ne da shi, da wurina ko bayan raina na ke jin ruɗin ƙuruciya ya isar da wani saƙo. Jigonsa gaba ɗaya a kan adolescent crises ne, yara masu tashen balaga a makarantun sakandare.


TAMBAYA: Da kyau. Kenan ko a yanzu muka ce ki kwaɗaitawa masu sauraran mu littafinki za ki zaɓar musu *RUƊIN ƘURUCIYA ne?*

AMSA: Sosai, dan akwai tunatarwa ga iyaye game da wani babban al'amari da ba su fiye bawa muhimmanci a rayuwar ƴaƴan su ba.


TAMBAYA: Ga ki ma'aikaciyar gwamnati kuma ƴar kasuwa, shin ta ya kike iya samun damar yin rubutu musamman duba da yanayin lokaci na ma'aikatan gwamnati? Hakan ba ya ba ki wahala ko ya zamar miki wata damuwa?

AMSA: Gaskiya akwai ƙalubale, dan littafina na bayan nan, na ɗan fuskanci matsala da wanda su ka saya book, suna ganin sun biya kuɗi amma posting sau huɗu a sati kawai. Abun babu sauƙi gaskiya amma da yake ina da passion ɗin Abun ina so, ina iya jure ƙalubalen dan galibi sai dai na bi dare nayi typing. Kuma sannu sannu ba ta hana zuwa ai, sai dai a daɗe ba aje ba, shi rubutu abu ne da yake buƙatar nutsuwa da lokaci, ka yi posting a sati sau biyu mai ma'ana, ya fi ka yi sau biyar babu ma'ana.


TAMBAYA: Ta ɓangaren masoyanki ma'abota bibiyar littafanki. Shin ya mu'amalarki da su? Akwai fahimtar juna a tsakani ko kuwa kaman yanda wasu ke kada baki ne su kira marubuta marasa mutunci da girman kai?

AMSA: Akwai kyakywar fahimtar juna tsakanina da masoyana, ina ba su muhimmanci sosai da sosai, sai dai ba a rasa ɗan ƙalubale nan da can, wanda ba sa yi maka uzuri. Ba na ce babu masu girman kai ba, amma kullum ina roƙon fans su din ga yi mana uzuri, hulɗa da mutane sai haƙuri, a ƙalla kullum zaka samu message goma mafi ƙaranci. Zaka yi rubutu, zaka je aiki, ga sauran hidimomi, wani lokacin sai ka yi da gaske zaka samu isasshen lokacin da zaka amsa kowa dai-dai da buƙatar sa.


TAMBAYA: Cikin shekaru biyar da kika yi kina rubutu haka ne ko? Ya ɓangaren matakin nasara an samu ko kuma dai tukunna ana ta faman gwagwarmaya ne har yanzu ba wani bayani?

AMSA: Alhamdilillah, Alhamdilillah Alhamdilillah ala kulli halin da na iya waƙa da na rera waƙar bana iyawa masoyana ta kawu ɗan sarki😂😂

Nasarori Alhamdilillah mun godewa Allah, an same su.


TAMBAYA: Alhamdulillah in taya ki nima, idan da kiɗi rawa in babu kiɗa rawa💃🏼ai mu cashe kawai abinmu sharrr😂to Allah ya daɗa dubban nasarori da albarka a ciki🥰🤝...Aka ce kowanne matakin nasara na zuwa ne tare ko kuma bayan fuskantar Ƙalubale...shin daga lokacin da kika ƙudurci fara rubutu har zuwa yanzu da kike amsa sunanki na cikakkar marubuciya. Ya lamarin yake ta ɓangaren ƙalubale a rubutunki? Lokacin da xa ki fara kin nemi yardar iyaye? Lokacin da kika shigo cikin harkar akwai ƙalubalen da kika sama daga wajen ƴan uwanki marubuta da su kansu masu karatun?

AMSA: Na fara karatun littafin da ƙanan shekarun da idan na faɗa wasu za su yi mamaki, dan haka na daɗe da sha'awar abun a raina. Ban nemi iznin kowa ba, sama da ka na tari aradu da ka na fara rubutu lokacin lockdown. Littafina na farko Abduljalal sai ya samu karɓuwa aka yi ta kirana a waya, daga baya na yanke shawarar bayyana ina rubutu. Kuma aka bani go ahead, tare da dukkan support ɗin da nake buƙata.

Ba wani ƙalubale daga marubuta, dan ban sha wahalar neman shawarar ta ina zan fara rubutu ba, ina samar da jigo mai kyau, sai dai babu ƙa'idojin rubutu suma sannu a hankali nake koya ina gyarawa. Makaranta su suka fara bani goyon baya, dan ban san kowace marubuciya ba da na fara, makaranta su na fara sani su ummu hanif, Abu zaid, maman zahra, bebi nijar, saifullahi da sauransu. Ƙalubalen ɗaya da nake nanatawa rashin uzuri daga makaranta, dan akwai wadda tayi mini abun da ta kaini bango nayi magana.


TAMBAYA: Amm Aishatu bari mu ɗan waiwaya wani ɓangare me muhimmanci...Topic ne zamu ɗakko wanda ka iya addabar al'ummar mu a halin da muke ciki yanzu, matsayinki na wadda ta amsa sunan marubuciya za mu so ki yi duba akan wannan topic ɗin/me ke haddasa shi/faɗakarwa/Illarsa/shawara/hanyar magancewa da dai sauran su.

(Istimna'i) that is (masturbation) a turance. ba sai na faɗa ba kema matsayinki na writer na san kin sani kuma wataqila kin cicci karo da neman shawara ko labarai da ke da alaqa da irin hakan, na kuma san kin san hakan lamari ne da ke damun zuƙata.

Muna sauraronki me xaki iya ce mana akan hakan?...

AMSA: Kai tsaye ban yi maganar istimna'i a littafin ruɗin ƙuruciya ba, amma duk tambayoyin da ki ka yi mini akwai amsoshinsu a cikin littafin RUƊIN ƘURUCIYA.

Lamari ne mai girma da faɗi, da yake buƙatar isasshen lokaci.

Abu na farko sakacin iyaye na taka muhimmiyar rawa tun a lokacin tashen balaga iyaye yakamata su san wasu kalar yara ne da su? Akwai wanda rawar kansu yayi yawa. Idan ba a tantance makarantar da zasu yi ba, suna iya koya a wurin abokai, dan lokaci ne da yara ke bawa abokai muhimmanci fiye da iyaye.

Iyaye mata su kiyaye yin maganganu kowane iri a gaban yara, musamman na batsa, dan mata idan muka haɗu wasu lokutan bama ji bama gani.

Iyaye su kula da son da suke yi a gaban yaransu tare da raya shimfiɗa da su.

Kula da su ta hanyar wayar musu da kai, a kan sexual assault including masturbation da illolinsa.

Yara idan sun kai munzalin aure idan har da halin su yi aure, kar ace sai sun yi boko mai zurfi.

Samar wa yara abun da zai yi keeping ɗin su busy daga kaɗaici.

Idan mace ta samu jinkirin aure, a jata a jiki, a kula da ita, tare da yi mata nasiha a kan tsoron Allah.

Masturbation yana da illoli da dama, kama da ga kashe sperm cells ga namiji. Idan mutum yayi mugun sabo da shi, baya iya dainawa cikin sauƙi, kuma babu lallai aure ya din ga gamsar da mutum, kuma yana leading ga lesbian ga mata.

Marubuta su tsarkake alƙalami, wurin rubuta abun da zai tayar wa da mutane sha'awa, iyaye su din ga bibiyar wayoyin yaransu sannan a haɗa da addu'a.

Topic ne faɗi gasky.


TAMBAYA: Wacece madubinki a duniyar marubuta? Kuma shin kina da wani jan hankali ne da za ki ga ƴan uwaki marubuta?

AMSA: Ayshercool ita ce madubina, dan idan na leƙa mudubin ita nake gani. Sai dai akwai marubautan da suke burgeni, kamar Hafsat A ladan, Fauziyya D Suleiman Abdulaziz madakin gini.

Marubuta, mu cigaba da haƙuri da juna da girmama masoyanmu, tare da ɗaukar gyara idan an yi mana.

Masu shigowa yanzu su sani, ba daga shigowa ake kaiwa matakin nasar ba, sai an jure an yi gwagwarmaya.


TAMBAYA: Kina da wani albishir ne ko saƙo ga makaranta littafanki?

AMSA: A cigaba da bibiyar rubutun cool, ina da abubuwan gaya musu da yawa ta hanyar alƙalamina, sannan ni ƙofata a buɗe take dan gyara, sharhi, ko shawara a kan litatafaina, cikin mutuntawa.


TAMBAYA: Saƙon yabo da godiya ga mutane uku a duniyarki

AMSA: Iyayena, Ƴan uwana, Ƴan birght pens.


TAMBAYA: Mafi faranta ranki da mafi baqanta ranki?

AMSA: Ayi mini addu'a, sai kuma kuɗi.

A ci mutuncina ko a raina ni.


TAMBAYA: Na'ima Sulaiman Sarauta(Nimcyluv), Zee kumurya...zaɓi mutum ɗaya a cikin su da dalilinki😄

AMSA: Bana amsa wannan tambayar, tamkar ki ce in zaɓi hannuna ne ko ƙafata😂


TAMBAYA: Daga ƙarshe Jawabin godiya ga Team Fitattu Biyar tare da sallama ga masu saurare.

AMSA: Masha Allah, ina godiya da karamci da aka nuna mini, na wannan gayyata da aka yi mini, fitattu Allah ya sa ku zarce zafafa.

Masu saurare, ina godiya sosai da sosai da bayar da lokacinku wurin bibiyar hira da aka yi da ni, Ubangiji Allah yayi mana jagora baki ɗaya.


TAMBAYOYIN MASU SAURARE GA MARUBUCIYA.

TAMBAYA: Tana da aure?? Ko Allah bai qaddara ba. Muna yimata fatar Alkhairi.

AMSA: BA NI DA AURE, Amin na gode.


TAMBAYA: Me yasa ta kasa amsa tambayar zaben nimcy da kumurya?

AMSA: Saboda ƙafafuwana da hannayena duk abun so ne a wurina, ba zan ɗau ɗaya na bar ɗaya ba🤥


TAMBAYA: Slam dan Allah zamu iya ganin hoton Aisha cool sabida mu shaidata kar mu hadu a hanya ta wuce mu wuce.

AMSA: Dan Allah mosoyiya kiyi haƙuri yadda ki ka san Ummi ta book ɗin CUTARWA haka na ke.


TAMBAYA: Tambayane shine, Akan littafin da takeyi ynxu ta fada Mana miye manufar littafin Kuma Ina ta dosa.

AMSA: 😂😂 haka fa suka ce ƙanwar maza ba su san in da na dosa ba, sai da aka kammala, zuwa yanzu ai saƙon littafin a bayyane yake, miƙaƙƙen salo ne fa.


SAƘONNIN FATAN ALHERI.

1- Aslam ina yiwa aisha fatan Allah ya mayar da ita gida lfy a gaishe da rumaisa da mai martaba 💃🏼💃🏼💃🏼

2- Ina son ki aisha Tsakani da Allah 😍

3- Ina sonki fisabilillahi nima😍

4- Aslm. Na siyi littafin kanwar maza kuma na futar matadashi ina roqon yafiyarta pls

5- ni dai don Allah ta tura muna hotonta ina so naga fuskar masoyiyta💃🏼

_________________________________

#follow halimahz

#comment

#share