SILAR AURE NA

p-4

by @rabiattu0444

_*🍇SILAR AURE NA🍇*_

      

TAKU NA 1

Book 1📖




*NA*

Rabiatu Bashir Abdullahi

*UMMU MAHER(MRS GREEN)*🍃


_*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*_



*UMMU MAHER COLLECTION👜👜*

_Domin siyan kaya masu sauƙi, da nagarta da kuma kyau kamarsu kayan kitchen, atamfa, les, ɗan kunne, duk muna siyarwa kuma aduk inda kake muna turawa oder da kuma siyan ɗai ɗai, adaɗe anayi sai da gaskiya🧤🧤 Domin shiga grp ɗin mu danna shuɗin dake ƙasa👇🏽_

***

C3tsX4CqiEp939DhYvJ3SZ


*Read SILAR AURE NA, on arewabooks*

https://arewabooks.com/book?id=65bd172f88cb015808e5fc25


*Ga masu son koyon sana'o'i 10 suyi min magana ta lambayar wayata*

***



SHAFI NA 4

_____________ Innah ta ce" to sai me idan tana naƙuda? yo nima ba naƙudar na yi na haifeku ba? ku sha huɗu haka na haifeku, shima munafukin mijin na ta matsiyaci ai yasan idan mukazo ba zamu barshi haka ba, shiyasa ya sanya mana ido sai yanzu ya yi niyyar kiranmu wato gamu sakarkaru muje mu biya kuɗin asibiti ko? to wallahi bazani ba, haka kurum ka siyar da akuyar ka tazo tana ci maka danga? ka faɗa masa shi da yayi cikin sai ya tsaya awajenta har ta haihu amman wallahi ko kai ban yarda kaje ba".


yaya Umar ya ce" haba Innah, ina daura ina funtua? yanzu muna ji muna gani sai mubar yarinyar agari alhalin ba tada kowa? ni idan ma kuɗi kike ji sai mu biya wajen Safiya, aƙwai ajiyar dana ke bata sai muyi kuɗin mota mu tafi".


 Innah tayi masa kallon kai yaro ne, bakasan dawar garin ba sannan ta ce" yo kaji munafuki, au daman kana ajiya gidan Safiyar na tambayeka kuɗi maimuna zata siya anƙwan biki ka hanata? saboda baƙar rowa sai yanzu ne ka tuna kana ajiya? to wallahi kaji na rantse? Allah babu wanda zai je, saboda ni bazanje in tuno da talaucin dana yi abaya ba, don ni dai nasan wannan matsiyacin gidan na su ba lallai ne ma asamu abincin da za'a ci ba, saboda haka ni dai bazan je ba kaima kuma haram agidan liman, ban lamunce maka kaje ba don wayon tsiya yana ganinka haka jibgege sai ya ɗauka wata tsiyar ce da kai, ya ɗora maka ɗawainiyar cikin daba kai kayi ba".


 ya Umar ya kasa magana saboda takaicin abinda Innah ke faɗa, ganin tayi stop azancenta ya ce"wai Innarmu miye laifin wannan yarinyar ne? don ta auri talaka shikkenan kika sanya ta agaba da tsangwama? Don Allah ki sassauta mata mana? ki barta ma taji da talaucin da take ciki, ni aganina tunda mijinta ba shida shi ai taimakonsu ya kamata muyi sai kiga muma Allah ya buɗe mana hanyayon samu".


 Inna ta ce" Allahu akhbar, me karatu na gaba shi ne Umar". ta faɗi hakan gamida riƙe baki tayi gaba abinta, bata ko ƙara waiwayowa ba ballantana ma har ya sanya ran zai samu amsa me kyau.


 ya daɗe atsaye awajen, har dai yaga tsayuwar ba zata yi masa ba ya wuce, kai tsaye gidan Safiya me bi masa ya yi gidanta dake nan cikin funtua ɗin, ai kuwa yaci sa'a lokacin zata tafi aiki da yake ma'aikaciyar lafiya ce daga ita har mijinta.

Tana ganinsa ta tsaya da buɗe murfin motar ta, ta ƙaraso tun kafin ya ƙaraso inda ya ke, wannan tarbiyyar Innah ce babu wani me raina wani kowa ana bashi girmansa agidan, amman fa ada ba ayanzu ba don ayanzu idan kana da abin aljihu kai ne mutum, amman idan ba kada shi kai da kashi duk ɗaya ne awajenta.


 ta ƙaraso bakin besfa ɗinsa ta fara gaidashi, tana ce wa" dama yanzu nake ce wa zan kira ka, sai kuma ga ka? don yanzu gama wayata da Innah kenan, take faɗamin wata magana mara daɗi wai ka fara sanya ƙafa kan sharaɗin da ta kafa mana kan Maryam, shi ne na ce wani sharaɗi ne? sai ta ce min wai ko ta mutu kasa wani ya taimaki Maryam wai tunda ta sanya ƙafa tayi fatali da wanda ta zaɓa mata ta auri matsiyacin miji".

 Umar ya ce" Safiya ashe ta kira ki ko? daman nasan za'ayi haka, amman abinda nake so dake don Allah ki sanar da mijinki kuje ko tare ne gobe, kije kiga ƴar uwarki don wallahi al'amarin Maryam yana bani tsoro sosai, yadda kika san an shiga tsakaninta da Innah duk da ada can ƴar gaban goshinta ce, amman kuma ayanzu sai reshe ya juye da mujiya".


 Safiya ta ce" daman zanje in dubata, amman bazan faɗawa Innarmu ba don naga ta ɗau abin da zafi, ni kuma aganina idan bamu taimakawa maryam ba wa zai taimaka mata? haƙuri zamuyi mu dukanmu muje mu duba ta, don idan muka biyewa Innah sai mu haɗu mu kashe Maryam".

 Ya ce" yauwa Safiya don Allah ki faɗawa su Zainab, don ni yanzu haka ma zan tafi tasha in hau motar daura ne, saboda ni dai ba zan iya yiwa Innarmu biyayya kan wannan sharaɗin na ta ba, daba dokar ubangini ba a'i ko baka duba mutum don wani abuba ka dubasa don taimakon musulunci".


Safiya ta ce" bari in isa wajen aiki, zan kira su dukansu har Safnah dake Abuja duk zan kirasu, tunda kaga ma sun kusa zuwa duk ƙarshen wata dama suke zuwa hutu gidansu dake katsina".


 Umar ya gyaɗa kai sannan ya ce" yauwa safiya ajiyata zaki bani, tunda bansan halin da zan samesu ba kinga sai inyi amfani da waɗannan kuɗin".

Ta ce" to". gami da komawa cikin gidan ta ɗakko masa kuɗinsa dubu hamsin da taƙwas ta basa, ya yi mata godiya gamida wucewa abinsa don komawa gida ya ajje mashin ɗinsa sannan ya wuce tasha don hawa mota.


.......Sosai nake shan wahala, don tun ina ganin mutanen dake kai na har na dena ganinsu gashi kuma ban haihu ɗin ba, Sulaiman ya shigo ina jinsa sama sama yana kuka, suna korarsa wai ya fita suyi aikinsu shi kuwa bai ma san suna yi ba kukansa kawai ya ke yana neman ɗauki awajen ubangiji, har sai da likitocin suka ga taƙi haihuwa suka sanarwa babbansu.

Nan da nan ya ce tiyata za'ayi mata, saboda haka ya bawa sulaiman wata zungureriyar takarda wai ya sanya hannu kai.


 Jikinsa sai rawa ya ke, ya sanya hannun amman zuciyarsa sai zillo take masa, don yaso maryam ta haihu da kanta ko don wannan wahalar da tasha ga kuma wata wahalar ta daban ta tiyata, wanda yana ji ana bashi labari har robar fitsari ake sanyawa mata idan anyi musu.

 Hannunsa dai tamkar ba zai iya ɗaukar biron ba, haka ya yi rubutun yana tunanin ina zai je ya samo kuɗin?.


 baturen likitan ya ce" Sulaiman zaku biya dubu ɗari da goma, don yi mata tiyatar sai ka je ka kawo kuɗin don asamu aceto rayuwarta da gaggawa".

Yana faɗar hakan ya cigaba da aikinsa tamkar ba shi ne ya yi magana ba.

Sulaiman ya kasa ko da motsawa,har sai da Abu jafar ya ce" tashi mu fita Sulaiman, nasan damuwar da kake ciki amman aƙwai Allah saboda haka muje nasan yadda zamuyi".


 ya tashi suka fita, suna fitowa Abu jafar ya ce" Sulaiman ina da naira dubu hamsin, ɗazu akayi min albashi mu fita in ciro su sai mu kawo, sai ka ƙara ɗan bubbugawa ka samo ɗari da goman don asamu abayar aceto rayuwarta da kuma ɗan cikinta".


 Sulaiman yaji daɗi, amman duk da haka gabansa faɗuwa ya ke don bai san ma inda zai je ya nemo waɗannan kuɗin ba? Kuma ko karen mahaukatane ya cije sa bai isa yaje wajen Baba hari don ya nemi rance ba, don yasan tana adashin mutane da sai ta ranta masa zuwa nan da ƙwana biyu yaje yayi aiko tuƙuru ya dawo mata da kuɗin, sanin halin na ta ya sanya sa barin zancen sa acikinsa.


kuma ko da ya furta ma ba amfani za tayi masa ba, don ko giyar wake yasha ba zata basa ba ko da badon tsanar da ta yiwa Maryam ba, ko don mugun son kuɗi irin na ta ba bayar wa za tayi ba. ya yi shiru yana tunani ya yinda suke tafiya don ciro kuɗin, wata shawara ta faɗo masa ya ce" yes".



      ~~~~~~~~

ABUJA WUSE 2

Gidan sady

        Cike da takaicin abinda AD ya yi mata ta yi fakin ɗin hamshaƙiyar motarta, sannan sady tazo ta buɗe mata ƙofar gidan tana fitowa da hucinta ta shige gidan, Sady ta bita da kallo tana ware hannu gamida taɓe baki ta ce"uhm bani nakar zomon ba, rataya ai aka bani".


 afalo ta baje tana huci, Sady ta shigo ta zauna akan ɗan stool ɗin dake falonta, sannan ta ce" wai ni lafiya kuwa aminiya? Ni naga kin shigo cikin fushi? ba dai ke da gogan bane"?.


 ta wani haɗe rai gamida buga ƙafa sannan ta ce" uhm ai wallahi AD ya Bani mamaki, just kawai don na yi tiktok shikkenan zai sanyani abaki, wai saboda haka ma ya ce inje sai ya neme ni? Ai wallahi yadda na zuciya ɗinnan ba zan koma ba, tunda haka ya zaɓa yaje ya zauna da waɗannan munafukan iyayen na sa". ta faɗi hakan tana buga wani mugun tsaki tamkar tsakar da ta yini bata ci ba.


 Sady ta ce" just tiktok kawai? haba ashe shi haryanzu bai waye ba? ai ni aganina Tiktok ba komi bane face nishaɗi da kuma rage lokaci, amman shi ne don kinyi har da ɗaukar wannan mummunan matakin?".


Hajara ta ce" ganemin hanya dai? wai kamar ni zai yi wa haka? ai wallahi ya taro mach, sai na yi masa abinda zai daɗe bai manta ba".


 Sady sake riƙe da baki ta ce" oh ki tashi kije ki ɗan watsa ruwa, wannan bala'in yaƙin da akasha har rana ta fara bugar ki".


 da kallon ƙasa ta kalle ta sannan ta ce" oh har ma na fara warin rana ko? to wallahi kema sai in bar miki gidanki yanzu yanzun nan, don ma bana son zuwa waccan ƙazamin gidan namu, wallahi da tuni na tafi".


 Sady ta ce" rufamin asiri, babbar yarinya kamar ki ai bai kamata aganki a wancan gidan na ku ba, saboda haka yi haƙuri tashi kiyi wankan sai musan ta inda zamu ɓullowa lamarin".


 ta tashi ba tare da tace mata komi ba, da ya ke tasan inda komi ya ke sai ta wuce ban ɗakin duk da tsaftar Sady amman gani take ina ai ita dai tafi ƙarfin zama acikin wannan gidan da Sady take, duk da ba laifi gidan yafi na iyayenta amman ita dai aganinta wannan ai ci baya ne ta auri miji me ƙaramin ƙarfi irin na Sady, ta fara wanka da ruwan ɗumin da ta tara a bokiti a famfon dake ban ɗakin, tana wani ya mutsa baki..................

MRS GREEN CE🫵


*MAMAN AMEER DILKA SOAP*


*muna siyar da kayan gyaran jiki, jikinki ya yi silɓi da kuma shining ki zama tauraruwa acikin mata*.


muna siyar da dilka

 soap

mulato soap

 white scrub

 da dai sauran kayan gyaran jiki har ma dana ƙamshi kamar👉🏽


Gab gab

Layal

Hawi

Cus cus

Coucounot sandal,

Marshoosh,

Frami

Kajiji,

Sandal.flask

Qalbul oud,

Noor hayaty,

Kindikaye,

Sultana,

Kajiji,

Sandal asly 

Malika

Night queen

Misk humra,

White humra

Dufur khumura,

Khumura mukabassiya.


 ga lambar wayata, don siyan ɗaya ko sari MAMAN AMIR GIDAN GYARA ƘAMSHI.

***