p-5
_*🍇SILAR AURENA🍇*_
TAKU NA 1
Book 1📖
*NA*
Rabiatu Bashir Abdullahi
*UMMU MAHER(MRS GREEN)*🍃
_*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*_
*UMMU MAHER COLLECTION👜👜*
_Domin siyan kaya masu sauƙi da rahusa danna wannan link ɗin na ƙasa_👇🏽
***
C3tsX4CqiEp939DhYvJ3SZ
*_KARANTA SILAR AURENA TA AREWA
BOOKS HANKALI ƘWANCE👇🏽_*
https://arewabooks.com/book?id
=65bd172f88cb015808e5fc25
*_KARANTA SILAR AURENA TA WATTPAD HANKALI ƘWANCE_👇🏽*
***
1420716493?utm_source=android&utm_
medium
=link&utm_content=share_published&wp
_page=create_on_publish&wp_
uname=Rabiatu333
SHAFI NA 5
_______________Sady ta ce"kyaji dashi dai, ƴar talaka amman sai shegen girman kai da kuma iya ɗagawa".
ta faɗi hakan tana ɗauke kayan da aminiyarta ta ajje mata akan kujera tana mita kaɗan kaɗan" mutum sai shegiyar ƙazanta, yo bama dole namiji ya koro kaba ni dai ba za'a zomin gida ahanani sakat da mijina ba, lallaɓata zanyi ta tafi gidansu can ta ƙarata wajen Innah da Baba, idan ma sakinta zai yi ni hakama nake so in samu hanyar cusa ƙamwata muyi ta amshe kuɗaɗen, muna biyayya sau da ƙafa".
Dai dai lokacin ta fito daga wanka, tana wani ya mutsa fuska ta ce" Gaskiya Sady ya kamata kuyi gyara agidan nan, ku kuma ma ku rushesa baki ɗaya don yayi datti da yawa wallahi, dubi fa? Sunan wai na yi wanka duk jikina kamar banyi ba, saboda ina sauri sauri wajen yin wankan".
Sady ta riƙe baki, gamida sakin baki sheƙeƙe ta ce" au Allah, sannu matar multi biloniya ai sai ki sanya arushe mana gidan, kinga sai asake wani tunda mu dai ba muda kuɗin canja rushewa".
ta wani yarr da idonta, yadda take wajen siye zuciyar maza da dama ciki kuwa har da mijinta, kunsan maza da son fari shiyasa da damansu ake siye su awajen fari.
ta ce" ni dai daɗi na dake Sady aƙwai son kuɗin tsiya, yaushe nema na turo miki da 100k yanzu har kin kashe su"??.
Sady ta yi mata wani kallo sannan ta ce" da kika turomin dubu ɗarin maganin kaina nayi dasu, ba maganin hana ɗaukar ciki aka siyo miki ba, da zaki wani ce kin aikomin da kuɗi? Malama idan kina son yimin gori ne kawai ki faɗamin"?.
Hajara bata son ɓacin ran Sady, saboda wani abu da ta ɓoyewa kanta sani saboda haka ta ce" to yi haƙuri yanzu dai ina cikin ɓacin rai ne, kuma wallahi inason ki bani shawarar yadda zanyi don so nake in koma very soon, don wallahi idan babu AD bazan taɓa iya rayuwa ba kinsan fa shi ne hope ɗina".
ta faɗi hakan cikin marairaicewar fuska.
Sady ta ce" uhm to ai ke ce kullum idan na ce miko kizo ki tsunduma cikin harka sai kice min ba haka ba, yanzu da kin bari na kai ki wajen SAGUDU da tuni kin juya kan banza, sai yadda kika yi dashi kika ce wai ke kina tsoron a cutar miki dashi, to ai gashinan sai juyaki yake a tanda tamkar tandar waina".
"Hajara yanzu ya za'ayi to"?.
Sady ta bushe da dariya sannan ta ce" ni ko yanzu indai har ashirye kike sai muje, sai dai fa ki zuge aljihun jakarki don wallahi kuɗi ke magana awajen, manyan mata ya kewa aiki ba jigari jigari ba".
ta cire taguminta sannan ta ja ajiyar zuciya ta ce" wai ke Sady kin manta yadda asiri ya ke ajikin AD ne? Ko da ya kamashi daga baya sai ya sake sa, yanzu duk irin abubuwan dana dingayi abaya duk abanza, common tiktok yana neman tara min mutane akansa? gaskiya abin ya bani mamaki wallahi, ban taɓa tunanin zai yimin abinda yayi ɗin ba, sai gashi yayi min kora mafi muni da ban taɓa zato ba, wallahi aminiya da wanine ya ce AD zai yimin abinda yayimin ba zan taɓa yarda ba, ƙarshe ma faɗa ne zai haɗani da wanda ya yi min wannan mummunan furucin".
Sady ta ce" aikin banza aikin wofi, yo an faɗa miki yanzu aikin ƊAN TSITU yana ci ne? shiyasa na laluba na shiga gari na nemo mana wannan, wanda zai share mana hawayenmu don wallahi yanzu idan har baki tashi tsaye ba bazaki iya zama da ƙafafunki agidan ki ba, ke idan ma ance ki fito wallahi baki isa ko fito ɗin ba".
"yanzu ina da miliyan biyar a accoun ɗina, ina ganin ai zai isa ko"?.
Tuni Sady ta fito da manya manyan idanuwanta na son kuɗi ta ce" yauwa ko ke fa? ai indai kina son ayi miki aikin da duk wata zai dinga turo miki wasu manyan kuɗi sai duk ahaɗa ayi miki, adaɗe mallake miki shi sai yadda kika yi dashi waɗannan munafukan iyayen nasa ma adaɗe nesa dasu dashi, ke sai ayi musu farraƙu ma baki ɗaya ta yadda zasu manta suna daɗa me suna IBRAHIM shima ya manta yana da wasu iyaye wai su dangin ME ƘAMSHI ko menene ma"?.
tuni Hajara ta saki fara'a don ita akullum burinta bai wuce araba mijinta da iyayensa ba, hai- hata hai hata ta yadda zasu manta dashi shima ya manta dasu.
Sady ta ce" yauwa tunda kinyi wanka tashi ki shirya, sai mu samu mu wuce ko"?.
Shiryawa tayi cikin wani tsadaddan less ɗinta, wanda ta taho dashi don ita Hajara ta tsani ta shiga waje taga wani ya fita sai dai ita tafi wata, shiyasa akullum duk kuɗaɗenta suke ƙarewa wajen siyan suturu masu masifar tsada, ta yadda ko kai me kuɗine kaji irin kuɗin sai ka riƙe baki saboda firgita.
ta buga uban ɗauri, tamkar babu wani abinda ya ke damunta alhalin zuciyarta cike take da begen mijinta, namijin ingarma shi ɗaya tilo me sarrafa zuciyar Hajara.
Sady na ganinta ta sara mata 👍🏻 sannan ta ce"kaga mata agidan Admiral Ibrahim ji ƙamshi, gaskiya kinyi kyau kuma dole asara miki giwar mata,Hajara tauraruwa acikin ɗibban taurari, gaskiya Ad ya yiwa maza zarra dole maza su dinga rububinki don wallahi ke ɗin ƙarshe ce awanka".
wani farr tayi da idonta sannan ta ce" uhm gaskiya naji daɗin wannan washin da kika yimin, sai kace ƴar maroƙa? Sady ko dai asalin familinku maroƙa ne"?.
Sady ta galla mata wani kallo sannan ta ce" to ai kanki kike zagi Hajara, tunda dangin mahaifiyarki kaf ɗinsu maroƙa ne, saboda haka kinga ni bani kike zagi ba".
Hajara ta wani galla mata kallo ta ce" mu wuce don Allah, don ke ba a abin arziƙi dake".
anan nake jan hankalin mata, don Allah ku dena bin bokayen nan ƴan tsibbu wallahi wannan abin ba zai taɓa barinku ku zauna lafiya ba, domin shi asiri lokaci ne dashi idan ya karye shikkenan.sannan mu daina bin shawarae ƙawaye wata ƙawar ma bata son zamanki agidan mijin, kamar Sady da Hajara kunga bata son aminiyarta ta zauna agidan mijin gashi ma har ƙwayar hana ɗaukar ciki take amso mata, ya Allah ka tsare mana zuƙatanmu amin!.
ga grp na koyon sana'ar mayafi da ribon na yara, naira 500 zako bayar ki koya. sannan aƙwai na koyar da graphics ga me so domin dogaro da kai.
ka danna wannan link ɗin.
***
/FHgAO8onZ0LHIRTHPG2qY4
~~~~~~~~~
…………Sulaiman ya buga amman bai samo wannan dubu sittin ɗin ba, sai suka yanke shawarar bada 50k ɗin daga baya sai su cika dubu sittn ɗin.
suna zuwa wajen biyan kuɗin sukace ba zasu amshi dubu hamsin ba, hankalin Sulaiman ya tashi sosai ya rasa yadda zai yi da rayuwarsa, yana cikin wannan halin ne Halima ƙanwarsa ta iso asibitin daman tun ɗazu ta kirasa awayarsa ya faɗa mata ce war yana suna asibiti sannan har ya faɗa mata sunan asibitin, duk gidan babu wanda ya neme sa sai ita kaɗai halin Baba hari har yanzu babu wanda ya canza sai ma gaba da ya yi.
Halima ta kalle shi cike da tausayin yayanta ta ce" yaya yanzu ya ake ciki? bata haihu bane"?.
ya buɗe bakinsa da ƙer ya fara magana" Halima bata haihu ba wai tiyata zasu yi mata".
cike da tausayin yayanta da matarsa ta fara ƙwalla, sannan ta ɗaga hannunta sama ta ce" ya Allah almusawwiru ka kawowa wannan baiwa taka ɗauki, Allah ya sauke ta lafiya Allah ka kawowa yayana ɗauki ya samu waɗannan maƙudan kuɗaɗen".
ta sauke hannunta tana shafawa ahankali.
tana ajje hannunta yaya Umar ya shigo, wayarsa na hannunsa yana duba ƙwatancen da Sulaiman ya yi masa, ita ce ta fara hangosa ta ce" la yaya ga Yaya Umar nan yayan Anty Maryam".
Sosai ya Umar ya ke kallonta, yana hango fuskar Sulaiman afuskarta saboda bai fi sau ɗaya ya taɓa ganin taba.
Sukayi musabaha da ya Umar, ya tambayi me jiki ya ce masa jikinta dai da sauƙi amman sunce tiyata za'ayi mata.
ya umar ya ce" to yanzu anyi mata tiyatar"?.
ya ce" a a ba ayi mata ba".
a matuƙar razane ya Umar ya ce" to me ake jira ne"?.
Sulaiman ya kasa magana, Abu jafar ne ya yi ta maza ya ce" wallahi ba kuɗi ne shiyasa, an samu dai rabi amman ba a samu rabin ba".
ya ce" nawa za a cika".
"dubu hamsin aka samu amman babu dubu sittin".
da sauri ya umar ya bada kuɗin dubu ɗari har da goman duka, sannan ya ce a ajje dubu hamsin ɗin ayi wani abu dashi.
nan da nan kuwa aka shiga tiyatar, cikin ikon Allah aka cirows maryam yaranta ƴan biyu mace dana miji masu kama da Sulaiman don sam basu ɗakko hasken Maryam ba, sai suka ɗauko duhun mahaifinsu Sulaiman....
wata likita macece ta fito, ta tsaya a ƙofar ɗakin da aka yiwa Maryam tiyata, ɗauke da jariri namiji a hannunta ai da gudu Sulaiman ya fanno shi da ya Umar da Halima, duk hankalinsu akan jaririn murna fal fuskarsu sai kuwa Sulaiman ya canja fuska gamida ce wa" ina matata likita? Allah dai yasa tana cikin ƙoshin lafiya"?.
Likita ta ce" tana ciki amman babu wanda zai ganta sai zuwa an jima don ta galabaita sosai, ɗayan jaririyar tana ciki yanzu za'a fito muku da ita ku ganta".
sosai suka kaure da murna, aka fito musu da ɗayar jaririyar bakin Sulaiman awaje tamkar an haifa masa duniya yana yi wa Allah godiya daya basa wannan kyautar da kuɗi baya iya siyar su sai dai Allah buwayi gagara misali ya azurta ka dasu, hawaye ne suka shiga sakko masa na murna ahankali ahankali masu sanyi.............
MRS GREEN CE🫵
COMMENTS
SHARE FISABILILLAH👏🏻
*to ƴan fans na Silar aure na sai agarxaya sunan maryam da yaranta twins, na hango maman amir dasu Sariya suna caskarewa afilin dj, gami da yi wa Baba Hari kallon banza.🤬🤔🤓🤪*
*MAMAN AMEER DILKA SOAP*
*muna siyar da kayan gyaran jiki, jikinki ya yi silɓi da kuma shining ki zama tauraruwa acikin mata*.
muna siyar da dilka
soap
mulato soap
white scrub
da dai sauran kayan gyaran jiki har ma dana ƙamshi kamar👉🏽
Gab gab
Layal
Hawi
Cus cus
Coucounot sandal,
Marshoosh,
Frami
Kajiji,
Sandal.flask
Qalbul oud,
Noor hayaty,
Kindikaye,
Sultana,
Kajiji,
Sandal asly
Malika
Night queen
Misk humra,
White humra
Dufur khumura,
Khumura mukabassiya.
ga lambar wayata, don siyan ɗaya ko sari MAMAN AMIR GIDAN GYARA ƘAMSHI.
***