44
by @azizat
*MUTUM.....Mugu ne*
44
Ɗakin Zaytunah zai nufa sai kuma zuciyarsa ta ingiza shi ƙasa, yana zuwa ƙofar ɗakin ya ji ta a rufe, ya shiga ƙwanƙwasawa amma ba alamar za a buɗe.
"Naziha open the door please"
Tana jin maganarsa ta ɗau filo ta toshe kunnen ta da shi.
Ganin no response daga wajenta ya sa shi haurawa sama dan ɗaukar spare key na ɗakin.
Yana shiga ɗakinsa ya tarar Zaytunah tana gaban mirror tana taje gashinta. Ba tare da ta juyo ba tace " my one, ina ga issue ɗin yarinyar nan tun kafin ta lalace anan gara ka maida ita inda ta fito"
"Ba inda za ta je, infact idan akwai mai shirin barin gidan nan ke ce"
A harzuƙe ta juyo tana kallonsa " my one what do you mean?"
" Zaytunah tsakanin ki da Allah mi kika nema a gidana kika rasa? I did everything for you amma kin kasa respecting ɗina, da girma na kina so ki zubar min da mutuncina"
"Wai mi na yi ne kuma?"
"Why did you beat her? Why!" Ya daka mata tsawa
Sai da ta firgita.
"My one akan banzan yarinyar nan kake min ihu. To wallahi ko ni ko ita a gidan nan"
"Get out of my room" ya faɗi da ƙarfi
" what!"
"Kin ji mi na ce ai, fita min daga ɗaki"
" my one akan Nazihan?"
"Get out before i loose my temper" ya sa ke daka mata tsawa.
Idanunsa ne suka nuna mata ba da wasa yake ba.
Ta wuce simi-simi ta bar ɗakin. Tana fita ya ɗau spare keys na gidan ya fita a hanya ya ke duba wanne ne na ɗakin Ziha a ciki.
Jin ya bar bakin ƙofar yasa Naziha ta taso ta fara tattara kayanta tana zubawa a akwati sai sheshsheƙar kuka take yi.
Ji ta yi an buɗe ƙofar an shigo, ta kalle shi ta kau da kai ta cigaba da abin da ta ke yi.
"What are you doing?"
Duk da Uncle Saj mai girma ne a wajenta amma dole ta nuna ma sa zaman ta ya ƙare a gidansa. Ta ce " kaya na nake haɗawa, zan koma Lagos gobe"
" bisa izinin wa kenan?" Ya tambaya yana matsowa daf da ita
" ra'ayin kaina"
"Ba inda za ki je"
"Uncle whether you like it or not tafiya zan yi, zamana a gidanka ya ƙare"
Hannunta ɗaya ya riƙe ya ɗago da fiskarta ya ce "kalli idona" ta ƙi ɗago ido sai ma hawaye daya cigaba da gangarowa.
Ya sa hannu ya fara share mata hawaye ya ce " I'm sorry Naziha, tabbas ni da matata ba mu kyauta miki ba. Ki yi haƙuri"
"Uncle...." sai kuma ta yi shiru
" kina da right ki yi fishi da ni Ziha, saboda na yi alƙawarin kula da ke amma a cikin gidana aka ƙuntata miki, aka ci mutuncin ki. Ki yi haƙuri dan Allah, ban san mi yasa na mare ki ɗazu ba, abin dana sani shine I'm just trying to protect you. Ke alkhairi ce a rayuwa ta, I can never hurt you"
Kalamansa suka kashe mata jiki. A hankali ta ce
"I'm sorry too"
"It's my fault ban yi bincike ba" ya ja ta ya zaunar da ita gefen gado shima ya zauna ya ce " Kaman kin saba da Amber Stevens ko?" Ta gyaɗa ma sa kai.
" gidansu na da nisa daga nan"
"Yes"
"Dr Jamal shi ya kaiki gidan ko dama kin san gidan ne?"
A hankali ya dinga mata tambayoyi a fakaice har sai da ya gano abinda ya faru.
" Ziha as your guardian, ina so ki fita harkar Dr Jamal. Ko kiran ki yayi kar ki ɗauka kin ji?"
" Yes Uncle"
Tambayarta yai ko ta ci abinci, Ta ce ta ci
"To gashi ni kuma yunwa na ke ji ya za a yi?"
Ta ɗago ido ta kalle shi, ya ɗaga mata gira ta yi saurin sunkuyar da kai.
Ki zo mu je ki haɗa min tea...
Kunnensu ƙaras jikin ƙofar Ziha, tunda Uncle Saj ya shiga ɗakin suka kasa kunne suna jin mi ke faruwa. Kaɗan-kaɗan suke fahimtar mi ake faɗa musamman Ziha da muryan ta yake ciki-ciki saboda kuka da ta yi.
Suna jin takun Uncle Sajid su ka bar wajen da gudu.
Cup biyu ya ce ta haɗa, suka zauna a dining suna sha a hankali.
Mamakin kanta ta ke jin few minutes ago ta yanke shawaran barin gidan ga shi Uncle Saj ya sa ta sauko.
" ko kaɗan bana ƙaunar ki yi nisa da ni Ziha" ya faɗa a zuciyarsa.
A fili kuma ya ce " Ziha kar ƙi ƙara tunanin barin gidan nan kin ji?"
Naziha ta gyaɗa ma sa kai.
Zaytunah na shiga ɗakinta ta ɗau waya ta kira Sady ta zayyane ma ta komai. Sady ta bata haƙuri ta ce kar ta ɗau mataki saboda plans ɗinsu ya tafi dai dai. Duk da ba ta ji daɗin haka ba, amma ta san muddin plan ɗinsu ya tafi dai dai to ƙarshen zaman Ziha a gidan nan ya zo. Ta jima tana juye-juye kafin bacci ya tafi da ita.
*
Washegari kamar babu abinda ya faru jiya, Zaytunah tsakaninta da Ziha sai harara, sai tsaki. 'Yanbiyu kuma sai tsokalar Ziha suke wai " ita ce zuciyar Uncle Saj"
Shi da kan shi ya ja mota ya kai su Asibiti haka nan shi ya kai ta makaranta. Su na tafiya ya sanar da ita zai yi tafiya ranar laraba.
Ziha ta ce da shi"Uncle, kai kam tunda aka shiga watan nan ba kya sati ba ka yi tafiya ba"
" Ziha kenan, responsibilities ne suka ƙaru min. Dukiyar su Yamin yana hannuna dole na kula da shi. Ga shi nima ɗan kasuwa ne"
'"Allah Ubangiji ya taimaka maka Uncle" ya amsa da Amin yana murmushi.
Ranar Talata da yamma Sajid ya samu Zaytunah a ɗakinta tana kwance ya ce mata " gobe zan yi tafiya, hopefully na dawo friday, idan kuma bai yiwu ba, Monday ina Nigeria"
Ko kallonsa ba ta yi ba sai ma wayarta da ta jawo tana dannawa
" Zaytunah for the last time zan sake mi ki warning, ko zunguri ban yarda ki yiwa Ziha ba balle ki dake ta. Na bar wannan ya wuce ne saboda ba girma na bane ace koyaushe muna hayaniya a gida yara na jinmu. Amma idan kika sake dukan Naziha a gidan nan, wallahi za ki yi mamaki"
" kai ka san wannan, abinda na sani shine wannan yarinyar ƙarshen zamanta a gidan nan ya zo"
"Try me Zaytunah" yana ji tana ƙananan magana ƙasa-ƙasa ya fita daga ɗakin.
Ƙarfe takwas na safe ta yi masa a airport, sai da suka sauke Ziha a Asibiti sannan driver ya wuce da shi airport ɗin...
*
Naziha ta yi mamaki da Zaytunah ta bari driver ya zo ɗaukanta duk da Sajid baya gari.
Ta shigo gidan babu kowa a falo, ta wuce ɗakinta direct. Jin ana ƙwanƙwasa mata ƙofa yasa ta fasa cire kayan jikinta ta zo ta buɗe ƙofar.
Ganin Zaytunah tsaye sai zuciyarta ya fara bugawa da sauri.
"Aaaanty ina wuni"
" Lafiya Naziha, an dawo?"
Da mamaki ta amsa mata da "eh"
" su Yamin ba sa nan, dan Allah ki je ta bakin layi akwai friend ɗina ba ta san gidan nan ba zata kawo min saƙo ki ƙarɓo min, na mata kwatance ba ta gane ba ga shi kaina ciwo yake da na je na ɗauko ta"
Maganar bai kama hankalinta ba dan akwai driver a gidan da za ta iya sawa ya je bakin hanya ya karɓo saƙon. Ta dai daure ta ce " bari na sa hijab na fito"
Minti biyu ta fito ta ce "Anty ki ban numbar ta in case ban gane ta ba"
Ta ɗau wayar ta ta kira numbar ƙarya ta ba ta "sunan ta Hajiya Aisha "
"Ok barin fita"
Da sauri ta fito daga gidan duk da zuciyarta na bugawa amma dole ta je aikan Zaytunah ko dan ta guji gori.
Ba ta yi nisa ba wata mota ta sha gabanta ta tsaya, kafin ta ankara aka damƙota aka cusa ta cikin motar. Tana ihu wani a cikin motar ya rufe ma ta baki da wani ƙyalle.
Jami'in yana cikin kewayawa ta anguwan Chief ɗin da ya ke aiki akansa ya ga tsayuwar motar da kuma ɗaukan yarinyar da suka yi. Kafin ya yi gudu ya je har sun figi motar sun gudu. Ya yi nasarar riƙe numbar motar wannan ya sa shi ciro wayarsa ya shiga kiran wani colleague ɗinsa, a lokaci guda kuma gudu yake dan ya isa wajen da ya parking motarsa.
Sun yi tafiya mai nisa sosai kafin suka tsaya, sun riga sun kulle idonta da bakinta ba abin da ta ke gani. Cikin zuciyarta ta ke kwararo addu'o'i. Ji ta yi an sungume ta ana tafiya da ita, daga baya aka kwantar da ita ƙasa, sai a lokacin kuma suka buɗe idonta amma ba su buɗe mata baki ba sannan ba su kwance hannayenta ba.
Ɗaya daga ciki ya ɗau waya yayi kira cikin seconds shida ya kashe wayar. Sai kuma ya kunna camerar wayar ya fara musu video. Dukkansu ukun sun saka mask kenan ba wanda zai gane su. Da ya gama ɗaukan fiskar Naziha sai ya turawa numbar da ya kira ɗazu. A lokaci guda kuma ɗaya daga cikinsu ya fara ƙoƙarin tuɓe wandonsa. Ziha na ganin haka ta shiga kici-kici idonta na zubda hawaye...
***
New York, USA
Ƙarfe goma na dare kenan a garin na New york, yanzu ya fito daga meeting zai wuce gida. Cikin taxi wata number ta fara kiransa, da kamar ba zai ɗauki kiran ba dan numbar Nigeria ce sai kuma ya ɗauka ɗin.
"Idan kana son lafiyar Naziha ka saurare ni" muryan ta faɗi wanda babu tamtama ya shaida muryan Sady ce.
"Me kike shirin yi?" Ya daka mata tsaya muryarsa cike da damuwa.
" na san kana son Naziha kuma ni duk abinda kake so ina so, shi yasa ba zan bari wani abu ya taɓa lafiyar yarinyar da kake so ba"
" Go straight to the point" ya faɗa murya a kausashe
" ka kalli videon dana tura maka, Zaytunah ta bada kwangilar a yiwa Naziha fyaɗe"
Hannunsa na rawa ya cire wayan a kunne ya shiga binciko video. Yana gani ya kunna 12 second video ne. Ziha kwance a ƙasa an ɗaure ta sai kuma maza biyu da shi mai ɗaukan video ɗin wanda dukkan su fiskarsu a rufe.
"Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'oun" ya maimaita da ƙarfi. Numbar Sady ya kira cikin tsawa ya ke magana bayan ta ɗau kiran " idan wani abu ya samu Naziha I swear to you a prison za ki ƙarasa rayuwarki"
"Ba ni za ka yiwa barazanar nan ba. Ka kira matarka sai ka gaya mata. I'm sure by now dukka mazan nan uku sun hau kan Naziha"
"Take me to airport"
Direban taxi'n ya ce " what did you say?"
"Take me to the fucking airport"
"Ok Sir "
Irin bugawar da ƙirjinsa ke yi kamar ana bugun ƙanƙara da guduma. Numbar Zaytunah ya ke kira ba a ɗauka ba, ya shiga kiran na Ziha shima haka. Hankalinsa ya daɗa tashi. Ya kira Yamin bugu ɗaya aka ɗauka, kafin Yamin ya ce wani abu ya ce da shi " Yamin duba min ko Naziha na gida"
" no Uncle, ɗazu mu ka dawo bata nan"
Sajid ya sake rikicewa yace " ka kaiwa Zaytunah wayarka"
"Uncle, is everything alright?"
"Na ce ka kai wa Zaytunah wayar" ya daka masa tsawa.
Yamin ya fita daga ɗakinsa da gudu.
" Aunt Zaytunah, Uncle zai yi magana da ke"
Ta karɓi wayar ta ce "My one ya han..."
" Zaytunah na roƙe ƙi, please kar wani abu ya samu Naziha, dan Allah ki hana su aikata mummunan hukuncin nan. Zaytunah idan suka ci galaba akan Ziha na rantse miki da Allah zamana da ke ya ƙare"
Zaytunah ta ce "dole ta bar gidan nan yau idan kuma ta ƙi komai na iya faruwa da ita" ta kashe kiran tana tsaki.
Plan ɗin da Sady ta gayawa Zaytunah shine wai za a kidnapping Ziha sai a mata barazana da bindiga akan ta tattara kayanta ta bar gidan idan kuma ba haka ba za su kashe ta. Hakan zai sa ta ji tsoro ta tafi. Sai dai Sady tarko ta ɗanawa Zaytunah akan idan aka kama Ziha sai a mata fyaɗe hakan zai sa Sajid ya ji haushi ya saki Zaytunah.
Kiran Mommyn Zaytunah Sajid ya yi ya ce mara ta roƙi Zaytunah kar wani abu ya samu Ziha, idan wani abu ya faru da Ziha ba za su ji daɗin matakin da zai ɗauka ba. Mommy bata gane zancen ba, jin ya kashe wayar yasa ta fara kiran numbar Zaytunah...
Roƙo yake yi a airport ɗin amma still magana ɗaya ne wai babu jirgin da zai je Nigeria sai nan da awa biyar. Sai kiran su Yamin ya ke akai-akai amma still amsar ɗaya ne Ziha bata dawo ba. Ga shi Sady ma numbar da ta kira shi da shi ya dena shiga. Haka ya zauna a airport ya zuba tagumi baya tunanin zai iya motsawa a inda ya ke sai an samu jirgi. Tunanin masifar da zai shiga idan aka yi wa Ziha fyaɗe ya ke, yayinda hawaye ke zuba a idanunsa.
Washe gari.....
A airport ya zauna tsawon awa biyar har aka samu jirgi suka tashi. Da ka kalle shi za ka ga tsantsan damuwa a tattare da shi. Gani ya ke yi kamar jirgin ba ya gudu. Idan da yana da ikon ɓacewa ya gan shi a Abuja yanzun nan da zai yi.
***
NIGERIA...
Hankalinsu Yamin ma ya tashi dan tuni Sajid ya faɗa musu abin da ke faruwa, suma ɗin kwanan zaune suka yi. Sun roƙi Zaytunah ta gaya musu inda Ziha ta ke amma ta ƙi, ƙarshe ma cewa ta yi kar su sake damunta da batun Naziga.
Ita kanta jikinta ya yi sanyi dan rashin dawowar Ziha gidan kamar an samu matsala ne a plan ɗinsu. Ga shi numbar Sady ba ya shiga.
Sai da ta karya sannan ta yi shirin zuwa gidan Sady dan ta ji abinda ke faruwa.
"Aunt Zaytunah Uncle na hanya probably nan da minti sha biyar za su iya sauka"
"kada na fita kenan Yassar?"
" no, kawai na gaya miki ne"
Ba ta saurare shi ba ta wuce ta fita...
" har yanzu ba a ga Ziha ba?"
Abin da ya fara tambaya kenan lokacin da ya shigo gidan.
Yassar yace "Uncle ko za mu sanar da police?"
"Ina Zaytunah?"
"Ta fita"
Sama ya haura suka bi bayansa da sauri. Study room ya shiga ya kunna system ɗinsa ya fara haɗa wasu abubuwa daga ƙarshe ya saita komai. Abubuwan da suka faru jiya a gidan ya ke tariyowa. Su kan su 'yanbiyu basu san akwai CCTV camera a gidan ba. Haka ya dinga tarewa har ya kai lokacin da Ziha ta dawo gidan da yamma da lokacin da Zaytunah ta aike ta har zuwa fitanta wanda daga nan ne kuma Ziha bata dawo ba. Yana kai wa nan ya ce "we need to tell the police"
Rashin samun Sady a gida yasa ta juyo gida dan ta san by now Sajid ya iso.
A farfajiyan gidan ta yi kiciɓis da Sajid za su wuce police station.
Tana ganinsa jikinta ya yi sanyi, a hankali ta ƙarasa wajensa yana tsaye yana mata kallon da shi kaɗai ya san fassararsa.
"Ina kika kai Naziha?"
"Haba my one, daga dawowa sai maganar Naziha. Ni ban san inda ta ke ba" saukan zafafan mari biyu ta ji a fiskarta, bakinta na rawa ta ce " Sajid you slapped me"
Ya fiddo wayarsa ya nuna mata video'n da Sady ta turo masa.
"My one ya aka yi ka samu wannan?"
"Dan Uban ki za ki gaya min inda Ziha ta ke ko sai jikinki ya gaya mi ki"
"Sajid mi ke faruw..."
Ya fizgo hannunta ya kai mata naushi a fiska, ta yi taga-taga za ta faɗi ya bi ta da naushi har ƙasa tana ihu. " you better start talking, ina Ziha ta ke"
Yamin da Yassar where speechless, tsabar mamaki sun ma rasa mi za su yi. Yamin ne yai saurin riƙe hannun Sajid yana faɗin" Uncle ba girmanka bane dukan mace, please a waje mu ke" hankaɗa shi yai gefe ya cigaba da dukkan Zaytunah.
Dukkansu biyu suka riƙe hannunsa suna ba shi haƙuri. Har wani huci ya ke yi idonsa ya kaɗa ya yi ja.
Yamin ya ce "Uncle, we should focus on finding Naziha not this"
Da ƙyar ya amince ya tashi daga ruwan cikin Zaytunah har lokacin bai bar huci ba.
Maigadi da driver da ihun Zaytunah ya sa suka ƙaraso wajen da gudu suka tsaya cak suna ganin abin mamaki. Tsawon shekara biyu da su ke aiki a gidan ba su taɓa ganin fushin maigidan ba balle har wannan abin kunyar. Lallai ba ƙaramin abu matarsa ta yi da har ya shi ɗaukan wannan mataki ba.
Kiran Mommyn Zaytunah ne ya shigo wayar Sajid, yana ɗauka ya ce " Mommy Zaytunah za ta zo gida koyon haƙuri da biyayyar miji"
"Sajid wai me ke faruwa ne?"
Bai amsa mata ba ya kashe wayar.
"Kai kuma je ka buɗe min gate" ya dakawa Maigadi tsawa.
Yamin da Yasssar sai ƙoƙarin fifita Zaytunah suke, gaba ɗaya jini na fita daga hancinta da baki saboda naushin da Sajid ya mata a fiska.
Ado driver ya ce " ku ɗauke ta barin tada mota mu kaita asibiti............