KWANKWASON JIMINA!! (MAI WUYAR SHAFAWA)

FREE PAGE 2

by @mssxoxo

*_KWANKWASON JIMINA!!_*

  _(MAI WUYAR SHAFAWA)_

     🦩🦯🦾


_NA_


_NANA HAFSATU_

  _MX_


*_ZAFAFA BIYAR 2024_*


*_arewabooks:mssxoxo_*



  *_Free page :02_*


__


 "Ba kiji ciwo ba ai ko?... Ki dai na tsalle tsalle Amna.." Ta karasa fada tana mai tambayar ta da hannu alamar menene?


Amna ta bude dan karamin bakin ta tana furta sunan yafendo a hankali. Ai kuwa bata karasa rufe bakin nata ba yafendo ta karasa dakin tana dogara yar sandar ta.


"Ah yafendo..." Cewar Nawra tana mai danne gefen katitar data zura littafin ta zauna akai.


"Amna tace baki da lafiya ko?"


Nawra ta kakaro murmushi tana kada kanta.


"Da sauki amma.."


"Tun dazu nake cewa kina ina ne duk su Layla suna nan.. Bake kwata kwata. Kwanakin nan na rasa gane kan ki. Na tambayi mahaifiyar ta ki tace zata miki magana. Sai Amna ce danasa Adam ya kirawo ki tace ai baki da lafiya "


Nawra dai kanta a kasa tana lankwasa yatsunta. Tace,


"Uhum... Amman da sauki ai. Nagode sosai"


"Sannu kinji?. Allah ya baki lafiya Nawrah. Kwanta ki huta"


"Tohm yafendo.. "

Nawra ta haye Kan katitar sosai ta kwanta tana mitsitsika idanu..


Yafendo ta mike dakyar tana dafe bango ta fice daga dakin 


Nawra ta sauke katuwar bahaguwar zuciya ganin yafendo ta fita. Tadaga gefen katitar da saurin gaske ta zaro littafin, ta bankada kasan akwatin ta ta saka.


Amna na gefe tana kallon ta. Nawra ta riko hannun kanwar tata tace,


"Nagode sosai Amna tah.. Yau da yafendo taga Ina rubutun nan ai sai an kusa yankani. " Ta karasa fada tana kada Kai.


Amnah tayi murmushi kawai. Tana Wasa da zaren jikin rigar ta.


"Ungo biyar dinnan na baki jeki sayi wani abun"


"Nagode" Amna ta karba cike da farin ciki ta fice da sauri.


Nawra ta kwanta akan katifar ta ta lumshe idanun ta.... Fuskar ta ta gauraye da murmushi. A zuciya take karantowa. idanuwan ta na hasaso mata rubutun haruffan da zanen su. Ya yinda labbanta ke matsowa ahankali tana karanta su...


"Nawra.... Nawra .... Nawra" Layla ta kwada mata kira. Ta shiga dakin nasu.


Nawra ta mike da sauri tana duban ta tace,


"Kai Kib katse ni wallahi"


"Dalla aiken mu akayi..."


"Ina aka aike mu ?"


"Gidan bappah Auwalu."


"Tam. Bari nasaka hijabi"


"Dalla muje a haka kaman wasu manya zamu saka hijabi?" Cewar Layla ta fada tana yiwa Nawra nuni da kanta.


Nawra ta girgiza kai tache,


"Zan saka.. Ammi tace da hakan ake dorewa har girma. "


"Shikenan sai ki saka ai"


Nawra ta girgiza kai. Ta bude wardrobe din kayan su ta dakko hijabin ta ta zura... tana duban kanta a wani madubin su karami dake jikin dressing mirror dinsu..


Tsaf da ita kamar wata babbar budurwa ta dubi Layla dake nannade kasan zaren hannun rigar ta tace,


"Muje"


"Yauwa."


A tare suka futa daga cikin dakin sukayi hanyar fita daga gidan yafendo na daga can runfarta ta hango su tace,


"Nawra kinji sauki me? Layla ba ke kadai aka aika bane sai dakika taso ta?"


"Wai ba..." Bata karasa ba Nawra ta saka hannu ta gwabe wa Layla baki. Da Sauri tace,


"Na ji sauki yafendo yanzu..."


"Mashaa Allahu. To kuyi sauri ku dawo"


"Tohm" suka hada baki..


Fita sukayi daga cikin gidan. Layla ta dubi Nawra cike da mamaki tace,


"Ina tsoron ranar da su bappah zasu Kama ki..."


"Ba zasu Kama nI ba inshaa Allah.. "


"Toh Allah yasa... Ni kam Dadi nakeji bama yi, karatun nan ba fa wani Dadi ne dashi ba kinaji yan maza na fada"

 


"Ni dai inaso"


"To ai shikenan..."


Suna tafe suna hira hadi dawasa a hanya Suka karasa gidan bappan na su. 


Basu dawani nisa sosai. Don hakan bazasuyi wata tafiya can ba Sika karasa.


Bakunan su dauke da sallama suka shigaa cikin gidan.


A zaure Suka ci Karo da shi Yana tafe Yana duban goro a hannun sa.


"Ahh.." Ya fada Yana kallon su


"Bappah Ina kwana?"


"Bappah Ina kwana?" 


Suka shiga gayshe da shi. Ya amsa musu Yana duban su da Karin bayani.


"Bappah Wai Kai ake jira.." Layla ta fada tana duban sa.


"Ai gabi Nan dama candin zani ai. Muje ko?" 


Ya nuna kofa.. suka matsa ya shige suka bi bayan sa suka futa .


"Zo mu biya dangaki.... (Dangaki shine sunan babbar gonar data mamaye rabin garin BUNZA. Gona ce data fi wani garin girma. Itace ake yankawa samarin garin idan zasuyi sure. Kowanne sai a shata masa wani yanki nadaga ciki ya nome. Shi daya ba dan tayi. Idan ya nome ita kuma amaryar dazaa hadasu sure. zata dinga ebo ruwa sawu goma daga Rafinrau (sunan babban rafi ne da wasu ke Kira da teku. Ance duk shekara ma ya kanci mutane sama da dari. To Nan amaren ke zuwa suna ebo ruwa daga rafin da take can bayan garin zuwa gidajen surukan su wato gidan iyayen mazajen. Su Kai su koma har sawu goma. Shikenan sai a daura musu aure. Gwarzon da gwarzuwa kenan. Amfamin noman da angob yayi shikenan sai suyita ci agidan auren nasu. Ruwan nan kuma haka za aita bawa amarya tana girki ko aikin abinci har adadin data evo Kafin aure. .. wannan wata babbar al'adace da Yan yankin BUNZA ke gudanarwa shekara da shekaru...



'Yau farisu ke nome gonar auren su da fiddau.. zo muje kinji?" 


Nawra ta girgiza kanta ,


"Jeki ke kadai "


"Kinsan fada zaa mun agidaa idan ba ke. Idan mu biyu ne kuwa fadan kadan ne bama lalle ayi ba."


Nawra badan taso ba. Tabi bayan Layla suka nufi dangaki don ganewa idanun su noman karshe da farisu angon fiddau zai yi...


 Bappah Muhammad sani ya karasa cikin gidan bakin sa dauke da sallama. Yayi hanyar sashen mahaifiyar su 


Ya durkusa har kasa ya gayshe da ita. Ta amsa kanta a gefe cike da kunyar dan fari.


Duk yaran nata sun hallara. Bappah sani, Bappah Auwalu shine na biyu amman yaci sunan Auwalu Lawan, Bappah salisu da bappah Junaid sai kuma mace guda daya yakunbo aminatu. Wadda itace ta biyun karshe. Bappah Junaid ne autan Dadaa (yafendo)..



_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_


_KU MARMATSO KUSA...🔊_



 _ZAFAFA BIYAR 2024_


_ZAFAFA BIYAR!!!_

_ZAFAFA BIYAR!!_

_ZAFAFA BIYAR!!_


_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_


_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_


 _GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_


_________


     _1_

 *_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_


      _2_

*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_


       _3_

*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_


    _4_

*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;***_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:***_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*****


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_