KWANKWASON JIMINA!! (MAI WUYAR SHAFAWA)

FREE PAGE 3

by @mssxoxo

*_KWANKWASON JIMINA!!_*

  _(MAI WUYAR SHAFAWA)_

     🦩🦯🦾


_NA_


_NANA HAFSATU_

  _MX_


*_ZAFAFA BIYAR 2024_*


*_arewabooks:mssxoxo_*



  *_Free page :03_*




   ***Hajiya Fanta... Wato Dadaa mahaifiyar su Bappah Auwalu kuma kaka ga su Nawra dake kiran ta da yafendo...


Tana a zaune ne akan babbar kujerar parlorn.. parlor ne matsakaici dauke da saitin kujeru dai dai misali. 


Yayinda yaran nata ke zazzaune daga kasa kowannen su yana fuskantar ta.


Dadaa tayi gyaran murya tace,


"Dalilin daya sa na kirawo ku nan gaba daya akan wannan taron abubuwa uku ne zuwa hudu... Kuma dukkanin ku nan babu wani dayasan dalilin hakan sai Allah mahaliccin mu. Sannan bana bukata wani acikin ku ya nemi bijerewa ko ince kawo wata shawara ta daban ga zantukan da zanyi. Ina fatan Kuna saurara?"


"Muna sauraron ki Dadaa" suka hada baki wajen amsa ta..


Dadaa ta kada kai ta cigaba da cewa,


"Allah ya muku albarka duka...Allah ya hade kawunan ku ya kauda fitnah a tsakani. Allah ya raya muku zuri'ah ya albarkace su.. Aamin"


"Aameen Dadaa"


"Aaameen"


"Yauwa ku saurari abunda Zan fada da kyau. Ku Kuma nazarci zantukana a kwakwalen ku. Kada wani yayiwa maganganu na fahimta a baibai ce. Sannan duk abunda na fada Ina fatan ya kasance mafi alkhairi agare mu baki daya"


"Aameen"


"Allah ya kara Miki lafiya Dadaa"


"Aameen... Maganar fitar da ni waje don gano menene gundarin wannan rashin lafiyar tawa ni Fanta na soke ta... Babu ita"


"Amma Dadaa...


"Ya isa karkace komai...sai da na ce muku da fari bana bukata wani acikin ku ya nemi bijerewa ko ince kawo wata shawara ta daban ga zantukan da zanyi. Ku ma kuka amince ko baa ayi hakan ba?"


"Anyi Dadaa."


"Tuba muke"


"Yauwa wannan magana ta futa na soketa. Dukkanin abunda Allah ya kadarta wa bawa na rashin lafiyar kai komai ma da sauran su. Allah ne kadai zai magance maka a duk sanda yaso.. sa'annan wannan lalurori nawa sunci kudaden da cikinmu basu ci ba. Garuruwa nesa dana kusa bawanda baa zaga da Ni asibutin sa ba don gano gundarin ciwo. Don hakan na hakura ni. Wannan ciwo bana warkewa bane .. Allah ne kadai zai mun maganin sa."


"Dadaa ki dai na cewa hakan"


"Me ake jira ne? Dukkanin munan kowa fa tasa yake jira... Mutuwarnan sai ta dauki kowa babba dayaro kowa ba Wanda zata Bari. Don hakan a kyale ni na zauna da ciwo na. Kankarar zunubai ce. Idan Kuma lokacin tafiyar ne yayi Allah yasa mu cika da Imani"


"Ki bar fadin hakan Dadaa"


"Magana ce ta gaskia... Allah ya sa mucika da Imani"


"Aamin Dadaa"


"Aamin"


Suka amsa mata dukkanin su. Dadaa ta Dan dubi fuskokin su. 


Bappah Auwalu ita yake kallo, Bappah sani ma itan yake kalla data kalle shi sai ya sadda kansa kasa. Ya yinda bappah salisu kansa ke akan agogon dake daure a wutsiyar hannun sa yana saita lokaci. Bappah Junaid Kuma kansa a kasa.. Sai yakunbo Aminatu dake lankwasa yatsunta tana duban mahaifiyar tasu Dadaa.


Dadaa ta sauke katuwar ajiyar zuciya tace,


"Allah ya hade kawunan ku...ya kauda fitnah a tsakani. Amin"


"Aamin Dadaa"


"Aamin"


"Sai magana ta gaba akan yaran wajen ku mazan... Wadanda ke makarantar boko yanzu... Tun ba yau ba ahali da yawa na yankin bunza ke aibatar mu kancewa mu muna qafafa muna fatali da al'adar kaka da kakanni. Bama koyi da sauran mutanen gari... Ku dubi ibtila'in daya saukarwa yar wajen ku kalatacciyar al'adar jigilar ruwan Rafinrau zuwa ga gidan surukan ta akan hanyar ta rasu a sawu na bakwai... Wannan munanan al'adu naki jinin su bana kaunar su.. Don hakan tun kafin rasuwar mahaifin ku muka gama magana dashi muka yanke shawara.. Zamu tarkata komai namu mu bar musu yankin nan. Zaman mu acikin sa babban ibtilai ne musanman da zuriyar mu ce kadai ke da kadarorin zinarai ragowa na dutsen bunza..."


"Mashaa Allah Dadaa... Wannan zance naki haka"


"Hakan shike Dadaa.. Allah ya amince"


"Amma Dadaa kina ganin Mutanen Nan zasu kyale mu mu bar yankin nan? Kinsan mugayen alkadarin su akan zuriyar mu"


"Babu abunda suka Isa suyi Mana Wanda Allah bai rubuta ba. Mu mayarda komai gare shi sai ya buda Mana kofa masaukakiya. Don hakan Kar ku wani damu da su. Idan aka sauya yanki sai a kyale yarannan maza suci gaba da karatun su. Matan Kuma a kyale su har zuwa sanda zasu tasa a aurar da su... Duk dai yadda ta kasance din..Kar a tsaurara akan matan nan" 


"Inshaa Allah hakan zaai Dadaa."


"Wannan zance naki haka shike Dadaa"


"Toh Allah ya Mana muwafaqa"


"Aamin Yaa Rabbi


"Sai magana ta karshe.... Dukkanin dukiyar data ragemun a duniya na hadeta waje daya na kasata kashi uku. Kashi daya zaa ajiyeta ayiwa Yara aure idan sun tasa... Su Sameer, Khaleed, Ashiir da ashfeef, Ahmad, Kashi daya zaa bawa miskinan yankin nan wajen mararrabar Ballo Mai sardii.. kashi daya na rabata tsakanin sani, salisu , Auwalu da Kuma ke Aminatu.....


Duk sukayi shiruu suna sauraron ta. Ta daga Kai ta dora akan autan ta Bappah Junaid da kansa ke a kasa tace,


"Kason daya rage na karshe kuma na barwa junaidu shi kadai.... A nan na kawo karshen maganganun da zanyi. Ina fatan Kuma zaku dauki zantuka da nayi kuyi amfani da su. Ko bayan rai na bana fatan wani acikin ku ko zuriyar sa da ya tada wata husuma ta daban. Kudi shirme ne karewa zasuyi su barku. Amman jinin Yan uwantaka na zumunta zumunci ne Mai karfi na har abada. Dan girman Allah kada ku yanke zumuntar dake tsakanin ku. Kada ku yanke alakar da kuka taso tare da ita. Kada ku bari duniya taji kan ku...kada ku bari ayi muku dariya ana zundar ku. Ku hade kawunan ku sai Allah ya shigaa lamuran ku... Hamidniyya Lebanon kada ku bari sunan zuriyar nan ya tagayyara Allah ya muku albarka"


"Aaamin suka hada baki wajen amsa ta.


Tana karasawa ta mike tana dogara yar sandar ta ta bar wajen ta koma daki. 


Donma kada wani ya kawo mata wata maganar ta daban data shiga dakin sai ta sakaya kofar ta turo ta.


Ganin hakan yasa daya bayan daya suka bar wajen. Kowanne da zancen da yake azuciyarta sa.. musnaman akan jimilar kadarorin ta da tayi...



 *Hamidniyya Lebanon....*


Mai karatu zai so yaji asalin tushen wannan zuri'ah dake cikin yankin bunza mai tarin albarka...


Ku biyo ni a next page don jin kanun labaran🏃


_INA MASOYAN ZAFAFA BIYAR?_


_KU MARMATSO KUSA...🔊_



 _ZAFAFA BIYAR 2024_


_ZAFAFA BIYAR!!!_

_ZAFAFA BIYAR!!_

_ZAFAFA BIYAR!!_


_SHIN YAN UWA KUNA DA LABARIN ZAFAFA BIYAR DINKU SUN SAKE ZUWAR MUKU DA WATA TAFIYAR LITTAFAN SU MASU MATUKAR MA'ANA DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA?_


_YA KE YAR UWA KADA KI BARI A BAKI LABARI... DOMIN DA A BAKI GWARA KI BAYAR...WAI AKACE ZUWA DA KAI YAFU AIKE_


 _GA SUNAYEN LITTATTAFAN WANNAN TAFIYAR... CIKE SUKE DA ILIMIN DARUSSAN RAYUWA KI KOYA KUMA KI GYARA DA KAN KI..CIKI HARDA ZALLAR KAUNA TACACCIYA MARAR GAURAYE_


_________


     _1_

 *_AMEENATUH_*🧕💖: _MAMUH GEE_


      _2_

*_TSUTSAR NAMA (ITAMA NAMA CE)🐛👣_*_:BILYN ABDULL_


       _3_

*_GUDUN KADDARA🏃🐾_*:_SAFIYYAH HUGUMA_


    _4_

*_KWANKWASON JIMINA(MAI WUYAR SHAFAWA)🦩🦯_*_:NANA HAFSATU (MX)_



_GUDA DAYA:400_

_BIYU:700_

_UKU:900_

_HUDU: 1200_


_BANK NAME:KEYSTONE_


_BANK ACC NO:6019473875_


_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_


_ATURA SHEDA ZUWA;***_


__

_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:***_


_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_


*****


*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*



_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_