Na ashirin da ɗaya
by @maikosai53
ƘADDARTA CE A HAKA
©Maryam Abdulaziz
Maiƙosai(Matar Abdul)
Page 21
Hamza ne ya zo da tunanin su bincika gidansa na gidan gona, saboda sun san shi sau tari idon abu ya yi masa zafi nan yak ɗan zuwa ya shaƙi iska ko ya sami sa'ada.
Babu musu Ahamd da Hamza suka rankaya zuwa gidan, bugu suke yi sosai sai dai a banza wai jefa agwagwa a ruwa! Domin ƙofar ɗakin a rufe take, kuma baba alamun cewa akawai mutum a cikin gidan. Haka sai ya sanyayar musu da guiwarsu. Har sun juya da nufin komawa Ahmad ya yi wani tunani nan da nan ya shiga dukan ƙyauren ɗakin da son ɓalle ƙofar, ganin haka sai shi ma Hamza ya hau taya shi.
Cikin sa'a suka sami nasarar ɓalla ƙofar ɗakin suka yi wa ɗakin tsinke.
Kwance yake kashirɓan sai faman narkar bacci yake yi, yayin da gefe guda kuma kwalaban giya ne baja-baja a gabansa zube.
Ɗago shi Ahmad ya yi, sai dai ya lura yana ciki bacci, abin da ya sake ƙona zuciyarsa bai son sanda ya kwashe shi da mari ba, ji kake tatas! A ƙufule ya soma magana.
"Giya! Giya Nasir? Me ya sa haka? Me ya yi zafi haka? Saboda kawai ummi ta shimfiɗa maka wani sharaɗi?"
Ganin babu alamon motsi tattare da shi ya sa Hamza furta. "Ka ga ka kamashi mu kai shi asibiti kawai." Ba tare da ya musa masa ba, ya taimaka masa suka kama shi suka sanya shi a mota sai asibiti. Cikin ƙudurar Allah aka karɓesu hannu biyu, nan likitan ya sanar musu da sai an ƙara masa jini saboda jininsa ya yi ƙasa sosai. Nan aka shiga gwada jininsu amma babu wanda ya yi daidai ƙarshe dai sai siya aka yi aka jona masa.
Bayan ya farfaɗo ne Hamza ya kalle shi cike da takaici kana ya ce. "Yaushe ne ka fara shan giya Nasir? Yaushe ne ƙunci ya sa ka manta da Ubangijinka har kake son saɓa mi shi? Me ya sa haka? Me ya sa kake son zaluntar Ummi da matarka Nuriyya?"
Bai ce da shi komai ba, sai ma kallonsa da yake yi kawai da ido.
"A tunaninka hakan ne zai sa Ummi ta sakko ta baka Nuriyyan?" Ahmad ya jefa masa tambayar cike da ƙuncin zuciya. Ji yake tamkar ya rufe shi da duka.
Sai da suka ga jikin nasa da dama-dama sannan Ahmad ya wuce kai tsaye wajen Ummi ya ɗakkota zuwa asibiti, yayin da suka kirawo Nuriyya a waya suka sanar da ita ta zo asibiti. Babu musu kuwa sai ga ta ta iso, yana kwance har ya ɗan faɗa, hawaye ta ji sun soma silalo mata zuwa saman kumatunta.
"Ka yi haƙuri yayana ba laifina ba ne ba" ta ce cikin kuka.
"Kin ga Nuriyya kada ki ɗaga hankalinki, ai dole ne ya yi biyayya ga mahaifiyarsa, domin ita ce ta kawoshi duniyar har ya ganki ya ce yana so." Faɗin Ahmad ransa a matuƙar ɓace.
Nasir kuwa bai tashi yin nadamar abin da ya aikata ba sai da yaga Umminsa ta yi fushi da shi sosai har ta kai ba ta amsa gaisuwarsa, sannan ya tuba ya nuna nadamarsa ƙarara a fili, don ko kaɗan sam baya son fushin umminsa.
Kwanan su biyu suna zaune Ummi, Nuriyya, Kawunsa, da maman Nusaiba suna sake yi masa sannu don har yanzu likita bai sallame shi ba.
Kamar daga sama sai ga Nusaiba ta faɗo cikin ɗakin.
Wani kallon tara saura kwata ta watsawa Nuriyya kafin ta kai ga cewa. "Sannu yaya Nasir! Ai tun farko sai da na ce kada ka amince da auren wannan watsattsiyar saboda ko ba komai jininka ne zai dinga zuƙewa, kasan dai mene ne sana'ar mahaifinta ko shan jin..."
Ba ta ida ƙarasawa ba Nuriyya ta kai mata wata iriyar shaƙa, babu abin da ta tsana a rayuwarta irin ta ji ana aibata iyayenta, ko ana jifansu da wasu kalami.
Ummi kuwa kwashe Nusaiba t yi da mari, yayin da kawu ya sake kwashe ta da wani marin da ya sa taga gilmawar wasu tawayen taurari.
"Fice mini a nan, mutuniyar banza" ya yi furucin cikin ɓacin rai. Nuriyya kuwa surar jakarta ta yi ta fice daga ɗakin cikin wani irin suyar zuciya.
Kai tsaye gida ta wuce, tana zuwa ta kira Munira a waya. Ko da tazo cikin kuka ta shiga sanar da ita abin da ya faru.
Munira ta murmusa kafin ta kai ga cewa. "Ke kuma da yake gaula ce ko? Sai kika ɗakko jaka kika taho, ba kin ce ummi da mahaifinta sun mareta ba? To ai ko haka ya cancanci ki gane ke ma suna baki wata daraja ko?"
"To yaya zan yi Munira? Me kike so na yi? Idon har na ci gaba da zama to zuciyata ce za ta fashe tamkar fashewar bam! shi ya sa kawai na taho." Ta ƙarasa tana zuƙe majinar da ta zubo mata.
"Kin ga dole fa sai kin nutsu , dole ki aro mayafin nutsuwa ki dinga lulluɓawa kanki a duk lokacin da kika haɗu da ita, saboda ita babu abin da take irin taga ta yi muku farraƙu ke da Nasir, dole sai kin zage damtse kin ƙwato mijinki a hannunki." Cewar Munira.
Nuriyya ta sauke wata iriyar ajjiyar zuciya, tana mai kamo hannun Munura tare zirashi cikin nata.
"Na gode sosai Munira, haƙiƙa kin ba ni wani haska sosai, na gode da 'yaruwa ta gari."
Wayarta ce ta ɗau ruri, ko da ta kalli gilashin wayar sunan ummi ta gani ɓaro-ɓaro ya bayyana akai. Wani murmushi ta saki tana sake jin soyayyar Ummi na sake nunkuwa cikin ranta, ko babu komai ummi mace ce da take tsantsan sonta, take son farincikinta. Ko da ta ɗaga umarni ta ba ta akan tana son ganinta gobe.
Washe gari kuwa da wuri ta shirya fisha ta wuce gidan ummi domin amsa kiranta.
Abinci ta saka aka ajjuye mata, wanda da ƙyar Nuriyya ta ci.
"Gobe za a koma koto ko?" Ummi ta jefawa Nuriyya tambayar.
Nuriyya ta sauke gauron numfashi kafin ta kai ga cewa. "I ummi"
"To abin da nake so ki nutsu ki ci gaba da addu'a, domin shi Allah yana tare da bayinsa masu haƙuri da kawaici, sannan ina so ki sani Nasir an sallamoshi kuma ina so ki tare a gidansa yau. Na so na yi wa su gwaggo magana sai na ga gwara na fara zantawa da ke na ji bakinki."
Har ga Allah ta ji daɗi sosai, domin itama tana son zama da Nasir ɗinta a inuwa ɗaya, tana son faranta masa rai, kamar yadda yake ƙoƙarin yi mata.
"Babu komai Ummi, duk abin da kika ce shi za a yi" cewar Nuriyya.
"A'a kin ga Nuriyya ba na son ki yi aiki da abin da zance, idon har ranki baya so to tabbas ba za ki tare ba. Ki yi mini magana daga zuciyarki kawai."
"Na'amin ce ummi" Ta ce a sanyaye.
"Allah ya yi miki albarka, ya baku zaman lafiya. Yanzu zan shirya naje na yi magana da su gwaggo, zan kuma roƙesu su barki a nan don ina son na kaiki da kaina."
Ba don ta so ba ta bi umarnin ummi, wayarta ta janyo ta shiga kiran Munira bayan ummi ta fita.
Sosai ummi ke shirya Nuriyya, duk abin da take yi ba ta sanar da Nasir ba, har sai da ta danganata da gidan shi, sannan ta kira shi ta ce ya yi maza-maza ya zo.
Bai wani ja dogon lokaci ba ya iso gidan nasa kamar yadda ta umarce shi. Sosai take musu faɗa da nasiha akan zamantakewar aure, domin shi zaman aure rayuwace ta dindin da akeso mutu karaba wato takalmin kaza!
Cikin farinciki da ɗoki ya ɗaga mayafin da ya rufe mata fuska yana mai sakar mata wani lallausan murmushi. Ita ma martani ta mayar masa.
A daren ba su sami murje juna ba sosai saboda binciken da yake ta yi akan yadda zai ɓullowa da shari'ar da za su shiga gobe.
***
Rana bata ƙarya, sai dai uwar ɗiya ta ji kunya.
Yau ta kasance ranar da za a sake zaman shari'ar Baffa wacca Nasir ya ɗaukakata ya kaita koton ƙoli.
Gaba ɗaya koton a cike take maƙil da mutane. Kowa ka gani a wajen yazo kashe kwarkwatar idanunsa ne. Alƙali na shigowa kowa ya miƙe tsaye har sai da ya zauna sannan mutane suka zauna da mazaunansu.
Nan magatakarda ya soma gabatar da shari'a, yayin da alƙali ya nemi da lauyoyin da su gfito su gabatar da kansu.
Lauyan gwamnati ne ya tashi ya soma gabatar da kansa, kafin Nasir ya miƙe.
Nan kuma shari'a ta soma, inda alƙali ya yi wasu 'yan rubuce-rubuce kana ya ce. "Ko lauyan me kare wanda ake tuhuma yana da abin cewa?"
Nasir ya miƙe tare da ranƙwafawa kana ya ce. "I ya mai girma mai shari'a"
Ya ɗan numfasa kafin ya sake furta. "Ina so wannan koto mai tarin albarka da ta ba ni izini akan na gabatar da hujjojina, domin tabbatarwa da koto cewa wannan bawan Allahn da ake tuhuma bai aikata abin da ya aikata ba."
"Koto ta baka dama" faɗin alƙali.
Nasir ya ɗan ranƙwafa kana ya ce. "Na gode ya mai shari'a!" Kan ya sake furta.
"Ina so koto ta bayar da izini da a shigo da mutane biyar ɗin da aka kamo a shekaran jiya waɗanda suke hannun 'yan sanda.?"
"Koto ta bayar da izini a shigo da su" Alƙali ya ce.
Wasu ƙartin mutane ne aka shigo da su, dukkansu ƙedarai ne in ka cire mutum ɗaya. Nasir ya sake kallon mai shari'a kana ya ce.
"Waɗannan mutane an yi nasarar cafkesu a shekaran jiya bisa binciken da dsp Lawan ya yi, wanda shi ne ya taimaka mini sosai matuƙa wajen gudanar da bincikena. Duba da kwana biyu ma bana da lafiya ina kwance kan gadon asibiti."
Ya numfasa ya kai kallonsa ga ƙartin kana ya ce. "Ko za ka iya gabatarwa da koto kanka?" ya ƙarasa da jefawa ɗaya daga cikinsu tambayar.
Ba tare da musu ba ya shiga furta. "Ola bude"
"Mece ce sana'arka?" Nasir ya sake jefa masa tambaya.
Ya soma wani irin muzurai ta gunguni ya furta. "Siyar da magunguna."
"Na ka ne ko kuwa a ƙarƙashin wani kake?" Nasir ya sake furta masa.
"Objection ya mai shari'a, bai kamata lauyan da ke tambaya ya dinga sako tambayar da ba ta da ma'ana ba" Lauyan da ke ƙarƙashin gwamnati ya ce yana mai miƙewa tsaye.
"Ƙorafi bai karɓu ba" Alƙali ya ce. Kana ya sake furta.
"Za ka iya ci gaba da tambayoyinka."
"Na gode ya mai girma mai shari'a." Faɗin Nasir, yana sakin wani guntun murmushi.
"Malam Ola ko za ka iya gayawa koto gaskiyar abin da ka sani dangane da magungunan, sannan kuma naka ne ko ba naka ba ne?"
Ola bude ya yi wani irin muzurai kana ya ce. "Ni ma ba nawa ba ne, a ƙasan wani nake."
"Ko za ka gayawa koto a ƙarƙashin wa kake?" Nasir ya ce.
Ola bude ya juya ya kalli mutumin da ya bambanta da su cikin mutanen da aka shigo da shi, kana ya ce. "Na wannan ne"
Nasir ya juya akalar tambayarsa kan wanda aka yi masa nuni da shi kana ya ce. "Shin ko za ka iya bayyanawa koto sunanka?"
Babu musu ya ce. "Suna na Nazy"
"Sunanka na gaskiya" Nasir ya ce.
A daƙile ya amsa da. "Naziru"
"Madalla! Shin ko za ka iya yi wa koto bayanin magaungunan da kake siyarwa.?" Nasir ya ce da shi yana tsare shi da ido.
"Ni ma na buɗe kemis ɗin ne domin taimakon al'umma sai dai buduruwar zuciyata ta kwashe ni ta kaini inda bai kamata ba silar huɗubar sanata I.B wanda shi ne ya shiga safarar gurɓatattun magunguna daga ostireliya zuwa nan, ake shigowa da su ake rarrabawa kemis-kemis ana siyar masa da shi, sai dai ba kowane zai gane ba saboda gaba ɗaya an sabunta mazubin magungunan hatta da lokacin expire ɗin su an sabunta, haka ya sa lokacin da aka buƙaci sanya hannun dr. Abdullahi ya saka ba tare da sanin abin da maganin ke ɗauke da shi ba, bacin an yi nasarar shigo da su shi ne aka soma siyarwa sai kuma ya kasance maganin na gurɓata lafiyar mutane wasu suka mutu wasu suka raunata."
Ko da ya tsagaita, sai Nasir ya yi guntun murmushi domin abin da yake son ya ji ke nan, ya karkata akalarsa ga alƙali kana ya ce.
"Na gama ya mai girma mai shari'a" ya koma ya zauna.
Alƙali ya ce. "Ko lauyan gwamnati na da abin cewa?"
"A'a a mai girma mai shari'a" ya ranƙawafa yana mai zama.
Yayin da alƙali ya sunkuyar da kansa yana rubutu kafin ya ɗago.
"Bisa hujjajar da aka bayar wannan koto mai albarka ta wanke dr.Abdullahi, sannan ta kama ola bude, Naziru da sauran yaran da laifi don haka koto za ta zartar musu da hukuncinsu, sannan ko to na umartar 'yan sanda da su kamo sanata I.B domin ya girbi abin da ya shuka."
Ba a tashi koto ba sai da aka zartar musu da hukuncinsu. Murna, farinciki suka ƙwame zuƙatan bayin Allah Nuriyya, Baffa, Gwaggi, Inna, Ummi, Munira. Babu abin da bakunansu ke furtawa sai hamdala da godiya ga Allah.
Nuriyya kuwa har sujjadar godiya ga Allah ta yi, hawayen farinciki na ta malala akan kuncinta. Ranar kwana Nuriyya ta yi a gidansu, ga ta ga baffanta wanda aka yafa masa mayafin sharri, yau ga shi mijinta ya tsaya har sai da gaskiya ta bayyana. Ba ta san me za ta ce masa ba, ba ta san me za ta yi masa ta faranta ransa ba.
Maiƙosai.