Zubar hawaye
by @maikosai53
HAFSATUL-KIRAM
©Mai Ƙosai
Babi Na 11-12
Gidan Dija suka nufa, Hafsa ba dan komai ta so nufar gidan ba sai don cika alƙawarin da ta ɗauka. Ba ƙaramin zantawa suka yi sosai da yarinyar da ke gidan Dija ba, al'amarin da ya haɗu ya sake tasowa da Hafsa famin ciwon da ke ƙasan zuciyarta, ji take duniyar na jujjyawa da ita ta rasa mafakar da za ta jingina jikinta ta samu sauƙi a zuciyarta. Me ya sa rayuwa take zuwa da ababe masu matuƙar wahala?
Kife kanta ta yi ta soma risgar kuka mai tsuma zuciya, gaba ɗaya hankalinsu ya tashi ainun musamman Afna da take jin kukan auntyn nata har ƙasan ranta, hankalinta ya kai ƙololuwar tashi, jin zubar ruwan hawayen Hafsa take na dukan ƙirjinta, ba ta san kukanta ko kaɗan tun da Allah ya haɗasu take jin Hafsa cikin ranta, take kuma ƙyamar duk abin da zai sanya Hafsan cikin wani yanayi.
"Don Allah Aunty ki daina ba na so, bana son kukanki yana ɗaga min hankali, yana dagulamin lissafina." Cewar Afna ita ma tana silalar da ruwan hawaye.
"Dole na yi kuka Afna, dole na zubar da hawaye, zuciya ta gaza ba zata iya rarrashina ba. Na ga al'amura da dama, amma ban taɓa ganin irin al'amarina ba. Ni fa wacve ta kawi ni duniyace ta tarwatsa rayuwata, ana cewa iwa mafi uba ko da uban sarki sai dai gareni uban ne mafi uwa domun shi ne kaɗai wanda nake kalla na ji daɗi, ta yaya zan ji sanyi a zuciyata Afna ba zan iya ba na gaza ba zan iya ɗauka ba." Ta yi maganar da wani irin sauti mara daɗin sauraro.
"Don Allah ki nutsu Hafsa kukan ba shi da amfani fa." Cewar Dija tana dafa kafaɗunta.
"Kin san komai Dija, kin san yadda rayuwata ta kasance amma me ya sa ba za ki barni na..." Ba ta iya ƙarawa ba ta sake fashewa da matsanancin kuka. Bubbuga bayanta Dija take yi, ita kanta a yanzu komai na rayuwar Hafsan dawo mata yake sabo dal tamkar yanzu ne ma rayuwar ke wakana, a ɓangarsn Hafsa kuwa ita ma ji take yi kamar yanzu ne shafin rayuwarta ya soma.
"Ni dai kun saka ni a duhu, aunty Dija na san ke ba za ki ɓoye min ba, na san ba za ki hanani labarin auntyna ba don Allah ki sanar da ne ƙaddararta." Afna ta ce tana kamo hannun Dija.
"Zan sanar da ke Afna, zan feɗe miki Biri har wutsiyarsa. Yanzu mu yi sallah kin ji."
"A'a Dija ni na fi dacewa na bayar da labarin rayuwata da kaina, mu je mu yi sallar zan gaya mata komai za ta san wace ce Hafsatul-kuram."
Faɗin Hafsa tana miƙewa tsaye, tare da dunfarar bayi don ɗaura alawa.
Sai da suka yi sallar duk da cewa lokacinta ya ƙure, domin daf ake da shiga sallar magrib, suka ci abinci, kafin zu zauna dukansu har da Bilkisu yarinyar da ke wajen Dija.
"Ban san ta ina zan soma muku da labarin nawa ba, domin kowane waje yana da matuƙar muhimmanci. Domin Labarin nawa yana da tasiri ta kowane ɓangare. Na kan rasa ta inda zan faro shi, domin ji nake kowane bigire mafi cancanta ne da na soma da shi. Amma bari na yi ƙundunbala, tare da rufe ido na soma muku daga bigiren da ƙwaƙwakwarku za ta iya fuskanta, albasshi sai na ƙarƙare muku daga sauyin da rayuwata ta samu.
Yadda za ku fahimci babana; da mahaifiyata, wacca ta yi rainona a cikin cikinta tsawon wata tara, ta kuma yasar da ni bayan ta kawo ni duniya na shaƙi iskar da ke cikin duniyar. Kana, ɗan'uwana wanda ya lasa mini zumar daɗi a baki, kafin daga bisani ya ɗanɗana mini maɗaci a saman harshena, wanda ya gurɓata wannan daɗin da ke kewaye cikin bakina.
Sunana Hafsa Abdallah Makafi. Ƙauyen Kiyawa, da ke cikin ƙaramar hukumar bici da ke jihar Kano shi ne ƙauyenna, mazaunata da asalina, a nan dangina suke zaune. Babana shi ne komai nawa shana, cina suturata, farincikina, jin daɗina, barcina hakanan uwa uba tarbiyata.
Tun da na taso gabansa kawai nake fuskanta na ji sauƙi da daɗin rayuwa, sai kuma kakata wacca take uwa ga mahaifina. Ba wai ba ni da mahaifiya ba ne a'a indai maganar kulawa ake batu to mahaifina shi ne mutum na sahun farko da ya nuna mini ƙauna.
Bazan taɓa mantawa ba, ranar wata asabar, da ta kasance na dawo daga gidan baba iro, wanda ya kasance ƙani ga baba.
Idanuwana suka yi mini mummunan gani, na yi tozali da abin takaicin da ya mutuƙar sosa zuciyata, kamar mai kirci na sosa inda yake faman yi masa sukuwar ƙaiƙayi. Sababin da ya sa na ji tamkar na rufe Inna da dukan ɓarin makauniya.
Ruwan da nake da tabbaci na wanki ne, shi ta kwarawa baba. In da ya gangaro tun daga kansa har izuwa sawayensa.
Tamkar 'yar mayen da tasha ƙwaya, haka na yi arangajin ƙarasawa inda suke. Na miƙa hannu na kamo hannun baba da ke tsaye tamkar bishiyar da aka dasa, na shigar da shi ɗaki, tare da zaunar da shi kana na miƙe a zafafe zan fice daga ɗakin. Sai dai jin amon muryarsa na kirana da wani irin amo ya tilasta mini tsayuwa.
"Hafsana!"
Na tsaya cak! Ba tare da na waiwayo ba, sai dai na ji ya ɗora,
"Ina za ki je? Bana son fitina dawo ki zauna."
Ban musa masa ba, na koma tare da samun gefensa na zauna jikina a sanyaye.
"Zan je na koya mata hankali ne baba." Na ce, muryata na rawa.
Kul! Kar na sake jin wannan furucin daga gareki. Ko kin manta mahaifiyarki ce, wacca ta kawoki duniya. Kin san kuwa illa da haɗarin da ke samun ɗan da ya yi wa iyayensa tataɓurza?
Kada ki kuskura ki wulaƙanta mahaifiyarki, ko ki ɗaga mata murya. Domin sam ba ɗabi'ar arziƙi ba ce, kuma Allah(SWT) yana matuƙar fushi da da ire-iren 'ya'ya masu tozarta iyayensu.
Har takai da ya yi kashedi akan haka. Inda yake gaya mana, cikin zancensa mai tsarki. 'Fala taƙul lahuma uffin wala tanhar huma waƙul lahuma ƙaulan karima.' Suratul Isra'i aya ta ashirin da uku(23). Ma'ana: Kada ka ce da su uffan, kada ka hantare su, ka gaya musu magana da girmamawa.
Kin san me kalmar iyaye take nufi kuwa?"
Na girgiza masa kai, yayin da shi kuma ya ci gaba da faɗin,
"Iyaye: Wannan kalma na nufin mahaifiya da mahaifi, waɗanda a sakamakon haɗuwarsu aka samar ko aka haifi mutum. Kamar yadda yake sanannen abu ga kowane musulmi, tun daga halitta ta Annabi Adamu(AS) da matarsa Hauwa'u, zuwa wannan al'umma ta Annabin Rahma, Annabi Muhammad(SAW). Allah (SWT)cikin rahmarsa, ya samar da tsari na saduwar namiji da mace a matsayin miji da mata ta hanyar aure. Ya sanya aure ya kasance sahihiyar hanya kuma amintacciya agare shi wajen haɗuwar namiji da mace ta yadda za a samar da zuriya.
Kin ga iyaye kuwa ba ababen wasa da wulaƙantawa ba ne, ko muzantawa agare mu, tilas mu kyautata musu ko da kuwa su basa kyautata mana."
Na sauke nauyayyiyar ajjiyar zuciya, domin nasiharsa ta shige ni ainun, wanda tuni na soma ƙoƙarin ganin na yaƙi zuciyata akan manufar da ta so saita ni wajen Inna.
Na kalle shi na ce,
"Yanzu haka zamu ci gaba da zuba mata ido baba, tana yin dukkan abin da take so?"
"Allahn da ya ƙagi halittarta, da tamu, da sauran bayinsa, da tsuntsaye da aljanu. Ya halicci duniyar baki ɗaya shi zai yi mana maganinta. Domin yana kallonta, yana sane da duk abin da take aikatawa."
Ni dai shiru na yi, cikin zuciyata na sake jinjinawa baba akan irin tarin haƙurinsa, da kawaicinsa.
Na miƙe jikina babu kuzari da nufin barin ɗakin. Cikin raunatacciyar muryasa ya ce,
"Ina za ki je Hafsana?"
"Zan je gidan kaka ne" Na ba shi amsa da haka.
"Ba za ki taya babanki hira ba? Ba za ki zauna ki ɗebe masa kewa ba?"
Sai na ji tausayinsa ya ƙume ni, na san badan komai ya yi wannan furucin ba sai don kaucewa tijara da masifar Inna.
Na ƙarasa kusa da shi da sauri, wata ƙaunarsa na sake lulluɓe ƙalbina(zuciyata). A kodayaushe takaici kan mamaye ni, musamman idan na tuna yadda Inna ke hura masa wutar rashin kyautatawa. Ko babu komai, shi fa miji ne wajenta.
Wunin ranar muna tare da baba. Muna manne da juna tamkar wasu cingam! Ko kaɗan ba na son ganin wani abu na tsikarar zuciyarsa...
Ayi maleji, saboda tsaron lafiya.
Ƙofar sharhi ko gyara a buɗe take.
Mai Ƙosai✍️