HAFSATUL-KIRAMFree

ArewaPen original

General fictionFreeOngoing

HAFSATUL-KIRAM

  • 1views
  • 40chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

About the author

Ni Marubuciya ce, kuma ina matuƙar alfahari da kasancewata haka. Ina girmama alƙalami, saboda alƙami yafi takobi. Ina sonku masoyana,na gode.😘

More from @maikosai53

Sample · Chapter 1-2: Uncle ne

HAFSATUL-KIRAM©Mai ƘosaiDa Sunan Allah Mai Rahma Mai Jinƙai.Ƙirƙirarren labari ne, ban yi shi don wani ko wata ba, idan ya yi kamanceceniya da rayuwar wani/wata to arashi ne.Ban yarda a juya min littafi ba, yin hakan ya saɓawa doka a kiyaye.Shafi na Ɗaya da na Biyu.Jikinta ne ke wani irin tsuma, yayin da haƙoranta ke haɗuwa da junansu, suna fitar da wani irin amon sauti. Wani zafi na ratsa kowane lungu da saƙo na jikinta, yayin da kainta ya ɗauki zafi sosai.Kalaman da har abada, ba za ta taɓa mancewa da su a rayuwarta ba ne ke sake dawo mata cikin kwanyarta, take ta runtse idanuwanta da suka ɗau zafi, ji take yi tamkar ana watsa mata yajin borkonon tsidigu cikin su. Muryar Kaka na sake amsa amo a cikin masarrafar jinta, daidai lokacin da take sanar da ita mummunan labarin da ya samar mata da giɓi a rayuwarta. Muryar ta sake ratsa fatar kunnuwanta."Ki yi haƙuri Hansatu! Babanki ya mutu. Sai dai ɗakin da yake ciki ya kama da wuta, babu abin da aka iya samu a cikinsa. Komai ya ƙone ƙurmus!"Waɗannan kalaman kullum suke sake taso mata, haɗi da yin iyo jikin masarrafar jinta. Har gaban abada ba za ta taɓa iya mancewa da su ba. To me ya sa ma za ta bawa ƙwaƙwalwarta damar gusar da su daga cikin ma'ajiyarta?A hankali ta ji wani sanyi na soma ratsa gaɓɓan jikinta. Rashin ganin gawar mahaifinta, da yabar ta a lokacin da ba ta shirya ba, na sake dukan ƙoƙan rainta. A zahirance, za ta iya cewa ta zama mutum mutumi ce kawai, duk da takaicin rashin babanta na maƙale cikin zuciyata, ya kasa barinta.Da ace kuwa rayuwa zaɓi ce a wajenta, to babu shakka ita ce za ta bata zaɓi akan irin rayuwar da take so ta yi da ita. To amma yaya ta iya? Zanen ƙaddararta ne ya zanu da tawwadar da ruwa ba zai iya wanketa ba.Ta yaya za ta iya samar da haske mai walwali a cikin wannan duhun duniyar tata? Ta riga ta sake amincewa da, kodayaushe ƙaddara ita ke yi wa fata zagi.Ji ta yi numfashinta ya shiga kokawa da ita, ta soma jansa da ƙyar tamkar wacce mala'ikan mutuwa ke ƙoƙarin zare mata numfashin."Hafsana! Ki bi duniyar nan a sannu, domin abu ƙanƙani ne ke komawa babba. Ba kowace rana ce, bawa ke samun ni'ima ba. Kada ki bari ƙiyayyar da mahaifiyarki ta nuna miki ta shafi 'ya'yanki. Ko bayan raina, ban yarda idan Allah ya nufeki da aure, ya kuma azurtaki da samun yara ki wofantar da su, kana ki kuma cuzguna musu ba.Na san yadda zafi, da ƙuncin rashin samun kulawar mahaifiya yake. Domin duk bawan da ya rasa ɗumin jikin mahaifiyarsa to tamkar alƙiyamarsa ta tsaya ne, tamkar ya rasa duk wani jindaɗi na wannan duniyar ne. Don haka kada ki wofantar da yaranki, ki tuna kema baki rasa ɗumin mahaifi ba."Kalaman mahaifinta, wanda ya zame mata garguwa ne suka shiga sake yi ma ta tariya cikin dodon kunnuwanta.A kullum yana ƙoƙarin ganin ya tafiyar mata da ƙuncin da Innarta ke ƙunsa mata cikin z...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters40
premium0
02

Chapter 3-4:Barista Jahid

Free sample
Updated 6 months agoAvailable now
20

Chapter : Tashin Hankali

Free sample
Updated 6 months agoAvailable now
21

Chapter 41-42: Wata uwa

Free sample
Updated 2 years agoAvailable now
22

Chapter 43-44 Zubar da ciki

Free sample
Updated 6 months agoAvailable now
23

Chapter 45-46: Zaman kotu

Free sample
Updated 2 years agoAvailable now
24

Chapter 47-48: Mummuman al'amari

Free sample
Updated 6 months agoAvailable now
27

Chapter 53-54 Wata ɗaya

Free sample
Updated 2 years agoAvailable now
29

chapter 57-58 Wankin hula

Free sample
Updated 2 years agoAvailable now
30

chapter 59-60 cutar hanta

Free sample
Updated 2 years agoAvailable now
32

Chapter 63-64 Spinal Cord

Free sample
Updated 2 years agoAvailable now
33

Chapter 65-66 Wasa da wuta

Free sample
Updated 2 years agoAvailable now
35

Chapter 69-70 'yar jarida

Free sample
Updated 2 years agoAvailable now
37

chapter 73-74 yaya lawan

Free sample
Updated 2 years agoAvailable now
39

chapter 77-78 farin ciki

Free sample
Updated 6 months agoAvailable now
40

chapter 79-80 kyautar Allah

Free sample
Updated 5 months agoAvailable now

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play