Rikicin Duniya...
by @maikosai53
*HAFSATUL-KIRAM*
©Mai ƙosai
Babi Na 29-30
*My Fans ku yi haƙuri mun yi shagalin biki ne shi ya sa ban zauna ba, na gd sosai*
"Ba za ki nemi na ƙarasa miki labarin ba?"
Kalaman suka sake dukan kwanyarta, har ga Allah tana son yi wa Hafsan magana, sai dai tana tsoro da gudun kar ta watsa mata ƙasa a ido shi ya sa ta haɗiye ƙwalamarta, amma yanzu da ta ji auntyn nata na maganar ƙarashen sai ta sake jin son ci gaban labarin.
"Me zai hana idan har kin ba ni dama zan zauna gabanki na ji sauran labarin kamar yadda kika karanta min karatu yanzu."
Murmushi Hafsa ta yi, tare da furta,
"Zo ki nemi waje ki zauna." Babu musu kuwa ta zauna har da tanƙwashe ƙafafu. Yayin da ita ma Hafsa ta fara da,
Kamar yadda masu iya magana suka ce, 'Rikicin Duniya da mai rai ake yinsa' Wannan magana haka take, domin rayuwa ta sake rikice mini, wacca har ta sa na sake yarda da cewa, 'rikicin duniya, da mai rai ake yinsa.'
Ko shakka ba na yi, da ace bana numfasawa a wannan duniyar, da ban tsinci kaina cikin ƙalubalen rayuwa ba, da ban kasance a cikin gidan kurku ba!
Sai dai yaya zan yi? Ba ni da wani zaɓi ne, dole tasa na karɓi abin da ake tuhumata da shi, ba wai domin na aikata hakan ba. To yaya na iya ma? Alhalin uwa uba ba ni da wani zaɓi ma face wannan. Hakazalika, babu abin da na fi ganin ya dace da ni irin na ga numfashina ya ɗauke na bar duniyar. Wannan ta sa ni ganin amsar laifin shi ne kaɗai mafi dacewa a gare ni.."
"Ɗan tsaya aunty, yaushe kika tsinci kanki a wannam bigiren? Kin juyar min da kai." Afna ta yi saurin katseta.
Dariya ta yi kafin ta ce, "Me kike ci na baka na zuba, ki dai bi ni kawai."
Ba ta bata damar sake magantuwa ba ta ɗora,
"Na runtse idanuwana, waɗanda take majigan cikinsu suka shiga hasko mini musabbabin da ya sa na tsinci talata a laraba.
Bayan zuwanmu ƙasar Dubai ni da baba Larai. Abin hawa ta sama mana. Sai dai har muka isa ƙofar tamfatsetsen gidan ban ji sunan unguwar da ta sanar da mai motar ba, saboda gaba ɗaya tunanina baya gareni.
'Ma sha Allah!' Na furta, sa'ilin da na yi arba da kyakkyawar wata mata, na kasa gasgata cewa an ya kuwa a duniyar bil'adama nake.
Sai dai jin furucinta cikin harshen hausa, ya tilasta mini yin mutuwar tsaye, take kwanyata ta shiga mamakin yadda na ji hausar na fitowa daga bakinta rangaɗaɗau.
"Zauna mana Hafsa!" Muryar baba Larai ta ba ni damar dawowa duniyata ta zahiri. Na ɗaga sawayena na cilla gaba, tare da neman matsuguni na zauna, ina mai gaisar da matar cikin harshen hausa.
Babu yabo, babu fallasa ta amsa mini fuska a sake. Nan kuma suka shiga zantawa da baba Larai cikin harshen nasara, wanda ya sa ban fahimci komai ba, saboda ɗan abin da yaya Lawan ke koya mana bai taka-kara ya karya ba.
Bayan tafiyar baba Larai, da damun kuɗin da matar ta bata da sunan kuɗin aikina na sahun farko, tun kafin na yi aikin. Matar ta kaini wani ɗaki, mai kyau da tsaruwa. Sai dai cike yake da 'yan mata kala-kala kowacce da irin fasalinta.
Kwana na biyu, a cikin gidan na soma fahimtar kowane irin gida ne, na gane gida ne da kowa ke da 'yancin kansa, gida ne da babu kyakkyawar tarbiya cikinsa.
Wannan matar da ake kira da hajiya, ita ce uwar ɗakin kowace budurwa da ke cikin gidan, ita ke umarta a yi duk abin da take so.
A cikin kwanakin nakan ga anzo an fita da 'yan mata, an kwashesu a mota kowacce ta caɓa ado. Idan kuma sun dawo, nakan ji suna batu akan kuɗi, da lissafe-lissafe.
Watana uku a gidan matar. Wata rana, ina zaune a ɗaki hajiya ta shigo. Fuskarta caɓe da kwalliya, bakin nan ɗauke da murmushi. Ta raɓa gefena ta zauna ta kai hannunta kan kafaɗata, kana ta soma magana cikin iyayi.
"Yauwa baby Hafsa! Maza ki shiga bayi(banɗaki) ki yi wanka, kizo ki shirya. Domin yau akwai babban samu."
Dubanta na yi, cike da son ƙarin bayani, sai dai bata ce mini komai ba, sai ma sake bani umarni akan na tashi na aiwata abin da ta ce mini, tana mai ajjiye mini wasu suturu akan idan na fito na sanya su.
Na bi umarnin hajiya, bayan na fito na isketa a falo, gabanta wasu 'yan mata ne jere tamkar masu karɓar sadaka. Umarni ta ba ni, a kan na shiga cikinsu.
Muna nan tsaye, sai ga wata mata ta shigo, jikinta sutura ce ta alfarma, fuskarta caɓe da kwalliya, yayin da bakinta ke tauna cingam ƙaras-ƙaras. Gabanmu ta ƙaraso, ta tsaya tana mai binmu da kallo, kafin ta kai hannu ta yi nuni da ni. Nan take kuma hajiya ta sallami sauran, ni kuma aka sake shirya ni, tare da yi mini jagora zuwa wani ɗaki.
Ina shiga na ja na yi turus! Sakamakon ganin matar da na yi kwance kan gado, haihuwar uwata ta, babu kaya jikinta, na runtse idanuwana ina mai karanto duk addu'ar da ta ratso maƙwallatona.
Ji na yi ta janyo ni, ta soma kiciniyar ida nufinta gare ni, cikin azama na yi nasarar kwaɗa mata wata kwalba da ke ajjiye gefen gado, aikuwa kanta ya fashe, take ta saki ihu. Hajiya da wasu 'yan mata suka shigo, ganin abin da ya faru ya sa hajiyar rikicewa, ƙarshe dai aka kai matar asibiti, ita kuma hajiya ta dinga yi mini faɗa akan ba zan illata mata sana'arta ba, ba zan ruguza mata kasuwancinta ba. In da ni ma na nuna mata ba zan yi abin da take so ba, idan kuwa har ta matsa tofa lallai zan tona mata asiri. Babu yadda ta iya haka ta ƙyale ni ta zuba mini na mujiya.
Sai dai duk da haka ba wai na tsira ba ne, ashe ina can ƙasan zuciyarta. Yayin da ta ɗaura aniyar ko ta halin ƙaƙa sai ta tsunduma ni cikin harkar.
A haka na sake shafe sati guda cikin gidan, sai dai bana taɓa yarda na keɓance da hajiya domin babu abin da hakan ke amfanar sa ni tun da kalamaine take guntsa minsu mara sa daɗin ji da sauraro, ƙoƙari take ko ta kowane hali ta ga ta cusa min baƙar harkarsu wacce ba ta amfanar mutum da kimai sai tsiyar da babu wasali.
Abubuwa da yawa sun faru a gidan hajiya, kuma haka dolenta ta zuba mini ido don babu yadda ta iya da ni, akwai lokacin da ta taɓa kawo wata hamshaƙiyar mata, matar kuwa da tun da ta ɗora idanunta kaina ta sha alwashin sai ta ɗanɗaneni, a lokacin da na gane nufinta na sake tashi tsaye, ko waje bana fitowa ina ɗaki a nan nake rayuwata a nan nake komai.
Na sake killace kaina a ɗaki kamar wacce ke neman karita daga kamuwa da cutar nan ta mashako. Idan har na fito kuwa to fita zamu yi ni da Anisa, yarinyar da muke kwana gado ɗaya da ita, tun bamu sake da juna ba har muka zama aminai.
Musamman da ta ba ni labarinta na ji yadda itama ƙaddara ta jefota nan. A yadda ta ce mini, wan mahaifinta ne ya kawota ƙasar dubai da nufin ta yi karatu, sai labarin ya sha bamban, domin dai karuwanci ya kawota yi ba karatu ba. Kasancewar iyayenta duka biyun basa raye, sai ya ɗauketa ya riƙeta.
Kusan kullum sai na yi kewar mahaifina, yayin da kewar kaka ke sake tumbatsa cikin zuciyata. Ina ji tamkar na zama tsuntsuwa na koma wajenta.
Ranar wata juma'a, na tashi da kasala, jikina jinsa nake kamar wacca ta sassaɓe gona. Hakan ya sa na ce da Anisa tazo mu ɗan zagaya. Kai tsaye wani babban kanti muka nufa, kasancewar tana son ta ɗan yi siyayyar wasu abubuwa nata da suka ƙare.
A wannan fitar ne kuma, na haɗu da Nasir mutumin da ya sabunta rayuwata. Shaƙuwa da soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakaninmu, har mu mallaki junanmu a matsayin ma'aurata.
Duk da an sha sa-toka-sa-tsaki kafin auren, domin ahlinsa sun nuna ba sa sona, sun fiso ya auri 'yar cikin danginsu. Hatta da hajiya ma ta so ƙin amincewa.
A daddafe na kwashe shekara ɗaya da wata uku a gidan Nasir, a lokacin kuma ina ɗauke da ciki a jikina, bayan wanda na yi ɓarinsa a watannin baya. Abubuwa suka tarar mini, ga rashin Nasir kusa da ni, domin tafiye-tafiye yake yi, kuma yakan ɗau tsawon watanni kafin ya dawo, ga kuma ƙiyayya da tsangwamar danginsa.
Cikina yana wata takwas da kwana biyu, Nasir ya shaida mini yana kan hanyar dawo wa daga wata tafiya da ya yi. Ban yi ƙasa a guiwa ba na shirya masa abincin da yafi so, na tare shi da ƙumajina(kuzari).
Sai da ya watsa ruwa, ya ɗan kimtsa, sananan ya soma cin abincin da ya zame masa ci na ƙarshe, a wannan ranar ne komai ya sake lalace mini.
Gyara, shawarwari, sharhi duka ƙofofinsu a buɗe suke.
Mai ƙosai✍️