BAƘIN HAURE..........

Chapter 16

by @maidambu41

*BAƘIN HAURE....🐾🐾*


  {Greed for Money is the roots of all evils🫀}

 Arewabooks:maidambu41

Wattpad:Mai_Dambu

Mallakar:Mai_Dambu

    *016*

Mutumin nan bai yi kasa a gwiwa wurin neman Mutanen unguwar tare da mai unguwa, ya zauna a tsakiyarsu ya ce musu. "Akwai matar nan yar kasar Nijar, tow gaskiya a da ina ganin mijinta yana zuwa, amma a yanzu an dauki shekara biyu ban ga mijin yazo ba, sanan ita kuma tana yawan fita aikatau domin ina yawan ganinta ta fita da sassafe ta dawo da la'asar lis, tow kada na kaiku da nisa Matar nan dai jiya bata kwana a gida ba, sannan ku yi nazarin idan mune ya zamu ji? Sannan yarinya ce domin bata kai talatin ba, don Allah ku duba lamarin."

    "Hmmm! Waye ya sani ko yawon bin maza ta tafi." Inji wani mutum a wurin, tsawa limamin unguwar yayi mishi. "Mene ne hujjarka?" Sunkuyar da kai yayi, kafin liman ya ce. "A yanzu muje gidan, ko akwai yaron da zai fada mana inda take zuwa aiki." Haka suka mike bakiɗayansu, suka tafi har gidan, sun samu Aryan yayi kashi ya b'ata jikinshi. Haka Mutumin farko ya kira Matarshi ta wanke su, sannan ta dauko musu kayan Yaranta, suka kasa sannan ta riko hannun Abdul Majid suka fito. "Abdul Majid!" "Hmmm!" Ya fada yana komawa gefe, domin har yau yana fama da rashin sakewa. "Kasan gidan da Mamanku take zuwa aiki?" Gyada kai yayi. "Ok Maman Luba tafi da sauran, bari ya kai mu inda take zuwa aiki."

   Haka suka saka Abdul Majid a gaba, har gidan dake tana zuwa da shi yana taimaka mata da Aryan yana wasa da shi, koda suka zo gidan babu wanda ya yarda yayi musu maganar Sa'adatu, sannan babu wanda ya kula su, sai da yan unguwar suke gayawa musu ai tun jiya da hantsi yan sanda suka tafi da ita office dinsu.


 Ba karamin kaduwa suka yi ba, domin kuwa har an rasa me magana, haka suka mai da Abdul gida, sannan wasu suka wuce kasuwa, wasu kuma suka hakura da kasuwa suka nufi Office din yan sanda nimanta. Musamman Baban Luba mutumin nan yayi halacci musamman da yake makocinta, haka suka yi ta yawo kafin Allah ya gajarce musu wahala, suka same ta goshin Magariba a wani Office din yan sanda. 

     A lokacin da suka je a bada belinta, kin sauraronsu aka yi, da suka nace aka kawo laifin da ake tuhumarta da shi na sata da yunkurin kisan kai. Shiru kowa yayi kafin, suka roki a basu ita tana da Yara kanana. Amma aka hana su, sai dai sun fito da ita, suka ga ko tsayuwa bata iyawa ga yunwa ga tashin hankali, haka Baban Luba ya tafi ya sayo mata tuwo hannu baka hannu kwarya haka take cin abincin.


      Tana ci a lokacin hankalinta ya dawo jikinta, duk yadda suka so jin me ya faru, kunya da zurfin ciki ya hanata magana. Haka suka maida ita hankalin kowa ya tashi, sai da aka mai data ta zauna tayi ta kuka tana jin me yasa ta kasa magana. Haka ta kwana kuka.


 Washi gari..

Gidan mutumin da take aiki suka je, dakyar da sannu sannu aka bawa mutumin hakuri sannan ya janye karar domin yace kotu ce zata raba su da ita, daga taimako zata kashe musu d'a da sata. Su dai tunda aka janye karar, suka yi godiya suka bar gidan. A can office din yan sanda, aka bada belinta, aka dawo da ita gida, Baban Luba shi ya fita can sai gashi da kayan abinci, ya kawo mata da dafaffen har da Yaranta. "Idan kina da matsala ki yi magana da Maman Luba, Allah ya tsare na gaba."

  "Allah ya biya maka bukatarka na alkhairi, na gode." Ta fada tana kuka, haka ya bar gidan, sai da tayi wanka tare da sauke sallolin danke kanta, ta samu wuri ta zauna ta sakawa yaran abinci, suka ci banda Abdul Majid da yake manne a jikinta, yana kallon yadda take sharar kwalla. "Hajiya kici abinci man." Ya faɗa kamar zai fashe da kuka. "Na koshi Alhaji!" Ganin taki ci yasa shima yaki ci. Yadda ta ga rana haka ta ga dare, Washi gari ta tafi har gidan Baban Luba tayi godiya, sannan ta ce mishi. "Ina son zan fita da yaran, ga gidan."

Kafin Baban Luba yayi magana Maman Luba ta yi maza ta karɓe zancen. "Ina zaki kuma?" "Ina son zuwa nijar ne, shine nake son fita muyi Bara ko za a samu kudin mota." Ta fada cikin matsanancin kunya, "Bara?" Suka hada baki, "ki je gida ki shirya gobe in sha Allah sai ku tafi, yau zan samu abokina Hamisu bazabarme na gaya mishi akwai fasinjar marad'i ko?" Gyada kai tayi, ya jinjjina kai ta koma gida, haka ta dawo gida, bayan fitar shi ta koma gidan ta cewa Maman Luba."idan kina da aiki kawo na rage miki."

"A'a Maman Abdul barshi." "Don Allah kawo ko wanki ne." Haka matar ta fito da wankin. Kafin azahar ta gama wanki, kuma kayan sun fita tass, ta shanya mata sannan ta basu abinci suka dawo gida, ita kan Maman Luba wani irin son Sa'adatu take, shi yasa take tsananin tausayinta. Tasan yarinya ce. Da dare Luba ta kawo musu abinci har gida, washe gari da sassafe makocinsu ya sakata a gaba, bayan ya gayawa me unguwa da liman, aka kaita tasha sannan suka bata guzuri me yawa, ta baro Kano zuwa marad'i. A lokacin da ta isa ta samu Alhaji Abubakar Abzin, baya gari a gidan ta zauna na tsawon sati daya, kafin ya dawo. Duk da tazo wurin shi da damuwa amma kuma tana ganinshi sai ta kasa fadar kome, ta koma kuka. Yana rike da hannun Abdul Majid, yake tambayarshi sai ya kalli Mamansu kafin yake magana, amma yaki fadar abin da ya faru. "Hajiya baki ce kome ba, sai kuka." Girgiza kai kawai tayi. Haka ya mike ya ce ta koma can wurin uwargidansa tunda dama a can ta sauka, Mutumin kirki, Washi gari ya tashi wani yaron shi ya je har Kano aka duba mutumin da ake bashi aika ya kai mata, ashe ya rasu, sannan dan aikan ya tafi har unguwarsu, anan yaji labarin abin da ya faru, kwana biyu tsakani sai gashi nan ya dawo da bayani, Alhaji Abubakar Abzin ya yi shiru. Sannan ya kira ta. "Me ya faru har aka rufe ki na tsawon kwana biyu?" Kanta a sunkuye ta ce mishi. "Babu kome Abba." Don a haife ya haifeta.


    "Shi kenan, amma Mamman yana zuwa?" Hawaye ne suka zubo mata, ta girgiza kai. "Shi kenan." Haka ya fita a ranar ya bar marad'i, wato koda ya isa Niamey. Faɗa suka shiga yi shida Alhaji Mamman kamar zasu yi doke-doke, kafin suka dawo Alhaji Abubakar Abzin ya gaya mishi halin da iyalinshi suke ciki. "fisabilillahi yara maza har uku fa, gasu nan duk da rashin kulawa amma yaran sun samu tarbiyya kaji tsoron Allah kafin ya tsayar da kai."

"Naji zan zo amma gaskiya Ya fada kuma sai yayi shiru, kafin yayi kwafa. Kwanan Alhaji Abubakar Abzin daya, suka juyo tare. Cikin farinciki yaran suka ga Babansu, sai dai Majid ya koma jikin Hajiya ya lafe, saboda kallon tsanar da Alhaji Mamman yake mishi. 


   Tambayoyi har da takardun ta, duk ta bashi sannan ya kalleta cikin isa ya ce mata. "gobe zaki koma Kano, ki sani ban baki damar kiyi karatu don jin dadinki ba, ban tara dukiya don yaranki su ji dadi ba, na tara su ne, don amfanin gobensu. Dole ki jajirce ki kuma koyi boye damuwarki, sannan kiyi hakuri da abinda kike da shi. Wannan shine abin da zan gaya miki ".

"Mun gode sosai hakan ma" ta faɗa muryarta a raunane. "Kada ki kuma kawo karana." "Allah ya huci zuciyarka, in sha Allah haka ba zai kuma faruwa ba." 

 Haka ya kwashi Amaan da Aryan, ya tafi da su yawo, sai dare ya dawo dasu. Duk abinda ya kawo musu haka yace kada ya bawa Abdul, amma abin ka da Uwa. Sai da sauran suka yi barci ta tashe shi ta bashi ya ci, sannan ya kwanta. Tausayin Abdul take ji, gani take kamar tana da laifi wurin duk abinda ya same shi. A hankali take shafa kanshi har barci ya dauke shi, tana zaune a wurin Alhaji Abubakar ya shigo ya cewa Matarshi ta turata wurin Mijinta, haka ta shirya ta tafi, za a iya cewa wannan karon rabo ya kawo ta, domin kuwa washi gari ya juya ya koma ya bar kome nasu a hannun Alhaji Abubakar Abzin. Ita kuwa a ranar ta dawo kano da tsaraba me yawan gaske. Ta kaiwa gidansu Baban Luba, sannan ta kai na gidan Mai unguwa da Liman, don sune iyayenta. 


   Bayan tafiyarta da binciken da Alhaji Abubakar Abzin yayi, ya ji gaskiyar abinda ya faru. Ai kuwa ya maka mutumin da yasa aka rufeta a kotu, rikici babba aka yi ta yi kamar me, sai da dattawan unguwarsu suka saka baki, haka ya sama mata yanci, suna dawowa ranar Monday aka zo aka kwashe Abdul da Amaan suka tafi makaranta. Ba laifi zuwa yanzu ta samu dan nutsuwa, tana dan sana'a kuma abincinsu yana nan.

  ***

A can kuwa Tani tana zuba mulkinta yadda take so, bata yarda ta kuma cewa tana son zuwa ganin halin da Sa'adatu take ciki ba, domin tsoron abinda ya faru kada ya kuma faruwa, haka ta zauna tana zuba musu isa da mallaka.


 Sannan a gefe guda ta mallake Nana sai yadda tayi da ita, kuma bata da katabus sai Abinda Tani ta ce, ana haka ta saka Alhaji Mamman a gaba ya saka mata danta Sajjid a makaranta tare da gaya mishi duk abinda yake so Sajjid zai mishi, ba sai ya damu da Abdul ba, fatanta kawai ya saka Sajjid a cikin Yaranshi. Amma mutumin nan yaki kula zancen. Idan ta dauko zancen zai ce mata yaji kawai don ta rabu dashi amma a ranshi baya jin zai yarda ya amshi Sajjid domin ba jininshi ba ne.

    Haka tayi ta kokarin lallai sai yaron, ya zama wani abu kai babu wanda ya isa yayi mishi fada balle tsawa. Ga rashin kunya da fitsara.

****

Tunda suka dawo ta fara laulayin cikin Jamilah don ma babu wani wahala, amma kuma tana yawan kwanciya. Saidai da sauki,haka taci gaba da rayuwa har Allah ya sauketa lafiya, ta samu yarta mace, Kyakyawa da ita, haka yasa ta saka sunan Yafendo Jamilah. 


   A lokacin ba laifi abinci da sakon yana samunta, haka tayi ta renon Jamila, amma ta turawa Alhaji Abubakar Abzin sakon ta haihu, shi kuma ya turawa Alhaji Mamman Ba'are, bai bi ta kanta ba, sai bayan shekaru biyu, rabon Anisah ya kaishi Kano, a lokacin Abdul Majid ya kusan gama primary, a wannan zuwan da yayi ne. Ya kama yaron ya mishi mugun dukar da ya suma saboda kawai an kawo kararshi wai ya dauki kudin wani me shago, ya mishi wannan dukar, ya tura shi gidan horar da kangararun Yara,. Wani abin tashin hankali ya dauke Hajiya da sauran Yaran suka koma Niamey. Suka bar Abdul Majid, da yayi fama da jinya ga cutarwar yan gidan, duk wanda ya fika ƙarfi zai zalunce ka, sannan yara ne masu banbancin hali, har da marasa jin magana masu luwadi, sai dai tunda suka barshi Hajiya ta bar amanarshi a hannun Maman Luba. Tana can amma addu'arta bai daina sauka a kanshi ba, 


 Sai da ya kwashe shekaru goma har ya zama kaman dan gida, anan ya gama primary school da secondry school, yayi jarabawar shiga jami'a, ƙoƙarinshi yasa shi samu tallafin karatu a wurin gwamnatin Kano, anan ya tsaya ya karanci bangaren likitanci, tsawon wannan lokacin, Hajiya tana marad'i, tunda Alhaji Mamman ya zubasu yayi tafiyarshi, Alhaji Abubakar Abzin shine kome nasu, har ta haihu. 


 Dukkan Yaran sun san Majid amma Anisah bata san shi ba, sai labarinshi. Zamanshi a gidan horan Yara, ya kara maida shi wani irin mutum mai murdadden hali, sannan baya hmm baya Humm. Dole yasa yake zama a cikin aji, amma baya son hayaniyar mutane ko kaɗan. Idan dare yayi kuwa baya barci domin idan ya fara barci zai ta mafarkin Babansu yana dukar Hajiya.  Haka xai bude idanu, sau biyu yana faduwa a aji, a duk ranar da yayi mafarkin tow zai fadi ya suma sai washe gari don bai samun isasshen barci. 


  Ganin haka zai shafi karatunsa, yasa shi fara ganin likitan kwakwalwa, aka fara duba shi, domin har dawanau aka tura shi. Lokacin da suka samu hutu, ya shirya ya tafi marad'i da tambaya da kwatance yaje gidan Alhaji Abubakar Abzin, Aryan yana kofar gidansu na maradin ya hango Abdul ba zai manta da shi ba, da gudu ya tafi ya rungume shi." Hammayo;" murmushi yayi ya kara rike shi suka nufi cikin gidan, ya kawo musu tsarabar Kano. Hajiya da ta ganshi, juya baya tayi tana kuka. Murmushi yayi bai ce mata kome ba. Ya zauna kanshi a sunkuye. Haka ta shiga daki Jamilah ta fito ta ce. "Hammayo kai ne" ta zauna a kusa dashi tana washe baki . "Yafendo kin zama yan mata " "sai buhun rashin mutunci." "Hammayo kaga Hamma Aryan ko?" Tashi yayi ya shiga dakin Hajiya, ya same ta a can kuryar dakin tana kuka. Zama yayi gabanta. "Hajiya ko daidai da rana daya ban manta daku ba."

"Amma ai na manta da kai!" "Hajiya nasha mafarkin kina sallah kina min addu'a da wannan na yarda a zuciyarki ina tare dake."

  "Alhaji baka yi fushi ba?" Girgiza kai yayi yana murmushi. "Hajiya kina karkashin mijinki, a kaina ba zaki kashe auren da na bude idanu na gani ba." Hawaye ne ya zubo mata danta dan kimanin shekaru goma sha takwas. "Gobe zamu je Niamey."

"Hmm! Allah ya kai mu!" Ya fada. 

Haka ya fita ta kawo mishi abinci, kannen suka zagaye shi, suna bashi labari can sai ga Anisah ta shigo tana kuka."Hajiya!" "Na'am Auta." 

"Hajiya Hamma Amaan ya kwace sauran canjin." 

"Allah ya shirya min ku baki daya." Ta amshi sakon, ta ajiye a kitchen. "Hajiya Ina hamma Aryan?" "Suna cikin daki Hammayonku ya dawo." Da sauri ta shiga Dakin, ta d'aga labule. Kura mishi idanu tayi idanunta cike da kwalla. "Hammayo!' bude mata hannu yayi, da sauri ta isa gareshi tana kuka. "Hammayo ban sanka ba, amma Hamma Aryan kullum sai ya bani labarinka." Murmushi yayi yana kallon Aryan. "Ya ce miki ina sat.." rufe mishi baki Aryan yayi. "Alkhairi nake gaya mata, yarinya ce bata san sharri ba please."

"Hamma Amaan yake gaya min wai sat..." Rufe mata baki Jamilah tayi. "Ke dai akwai bakin allatsine, idan kika bi na wancan sakaran sai an daure ki igiya tayi saura."


 Domin daga Jamilah har Aryan basu shiri da Amaan,.kamar wuta da auduga. Mikewa yayi suka tafi masallaci, suna dawowa suka samu Hajiya tana kokarin tuka tuwo.. "Hajiya bani na miki?" "Yau.girkin maza zamu ci?" Ta tambaye shi, "zamana a gidan Horon kangararrun Yara, yasa na rike bangaren girki har gasar girki muke " ya faɗa a sanyayye, Duk da cikin raha yake maganar amma fuskarshi bata nuna haka ba, yanayinshi babu yabo babu fallasa, suna zaune ya tuke tuwon ya kwashe tas, yana gamawa wata mata ta shigo kawo kar'ar Amaan. "Maman Jamilah ina jin kunyarki, ki jawa danki kunne wallahi ya fita harkata da yarinya ta."

"Kiyi hakuri;" shine abinda Hajiya ta faɗa, sannan matar ta fita tana zage-zage. Can kafin magariba sai ga Amaan, ya shigo yana zage zage da rashin kunya. Kallon Abdul yayi ya ce mishi. "Barawo ka dawo ne?" "Hammayo muje masallaci!" Inji Aryan, domin a cike yake da Amaan babu ranar da zata waye ba a kawo ƙarar shi ba, "Kai dan shegiya da kai nayi?" Wani irin mari Abdul ya kifa mishi, a wurin ya zube yana nishi, "kayi yadda kake so, idan kaso ka fadi abinda yayi maka. Amma ka sake ka zagi wani cikinsu sai na cire ma hakori."

 "Hajiya kina ganin barawon danki zai kashe ni." Alola yayi ta wuce daki, shima ya wuce dakin. A masallaci Aryan yake bashi labarin abinda yake faruwa, sannan wani abin tashin hankalin shine duk bayan wata biyu Hajiya xata kwashe su har Niamey, su je can ayi ta wulakanta su ana ganawa Hajiya azaba da masifa.


     Lashe baki yayi yana jin daci a ranshi, haka sukayi sallah sai bayan Isha suka dawo, tun a kofar gidan suke jin muryar Jamilah, Hajiya tana gefe bata yi magana ba ta xuba musu idanu Amaan sai dukanta yake. A fusace Aryan ya nufi Amaan Majid ya rike shi, "sake ta!" "Idan naki fa?" "Aryan wuce da hajiya ɗakinta!" Ai dama ganin hajiya a wurin zai saka ya kyale shi, sai gashi cikin fushi ya kai mishi wani irin duka a kafa, dauke wuta yayi wato Majid zama gidan horon nan ya koyar da shi mugunta sala sala. Targad'a shi yayi ya ce mishi. "Kafin ka warke ka fara fita zaka fahimci muhimmancinsu, idan ma baka horu ba, akwai hanya dayawa da zaka nutsu."

     Haka ya wuce da ita daki, yana faɗin. "Kin mishi rashin kunya ne?" "A'a Hammayo, kiranta yayi tana sallah shine tana idarwa ta fita ya kama dukanta da hajiya tai magana yace babu ruwanta."

Cizon fatar bakinshi yayi yana jin tafasa a ranshi, a daren Aryan ya gyara dakinsu, da Inda Hammayo zai kwana. Haka suka kwana suna hira, sai asuba suka yi barci.. wurin karfe goma motar kai su Niamey tazo, suka tafi sai cika Amaan yake yana batsewa. Har suka isa gidan, wanda daga kofar gidan zaka fahimci ana sha'ani ne.


Lokacin da suka isa gidan, ba laifi ana ta hada-hada, falon Alhaji Mamman suka nufa suka gaishe shi sama sama ya amsa. "Kai me yasa meka?" 

"Ba Barawon can bane ya dawo ya targad'a min kafa ba." 

"Waye barawo!"

"Abdul Majid!" Wanda ya shigo falon, mikewa Alhaji Mamman yayi ya ce. "Sa'a me yasa kika kawo min shi gidana!" Juyawa yayi ya bar falon. Ai kuwa garin bashi hakuri ya rufeta da duka, har waje. Wannan abin ko a jikin Amaan domin shi gani yake Hajiya ta rabasu da jin dadin gidan Ubansu ta kawo su wata duniya suna wahala. Shi yasa duk abinda Alhaji Mamman zai mata baya tausayinta ko kaɗan.

    Da gudu Anisah ta fita waje, "Hammayo kazo Alhaji xai kashe Hajiya." Sun saba duk lokacin suka zo haka xai mata duka a gaban jama'a. Amma na yau ya wuce tunaninsu domin biki ake yi a gidan, kuma ga mutane babu wanda ya damu sai ma tsayawa da suka yi suna kallon abin. Haka ya ratsa taron ya shiga. Ya rike hannun Alhaji Mamman Ba'are da yake zuba mata duka. "Ya isa haka!" D'ago kai yayi yana mamakin waye ya isa ya dakatar dashi daga dukar Sa'adatu. "Ya isa haka Alhaji Mamman Ba'are!" Ya sake hannun shi yana kallon cikin idanunshi. "ya isa haka nace!" Ya fada yana me dago kai yana kallon Hajiya Nana. " Na rantse da Allah,duk ranar da danki ya kuma d'aga hannu ya tab'a min Uwa, sai na hauro sama na bugaki da kasa daga saman zan wurgo ki billahi azim, Uwa bata fi Uwa ba duk sunansu Uwa." Ya faɗa yana d'ago Hajiya. ""Kai waye ya baka damar shigo mana gida?" Inji Sajjid Mamman Ba'are, cikin wani irin fushi, ya juya ga Sajjid wanda ganin idanun Abdul ya bashi tsoro. Ƙwayar idanunshi a fusace yake fushinsa daga zuciya take kunno kai ga idanunshi, kamilalliyar fuskar shi bata nuna fushin ba..

    "Kace me?" 

Hadiye yawu yayi, ya juya ga Alhaji Mamman Ba'are zai magana Hajiya ta ce mishi. "Kul ka kara magana!" "Hajiya idan ya kuma dukanki sai kashe shi, Nana kin ji me nace." Ya fada da karfi, juyo shi hajiya tayi ta watsa mishi mari, ta kuma marin shi. Jikinshi ya hau cira kamar zai tashi sama. "Ban doraka akan haka ba,me yasa zaka min haka?" Inji Hajiyar tana kuka."Mahaifinka ne me yasa zaka mishi haka a gaban jama'a?" Zube gwiwarta tayi ta ja hannun Majid din, sai yaki. "Ki cewa danki ya fita na tsame shi cikin zuri'ata."

"Haka yayi ai dama kafin yau ni ba danka bane."

"Ba zai fita ba, rashin kunyar da yayi sai Uwarshi ta biya akan idanunshi." Jin Nana tana saukowa. A fusace yayi kanta tare da tsare ta da idanunsa masu Bala'in ban tsoro. Da gudu Hajiya ta rufe shi da duka, "ka bar tashin hankalin nan, ka koma inda ka fito na roke ka, don Allah na roke ka ka tafi ka yi nisa da mu na yafe maka zuwan."


        Juyawa yayi zai tafi Nana ta dauki sandarta ta shiga bugawa Hajiya, "Hammayo tana dukan Hajiya" bai ce kome ba, ya nufi falon Alhaji Mamman ya ce mishi. "Ka fita ka jawa Mamarka kunne ko na kona gidan nan baki ɗaya wallahi billahi azim." Ya fada a haukace, zuwa yanzu shi kanshi Alhaji Mamman Ba'are tsoron Majid ya darsu a zuciyarshi. Ganin yadda ya fita da gudu, inda motar gidan take ya nufa, ya cire rigarshi ya bude wurin tanki, ya saka rigar sai da ya jike da fetur, ya Ciro yana watsawa a kan kome na gidan, "Hajiya kyale ta don Allah." Alhaji Mamman Ba'are ya fada, sannan ta tsaya tana hakki. "Me yasa ka dakatar dani?"

"Saboda d'anta zai aikata kome don mahaifiyarshi."

"Kenan idan aka dake ta zai dau mataki?"

"Zai aikata kome.ma". Ya faɗa yana kallon yadda Majid din ya d'ago Hajiya suka dauki kayansu, suka nufi gidan. " Ita da Yaranta su zauna a gidan shi ya bar magana gidan mu!" Inji Nana domin ta shirya sai Hajiya ta biya abinda Abdul Majid ya aikata musu.


 Suna da kudi suna da karfi, Majid ba xai zubda musu kimarsu ba. Don haka suka hana Hajiya tafiya, suka sakata a gaba. Shima Majid din kin tafiya yayi yana tsaye a kofar gidan, yana jiran ganin ko Aryan ne, suna can Alhaji Mamman yasa Hajiya a gaba da cin mutuncin, har aka gama bikin cikin kuka take, karshe ma turawa maradi yayi aka rufe gidan wai kada Majid ya tafi can ya zauna.


 Shi kuwa rubuta wasika yayi ya bada aka kaiwa Hajiya da ban hakuri, 


Bayan tafiyarshi da wata biyu, Alhaji Mamman ya yanke mata rabin wahala ya sakata a gaba ta fara zuwa aikin kamfaninshi. Da iliminta da kokarinta ta fara aiki inda ta fahimci wasu na azurta kansu da dukiyarshi, don haka ta fara aikin binciken anan ta gano har da hannun Alhaji Haladu da Kamilu. Ta mika mishi duk wani abinda ta tattara, sannan ya ce mata. "Ki saka Yaranki a gaba su koma makaranta, naji ance wancan dan mahaukaciyar, likitanci yake karantawa. Tow sai ya cigaba amma ya sani ko ya gama karatun anan zai yi aiki xa a fara gina mishi asibiti."

 Zuwa yanzu baya shakkar mutuwa dama abinda yake so ya samu, Yaran hajiya zasu iya tsaya mata, duk da yasan yayi kuskure amma a yanzu yana da damar barin mata kome domin shima yanzu ya san girma ya cimma shi.

Majid da y koma sai da yayi jinya, a haka yake karatu, bayan wata uku aka kawo shi har marad'i, don bai san waye akanshi ba, abu daya yake faɗa sai na kashe ka idan ka tab'a min Mamata. Hajiya bata iya ganinshi a wannan halin ba, kamar an mata bushara ta wuce da shi wurin danginta,. A can ya zauna har ya samu lafiya sannan aka yi cuku-cuku ya dawo nan da karatu, amma abin ya zame mishi cutar damuwa dan mental health ɗinshi ya tabu, don ma Kakanshi yana tsaye akanshi da sauran dangin Mamarshi haka yasa shi ya boye yadda yake shan wahala, ya cigaba da karatunshi....

Bayan shekaru bakwai.....

#Dambuje