BAƘIN HAURE..........

Chapter 17

by @maidambu41

*BAƘIN HAURE....🐾🐾*


  {Greed for Money is the roots of all evils🫀}

 Arewabooks:maidambu41

Wattpad:Mai_Dambu

Mallakar:Mai_Dambu

    *017*

Bayan shekaru bakwai.

Duk da wannan shekarun zaka dauka Hajiya ta huta daga jidalin dangin Alhaji Mamman Ba'are, amma ina domin bala'in ya kara hauhawa ne bayan Alhaji Mamman Ba'are ya nad'ata sabuwar shugabar kamfanin ya sauke wanda yake kai ya dorata, ai kuwa sai gashi fitina ta kunno kai, daga kamfanin har gida bata da sukuni.


     A lokacin ko barci neman gagararta yake, wata irin wahala take sha da kamfanin Mamman Ba'are, gashi yadda ta tsaya ba ƙaramin bunƙasa kamfanin tayi ba, domin idan har kana son gane yadda kamfanin ya cigaba tow ka shiga office dinta, ita da Aryan suke tsara duk wani cigaba dake Allah ya taimaka shi mutum ne mai kwazo kamar Abdul sai gashi ya hada karatu da aikin da yake taya mahaifiyarshi, duk da wannan jigilar bai hana idan ta koma Nana ta sauko ta shiga gaya mata magana marasa dadi ba, ana cewa idan duka yayi yawa na kai ake karewa tow ita Hajiya baki daya da ta ko ina kare dukan take, sannan Yaranta tsayawa tayi akansu, domin idan ba haka tayi ba Yaran so ake a lalata mata rayuwarsu.

      A cikin shekaru bakwai din nan, suka tafi bikin gama makarantar Abdul Majid, wanda kana ganinshi kaga babban mutum, sai dai har yau yana nan babu sakewa kamar baya, ga shi nan dai amma yanayinshi zai nuna maka yadda yake jin babu dad'i a cikin mutane. Haka aka gama a hanyarsu ta komawa gida ne, Hajiya ta amshi takardarshi. "First class, Alhaji ka fito da shi amma baka farinciki." Yake yayi ya ce mata. "Ya Amaan yake?" Ajiyar zuciya tayi tana kallon Aryan da Jamilah da kowannensu yayi tsaki. "Yana lafiya." Ta fada tana son ta manta da abinda Amaan din yake mata. "Hammayo yaushe zaka dawo gida?" Shafa kan Anisah yayi yana faɗin. "Zan dawo." "Ka dawo ko Hamma Amaan zai daina saka Hajiya magana, shi ba karatun ba, shi ba aiki yake ba. Sai dai kullum a bashi kuɗi. Hajiya tayi magana har ta gaji "

    Bai ce mata kome ba, shi dai ba zai je Nijar ba, wallahi ko a kai za a kai shi ba zai je ba. "Hmm tayi hakuri ta cigaba da addu'a." 

"Ba zaka dawo gida ba!" Shiru yayi bai ce mata kome ba, zata kuma Magana Aryan ya ce mata. "Nisah ya isa haka, Hammayo ya gaji." Ya faɗa yana kallon Abdul Majid din, dake su sun iya turanci duk haka suka juya harshen turanci. A hankali Aryan yake tambayarshi me yasa ba zai dawo gida ba.

"Kawai ba kome, zan tafi karatun sanin makaman aiki a Nijeriya ne " 

"Amma.". "bana son hayaniya don Allah." Hajiya tasan halin Yaranta, kowa da irin nashi hakurin, amma hakurin Majid daban ne, haka fushinsa daban ne kuma zai iya hakura da kome musamman idan akwai wulakanci da cin mutuncin. Haka suka iso gida, Innarsu kanwar Hajiya wato Kabo wacce aurenta ya mutu take gida dauke da karamar yarta mai suna Zaytoonah. Yarinyar suna shiri sosai da shi, yana shiga ta tare shi da kyaututtuka masu yawan gaske. Tana murmushi ta ce mishi." Hammana ina tayaka murnar kammala karatun ka!" 

Amsa yayi yana faɗin. "Na gode dear!" Daga haka suka wuce ta tsaya tana kallon Aryan da yake mata dariya. "Hamma Aryan dariyarka kamar gwalo kake min"

"Tow Allah ya baƙi hakuri, ina Nabeeha?" Murmushi tayi ta ce mishi. "Ka bani cin hanci dai na kira maka ita."

"Ok idan na shawo miki kan shi fa?" Murmushi tayi ta ce mishi. "Karya kenan domin kuwa zuciyarshi da kiyayya ta ginu, duk macen da zata samu damar kutsa kai cikin zuciyarshi mace mai Sa'a ce, mu shiga ciki zankirata."

Shi kan Aryan tausayinta yake ji, duk da ba bata wuce sha uku ba, yarinyar tana da hankali da nutsuwa, kuma kowa yana musu kwadayin zama ma'aurata, domin ahalin Sheikh Aliyu Wodabbe, suna da nutsuwa da hankali uwa uba Ilimi idan Yaro yayi magana ba zaka dauka shi yayi ba, domin an samar mishi nutsuwa tuntuni.

 Bayan isha Nabeeha tazo suka sha hira, sannan ya rakata bangarensu, waye zai ce wannan haɗin bai mishi ba? Ai babu kaf gidan domin soyayyar da sukewa Sa'a na musamman ne, shi yasa suka dorawa Abdul Majid wata irin kauna.

Bayan sati suka koma Nijar, suka cigaba da abinda yake gabansu. Shi kuma Abdul ya gama abinda zai yi ya dawo Nijeriya domin a can Nsukka yayi course ɗin shi na likitanci, wani ikon Allah sai gashi ya dace. Ana yaye shi aka tura shi asibitin Malam Aminu Kano, anan ya fara Internship ɗinshi. Yana tsaka da aikin ne aka fara diban sojojin sama. Yayi join amma suka ki amsarshi. Saboda wasu takardun shi, sau uku yana gwadawa amma baya samu karshe sai suka makale a bayan matsalarshi na cewa idan ya shiga damuwa zai iya kawo musu matsala a yanayin mental health din shi. Haka ya hakura da sojan sama, yayi apply na kasa shima ya makara, haka ya hakura wata shekara kamar wanda aka ingiza shi ya cika sojan ruwa, wani ikon Allah yana tura takadunshi, suka yi approved.


   Amma a lokacin suka bukaci suga iyayenshi, kamar ba zai je Nijar ba. Amma haka ya tafi wurin Alhaji Abubakar Abzin, ya gaya mishi. Shiru yayi sannan ya ce mishi. "Dole Mamman ya tsaya maka." "A'a ni bana bukatar taimakon shi, kawai kai ai ka wadatar."

"A'a dole ya ga matsayin da ka taka, duk da nasan wata rana haka zai faru dole a bashi matsayinshi na uba."

  Haka Alhaji Abubakar Abzin ya tawo har Niamey, ya gayawa Alhaji Mamman Ba'are abinda yake faruwa. "Amma har na kusan gama.aikin asibitin yaron nan zai dauko wani zance?" Ya fada a harzuke, wai ma girma ya cimma shi. "Baka da iko akan karatun shi, lokacin da nake gaya maka ka janyo danka a jiki ki kayi, yanzu kuwa ya tsaya da kafaffunshi kace ya dawo jikinka, shi wancan da kake hidima dashi har yau babu cigaba jikinka ne?" Shiru yayi, Alhaji Abubakar Abzin ya mishi tass, haka yasa bayan kwanaki ya tawo har kano shi da Hajiya, duk yadda Hajiya taso ta janyo ra'ayinshi ya dawo ga asibiti ki yayi ya ce mata. "Babu dukiyata a cikin asibitin, ni nawa zan nima don Allah ki kyale ni na cika mafarkina." Alhaji Mamman Ba'are yana jin shi, amma bai ce kome ba dukiyarshi ce wato Majid yake kyama? Wani irin kuskure yayi ne haka? Lallai Majid shine magajin GOLDEN EMPIRES, shi daya zai rike da zuciya daya domin babu buri ko kwadayi a ranshi.

"Zan biya ka miliyan goma duk wata kazo ka taya mahaifiyarka aiki." Juyawa yayi ya kalli Alhaji Mamman Ba'are, ya saki murmushi ya ce mishi. "A'a bana bukata na gode."

   "Abdul Majid ka manta da kome, ka dawo zan bar maka kamfanin BA'ARE GOLDEN EMPIRES " juyar da kai yayi yana murmushi. "Da kake gabar mutuwa ko? Hmmm wallahi idan na cire ahalina mahaifiyata da yan uwana har duniya ta nad'e bana fatan had'a alaka da dukiyarka, rayuwarka ka saka ka nimo dukiyarka nima rayuwata zan saka na nimo tawa. Hajiya ki gayawa Mijinki ya daina shiga rayuwata." Daga haka ya mike, ya nufi can wurin da aka saka water dispenser, ya dibi ruwan ya sha, sannan akan lokacin aka ce su shiga, koda suka shiga cikin dakin. Suka tattauna a lokacin da ake gaya musu sharudan aikin da sauransu, sannan sunan da yake jikin takardunshi yasa masu daukar sojoji a matakin farko yasa yake son ganin da gaske ne shi ɗin, family mahukuntan kasar nijar ne. Takaici yasa Majid cewa. "Sir ban nemi aiki a matsayin dan Mamman Ba'are ba, na nima ne a matsayina na dan Nijeriya kuma farar hula, bani da alaka da nijar." Juyawa hajiya tayi ta rufe mishi baki. "Me yasa baka jin magana ne?" Kwafa yayi cikin fushi ya ce. "Na fasa aikin ma." Ya juya zai fita, Alhaji Mamman Ba'are ya ce mishi. "Asibiti ko kamfani ina zaka yi aiki da su." A fusace ya juya zai magana Hajiya ta tsinke shi da mari, rike kunci yayi yana kallonta. "Wannan rayuwarka ce, va zan maka dole ka san daidai ba, amma ba zan matsa maka kayi aiki a ko daya daga cikin kamfanin Ba'are ba, ka tsaya akan ra'ayinka anji kai jinin ba'are ne, so what? Duniyarka zaka gina sai kayi fushi da damarka? Waye kai? Oya wuce kayi sign kai ba bawa bane, mutum ne mai ra'ayin kanshi don haka ka tafi aikinka Allah ya baka sa'a."

     Haka yasa shi amsar kome cikin dadin rai, Hajiya tana tare da shi bayan sun fito, Alhaji Mamman Ba'are ya ce mata. "kin nuna min bani da iko da d'ana kenan?"

"Me yasa lokacin da yake bukatarka baka damu da shi ba? Sai yanzu da kasan iya shi zai iya rike sauran abubuwanka. Nima ajiye maka aikinka zan yi na gaji zan koma wurin dangina."

  A matukar tsorace yake kallonta, bayan Majid ya fito. "Kina nufin zaki juya min baya kenan?" "Hajiya muje!" Uffan bata ce mishi ba, haka suka tafi gidan da yake haya shi kuma Alhaji Mamman Ba'are ya wuce hotel, tunda ya isa can ya fadi rike da gefen kirjinshi, a kayanshi aka samu passport dinshi da hoton Majid da wasu abubuwan, haka aka wuce da shi asibiti. Sannan a nan suka shiga niman Abdul Majid a cikin asibitin, dakyar duka samo shi, koda ya zo kanshi bai wani girgiza ba, kawai dai ya tsaya duba wasu daga cikin tests din da aka bashi, anan suka yi magana da daya daga cikin likitocin. Ya ce mishi."Doctor kasan ya auna arziki?" Sosa kanshi yayi yana kallon Likita. "Ban gane ba?" "Hmm guba ne a cikin jininshi, wanda yayi yawan da." "Bar zancen haka, Allah ya bashi lafiya." Daga haka yaki yarda ya amince da sauran bayanan amma tabbas yasan abin da Alhaji Mamman Ba'are ya shuka shi ne zai girba. Ya je har gidan shi ya tawo da Hajiya ko ita bai yarda ya gaya mata ba, sai a bakin likitan taji. Wani irin tsoro ya cika mata zuciya. Tow Yaranta da suke can waye zai kare mata su. "kina tunanin su Anisah da Jamilah ko? Ai su ba za a musu kome ba, koda za'a yi sai don a kuntatta miki ta hanyar niman wani abu, amma ba wai don tab'a ki ba." Kwanan shi uku aka sallame shi, suka wuce nijar.


 Tunda suka koma jikin Alhaji Mamman Ba'are ya ki,asalima jinya ya kwanta inda aka kwantar da shi asibitin da ya ginawa Majid a can yake kwance. A hankali jinya tayi jinya domin ya kai sama da shekaru biyu a kwance, har wannan lokacin bakin shi bai daina kiran Majid ba, yazo ya yafe mishi. Dakyar Hajiya ta samo shi A Lagos yazo ya ganshi a ranar da yazo yake gayawa Lauyan shi. "Kuri'ata na barwa Abdul Majid Mamman Ba'are, akwai wasu kamfanoni na guda uku da asibiti duk da sunan Majid Mamman Ba'are na ajiye su, lauya ka rubuta a matsayin wasiyyar da na bari, Abdul Majid Mamman Ba'are, ka yafe min." Dauke kai yayi yana latsa wayarshi ya ce mishi. "ai ban kullace ka ba, don haka Allah ya baka lafiya " daga wannan ranar Majid ya bar Nijar dama kwana uku aka bashi, ya bar musu kome nasu kai ko ruwan gidansu baya sha, sannan ya gayawa Hajiya matukar ba ita zata yi girki ba, kada ta sake Yaran su ci abinci daga wani waje don kashe su za ayi.


    Daga lagos tura shi cotonou aka yi, a lokacin jikin Alhaji Mamman Ba'are ya kara rikicewa sannan ana ta nimanshi, a lokacin yana can teku Hajiya tayi sintiri ya kai sau uku. Babu labarinshi. Bata jima da dawowa ba, Allah ya amshi rayuwar Alhaji Mamman Ba'are, ya rasu ya bar wani irin tukekken rikici, domin bayan rasuwarsa, yan uwanshi da Hajiya Tani suka ce da kason su a cikin dukiyarshi.. sannan wasu suna jin haushin Majid domin gani suke saboda son da Alhaji Mamman Ba'are yake mishi ya mutu domin an ki fadar asalin abin da ya kashe Mamman Ba'are.

  

 Ana cikin wannan tashin hankalin har aka kai shi makwancinsa ana rikici. Bayan anyi Addu'ar bakwai sannan aka fara batun gado, domin sai da aka kira Alhaji Abubakar Abzin, sannan aka fara rabon matanshi da suka mishi takaba aka ware musu nasu, sannan aka koma kan Yaranshi mata da maza aka raba, wasa wasa sai ga Hajiya ta tashi da wani irin kaso saboda ita Yaranta maza ne, sai Hajiya Rabi da itama ta samu ba laifi amma ina gani ake kamar da gayya aka tulawa Hajiya Sa'adatu.


    A hankali Lauya ya fitar da kuri'ar kowa ya bashi, da sunanshi sannan ya cire na Alhaji Mamman Ba'are ya ajiye a gabansu. Wannan na Abdul Majid Mamman Abdul Majid ba'are ne, har aka gama raba kome ba a kira sunan Tani ba, nan tayi tsalle ta ce musu. "Shi Sajjid bai da kaso ne?" "Saurin me kike? Akwai kamfanin da take shigo da man fetur kasar nan, ita ce Alhaji Mamman ba'are ya bashi gashi nan." Ya tura mata. "Ban gane ba asibiti da mattan man fetur da ya gina fa?"

 "Mallakar Majid Mamman Ba'are ne?" Sakin baki tayi tana kallon kowa. "Sajjid shima fa jinin shi ne." "Ta ina ya zama jininsa? Mamman Ba'are yana da yara talatin da biyar, biyar din kai sune Yaran Sa'adatu, sauran ashirin Yaran, Rabi, Fauziya, Harirah. Yaran rabi goma sha daya, Hajiya Fauziya goma sha biyu, ashirin da uku sun tafi, Yaran Harirah bakwai da dan karami auta. Lissafi ya fito?"

 "Eh!" 

"Tow bamu ji labarin ya kuma aure ba, domin ko Sa'adatu da ya aureta ya faɗa ke kuma a ina kuka yi auren?"

"Bai gaya muku Ni dadiron shi ba ne?"

"Eh koma meye Muslunci ba zata bawa danki gadon shi ba, domin duk wanda suka ci gado ya halatta a gare su."

 "Ban gane ba?"

"Su aure ya basu uba, ke kuma dadiro kuka yi aka same shi, ba dan shi ba ne danki ne ke ɗaya "

 Wani irin abu taji ya dake ta, tun daga ranar ta hana kanta sukuni ta saka masifa da bala'i a ranta, ta hada kai da wannan ta hada kai da wannan burinsu ace za a sake raba gadon, sannan har bincikan jini sai da taso a ciro gawar Alhaji Mamman Ba'are ayi domin a halatta Sajjid Mamman Ba'are akan dan shi ne Amma abu yaci tura. Don haka ta samu mutanen gidan ta basu shawarar saka hannun jari a kamfanin idan kudinsu yafi na Hajiya da Yaranta yawa, sai su kwace kamfanin. Haka aka yi har Nana da take kan gangara ta zuba hannun jarinta.dukda dai tsufa ba shine mutuwa ba.


 Dake ana bada na Abdul Majid Hajiya ta zuba nashi bakiɗaya, sannan kamfanin sa biyu ana aiki ana tura kuɗin, asibiti ma haka, duk bayan wata sai ayi rigima a board meeting. Dakyar ake shayo kan rigimar, bayan shekara daya da rasuwa Alhaji Mamman Ba'are Aryan yayi aure ya auro Nabeeha, aka sha biki a lokacin Nana ta ce kada Hajiya ta kuma shiga harkar jikokinta har ta yanke hukunci bata gaya mata ba, ita da aka ciyo a caca. Dake sun san Aryan bai da kunya, tass yaje har sama wurin Nana yace mata. "Hammayo bai wurgo ki ba, wallahi kika kuma shiga harkarmu sai na turo ki daga sama." Ya janyota har bakin matakalar. "Sake ni mara mutunci, idan kace na fita Harkar uwarka zan fita ba sai ka kashe ni ba." Tun daga lokacin suka samu salama.

***

 Bayan shekaru biyu da rasuwar Alhaji Mamman Ba'are, kamar wanda aka mishi kiranye, kuma ai kusan haka ne domin Hajiya ta hana idanunta barci akan Yaranta. Addu'a ba dare ba rana ga kome ta samu amma kuma kan Yaranta a watse, sannan a wannan lokacin ita ce me yara kanana, sannan tana cikin wani irin tashin hankali Sajjid ya saka Anisah a gaba. Ta rasa me yake nufi da ita, tayi mishi magana ya ce ta sa a dakatar da shi, da ta gayawa Amaan budar bakinshi ya ce mata. "Hajiya ki saka idanu akan Yaranki mata, kada kina can kina niman kudi da barci wasu su lalata musu rayuwa " sai da ta shiga tsakaninsu domin dambe suka so yi da Aryan abin ya mishi ciwo.

 Wata laraba kwatsam sai ga Majid, lokacin Sajjid ya biyo Anisah wacce ta fito wanka daga ita sai towel, tana ihun niman ceto sai dariya ake mata, shi kuma da abokanshi sai ihu suke. Ranar da kayan shi na aiki ya shigo yaga yadda Sajjid yake kokarin jan towel din. Jan get din gidan yayi ya rufe, sannan ya dauki wani dutse ya jefi Sajjid din sai da ya fadi can gefe. Juyawa tayi ta hango Hammayo, da gudu ta rike towel din ta nufe shi. Rungumeta yayi yana faɗin. "ya isa haka." Ya janye ta, tare da cire rigar jikinshi na kakin soja ya saka mata.

"Wuce part din Hajiya!" A tsorace ta wuce, wato ba zaka san soja wala imani ba, sai da bawan Allah nan ya rufe idanu yayi ta zane su da duk abinda ya zo hannunshi. Ya kwabe Sajjid zigidir ya mishi dukar kawo wuka, Hajiya Tani zubewa tayi tana faɗin. "Idan ka kyale shi wallahi ba zai kuma kulata ba."

"Tani ni bana son ya daina kulata, don Allah ya kulata ni zan kula da lamarinshi."

 "Nana ki bashi hakuri don Allah ya yafe mishi ba zai kuma ba." Wato dukar da Majid yayiwa Sajjid yasa baki daya kowa ya shafawa kanshi ruwan sanyi, domin Hajiya ta haifi zaki, shima kuma Sajjid ko ba a ce mishi ya fita harkarta ba, ba zai kuma shiga harkar nata ba. Don haka ya rufawa kanshi asiri bayan ya kyale shi, ya koma part dinsu, ya same ta ta saka kaya. Tana takure a wuri guda sai kuka take. "Me yasa baki tafi makaranta ba?"

"Bani da lafiya ne!" 

"Kina da saurayi?" Gyada kai tayi, "Jamilah fa?" Tana da shi." "Kice mishi yazo ya samu Alhaji ayi magana" domin bai san Alhaji ya rasu ba, kuka ta kara sosai sannan ta gaya masa Alhaji ya rasu ana niman shekaru uku kenan. Jikin shi yayi sanyi. Amma kuma sai bai nuna ba, sakata yayi a gaba suka tafi kamfanin, a can suka bude farinciki, bai gayawa Hajiya kome ba domin ya gargad'eta kada ta faɗa.


  Daga kamfani gida suka dawo da ake gaya masa abubuwan da aka bar mishi. "Ni dai na yafe dukiyar Mamman Ba'are" 

"Baka isa ba!" Haka suka dawo gidan. Kallon gidan yayi sannan ya cewa Aryan. "Gidan a warewa kowa wurinshi baka san me wani yake yi ba haka zai saka kowa ya zauna lafiya babu saka ido ko cin zarafi. A cikin dukiyar da ya bari a ware part din hajiya a zagaye shi ina son ayi aikin nan da kwanaki arba'in." 

"Tow ina Hajiyar zata?"

"Zata wuce garinsu, hutu na samu na wata biyu, don haka tafiya zamu yi sannan ka samu me niman Jamilah da Aneesah, su nufi Agadaz, su nime aurensu."

A gaban Hajiya aka yi kome, wani abu da Hajiya tayi ta karawa kanta kima shine, dangin Alhaji Mamman Ba'are, bata yarda ta ki su ba, binsu take har inda suke take takai har Hajiya Latifah mahaifiyar Mohan(Bororoji) tana zumunci da ita, sannan yana zuwa wurin Hajiya Umamata mahaifiyar Khalil Dan Ba'are,. Haka yasa suka tura su wurin Ibrahim Dan Ba'are, mahaifin Khalil Dan Ba'are.


 Bayan masu niman auren sun gabatar da kome daga can, Aka kira Aryan aka gaya mishi an kai har da sadaki, ya ce tow ya gayawa Abdul Majid. Daga nan garinsu Hajiya. Basu bi tanka Amaan ba, suka yi tafiyarsu domin Hajiya ta gaya mishi, ya ce ba zai je ko ina ba, wato Amaan shine matsalar dakin Hajiya munafiki. Duk da uzurin da Hajiya take mishi baya gani.


  Watan su daya da rabi suka dawo an gama gyaran gidan har an zuba kome na gidan, daga cikin gidan zaka shiga asalin cikin gidan baki daya, shi dai Majid ya ware layinsu baki ɗaya don abin da yake faruwa babu wanda ya shiga musu. Bai bar kasar ba sai da aka yi bikin kannenshi, sannan ya saka Aryan ya dawo da Matarshi kusa da Hajiya inda shima ya cire flat me kyau aka mata, suka zauna lokacin tana goyan d'anta Abdul.

    Tunda ya bar kasar bai kuma waiwayonta ba, tsawon shekaru shida. A wannan shekarun babu ranar da Hajiya ba zata tafi niman shi ba, ko tasa a nima mata shi ba, sai gashi wannan karon Aryan ya dauko mata shi a kai.

 Wannan shine labarin Hajiya da Yaranta.

-------------

Mu dawo labari.

-------------

Sansanin Yan gudun hijira..


 Wato kun san meke faruwa a cikin sansanin gudun hijirar da muke kuwa? Hmmm wato wani murdadden al'amari ne, adamawan Kamaru tana iyaka da Nijeriya da nijar ta yamma, sannan ana smuggling na kwayoyi safara da yara da mata, wasu ana tura su cikin kamarun, wasu kuma a tura kasashen Afrika da turai.


  Sannan babban wani abun mamaki ta hannun Uwar mugu ake wannan aikin, sannan asalin miyagun kwayoyi da makamai, ana shigowa da sune ta nan ana shiga da shi Nijeriya da nijar.


 ---- Kwana muka yi muna hira da Zuzu da Ummi Addah bata dawo ba, sai wurin asuba ta dawo tana kuka wiwi. "Addah lafiya!"shigowa da Munaisah aka ayi dakin kamar bata da lafiya ko taci duka. "Allah yayiwa Nenne rasuwa?" Tashi zaune mukayi. Murmushi Ummi tayi ta ce mata. "Hankalinku ya kwanta "

"Me kike nufi? Babu kowa a wurinta sai Munaisah naje domin na tayata zama ne!" 

"Ya isa Addah" inji Zuzu, wallahi duk sun saka ni cikin duhu. "ina gawar?" "Tana can ana mata sutura" nida Zuzu muka fita, Ummi ta kalli Munaisah ta ce mata. "Daga nan karatun daya ce har birnin lantsandaal, kin biyewa Addah kun kashe Mahaifiyarki, ki rubuta ki ajiye. Addah sai ta ci amanarki wallahi kuwa sai ta saka ki kuka lokacin babu Zahra da zuzu, matukar zata sayar da Yarta ke din banza ce ba zata iya miki butulci ba. Na tausaya miki matuka gayya."

  Tun bayan an yi jana'izar aka kaita makwancinta, da zamu koma Balali ya kirani ya ce min."don Allah ina son magana dake."

"Ok me ya faru?"

 "Ki saka idanu akan matar da take dakinku da ita wancan me cikin." Hadiye yawu nayi, na ce mishi. "Lafiya kace haka?"

"Kiyi hakuri anan sansanin tunda wancan gayen yazo tow wallahi numfashin ki ma da zai saya tow tabbas zai saya ya samu kuɗi."

 "Me zan iya yi?" D'ago kai yayi ya ce min. "Jeki zan baki sako!"

 Haka na juya na tafi sai lokacin na lura ashe Uwar mugu ya gani. A hankali muka hadu da ita ta ce min. " Me yake gaya miki?" Murmushi nayi nace mata. "Ta'aziya yake min."

"Bayan nan bai ce wani abu?" Girgiza kai nayi nace mata. "Haba bai ce kome ba!" "Zahra'u kenan! Mu shiga ki karya." Girgiza mata kai nayi ina faɗin. "A'a na koshi."

"Muje mana, ko an gaya miki wani abu ne?" Ganin tana son daura zarginta akan Balali yasa ni binta har dakinta, muka zauna ta shiga zuba min abinci da kayan ciye-ciye. Duk abinda ta zuba min sai da na raba biyu tana kallona, tana gamawa na ce mata. "Muci tare."

 "Kin xata zan saka miki guba ce?" Girgiza kai nayi nace mata."ko daya kawai muci tare wannan zan kaiwa Zuzuna." 

"Tow muci" haka muka ci tare da ita, sannan na mike ta kara min abincin. "Kina da wani irin kyau, kiyi amfani da kyan nan mana." Girgiza kai nayi nace mata. "ai kyauwa na muni ne ga wancan abin"

"Kina son zuzu ko????????? "

 🤔🙄Me ya kawo irin wannan tambayar... Jama'a me uwar Mugu take nufi.

#Thedambuje