ABIN DA CIWO

Page 17

by @rahmakabir13

*ABIN DA CIWO*


Na

©Rahma Kabir MrsMG.

Wattpad @rahmakabir


Page 17.

      Last freepage season 1.


*

Binafa.


Bayan zuwan farko da suka yi sai da suka sake zuwa kusan sau biyu kuma duk basa samun Sameeha a gida, sannan duk in sun tashi tafiya sai sun tabbatar mai gadi baya gurin, yana ganin shigarsu amma baya sanin fitansu, shima sosai yake mamakin zaryan da suke yi dan in Sameeha ta dawo baya sanin lokacin da baƙin suka tafi, zuwa na ƙarshe da suka yi ranar monday wanda ya kama zuwa na huɗu kenan, kuma a cikin satin da Aminu yace zai dawo ne, sun samu Sameeha tana gida dan plan ɗinsu kenan da suka tsara, dan mai gadi yau ya tabbatar da zuwansu sun sameta a gida, suna zaune a falo sun sha dogon hijab suna jiran Sameeha ta fito wanda Jamila ta shiga ɗakinta ta sanar da ita, lokacin wanka ta fito shiyasa tace su jirata ta kimtsa, shadda ta saka doguwar riga bubu tasha aiki, sai ta saka hula akanta dan bata so ta ɓatawa wanda suka zo gidan duk da bata san ko su waye ba, a haka ta fito har ta ƙaraso gunsu tana yi musu kallon rashin sani, sai suka gaisheta ta amsa fuska sake.


Amma ban waye ku ba daga ina?


Muma munyi mamakin ganin ke ce matar gidan saboda kwatance aka yi mana da nan gidan, cousin ɗinmu ce aka yi bikinta to lokacin bama gari shine tayi mana kwatance domin muzo muga ɗaki, amma kuma sai muka ga ashe ba gidan muka je ba.


Allah sarki, gaskiya ba nan bane ƙila baku gane kwatancen bq amma da kun kirata a waya kunji.


Sai dai na sake gwadawa dan tun ɗazun muke kira baya shiga.


Allah yasa ya shiga to.


Sameeha ta faɗa tana mikewa dan ta kosa su tafi saboda so take ta fita lanbun gidan ta sha iska tare da jin kamshin furanni, saboda ita kanta gidan yayi mata ba daɗi ita kaɗai ta saba da kwaramniyar su Amrah, su Binafa suka miƙe suna yi mata godiya sai kallonta suke suna hararo garar da zasu kwasa, ji suke dama ta zama 'yar hannu su morewa rayuwa, ita dai sai anjima tayi musu sai da suka fita kafin ta kwalawa Jamila kira ta fito ta rusuna a gabanta.


Daga yau kar ki ƙara barin mini ƙofar falo a buɗe duk wanda ya buga sai kin tabbatar da gurina yazo kafin ki buɗe masa, waɗannen matan ba saninsu nayi ba kin barsu su kaɗai a falo sunyi kane kane, idan masu cutarwa ne shikenan anyi an gama, to ki kula da kyau.


Kiyi haƙuri zan kiyaye.


Yauwa gwara dai ki kula saboda duniya ba gaskiya kowa ya zama mugu dan dama mugu bai da kama, haka kurum ki barsu su shigo ashe bani suke nima ba, kuma kin tafi ɗaki kin barsu su kaɗai, ai da sai ki zauna inna fito sai ki tafi. 


Wayarta da ta yi ƙara yasa ta ɗaga ta koma ta zauna bayan ta gaisa da Aminu sai suka shiga hirar biki daga bisani tace masa.


Noor yaushe zaka dawo ne gaskiya gidanmu yana buƙatar Haskenka.


In Sha Allah ranar asabar zan shigo da Safe saboda zanje kano wani meeting, kuma tunda su Abi basa nan ki shirya mu tafi tare sai ranar monday mu dawo.


Allah ya kaimu amma me kake so in shirya maka ranar asabar ɗin in kazo sai ka ci mu tafi.


Karki wahalar da kanki, kuma ai da sauran lokaci tunda yau monday idan Allah ya kaimu friday in ina son wani abu sai na sanar dake.


Haka suka ƙara taɓa hira akan bikin Salma domin a satin bikin zai dawo, da suka yi sallama Jamila ta ƙara bata hakuri Saneeha ta sallameta ta wuce, a zuciyarta kuma tana mamakin cewa da tayi bata sansu ba, sosai kanta ya ɗaure tunawa da zarya da suke yi a gidan, koda yake duk zuwansu basa samunta wataƙila kuskuren kwatance aka yi musu suke ta zuwa, amsar da wani ɓangare na zuciyarta ta bata kenan sai ta miƙe ta wuce dan tuni Sameeha ta wuce ɗakinta dan ta ɗauki ƙaramarta waya ta tafi lanmu. Jamila tana shiga ɗaki ta tadda wayarta ta ƙara koda ta duba Najwa ce, ta ɗauka da sauri tana shigewa bayi ta kulle, tambayar data yi mata ya girgiza lissafinta da tace.


Me Sameeha tace batan baƙin mata biyu da duka zo sun tafi?


Dama kin san da zuwansu? tace to bata sansu ba karna sake barin Kofar falo a buɗe.


Nan ta kwashe komai ta faɗa mata, Najwa ta sauke numfashi tana cewa.


To bakin Yaya Hauwa ne domin suma ta ɗauke su aiki ne akan Sameeha, shiyasa bata sansu ba kuma Hauwa ita ta turosu akan yau su zo su sameta a gida, dan haka idan sun ƙara zuwa ki buɗe musu ƙofa ki barsu su shiga ɗakinki su ɓoye a nan, koda kwana ya kama zasu yi to a ɗakinki zasu zauna, karki bari Sameeha tasan suna cikin gidan. Yaushe Aminu zai dawo ko har yanzu baki sani ba.?


Ɗazun nan tayi waya dashi a gabana wai ranar Asabar da safe zai dawo.


To ranar Juma'a baƙin zasu zo domin suna so su haɗu da Aminu ne. Ki dai kula dan karki ɓata mana aiki.


Cewar Najwa cike da gargadi, To Jamila tace kana ta yanke wayar, Jamila dai duk sun gama ɗaure mata kai dan ta kasa gane wani abu suke son shiryawa Sameeha, tsoronta da fargaba ace asirinsu ya toni, addu'a ta shiga yi Allah yasa su gama komai cikin nasara ba tare da ɓarkewar wata matsala ba.


.

Najwa.


Shigowar inna ɗakinta yasa ta yanke kiran da sauru, inna ta bita da kallo tana cewa.


Ina sallah naji kina ambatan sunan Sameeha shine na zo naji me ya faru?


Au! kai inna wato kunnenki ya nan ke da kike sallah, to maganar bikin ƙanwar mijinta nake da wata 'yar islamiyarmu tada ce tasan Salma shine na ce mata nima 'yar uwata Sameeha tana auren yayanta.


Ohoo na ɗauka ko kin je gidan ne dana hanaki zuwa.


Haba inna ai nayi Hankali me zai kaini gidan kuma bayan naga sai shamin ƙamshi suke dan na rabu da yayansu, ko da yake ita Anty Sameeha ba ruwanta Ikram ce dai uwar kanzagi.


To ai da gaskiyarta tunda ɗan uwanta kika wulaƙanta, koni nan haushinki naji da kika watsa mini ƙasa a ido.


Ni dai Inna ki mini addu'a Allah ya cika mini burina.


Idan na Alkhairi ne ya cika miki, dan nasan bai wuce na shegen burin auren me kuɗi ba. Kwana biyu ma naga kin rage yawo kin natsu Allah yasa ki ɗaure.


To inna bani da wani sabga shiyasa na natsu tunda muna muraja'an musabaƙar da za muyi na makaranta, kuma fitana ai sai da dalili nake yinsa.


Hmmm Allah ya nuna mini aurenki dai na huta.


Ta faɗa tana harararta, Najwa dariya tayi tabi bayan inna da kallo data fice daga ɗakin, ta gyara kwanciya tana jin wani farin ciki na kusantowar cikar burinta daya kusa cika.


*****


Ranar Juma'a.


Sameeha.


A ranar gidan kakanninta dake kawo ta kai ziyara, wato gidan iyayen ummansu, a can ma ta samu su umma dan sunyi dama zasu haɗu domin su sada zumunci. Ɓangaren su Binafa kuwa bayan sallar la'asar sun zo gidan Sameeha da shirinsu dan ƙaddamar da aikinsu da suka gama shirya masa, ko da suka zo mai gadi ya buɗe musu suka shiga ya saba da ganin sun zo ko da mai gidan bata nan hakan yasa bai damu ba, dan ya hango akwai alaƙa mai ƙarfi a tsakannsu da Sameeha ta 'yan uwanta taka. Jamila ta san da zuwansu dan komai Najwa ke faɗa mata, hakan yasa suna buga ƙofa ta zo ta buɗe musu suka wuce ɗakinta Jamila suka zauna a gefen gado bisa umarnin Najwa data ce ta basu damu su zauna a ɗakinta kuma zasu jira Saneeha ta dawo amma kar ta sanar da ita akwai baƙi, hakan yasa tayi gum da bakinta domin cike aikin sauran dubu goma daya rage zata bata, saboda tun ranar farko data samu sa'ar sakawa Sameeha maganin nan to Sameehan bata sake shan wani fruit ba sai juice ɗin roba take sha, kuma abinci da kanta take dafawa ta ɗiba nata kafin take kiran Jamila ta ɗauka nata, kamar tasan ana shirya mata wani abu kuma ita a bangaren ta gani tayi smoothy ɗin data sha rannan shine ya sakata sha'awa, shiyasa ta hakura da shan duk wani fruit dan kar ya tada mata zaune tsaye tunda ba miji a kusa, sai ta koma shan lemun gora kuma tunda ta daina shan fruit ɗin bata sake jin wani matsala irin da wancen ranar ba, shiyasa ta samu nutsuwa saboda tayi maganin matsalarta. Jamila kuwa sanar da Najwa tayi komai hakan yasa Najwan ta sanar da Binafa, sai Binafa tace kar ta damu akwai wani hanyar da zasu bi koda basu yi nasarar tada mata sha'awa ba, to akwai maganin da zasu bawa Jamila ta tabbatar ana gobe mijin zai dawo ta saka mata a abinci ko abin sha, abin maye ne mai zautar da mutum kuma baya saka barci sai dai mutum ya jishi a rikice kuma ba cikakken ƙarfi saboda yana kashe jiki, hakan yasa Najwa ta samu natsuwa tace zata haɗasu da Jamila wanda hakan ne ya faru a zuwan su yau gidan, kuma Jamila ta tabbatar musu da Aminu gobe Asabar zai dawo, saboda a gabanta Sameeha tayi waya dashi har tana tambayarsa abin da yake so a dafa masa saboda yace da sassafe zai fito dan zai je Kano akwai wani meeting da zasuyi mai muhimmanci, to zai biyo ta gida kafin ya wuce ta shirya tare zasu je, Jamila sai ta tsinci kanta cikin zullumi wanda yasa ta kasa zama a ɗakinta ta dawo falo ta zauna cike da tunani barkatai, wanda maganin da suka bata akan lallai ta saka wa Sameeha a abinci ko abin sha ya tsaya mata a zuciya, haka dai ta danne komai dan dole ta ƙarasa aikin da ta yi alkawari akai, kuma hange dubu goman yasa ta ƙara aro jarumta. 


Sameeha sai bayan sallar magrib suka baro gidan kakanninsu a motarta ta kwaso su, sai da ta wuce gidan umma ta sauke su har da yaranta kafin ta juya akalar motarta ta dawo gida, bayan ta shiga falo ta samu Jamila a nan falo da ta samu a buɗe, da yake in tasan ta kusa dawowa takan buɗe ƙofar, ta kalleta da kyau.


Yau kuma me kike yi a falon ke kadai? kuma baki saka kayan kallo ba. 


Zaman ɗakin ne ya isheni shiyasa na dawo nan, kuma ina tsoron na kunna kayan kallo ki gani kiyi faɗa.


Babu faɗan da zan yi miki in dai ba zaki yi mini ɓarna ba, tashi kije ki yanka mini tattasai da albasa, ki ɗauki kaza ɗaya dake fridge ki tafasa mini, gani nan zan zo na dafa mana taliya shap shap.


To tace mata kana ta miƙe ta wuce kitchen Sameeha kuwa ɗaki ta shiga ta rage kayan jikinta ta fara gabatar da sallar magrib kafin ta fito daga ita sai vest da siket ta shiga kitchen ta samu ta yi mata duk abinda tace, sai da naman ya tafasa kafin ta daura mai ta soya su kafin ruwan tafashen ta ɗaura musu sanwar taliyar, bayan ta gama tace wa Jamila ta kula da girkin zata je tayi sallar isha'i da aka kira dan har an shiga masallaci an tayar da sallar, Jamila ta ce to, kamar tana jira ta fito ta ciro kwalbar maganin da suka bata ta zuba shi duka a cikin sanwar taliyar ta saka dulayi ta motsa kana ta rufe ta ɗaure kwalbar a cikin baƙar leda ta fito ta shiga ɗakinta da sauri, ta samesu a zaune ko wacce da waya tana charting, ta miƙa musu ledan data ɗaure kwalbar tana cewa.


Na zuba shi duka a cikin sanwar Taliyar data ɗaura yanzu.


Aikinki na kyau 'yan mata, dan har na ƙara miki dubu biyar akan cikon dubu gomanki. 


Cewar Binafa da take magana a hankali tana yi mata jinjina da babban yatsa, Jamila murmushi tayi ta juya da sauri ta fita zuwa kitchen.


.

Aminu.


Wajen ƙarfe shida kira na gaggawa ya shigo wayarsa akan meeting ɗinsu da za ayi a gobe asabar ƙarfe biyun rana an dawo da shi ƙarfe tara na safe bisa wani babban dalili, hakan yasa ba shiri ya taso driver sun wajen aikinsu ya bashi motarsa yace su kamo hanyar kaduna, daga shi sai briefcase ɗinsa sai wayoyinsa guda biyu, bai sanar da kowa zai zo ba hatta Sameeha bai faɗa mata ba, dan ya san in ta sani zata hana shi zuwa saboda halin da ƙasar yake ciki na rashin tsaro musamman a arewacin Nigeria, sannan kidnapers sun yi wa hanyar Abuja baƙin fanti wanda kowa yasan ba ƙaramin ta'asa suke yiba sai dai Allah yayi mana maganinsu, hakan yasa bai faɗa mata ba dan ya zame mata zuwan ba zata.


Sameeha da ta idar da sallah sai ta ce bari ta kira Aminu taji muryansa, koda ta kira ya ɗauka amma bata jinsa saboda rashin network hakan yasa ta kashe kiran sai ga text ɗinsa ya shigo.


_Meehata karki damu zan kira ki anjima kaɗan._


Murmushi tayi ta aje wayar ta fito zuwa kitchen lokacin har ta sauya kayan barci dan so take tana cin abinci ta yi barci, dan gobe In Allah ya kaimu ta tashi da ƙarfinta saboda zuwa kano da za suyi, ɗoki take sosai dan rabonta da kano ta manta akwai ƙawayenta na WhatsApp group Sirrin 'ya mace da yawa a can da suka yi mugun sabo, ana zumunci da kuma abubuwan ƙaruwa da ake gudanarwa, sosai take ƙara samun ilimin rayuwa a wannan group ɗin, komai a tsari suke yinsa kamar yadda musulunci ya tanadar, sun zama tamkar 'yan uwa, hakan yasa ta fara lissafin inda zata je kai ziyara dan har ta yi magana da mata kusan uku ta pc akan in ta shigo zasu ganta. Ta samu Jamila a kitchen tana zaune.


Kin duba taliyar tayi kuwa.?


Ruwa ya rage ya tsotse.


Sameeha tace ok sai ta isa tukunyar ta buɗe taga tayi tace.


Ai ni haka nake sonta nasha da romo romo tafi mini daɗi, ɗauko plate na saka miki nima ma saka nawa.


To Jamila tace ta dauko plate biyu ta bata, Sameeha ta amsa ta kashe gas ta soma zubawa Jamila ta saka mata yankan naman kaza ɗaya tace ta sallameta, kana ta zuba nata, saboda ta ƙosa ta ci a kitchen ɗin ta zauna tayi masa cin tsaf, sai da ta cika cikinta sosai kafin ta gama ta aje plate ɗin ta sha fanta da ruwa ta fito tana jin jikinta ya fara yi mata nauyi, zarginta barcin da take ji ne ya fara kawo jiki, taso ta zauna a falo abincin data ci tabi jikinta kafin ta kwanta, amma ina idanunta sunƙi bata haɗin kai sai ta wuce ta shiga ɗaki ta kwanta, dan har ji tayi ɗakin yana juya mata, sosai ta shiga mamakin yadda jikinta yayi sanyi kalau kamar dai ana jira taci abinci ne ganiyar data kwaso ya rufeta.


Nan muka kawo ƙarshen season 1 wato ƙarshen freepages..


Ko me zai faru? Ga Aminu yana hanyar dawo wa dan yana gabda shigowa gida...


Sameeha taci magani a cikin abincinta bata sani ba ta soma shiga wani yanayi na maye...


Binafa da Hanan suna cikin gidan wanda gabaɗaya shirinsu na safiyar asabar ne, sai kuma ga kuma Aminu yana hanyar dawowa. Me zai faru?


Shin burin Najwa yana cika? Ya ƙarshen ta zai zama?


Su Binafa suna cin sanara akan Sameeha kuwa?


Ya bikin Salma sai kazance da Su Hauwa suka ci burinsa.?


Burin Hauwa yana cika kuwa akan aurawa Aminu Najwa da kuma sakin Sameeha da take so yayi.?


Ya ko wanne yake karɓan sakamakon karshensa.? Sai mu tara a cigaban wannan labarin don samunsa kai tsaye har zuwa ƙarshe In Sha Allah.