Idan Rabo ya Rantse

C

by @kwalisa

         BABI NA BIYU

W

ashe gari xaukacin al’umar musulmi suka tashi da murnar qaramar sallah, sai da suka qare kacaniyar gama girki sallah da rarrabawa, sannan Fauziyya ta je ta feso wankanta ta zuba atamfarta Holland da Malam ya yi musu, atamfar ta fito da kyawun sigarta da kyawun dirinta mai tsari da yake gashinta baqi ne sixik kamar tana dyen, gashi da yawa sosai irin me aka kai har gaban goshi, hakan yasa ta yi kitso qanana zig-zag yiri-yiri gashi ya harhaxe ko tsagar ba a iya gani, gaba xaya ya yi baya sai sheqi yake yi, fuskarta ta fito sosai a ranar ta qara yin kyau fiye da kullum duk da yake ba wata kwalliya ta cava a fuskarta ba, farar powder kawai ta saka, sai wetlips mai qamshi, da yake kuma haqoranta a jere suke reras farare tas ga kuma ‘yar siririyar wishirya hakan ya saka data yi ‘yar dariya sai ta bada sha’awa da xauke hankali da wuya qwayar ido ta dubeta sau xaya tak ba tare da ta sake kallonta ba. Ta shafa turare das aka role one sannan ta yi xaurin daya dace da ita, ta kama can qarshen jelinan kitsonta tax an tufke abinta ta saka takalmi da gyalenta iri xaya ta fito xas-xas, Maimuna ta zo ta tsaya tana kallonta sama da qasa. Fauziyya ta yi murmushi tace “Me ye haka kamar yau ne kika tava ganina?” Maimuna ta yi dariya tace “Ni kullum sai in ga kina qara kyau sosai, kalli idonki ma ba ki sa kajol ba kuma baki sa jan baki 24 hours da jagira kajol amma kullum sai naga ke da ba kya yi kin fini kyau sosai, kuma idan muna tafiya sai naga mutane suna ta kallonki har su kixima da Aunty Maimuna da wannan qawayen naku su Murja sai in ga kamar duk abinda kike yi sai sonata kallonki kawai”.

Fauziyya ta yi ‘yar dariya ta girgiza kanta tace “Ke ma in kin girma kin kai kamar ni za ki zama mai kyau” Maimuna ta tsale tace “Allah yaya Fauziyya Allah ya kai mu musha biki” tayi murmushi.

“Maimuna kenan sarkin shiririta ‘yar umma taso muje mu kai abincin gidan Hajiya” Maimuna ta xauko abincin suka fita suka shiga gidan da sallama Rashida tana jin sallamar su ta gangaro daga saman bene da gudu tana sanye da wata shadda tasha sirfani xinkin senagal tasha retouching, duk da bata da gashi sosai ya yi mata kyau ta zo ta rungume Fauziyya suna dariya sannan ta saketa tana qare mata kallo “Wai ubangiji ya yi baiwa a wajen nan Gimbiya kenan” ta doki kafaxarta tana faxin.

“Kin fara ko?” Duka suka kwashe da dariya Rashida tace “Ina tuwon Umma, ko karyawa ban yi ba wallahi ina jiran abincin Umma” Ta tafi da sauri ta buxa qaton flask xin miya tace “Woo! Fantastic daga buxewa har qamshin ya buge ni” Ta saka hannu zata xauki qatuwar cinyar kaza sai ga Hajiya nan ta fito daga kicin ta xauke flask xin Rashida kuwa sai ta bita cikin ‘yar tsokana wai zata qwace duka suka saka dariya Hajiya tace “Wato qarfi da Yaji kin maida ni kakarki, to yau ba za ki ci abincin nan ba don kin san wanda zan ajiye wa ga abinci nan kala-kala ki zavi wanda kike so” Rashida ta vata rai.

“Bana so bayan ke ba za ki girka ba sai dai a xauko wasu banzayen masu aiki su riqa yi mana abinci babu daxi daxaxawa kullum sai Alhaji ya yi faxa baya iya cin abinci gidan sai dai idan ni ce na je na yi masa, wallahi Hajiya ta iya girki duk ranar data yi sai kowa ya yi santi, Allah sa Alhaji ya auro ‘yar jami’a ai Hajiya kya riqa yi idan kika ga zata kwace miki miji” Duka suka kwashe da dariya Hajiya tace.

“Ai ina jinki aniyarki ta biki, kishiya ba a gidan nan ba” Dukan su suka kuma kwashewa da dariya Fauziyya ta zauna akan step dan ba zata iya jure tsayuwa ba saboda dariya, sai da suka qare dariyar Fauziyya tace “Kai dirama kenan ina son zuwa gidan kodan na yi dariya, a dole Hajiya tace kin maida ita kakarki” Rashida tace.

“A to ai ni da Hajiya sai Allah bari naje na sake tsokanarta” Fauziyya ta riqota tana dariya tace “Don Allah ki bari ki qyaleta haka nan...” Kafin ta rufe baki sai suka ji ihu da sowar yara suna oyoyo Mukhtar, oyoyo Mukhtar suka zubawa qofar shigowa ido sai ga yaya Mukhtar ya shigo duk yaran sun qanqame shi Fauziyya ta saki dariya tace “Yaya Mukhtar” Rashida kuwa sai taje da gudu ta faxa jikinsa tana dariya, Fauziyya ta fito ido tana kallon sakarcin Rashida tun yaushe suka daina wannan shirmen tun da quruciyarsu ta sake ido qasa tana wasa da gyallenta Hajiya ta leqo tana faxa tace “Ke Rashida wai sai yaushe za ki yi hankali ne sai kace wata qaramar yarinya?” Rashida bata ma san tana yi ba Mukhtar ya zuba idon shi akan Fauziyya cikin wani irin salon kallo Fauziyya ta kalleshi tana murmushi yana cikin wani xanyen boyal brown color ya fito da shi sosai duk qamshinsa ya cika musu gida, ganin irin salon kallon da yake yi mata ya saka ta sunkuyar da kanta qasa. Rashida ta kai hannunta daidai fuskarsa tana karkaxa hannu sai ya qifta idanu,sannan ya yi dariya haxe da shafa sumarsa da hannunsa, duk suka yi dariya ganin haka ya sa Fauziyya ta miqe zata tafi ya gano manufarta dan haka ya zo daf da ita ya tsaya yana kallonta cikin idonta fuskarsa taf cike da wani sirrin so da qauna, cikin murya qasa-qasa yace “Madam you look pretty today nice to see you” Ya yi shiru yana kallonta ita kuma sai ta dube shi tana murmushi tace ‘Yaya Mukhtar ka sauka lafiya?” Cikin kwaiwakyon muryarta yace “Na sauka lafiya” Har ya sata dariya ya bi ta gefenta yah aye sama ita kuma sai ta yi kasaqe kamar bata da kuzari, suna haxa ido da Rashida sai suka yi dariya su Rashida da qanenta suka bishi can sama suna hayaniya don sunsan Mukhtara ya dawo musu da tsaraba, Mukhtar akwai kyauta tamkar baya son abin hannunshi baya qaramar kyauta sam.

Fauziyya dai ko sallama ba ta yi musu ba ta nufi gida tana zuwa ta fara arba da Abdul da wani abokinshi sun zo har an kawo musu abinci na musamman sun gama ci suna shirin zuwa can su sameta.

Anan suka shiga hira yau Abdul ya qara yi mata kyau sosai yana sanye cikin shadda mirrow blue xinki tazarce ga takalminsa baqi cover shoe sabo fil yana sheqi, Abdul ya dameta da sambatun bege, saboda yadda Fauziyya ta qara yi mishi kyau da Annuri suna hira tasu taga yana neman zarewa da sambatu na shi,wanda ya yi nisa ba ya jin kira don haka tace zata je gida bacci take ji ‘Mu je na ga naki, ki yi kwanciyar ki anan” Ya nuna qirjinsa da hannu, Fauziyya ta rufe fuskarta da tafin hannunta ta fice da xan gudunta tana dariya.

Ranar ko sallama ba su yi ba sai kuxi daya aiko mata ‘yan dubu xaya sababi na dubu xari sai kuma taga saqon shi ya shigo a wayarta. Tana cikin karatun saqwanin Abdul masu sanyaya rai sai ga Abdulu qaramin qanin su Rashida, ya shiga da gudu yana haki Fauziyya ta dube shi a tsorace sannan ta xan Harare shit ace “Koma ka yi yo sallama ai Abban Fauziyya ya hanaka shigowa gidan ba sallama bare kuma cikin xaki” Da yake Abban Fauziyya qarami yana xan shakkarta bata sakar masa fuska da yake Hajiya duk ta shagwava shi wai shi auta, gashi nan a sangarce babu ladabi ba tarbiya ba xa’a don Abban Fauziyya ya zage yana tsawatar musu, sai daya koma ya yi sallama sannan ya sake dawowa yace “Wai ki zo inji Mukhtar” Ta sake hararar shi tace “Idan na kuma ji kace Mukhtar direct sai na zaneka, daga yau sunan shi yaya Mukhtar ka ji ko” Yace “To” sannan ya fice da gudu.

Mintina kaxan ta figi gyalenta, ta sa silifas ta nufi gidan tana tunanin dalilin da yasa yake nemanta, tana shiga gidan ba ta ga kowa ba taji hayaniyarsu can saman bene suna kallon talbijin.

Ta wuce can sashensa sai ta tsaya a qofa ta yi sallama sai qarar music da yake tashi a hankali ta sake qwaqwansa qofar a hankali, can ta ji ya zo ya buxe qofar, ya tsaya yana kallonta yanzu ya sake wata shadda sababbi fil ash colour, xinki tazarce yasha aikin wuyan rigar bai ce mata komai ba, sai ya juya ya koma cikin hakan ya bata damar shigowa, haxe da sallama sanyi ac da qamshin turaren ya sax akin ya yi wani sanyi mai daxi,ta nemi kujera ta zaunashi kuwa sai ya xauki remote ya kashe maganar talbijin da yake kallo channel O sannan ya zauna a xaya kujerar ya dubeta ya saki sannanyar ajiyar zuciyar sannan ya ce “Wall ina son mu yi magana dake gashi ina bala’in jin yunwa kin san sai yanzu na samu kaina yara sun dameni, so shi ne na xan yi wanka”.

“Yaya za a yi kenan?” Ya dubeta a cikin idanu maye kallon da ta tsana kenan ta kalli gefe ta ce “Shi kenan sai in dawo in ka kammala” Ya kalleta ya girgiza kai yace “No, kije wajen Hajiya ki kawo min abinci kaxan” Bata musa masa ba tace “To” ta miqe ta fice ya bita da kallo har ta fice, sannan ya qurawa fuskar talbijin idanu.

Mintina kaxan ta dawo da diren silba xauke da flask da filet da jug da qaramin tambulan ta zo kan tebur xin gabanshi ya ajiye, zata zauna sai ya yi kiranta da wata irin siga daban wanda ya sa ta ji gabanta ya xan faxi ras, kaxan ta dawo ta haxa mishi abinci a flat duk yana bin ta da kallo tamkar zai cinyeta hakan ya haddasa mata slow active, ta riqa yin komai a hankali saboda jin kunyarshi, ta koma ta zauna tayi shiru tana yin saqe-saqe a cikin zuciyarta, tana nan a zaune yaje ya wanko hannu a kicin ya dawo ya fara cin abinci a yangance,kamar mai baiwa na goye, ko yaya tax ago kanta sai tag a idanunshi a kanta tsaf, ta ji duk ta takura da qyar take motsawa, ta ji haushi ya kamata kamar ta tashi ta fice daga xakin, gaba xaya duk kasala ta rufeta, saboda sanyin da yake surara a xakin, kuma dama barci take ji saboda jiya bata yi barci da wuri ba, suna ta kacaniyar aiki, sai daya xauki mintina da dama sannan ya kammala cin abinci ya rufe sauran ya je ya wanke hannu ya dawo sannna ya sake kiranta, irin salon maganar da ya yi xa zun yace “Zo ki zuba min lemon” Da qyar ta taso kamar bata so ta zuba mishi ginger drink mai sanyi ta ajiye a gabanshi, zata juya sai ya kamo gefen gyalenta, ta juyo tana kallonshi cike da alamomin tambaya a hankali ya haxe fuska cikin slow voice yace “Me kika fahimta a cikin qwayar idona?”.

“Ba komai” ya sake yin luu da idanun sa kamar zai rufe su a hankali ya furta “Fauziyya ina fama da ciwon qaunarki a cikin zuciyarta, Fauziyya ki amince min domin na zama abokin rayuwarki kuma uban ‘ya ‘yanki insha Allahu” Da hanzari taji gabanta ya faxi das ta fiddo idanunta, tana kallon shi a hankali ta zame jikinta ta dinga girgiza mishi kanta a hankali take furtawa “Haba yaya Mukhtar kar ka yi qoqarin ruguza rayuwata, don Allah kada ka qara furta wannan maganar, don akwai wanda zuciyata ta aminta da shi don Allah...” Mukhtar ya katseta a hasale yace “Impossible” ya taso ya zo kusa da ita ya tsaye cikin faxa-faxa yace “You better control your tongue,(ki san me kike faxa min) kin san yadda qaunarki take a zuciyata, ai duk duniya ba wanda nake tsananin qauna da bege tamkarki ina son ki fahimta b azan iya kwatanta qaunarki a raina ba” Ya sassauta murya cikin raunanniyar murya mai qunshe da salo na nuna tsantsar qauna da nuna mata ita ce gaba xaya rayuwarsa “Fauziyya please help me you are my life totally(kin tafi da dukkan zuciyata da ruhina) Fauziyya don Allah don girman Ubangiji ki ji tausayina, I become mad against your love, Fauziyya qaunarki tana azabtar da ni na shiga ruxani da damuwa da tamvele da buguwa a cikin mayen qaunarki da sallamawa da afkawa cikin haxari, faxawa kogin son ki kuma shi ne rabin rayuwata, please don’t let me down” Fauziyya ta sake ja da baya kaxan zuciyarta tana bugawa da qarfi kamar zata faso qirjinta cikin raunananiyar murya tace “Don girman Allah da darajar zumuncinmu ka qyale ni, akwai wanda nake qauna har abada...” ta yi shiru ya yin da tsohon ciwonta ya motsa gaba xaya a take zuciyarta ta soma narkewa, ta dafe qirjinta sai ga hawaye nan yana fitowa daga idanunta bakinta ya soma yin rawa kamar mai jin sanyi, Mukhtar yana tsaye yana dubanta cikin haushi, a hankali ya kamo hannunta ya riqe sannan ya sassauta murya yace “Please Fauziyya ki riqeni ni mai qaunarki ne har abada” Ta dube shi idanunta cike da hawaye a hankali ta zame hannunta daga cikin nashi jikinta a sanyaye tana hawaye ta bar xakin, Mukhtar yana tsaye yana kallonta har ta fice, ya koma kan kujera ya zauna cikin vacin rai ya xan buga tebur da hannunsa, haxe da rintse ido ya sa hannayenshi ya dafe kanshi ya yi shiru shi ya san abinda yake ji.

          **

Fauziyya ta tsaya a zaure ta goge hawayenta, sannan ta nufi gida isowa ta shige xakinta ta faxa kan gado kuka mai qarfi ya kwace mata, yaya ma Mukhtar zai bijiro mata da wannan zancen? Ina zata sa ranta, ita dai wacce irin jarrabawa ce ubangiji yake yi mata, wannan ciwon da take fama da shi a cikin ranta ya zata yi da shi? A hankali ta furta “Haba Mukhtar ya ya zaka yi min haka? Ka barni da masoyina Abdul” Ta ci gaba da kuka, hawaye sharkaf ya jiqa filonta, ina ma zata ganshi ina ma shi ne ya zo yace yana qaunarta maimakon Mukhtar! Ina ma Allah ya cika musu burinsu, tabbas duk abinda kake so yana tare da kai har kullum, ina ma ubangiji ya jiqanta ya cire mata wannan ciwon, kullum a cikin addu’a take, ko ta samu rahama ta manta da shi, gashi yau rana xaya Mukhtar ya taso mata da shi, ta saki hawaye “Dole ne na so ka Abdul ubangiji ka sanya min qaunar Abdul a cikin raina, Allah ka yaye min wahalar da nake ciki” Da haka wani nannauyan bacci ya saceta.

Da yammaci kamar qarfe biyar da rabi tana sanye cikin wata doguwar riga har qasa, tana tsakar gida a zaune tana karatun wani littafin addini, Mukhtar ya shigo da sallama sai data ji gabanta ya faxi ras, tayi shiru ta ci gaba da karatu, tamkar ma bata ji shigowarsa ba Umma ce ta amsa suka gaisa sannan ya qaraso wajenta ya tsaya a kanta, qamshin daddaxan turarenshi ya gauraye wajen, a hankali ya sa hannu ya karve littafin ta xago idanu tana dubanshi yana cikin wasu fararen shadda fuskar shi babu fara’a yace “Are you okey?” ta maida idonta qasa bata ce komai ba ya tsuguna gabanta yana dubanta, cikin murya qasa-qasa yace “can’t you talk?” taxan dube shi tace “Umma fa tana kallon ka fa” Ya xan gyaxa kai yace “So what ai hakan nake so ta tabbatar da manufata a kanki,wai mene ra’ayinki game da maganar xa zu?” Ta xan langwave kai cikin marairaita tace.

“Na faxa maka ina da miji Abdul…” Bata qarasa ba ya katseta a hasale yace “Qarya ne! insha Allahu ko kina so ko bakya so ni ne mijinki, abokin rayuwarki” Ta miqe ba shiri a tsorace tana yi mishi kallon tavavve ya tsareta da idanuwanshi yace “Yes ni mahaukaci ne akan qaunarki” Shima ya miqe tsaye da sauri ta juya baya a tsorace ta faxa xaki kamar zata yi kuka anan Malam ya shigo da sallama Mukhtar ya jiyo yana murmushi yaje da sauri ya rungumi malam “Kawu barka da zuwa” Malam ya yi dariya yace.

“Yaushe ka zo ka sauka a garin?” Ya kama kafaxar Mukhtar suka yi xaki suna magana cikin dariya.

Bayan sun gaisa malam ya qwallawa Fauziyya kira ta xauko hijabinta ta sanya ta nufi xakin malam ta durqusa gefenshi, idanun Mukhtar suna kanta da qyar malam yace “Ki kawowa yayan ki ruwa” tace ‘to’ ta tashi ta fice can ta dawo da jug da kofi duk na roba ne, ruwa mai sanyi don daga firji ta xauko su ta ajiye Mukhtar ya riqo fegen hijabinta ya dubi malam yace “Kawu me ne yi wa yarinyar nan sam bata yi min magana ko kaxan” Malam ya yi dariya “Gani take yi yanzu ta girma ne shi yasa take zame-zame” Mukhtar ya yi dariya ya saki hijabinta ta fice da saurinta ranta a vace.

Mukhtar ya matsa kusa da malam kamar zai haye cinyarshi yace ‘Kawu ina son zan yi aure ne” Malam ya yi murmushi ya dafa kafaxarshi yace “Madallah ubana a ina ka gano matar kenan? Zancen da nake son ji kenan cikar mutuncin mutum aure kaga kai ne babba a duk gidan nan, gashi ka zama tuzuru dole qarfi da yaji kuma Alhaji ya saka maka idanu yana kallonka ko?”

Mukhtar ya yi murmushi ya sunkuyar da kai yace “Insha Allahu na gano matata” Malam yace “Ni fa ka san bana son shiriritarka a ina matar take?” Mukhtar yace “Ba da nisa bane” ya duba agogon hannunshi “Yanzu zanje unguwa idan na dawo ma yi maganar”.

“To a dawo lafiya ka biya ta gida ka saka hula ka ji”.

“To malam na gode sai na dawo” Ya miqe ya fita malam ya bishi da kallo domin gani yake yi tamkar shi ne a zamanin quruciyarshi, babu abinda Mukhtar ya baron a shi, tsayi fari da hanci da kyawun siffa duk gunsa ya xebe ya yi murmushi yana bala’in son Mukhtar a ranshi tun yana qarami.


Washe garin sallah Abdul ya zo da yammaci amma ya yi rashin sa’a Fauziyya bata nan sun je gidan Aunty Maimuna hakan yasa ya tafi bai ji daxin rashin ganin nata ba, don ya zo ne su yi muhimmiyar magana da ita.

Daya koma gida sai ya nufi falon Alhaji dake ana hutun sallah yana nan gida. Ya sameshi yana zaune shi da Hajiya Ziza suna hira Abdul ya zauna akan dardumar tsakar xakin sannan ya gaishe da Alhaji da Hajiya Ziza amma ita da qyar ta samu amsawa ya share don ya saba ganin haka daman. A haka ya sake jadaddawa Alhaji maganar auren shi, Alhaji ya yi murmushi yace “Lallai Abdul idan ba a yi auren nan baka barin mu mu huta, shi kenan insha Allahu yau xin nan zan tura mutanena wajen shi malam xin, In sha Allahu ai komai ya zo qarshe” Abdul ya yi murmushi “Na gode Abba madalla” Ya miqe ya ficewarsa.

Alhaji ya gyara zama ya dubi Hajiya yace “Hajiya baki ce komai ba, kija jina da xan ki ya xingimo aure ko?”

Hajiya ta turvune fuska kamar kashan shanu ta tave baki tace “Ni a suwa kare da gudun laiya ni da yake gani ban isa da shi ba, tunda yake ban ice na haife shi ba, in banda haka ga yarinyar kirki da take mutuwar qaunarshi tana bin shi a gindi a gindi kwanaki wani hamshaqin mai kuxi ya fito neman aurenta ta liqewa Abdul amma yaron nan yaqi ya shafawa idonsa tokay a cicci mata mutunci wais hi akwai wacce yake so, waye-waye so dai haka ya riqa goggocewa wallahi ni kaina tausayinta nake ji saboda irin nacin da take yiwa yaron nan said a ya kwance mata zani a kasuwa”.

Alhaji ya numfasa yace “Wai wace yarinya kenan ki ke magana a kanta?” Ta gyara zama tace “Haba Alhaji yarinyar nan fa Kulu ‘yar wajen qawata Hajiya Jabu Kano jidda”.

Alhaji ya xauki hularsa yana karkaxawa sannan yace “Ki gafarceni a gaskiya ba zan goyi bayan Abdul ya auri ‘yar Hajiya Jabu ba domin ba qimata ba ce…” Hajiya ta katse shi.

“Me kake nufi Alhaji me Allah ya rageta da shi a matsayin xiya mace…?” Alhaji ya xaga mata hannu “Dakata don Allah ki gafarce ni gaskiya yarinyart bata da cikakken asali ga rashin kyakkyawar tarbiya sam bata dace da Abdul ba nutsattsen yaro da nake alfahari da shi, ai yarinya da yake so ita ce ta dace da shi, domin ‘yar mutunci ce na yaba kwarai da irin tarbiyar da ta samu, don haka kar a sake kawo min maganar wannan yarinyar don wallahi ko da shi Abdul yace yana son ta bani bari ya aureta mai zai yi da ‘yar mace? Allah ya kyauta” Ya miqe yana saka hularsa Hajiya ta yi masa wani mugun kallo a fusace tace.

“Sannu mai xa to kar Allah ya sa ya aureta, ya je ya auri ‘yar gafaka ma qarewar ‘yar malamai” Ta miqe a fusace fuu ta shige xaki haxe da doko qofa Alhaji ya girgiza kai ya yi qwafa ya saba da ire-iren halayarta ya yi ficewarsa.

Tana jin fitar Alhaji ta dawo ta xauki waya ta latsa lambobin mintina kaxan layin Hajiya Jabu ta xauka sama-sama suka gaisa sannan Hajiya ta warware maya duk yadda suka yi da Alhaji har da qarin gishiri don miya ta yi zaqi “Qyale ni da shi zancen banza yake yi ni ce fa tsautsayi zagin mahaifa, kuma ni ce kwalba ko kin fashe akwai sauran sharri wallahi na rantse idan ina raye ba dai ayi auren nan ba ai nafi gaban a watsawa ‘yarta qasa a idonta haba ‘yar uwa kin manta da irin gulluguzu na… ni ce fa kuxufi fingil uwar ‘yan makirci tsiya ai na san tsiya iri-iri ki barni da su kisha kallo ikon Allah ni na tabbatar miki wannan” Hajiya Ziza tace “Za ki iya tsumma maqunshin cuta” Suka kwashe da dariya mugunta.

          **

Dubu ashirin cif suka miqa a matsayin sadaki domin malam yace bashi buqatar komai banda sadaki. A vangaren Rashida sun bada dubu talatin a take malam ya yanke ranar xaurin aure sati huxu masu zuwa wata xaya kenan dattijan nan sun tafi da yabon dattakon da kyautatawa irin ta malam.

Washe gari ranar da safe Mukhtar ya zo wajen malam bayan sun gaisa sun xan tava hira kaxan Mukhtar bai ji kunyar malam ba ya fayyace mishi gaskiyar qaunar da yake yiwa Fauziyya, malam ya yi shiru ya sunkuyar da kanshi fuskarsa cike da jimami da nuna alhini yace “Babana ka yi haquri da kaina na so haxa auren ku da Fauziyya, na so hakan qwarai amman shigowar wannan yaron danaga sun amince da juna na voye wancan qudurin nawa, ba martaba ta bace ba girma na bane inyi yinqurin rushe wancan maganar saboda na riga na yiwa yaron alqawari, kuma ya daxe yana wahala akanta xawainiya da nuna qauna akanta idan har na musu rusa maganarshi na zalunce shi kuma ban yi mishi adalci ba matsayina na dattijo ban kyautata mashi ba, gashi jiya-jiyan nan iyayen shi suka kawo sadaki…” Mukhtar ya xago kai haxe da fiddo idanu a cikin firgici.

Ya ce ‘What?” Malam yace “Kwantar min da hankalinka ka yadda da qaddara ka yi imani da Allah ya baka wacce ta fita alheri a gareka”.

Mukhtar ya girgiza kanshi cikin bala’in vacin rai da qyar yake magana cikin raunin murya yace ‘Kawu ni a gaskiya na fi kowa a duniya qaunar Fauziyya, na gamsu da mafi alheri ce gareni har abada, kuma tunda na rasa Fauziyya bana jin zan auri wata xiya mace don so, sai don raya sunan ma’aiki da samun zuri’a kuma zan je na danne zuciyata na xau tawakkali Amma ka sani kawu na yi babbar asara na vangaren rabin rayuwata” Ya yi shiru haxe da sunkuyar da kansa qasa yana fidda qwalla malam ya ji matuqar tausayinsa anan take ya rungume shi yana rarrashi ya ji ciwon rashin auren Mukhtar da Fauziyya saboda qaunar da yake mishi, gashi jininsa amma saboda girman alqawari da adalci da tausayi Abdul yana ji yana gani dole ya ture maganar a gefe daga rarrashin Mukhtar har ya dangana a ranar da yamma ya zo ya yi wa malam sallama da bashi kuxi dubu goma ya wuce Legos.

A cikin sati na biyu Abdul ya turo da lefenshi akwatina manya guda uku da kayan na gani na faxa abin sai wanda ya gani, Abdul ya sake buxe wani sabon babi fil na nunawa Fauziyya qauna gaba xaya ta gama sakankancewa ta miqa wuya ga Abdul ta amince da shi babu kuskure.

A cikin safiyar Lahadi Fauziyya tana kwance a xaki tana karanta wani novel ‘One more chance’ sai ta jiyo sallama a tsakar gida da yake Umma bata nan ta shiga nan maqwabta sai ta ji Maimuna ta amsa da yake tana xakin Umma tana goge Uniform xinta, hakan ya saka ta miqe daga kan gadonta ta leqo sai suka yi kicivis da wata budurwa fara doguwa, tana sanye cikin wani baqin material ya yi matuqar sake fitowa da farinta sosai suka dubi junansu sannan Fauziyya tayi murmushi tace mata “Shigo mana” Itama baquwar ta xan yi murmushi ta shiga ta zauna a baking ado fuskarta akwai yanayin baqunta Fauziyya taje ta xauko mata orange drink da cincin a flat ta kawo mata sannan suka gaisa a mutunce sai kuma suka yi shiru.

Yarinyarce ta kauda shirun tace “Nasan baki gano ko ni wace ce ba, ko da yake zai yi wahala ki sani” Fauziyya dai tayi shiru tana sauraronta budurwa ta ci gaba da bayani “Suna na Husna Aliyu amman a gida ana kirana da Kulu, kuma na zo gare ki neman alfarma koda girma ko ba girma” Fauziyya ta xago ido tana kallonta Kulu ta daxa gimtse fuska saboda tsananin kishin da yake zavalvalar zuciyarta a yanzu ta tabbatar ta ko ina Fauziyya tayi mata fintinkau, domin ko kyau dirin Fauziyya ya isa sanya xiya mace tsabar kishi bare ita da Fauziyya ta juye mata masoyi sannan cikin muryar Gadara tace mata “Wallahi ba zan tava saurarawa duk wanda ya yi yunqurin shiga tsakanina da masoyina ba, domin na makance da qaunarshi na ximauce na diririce na rasa tunanina da nutsuwar zuciya duk a dalilin masoyina ya bijire min kuma na yi ammana kece ummul aba’isin wargaza masa duka tunaninshi domin yadda nake fama da ciwon son shih aka ya dulmiye a kogin qaunarki, kuma na lashi takobi ko ta wane hali sai na mallaki Abdul ban damu da rashin so da yake nuna min ba domin a sannu zan juya abina a tsakiyar tafin hannuna. Don haka na zo musamman don na gargaxe ki shisshigi da rawar kai da giggiwa da azarbabi da kika yi wajen fashin zuciyar masoyina ina fatan kina fahimta” Taci gaba “Ina nufin ki rufawa kanki asiri ki sayawa kanki rigar mutunci saboda ni xin nan bani da mutunci ban san rangwame ba ba akan duk abinda nake so na ke kishinsa a raina, don haka idanuna a rufe suke ruf saboda haka ki kiyayi kanki ki shiga taitayinki don zan iya xaukar ko wane irin mataki akan ki musamman idan kika bijirewa uwamarnina” Ta tsagaita ta tsaya tana duban Fauziyya da take yi mata kallon mamaki, sai taga tayi murmushi tace “Koda yake idan mai faxar magana wawane majiyinta ba wawa bane, ni nasan kanki ma ba xaya bane da yaushe ne zan tsaya vata lokacina da kasa kunnuwa ina sauraron kanun labarin al’amarinki? Koda yake na jinjina miki na baki babban matsayi shugabar sakarkaru da ta yo rakiyar mata duniya to ina tabbatar miki idan barci kike yi ki ciji yatsanki domin ki farka daga mummunan mafarkinki kin yaudari kanki wallahi ke a matsayinki na ‘ya mace wacce riba kika ga za ki tsinta a wajen namijin da kike qauna… shi kuma yana qaunar wata? Wane daxin rayuwa za ki ji? Wannan ai tauyewa kai girma ne kuma wata daraja za ki yi ba don haka idan har kin xauka wata tsiya ne ki je kema Abdul xin ya qaunaceki, kuma kije ki yiwa Abdul xin barazanar ya rabu da ni domin shi ya kawo kansa gareni, ba kamar ked a kike manne mishi ya yakiceki ba, a qarshe ina miki addu’a a matsayinki na musulma mai shirin kafircewa saboda rashin yadda da qaddara, mugun nufi da yunqurin mallakar abu ko ta wacce hanya da rashin kaxaita da Allah, ubangiji ya shirya da ke akan hanya madaidaiciya”.

Kulu ta miqe a fusace tana huci cikin fushi tace “Shi kenan mu zuba ni dake za ki gani marar kunya, dan kike zance” Fauziyya ta yi dariya tura haushi tace “Allah ya shirya”.

Kulu ta fice a fusace ba ko sallama zuciyarta kamar zata tarwatse saboda tsabar baqin kishin da yake cinta.

Amma ta koma kan gado ta kwanta zuciyarta tana yi mata zafi da raxaxi da qunci, a take ta ji hawaye yana fita a idonta, yanzu ashe Abdul duk rawar kan da yake yi akanta yana da wata budurwar bayan ita? Kai lallai namiji bashi da tabbas koda yak eta wani vangaren bashi da laifi, wala Allah ya san haqilon da Kulu take yi a kansa ko bai sani ba? Lallai kam ba zai rasa sani ba, koda yake itama da bakinta Kulu ta furta son maso wani qoshin wahala take yi, kai bai kamata ta saka sakarcin Kulu a ranta ba, taje can ta qaraci shirrinta domin rabata da Abdul yadda take ji da shi a zuciyarta a yanzu tamkar ka yi kasadar raba hanta da jini ne har abada mutum mai makirci da qulla sharri tavavvene ba zai wadata ba, ta sauke ajiyar zuciya Allah ka shiryi al’aummar annabi.

Qarfe takwas Abdul ya zo sai data vata lokaci kafin ta fito ta same shi,ya yi shigar qananan kaya shet da baqin wando ya yi kyau sosai, yana ganinta ya kalli agogo ya girgiza kai yace “Yau kuma yanga ake yi min, kinsa kin vata min kusan minti goma sha biyar’ Ta tsuke fuska ta tayi shiru ya sake watso mata wata tambayar “Fauziyya me yake faruwa ko baki jin daxi ne yau? You are so quite” Nan ma tayi shiru a hanzarce ya ce “Oh my god! Fauziyya kina jina kin yi min shiru kina son jinina ya hau ne?” Sai ana ta yi murmushi ta girgiza kanta yace “Oh! har kin sa hantar cikina ta kaxa duk kin rikitani wallahi, ke miskila ce Fauziyya” Suka yi dariya yace “kina son ki dinga wanani, kiji tausayina Fauziyya ni fa marayane a gareki” Tayi dariya kawai tace“To ai babu maraya sai rago ko?” ya katseta yana mata wani salon kallo yace “Kinga na yi miki kama da rago? To shi kenan” Ya girgiza kai yace “Za ki bani labarin ragwantakata da kyau” Tayi dariya har da qwalla tace.

“Ni dai ban ce ba wannan kuma ra’ayinka ne ni babu ruwana”Ya jinjina kai yace “To shi kenan yanzu na bari zuwa jibi, everything you write it down dan nasan ki da nayin tsiya zai yi wahala ki faxa min abubuwan da kika yi arranging na bikinmu”.

Ta sunkuyar da kanta tace “Ba wani abu da nake buqata don ka san halin malam bai bari na karvi wani abu a gunka” Ya xaga mata hannu “Wannan is our personal secret kin gane kar ki bari malam ya sani?” Ta girgiza kanta “Bana voyewa malam komai’ Yace “Oh Fauziyya please wanna fa tsakaninmu ne ba ruwan malam dan nasan shima yanzu ba zai hana miji ya yiwa iyalinsa hidima ba ko?” Tace “Mhm… su waye iyalin kuma?” Ya yi dariya yace “Ga kinan ina sa rai akwai kyawawan zuri’a a tsakaninmu” Tayi shiru tana murmushi cikin jin kunya bayan sun jima suna hirarsu ta soyayya ta miqe tace “Zan shiga gida” Shima ya miqe yace “To big madam muje na tabbatar kin shiga gida lafiya, kin sannan malam ya bani amanarki na kuma karva da muhimmancin gaske” Suka yi dariya suka fito har tsakar gida ya rakota sannan ya tafi da qyar.

         

An shiga satin da za a fara bikinsu, a qalla ta shiga kwanaki goma cif bata ga Abdul ba, koda yake ya aiko wasiqa sau uku ya koma aiko abonanshi da invitation da kuma neman afuwa akan rashin ganinsa, sabida yana shige da fice da qoqarin kammala gininsa wannan hujjace mai qarfi da ta gamsu da ita, ranar laraba ga al’ada ake saka amare a lalle tun qarfe takwas na dare aka yi kamun Rashida da yake gaba xaya bikin gidan Alhaji aka shirya yinsa, don Malam baya son bidi’a don haka ba a yi masa taron biki a gida ba don ance gidan su Rashida suje can su qaraci gayyatar bikinsu na mata duk ‘yan uwansu sun zo jama’ar Xanbatta anan Fauziyya ta tabbatar su ‘ya ‘yan dangine gaba da baya, Fauziyya bata ji daxin rashin ganin ‘yan matan Ummi ba wai suna jarrabawa basu samu damar zuwa ba.

Abin takaici har qarfe goma sha biyu na ranar Laraba ba dangin Abdul ba dalilinsu Fauziyya ta shiga damuwa sisai.

Anti Maimuna ta dinga rarrashinta tace “Don Allah ki saki ranki, kinsa duk wannan shirmen al’adar ba addini bane, abinda ya zama shi ne dole sune shika-shikan aure kamar sadaki, waliyai, shaidu don haka ga wasu tsiraru mutanen masu aqida basu yin irin wannan bidi’ar kar ki damu ki saki jikinki kar a tafi da mu a baka” Fauziyya tace “Shi kenan Allah yasa Abdul xinta yana cikin lafiyarsa da kwanciyar hankali.

Washe gari suka je saloon gyaran gashi sannan direban Alhaji ya kai su gidan ‘yar sudan mai qaunshi sam Fauziyya ta qi yin qunshi ba yadda basu turza da Rashida ba amma fir taqi yarda said a suka yi mata taron dangi suka yi mata caa suna mata magiya sannan aka yi mata kaxan iya hannu suka dawo gida rai a vace.

Ita da kanta ta rasa dalilin daya sat a kasa sakin zuciyarta sam-sam ta ji bata wani farin ciki da wannan bikin, tambayar da take yiwa kanta shin mene ne dalilin shigarta damuwa?

Da yammaci ta nufi gida ta baro ‘yan kacaniyar biki a can, haka kawai take son ta keve don qwaqwalwarta ta samu isasshiyar nutsuwa da zata bi diddigin dalilin da yasa komai ya cakuxe mata a rai, mene ne yake da nasaba da yin haka, tana shiga malam ya yi kiranta ta nufi xakinsa ta zauna a kusa da shi ya dubeta a hankali ya riqa yi mata nasiha mai ratsa zuciya ya dinga jaddada mata bin aure da riqo da ibada da riqo da zumunci, tabbas nasihohin malam sun tava mata zuciya haxe da narkar da ita domin nasiha ce mai shigen kama da wasiyya bata san sanda hawaye ya suvuce mata ba, malam ya xora hannunshi akanta yana rarrashinta abinda ya sake raunana zuciyarta don tausayinsa har ta kifa kanta a kafaxarsa tana kuka. Anan Fauziyya ta dinga jin ciwo da xacin rabuwa da iyaye har ta riqa jin tama tsani aure, da qyar ya shawo kanta ta haqura sannan ta yi masa sallama ta fice, har ta fita ya kirawota yace “Yan uwanki na Kaduna ba su zo ba ko?” Tace “Eh Umma tace suna jarrabawa ne shi yasa ba su zo ba” Yace “Madallah kar dai kiyi fushi da su kinji?” A sanyaye ta amsa “To Abban Fauziyya”Daga haka bai sake cewa komai ba ta miqe ta nufi xakinta ta kwanta lamo kamar mara lafiya duk jikinta ya yi sanyi ta xauki fillow ta xora a kan cikinta a hankali tunanin Abdul ya addabeta “Allah ubangiji kasa ba wani abu ne ya same shi ba” tace cikin ranta nan da nan taji hawaye ya fara silalowa duk ta ji duniyar ma ta isheta ta rasa mene yake mata daxi, duk da iskar fantakar saman tana wulwulawa a kanta hakan bai hanata tagumi ba a hankali ta ji idanunta suna rufewa da haka barci ya soma xaukarta saboda rashin yin isasshen bacci jiya.

Cikin barci ta ji ana ja mata yatsan qafa hakan ya sa ta buxe idanunta da qyar saboda barcin yana fizgarta sosai, ganin Mukhtar a tsaye a kanta yasa ta miqe firgit ta fiddo idanu da suke cike da barci tana dubanshi, Mukhtar yana cikin wasu shet mai dogon hanu da baqin wando ya xora farin glas a idonshi ya kalleta a hankali sai yaji ta burge shi sosai ya yi murmushi yace “A tashi ango ya zo” Da sauri ta kalleshi ta ce “Allah da gaske ne yaya Mukhtar?” Ya ji wani bala’in kishi ya ratsa zuciyarsa ya haxe fuska ya nuna qirjinsa da hannu yace “Insha Allahu ni ne mijinki” Jikinta ya yi collapse (sanyi) ta yi sassanyar ajiyar zuciya sannan ta xan sha mur tace “Don Allah Mukhtar… ji nake da bakinka ka yiwa malam alqawarin ka haqura? To mene ne na kawo maganar?” Ya matsa dab da ita ya tsaya yana kallonta fuskarshi a xaure yace “Wai me yasa kike nuna min qiyayya qarara a fili a tsamaninki zan fidda raid a mallakar ki ne? ke ko aure kika yi kika fito zan iya aurenki no matter how you are duk tsufanki domin qaunarki a gare ni (natural) ce amma na fuskanci kwata-kwata ko xan rusunawa ba kya yi akan qiyayyar da kike yi min why?” Ya tsareta da kallon data tsana, cikin xan marairata da tausasa murya tace “Haba yayana ya ya kake tsamanin mutum zai qi jininsa, wallahi ina qaunarka hundred percent kuma bana nufin suna qiyayya a gareka, ina tsamanin zuciyarka take qissima maka hakan, amma kaifa xan uwana ne tun daga duniya har lahira yaya jinina zai qi jininka? Ina dai janye maka ne domin babu wani abu dazan amfana maka tunda dai ina ganinka dole za mu rabu” Tayi shiru ta sunkuyar da kanta sabida taji zuciyarta ta karaya da tausayin Mukhtar.

Mukhtar ya yi jim kansa yana kallon qasa, sun xan daxe a haka kafin ya xago kai yana kallonta, idanunta sun canza launi sun yi ja alamun damuwa na wanda ya rasa rabin rayuwarshi ta bayyana qarara a fuskarshi a hankali ya riqa furtawa “Fauziyya tausayina ya fi rinjaye akan qaunar da kike yi min, kuma qaunar da kike ikirarin kina yimin na tabbatar qaunace ta ‘yan uwantaka” Ya numfasa ya gyaxa kansa “By all means, bakin alqalami ya bushe amman duk da haka I fill in my mind(Ina ji a raina) wata rana za mu yi aure Fauziyya, ban fidda rai dake ba domin Ubangiji yana taimako na akan duk abinda ya jarrabeni da qaunarshi, so i wish you good luck” Ya ajiye mata wata farar leda mai kyau sannan ya juya ya fice Fauziyya ta ji wani bala’in tausayinshi shin yaya zata yi ne da ranta?

Mukhtar ya faxa cikin haxarin tarkon soyayyarta, Ubangiji ne kawai zai iya wannan lamarin gashi dai a kyan siffa da wayewa da gofewa ta kowane fanni Mukhtar ya tserewa ajin irinsu Abdul to amma babu wani qwaqqwaran son shi da zata xorar a zuciyarta idan ka fidda qauna ta ‘yan uwantaka shi kansa Abdul ba wani cikakken qauna take mishi ba,shaquwa da tausayinshi su suka yi taron dangi suka rinjayi zuciyarta yaya ta iya? Haka Allah ya tsara mata rayuwa.

Sai da aka qwala kiran sallah ta je ta yiwo alwala ta zo ta gabatar da sallah ta daxe tana addu’o’i sannan ta shafa ta lalubo ledar da Mukhtar ya bata ta buxe sai ga Katina masu kyau tsari duk sun turareta da qamshi irin turaren Mukhtar sai kuma cak na kuxi ta xauka ta duba ya rubuta dubu hamsin sai data xan jinjina abin kaxan da aikin Mukhtar,almubazzaranci sam bai tausayin kuxi Allah bani na zubar ne shi, ta xebe katunan ta duba duk na murnar taya aure ne sai wata ‘yar takarda ta buxe ta karanta zafafan kalamai ne na wanda ya dulmiya yayi nisa a tafkin qauna saboda kalamai ne masu girgiza zukata saboda nuni da rauninsa da maraicin rashinta da tamvele da buguwa a cikin giyar begenta da nuni da jimami da karaya da rashin madafa rashin sanin manufar rayuwarsa da alhinin saboda rashin da asarar sashen rayuwarsa qarshe ya rufe da yi mata fatan alheri da zama lafiya.

Hawayene kawai yake fita har ya jiqa mata hijabinta saboda tsananin bala’in tausayawa xan uwanta a take ta tsani soyayya gashi ita da xan uwanta basu kasance masu sa’ar soyayya ba sai zallar wahalar da su da take yi, Allah sarki yaya Mukhtar ya ya zai ji a ranshi? Asarar masoyi wanda kake yiwa irin wannan qaunar tabbas asarar rayuwa ce dole ta dinga sako shi a cikin addu’arta domin duk wannan jagulallen al’amarin wata jarrabawa ce daga rabbi izzati a taqaice dai dukkansu suna mata son maso wani ne domin itama akwai wanda take so a can qasan zuciyarta shima kuma babu mamaki yana can da wadda yake so tabbas rayuwar nan wahala zalla ba don dai shigowar Abdul ba tabbas zata amince da auren xan uwanta ba don komai ba sai don qarfafa zumunci da tausaya masa domin shi kansa auren Abdul soyayyar sadaukar da kai ne, saboda soyayyace ta tausayawa zuciyar masoyi da yin biyayya da faranta ran mahaifinta.