FreeArewaPen original
Idan Rabo ya Rantse
- 1views
- 10chapters
- 0audios
- words
- 0likes
Share:
The story
Synopsis
No synopsis yet.
About the author
Marubuci... Kuma Mai harka buga littafi.
Sample · A
SHIMFIDA TSATSON LABARINRayuwa tsere ce, tun daga cikin mahaifiya har zuwa duniya.Qauyen mu can nesa yake da qwaryar birni. Amma duk da haka muna amsa sunan ‘yan jihar kano.Abubuwa biyu jama’ar qauyen mu suka iya, sai kuma idan damuna ta wuce su koma farauta. A ya yin da yara maza daga sun xan tasa ake xaukar su akai almajiranci,mu kuma ‘ya ‘ya mata daga mun xan xaga sai a soma xora mana dafaffen rogo ko gyaxa muna kawo wa birni muna siyarwa, idan muka kai shekaru sha uku sai a aurar da mu.Jama’ar qauyen mu sam ba su aminta da karatun book ga xiya mace ba. Domin suna ganin ita rayuwar xiya mace kawai zaman aure da bautar tarbiyantar da yara shi ne aikinta.‘Ya ‘ya maza ma ba kasafai ake barinsu su yi karatun boko ba bare kuma mu mata, hakan ya saka sam ba su damu da rashin makarantu boko da asibiti da muke da shi a qauyen mu ba.A wata majiya mai tushe dana ji, ance mun mai...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.