D
by @kwalisa
BABI NA UKU
A
bdul yana kwance akan gadonshi kan sa yana duban cerling duniya ta taru ta kacame masa qwaqwalwarsa ta ruxe basirarsa ta toshe ya kasa “Iya ruwa… bare ya fidda kansa” a duniya ma ya rasa meke masa daxi ne? zuciyarsa tana maqare da wani irin qunci ya kasa tunanin komai tamkar wanda aka asirce, ya kuma rasa hanyar da zai bi ya kamo bakin zaren yana xagowa ya zauna sai ga Kulu ta shigo ba ko sallama ta tsaya qiqam tana kallonsa tasha kwalliya sai taunar cingam take yana haxa ido da ita sai ya yi zumbur kamar wanda aka tsikarawa dab akin bindiga ya miqe tsaye yana mata dariya, haka nan kawai ya ji wani sanyi a cikin ransa tamkar wanda aka yiwa wahayi da shiga aljanna. Yana xan murmushi yace.
“Kulu dama ina son yin magana dake” Kulu ta wani yatsina fuska ta tave baki tace “Ni asuwa wannan martabar ai sai su Fauziyya wane mutum inji mutuwa” Jin ta ambaci sunan Fauziyya sai ya ji kamar ta soke shi da mashi a zuciya yaja tsaki yace “Don Allah manta da wancan maganar ki bani hankalin ki” Jin haka ta kuma wani far da idonta cikin salon yanga da jan hankali tace.
“Bani da time yanzu zan shiga ciki wajen Hajiya ne” Ta juya zata fice tana wani karairaiya gaba xaya ya qura mata ido cikin bala’in sha’awarta da hanzari ya bita kafin ta fice ya jawo hannunta ya riqe yana mata wani kallo hakan ya sat a saki wani murmushi samun nasara da ta yi domin kuwa daman hakan take so, tarkonta ya kama domin ga hannun Abdul a cikin tafin hannunta da ta cakuxe shi da wani sinadarin turaren sihiri lalle Abdul ya faxa(trap xinta) ya tsaya yana mata wani irin kallo gaba xaya ya ji wani irin sonta yana ratsa zuciyarsa ya ji babu wanda yake so da gani tamkar ta da qyar ya iya yin ajiyar zuciya yace “Kulu a yanzu bani da tunanin wata xiya mace sai na ki, kin amince a xaura mana aure?” Kulu tana wani yauqi da yanga tace “Ai you are too late don nima na samu mai sona” Abdul ya rikice ya ruxe ya dinga faman yi mata magiya da qyar ta ce ta amince ka ji aikin sihiri(bokanci)
Ahmmad ne a falon Alhaji ya tada hankalin Alhaji domin kuwa sun xauki ‘yan daqiqu suna musayar yawu da Alhaji, Alhaji ya harari Abdul yace “Qarya kake yin a faxa maka qarya ka tasha qarya ka maida ni dattijon iska a garin nan akan mene ne zaka yi min haka Ahamad?” Ya fiddo idanunsa yana dubanshi Abdul ya daxa cakume fuska “Ai dama ni na ga yarinyar nace ina so, yanzu kuma nace na fasa saboda wani dalili na qashin kaina” Alhaji ya fusata yace “Rufe min baki mara mutunci ni zaka faxawa wani dalili, dalilin xin ka na banza wane dalili gareka eye?” Hajiya Ziza ta kalle shi “Haba Alhaji banga abin zafi anan ba yaron nan shi yaga ‘yar nan yace ta yi masa yanzu kuma dan ya dawo yace bata yi masa ba ai banga abin zafi ba ai ba a tilastawa namiji auren dole…” Alhaji ya katseta a fusace “Ke saurara min bana son zancen banza ni zai mayar dattijon banza? Jama’a suna ganin mutuncina iyayen yarinyar nan dattijai ne na qwarai sun nuna mana halarci sannan don rashin mutunci sauran kwana xaya rak a xaura aure ka ce ka fasa, to wallahi aure ko kana so ko baka so sai an yi shi”.
Abdul yace “Gaskiya Abba na canza ra’ayi a kanta ai ana xaura aure ma a warware bare kuma ba a xaura ba, ni a gaskiya akwai wacce nake so yanzu”.
A fusace ya Harare shi yace “Wacece kake so?” Ba kunya ba tsoron Allah Abdul yace “Yarinyar nan Kulu nake son na aura” Hajiya ta rangwaxa guda da shewa tace “Ka cika xan halak amman Allah ya shi maka albarka” Alhaji daman da yake fusace ya qara qufulewa a fusace ya wanke shi da mari tas! Har sai da Hajiya Ziza ta tsorata ta miqe tana tsuma Abdul yaga wuta ta gifta ta gefen idonshi fal amma sabida tsabar taurin kan tsiya ko gezau bai yi ba Alhaji ya rufe shi da duka ya tattaka shi,daman ga Alhaji irin masu qirar qarfin nan don Abdul bai biyu Alhaji ba sai ya xebo duka siffar uwarsa Fanna ‘yar Borno da yake da Alhaji da Fanna Bare-bari ne Fanna kyakkyawa ce don haka Abdul baqi ne mai kyau matsakaici gashi da fara’a da mutunci da nutsuwa.
Shekarunsa sun kai ashirin da bakwai yana qarami mahaifiyarsa ta rasu a hannun Hajiya Ziza ya girma ita kuma mutuniyar Boxiya ce a can garin Sakoto sun kai shekaru sama da ashirin da Alhaji bata tava haihuwa ba, ta tsani Abdul bata son ta buxe ido ta gansa a gidan, yasha wuya sosai da azaba iri-iri kafin ya mallaki hankalin kansa, Hajiya Zilai baduniya ce idonta a buxe suke tarr sosai saboda ta xan tava bariki a da can baya kafin ta auri Alhaji. Gidan bokaye da ‘yan tsubbu ba inda bata tsoma qafarta don ta samu kan Alhaji a hannunta amma a banza don shima Alhaji a tsaye yake da qafafunsa ya san halin shexaniyar keyayewar Allah kenan rigafin mugaye yana sane da irin munanan halayenta sarai kawai ta wuri xaya ta gama dashi yana sonta sosai hakan ya yi masa iyaka da rabuwa da ita, shexaniyar ta iya kitifi da kissa da iya haxa kutungila sanabe da iya salon yaudara ga kinibibi da haka take shan gaban Alhaji sai dai duk shaixancinta ta sallamawa qawarta Hajiya Jabu Kano jidda, hatsabibiyar gaske ce sam babu Allah a zuciyarta irinsu ne shi kansa shaixan tsoron haxa hanya yake yi da su.
Sai da Alhaji ya tumurmusa Abdul yana faxa yana zagi sa gaba xaya Hajiya Ziza ta zo ta riqeshi tana bashi haquri Alhaji yasa hannu ya tureta can gefe ta faxi da xuwawu tayi zaman ‘yan bori abin ban dariya ganin haka ta fasa kuka “Wayyo na shiga uku zai kashe min xa” Ta kuma riqe shi da qyar ya haqura ya qyale shi yana ta faman faxa, shi kuma Abdul sai ya miqe yak axe rigarsa qirmijiji ko gezau bai yi ba don tsabar taurin rai, sai kumburi yake yi kamar zai fashe idonsa duk ya yi jajawur saboda tsabar vacin rai duk kuwa da uban dukan da Alhaji ya yi masa, Alhaji ya dube shi yana huci yace “Wallahi matuqar baka canja ra’ayinka ba, ba ni babu kai kuma ka haxa kayan ka ka barmin gidana kafin na dawo” Ya sa kai ya fice duk rai a vace.
Hajiya Zilai ta riqa kiranshi ko sauraronta bai yi ba tace “Oh na shiga uku ni Zinatuwa a ina uba ya tava da xansa tilo akan wata gayyar tsiya can?” Ta koma ta zauna tace “Zo ka ji Abdul xina, qyale shi ni nasan hanyar da zan villowa lamarin zan samo mana kanshi” Nan ta ci gaba da iza wutar fitina ‘Kasan ba a hayyacinsa yake ba ai malam xin nan na samu labarin hatsabibin mutum ne, ai roqon Allah ya yi muku kai da mahaifinka ya malleke muku zuciya don ‘yarshi tayi kwantai ta rasa mashinshini, kasan ‘ya ‘yan malaman nan hatsari ne auren su, suna zuwa gidanka abinda ka mallaka sai ya qare ai kai Allah ne ya yi maka gamon katar, ko ruwan gida qafewa yake yi saboda tsinanniyar farar qafa ai kai Allah ne ya qatoka a hannunsu shi Alhaji yanzu ba zai fahimta ba ka qyale shi iyakarta dai yace ba ruwansa da harkar bikin ku ni zan yi ruwa na yi tsaki a kai ga qanina nan Alhaji Salmanu zai tsaya maka ayi komai lafiya kar ka damu ka ji xana” Ya ji daxi ya dinga yi mata godiya ya fice yana fita Hajiya ta hau rawa da juyi har da guxa tace “Shege mun samu bakin zaren a gaida uban matsafa barbushe”.
**
Washe gari ranar juma’a da safe al’umma Annabi suka shaida xaurin auren Mustapha da Rashida har jama’a suka gaji suka watse ba jama’ar Abdul ba dalilinsu Malam ya ji abin babu daxi a ranshi amma sai ya dake, kafin jama’a su qarasa watsewa malam yana gaisawa da malamai da yi musu godiya wani xan matashin mutum ya zo ya russuna suka gaisa da malam sannan ya miqa masa envelop yace saqo ne daga Abdul malam ya karva ya sa a aljihu yayi masa godiya ya tafi wajen baqinsa manyan malamai da dattijai unguwar don ya sallamesu.
Umma tana tsakar gida tana tabkewa Maimuna gashinta sai ta ji mutane sun shigo babu sallama da yak eta ga baqin idone sai ta ce “Sannunku da zuwa” Ta miqe tana “Ku shigo mana” Hajiya jabu da take sahun gaba da ta jagoranci ‘ya ‘yan iskan mata da suka xungumo kamar za a je yaqi ta katse Umma cikin qasaita da nuna Gadara tace “Ke dawo ai zance bana zama bane, saqone za mu isar daga yaron wajen mu Abdul maza-maza a haxo mana duk abinda aka sani na mu ne a gidan nan… ina xan mu ina ‘yar matsiyata?” Hajiya Ziza ta café “To ke baiwa Allah da ganin mu ai kin san ba irin gayyarku bace matsiyata to Allah kawo me bamu da kuka mallake mana yaro da asiri kuka tura masa ‘yarku da ta yi kwantai ta rasa mashinshini to Allah ya karya alqadarinku yanzu xan mu ya fasa auren ‘yarku don haka a haxo mana dukiyar mu faqat”.
Hajiya Sabuwa qyaftin tace “Can gayyar matsiyata ku je can ku nemi ya naku-ya-naku tagajan-tagajan” Hajiya Jabu ta café “To ku in banda abinku ma ba kwa neman irin gardawan nan (almajirai) ku bashi sadaka”.
Umma ta ji cin mutuncin ya yi yawa tace “Kun ga don Allah ku saurara mun fi qarfin cin mutunci da zarafi, ai tun farko rashin sani ya sa kaza kwana akan dami… ku asuwa kare da gudun layya daman ku jahilai ne kidahumai marasa sanin darajar mutane? Ai kun tauyewa kanku girma baku da wata daraja a idon mutane baqaqen ashana qona gari, ni za ku zo har gida ku nunawa ku tsofafin karuwai ne? to a yau na godewa Allah day a yi min tsari da haxa zuri’a da ku gayyar tsiya, annoba irin jaraba shashashun banza da wofi” Ra shiga cikin xaki a fusace ta fara xebo musu akwatunan su, su kuwa sun hayyaqo mata kamar za su cinye ta xanya tana gama ajiye musu akwatunan ta kalle su xaya bayan xaya tace “Maza ku xebe tsiyarku ku fice min a gida gayyar na aiya, wanda basu gaji albarka ba” Anan suka tsaya suna caka mata baqaqen maganganu harda zagin cin mutunci Hajiya Jabu ta zaqalqale kamar zata daki Umma tana wani zaburowa amma da yake Umma jarimar gaske ce ko gezau bata yi ba tana tsaye tana maida musu martani don duk abinda aka yiwa xan halak sai ya rama, kuma kunyar mara kunya asara ne, ana haka malam ya shigo ya ji hayaniyar ta yi yawa kamar za su qona gidan don bala’i malam yace “Subhanalillahi me nake gani haka Hindatu lafiya?” Anan Umma ta sassauta murya domin ta san darajar wanda take magana da shi ta bayyana masa duk cin mutuncin da suka yo takakkiya sukai mata malam ya dubesu a taqaice da ganin ya san za a rina,domin kana ganinsu yasan za a rina ‘yan bariki ne yace.
“Haba bayin Allah don za ku karvi kayanku ai ba sai kun yi wani tashin hankali ba ko?” Duk suka yi tsit don malam xin ya yi musu kwarjini sosai duk da haka sai da hatsabibiyar cikinsu ta zaqalqale tace “Ka gafarce ni malam kawai mu a fito mana da kayanmu” Malam ya xaga mata hannu yace “Saurara ku ba abokan maganata bane saboda ku mata ne ba maza ba” Ya yi shiru sannan yace “Yanzu dai kuna buqatar kayan ku ko?” Hajiya Ziza tace “Eh a bamu auren ne bamu yi” Malam ya yi murmushi yace “Alhamdu lillahi Allah yasa haka shi ne mafi alheri a garemu gaba xaya” Ya shiga xaki ya tattaro duk abinda ya san Abdul ne ya bawa Fauziyya hard a irin kayan day a kan aiko mata da kuxexen daya bata da kuxinsa na sadaki ya haxosu cin ya bawa Umma yace ta basu Umma ta karva taje gabansu ta zube musu hakan da malam ya yi ya basu mamaki sosai, anan dai jikinsu ya yi sanyi don abinda suka zo nema gashi nan har da qari suka kwashi kayan kunyarsu suka fice fal da borin kunya.
Umma ta zauna ta zuba tagumi qwalla suka ciko mata idanu ta girgiza kanta wannna wane irin bala’i ne a zo har gida a ci musu mutunci su akan abinda bai kai ya komo ba, Allah wadaran irin wannan neman auren.
Malam ya leqo daga xaki yace “Haba Hindatu mene ne na damun kanki akan wannan shirmen banzan duk abinda mutum ya yi ai don kanshi irin waxannan mutanen ba masu daraja bane ko a wajen Allah, suma basu san darajar mutane ba to mene ne wani abin damuwa Allah ya sa hakan shi ne mafi alheri addu’ar kenan” Ya koma xaki ya kwanta zuciyarsa cike da baqin cikin abinda Abdul ya yi masa Umma kuwa shigewa xaki ta yi cike da vacin ran cin mutuncin da aka yi musu akan rigimar neman auren Fauziyya.
Malam yana kishingixe akan gado abin duniya ya dameshi babu abinda ya tsana irin karya alqawari da yaudara da cin amana shi ya sanya tun da fari ya gindayawa Abdul sharuxansa ya kuma amince yarda da aminci da sakankancewar da suka yi da Abdul amma said a da ya watsa musu qasa a idanu abin kuma duk bai tsaya anan ba har sai ya turo an yi musu wulaqanci da cin zarafi? Ba gaira ba dalili zuciyar malam ta cunkushe da takaici da baqin ciki wannan al’amarin abin ya yi matuqar tsaya masa a ransa, abubuwa da ya tsana kenan sakamakon amana da yarda da ya yiwa Abdul kenan? Ya ji tausayin Fauziyya ya kamashi ya tabbatar idan ta ji wulaqancin da aka yi musu ranta idan ya yi dubu zai vaci, kuma sai ta fishi shiga damuwa.
Ya ja pillow zai kwanta sai ya ji alamun takarda a jikinshi sai a lokacin ya tuno da saqon Abdul ya xauko ya buxe sai yaga katin biki sabo fil mai kyau a ‘yar takarda kuma an rubuta.
Ka gafarce ni mala mina fatan ba zaka ga laifina ba saboda samun canji ra’ayin auren Fauziyya, hakan ya biyo bayan wasu dalilai nawa na qashin kaina… ina fatan idan ta samu wani miji sai ta aura ga katin xaurin aurena nan a yi min afuwa.
Na gode.
Abban Fauziyya ya ninke takarda ya saka a qarqashin pillow ya yin da qirjinsa ya riqa bugawa da qarfin gaske, lokaci xaya kansa ya soma sarawa da qarfin tsiya yana juyawa zuciyarsa ta riqa bugawa da qarfi da qarfi lokaci guda numfashinsa ya soma fita sama-sama da qyar ya riqa salati cikin halin rikita da ximuwa anan take ya soma fita daga hayyacinsa cikin ikon Allah sai ga Umma ta shigo da sallama ta tarar da malam a cikin mayuwanci hali cikin hanzari ta tallaba shi tana faxin “Innalillahi wa inna ilahir raju’un malam! Malam!” Sai ta fashe da kuka a gigice cikin ruxewa ta rasa me zata yi masa, ana cikin wannan halin sai ga Mukhtar ya zo yiwa malam sallama saboda ko wajen xaurin auren bai je ba don tsabar baqin cikin da yake cinsa yana can gidan wani abokinsa a kwance yana leqa xakin malam sai yaga halin da yake ciki da gudu ya qarasa a ruxe yana salati cikin sauri da zafin nama ya xago malam yana faxin.
“Kawu! Kawu!” Ina Malam ba bakin magana yana cikin halin ciwo gaba xaya cikin rikicewa Mukhtar ya xauke shi ya saka shi a mota Umma ta xauko gyalenta ta shiga motar ta rungume shi suka tafi asibiti.
Emegenecy aka tura shi Doctor on duty ya fara binciken kansa ya yi masa B/p nan take jininshi ne ya yi mummunan hawa irin wanda kan haddasa(stroke) shanyewar varin jiki kuma ya samu (heart attack) at once mummunar bugawar zuciya (beart bite) ya fara dawowa normal sai bacci mai qarfi ya xauke shi, Doctor ya kirawo Mukhtar office ya dinga yi mishi bayani a hankali a bayanin na shi ya samu vacin rai ne(tension) ya taso da mummunan hawan jininshi wanda ya haddasa zuciyarshi kamuwa.