Idan Rabo ya Rantse

E

by @kwalisa

BABI NA HUXU

B

ashir yana zaune a gefen gadon malam fuskarshi xauke da damuwa qara-qara. Umma tana gefe a zaune ta rafka tagumi tana faman zabga addu’a a zuciya Allah ya tashi kafaxar malam xin.

Sai da aka kwashi awa biyu sannan malam ya farka ya buxe ido yana salati cuta lokaci kaxan tasa ya yi fari qal, fuskarshi ta faxa kamar wanda ya shekara da ciwo ya buxe idanu tar yana dubansu. Mukhtar ya miqe zumbur cikin damuwa ya riqo hannunshi yana masa sannu, malam ya yi murmushi yace.

“Ya ya Mukhtar?” Cikin murya mara lafiya yana kallon Mukhtar yace “Kaga abinda yaron nan ya yi mana ko?” Umma ta matso daf da shi tace “Don Allah malam ka bar maganar nan ba lafiya gareka ba, kar ciwon nan ya sake taso maka kuma duk vacin rai ne da ka sakawa ranka ka yi haquri kabar wannan batun”.

Malam ya yi murmushi yace “Haba Hindatu ai na riga na rufe wannan babin tuni” Ya maida kallonsa ga Mukhtar “Ina fatan wannan abu da Allah ya shirya ya zama alheri a garemu daman har raina na so ace Mukhtar ne ya auri ‘yar uwarsa, Allah ya cika min burina, Mukhtar mene ne ra’ayinka akan Fauziyya? Har yanzu kana sonta ko ka sauya ra’ayi akanta? Daman saboda girman cika alqawari na daure na cije nace ka haqure wa wannan batun domin a cika alqawari don Annabi yace ka sowa xan uwanka abinda kake sowa kanka, amman sabida halin xan adam yaron ya nuna mana butulci. Daman kuma xan adam ko ubangijin daya halice shi sai ya nuna masa butulci, don haka Mukhtar na baka Fauziyya duniya da lahira ko bayan raina ka faxawa Alhaji ya yi qoqarin ya ida cika min burina, Mukhtar na baka Fauziyya ka riqe Fauziyya kaine uwarta kai ne ubanta kuma nasan Fauziyya mai biyayya ce da haquri da tawakkali na tabbata ba zata savawa umarnina ba, Allah ya albarkace ku ya haxa fuskokinmu da alheri…” Ummi ta katse shi cikin murya kuka.

“Haba malam ya kake irin wannan maganar ne, ai sai ka faxar mana da gaba Allah ya baka lafiya” Malam ya yi shiru yana murmushi.

“To shi kenan dai Allah ya bamu sa’ar tafiya ko?” Sai yace “Na manta casbahata a gida ko?” Sai ya yi salati da Kalmar shahada ya yi shiru bai sake cewa komai ba. Mukhtar duk dauriyarsa sai da ya kasa magana ya haxa hannayenshi ya rufe fuskarshi idonsa sun yi ja jijiyar kanshi duk sun tashi saboda bala’in tashin hankali da haka malam ya koma barcinsa a hankali hakan ya saka hankalinsu ya kwanta, mintina talatin da biyar a tsakani sai ga likita ya shigo ya zo ya tsaya akan malam ya qura masa ido sai yaga baya numfashi da sauri ya je kansa yasa (sfethescope) abin auna bugun numfashi ya xora a qirjinsa shiru ya sake kama hannunshi ya dafa wata jijiyar kusan sakan goma sittin nan ma shiru bata harbawa a sanyaye ya gyara mishi kwanciya yaja farin mayafi ya lillive shi Mukhtar ya xago kanshi yana kallon likitan, Likitan yace “I am very sorry may his soul rest in perfect peace”.

Basher yana jin haka ya miqe a razane haxi da cewa “Inna lillahi wa inna ilahir raju’un” Kawai sai ya rungume malam yana hawaye haxi da cewa “Shi kenan kawu ka tafi ka barmu” Umma ta tsuguna ta haxa kai da gwiwa ta rasa me yake yi mata daxi a duniya sam idonta a bushe suke ba xigon hawaye ko kaxan sai tsabar baqin ciki a zuciyarta kamar ana hura wuta, mai yanke jin daxi mai yanke hanzari mai katse duk buri mai yanke qauna Likita ya riqa baiwa Mukhtar haquri yana faxin.

“Please my friend be a man(Kulli nafsin za’ikatul maut) kowa lokacinsa yake jira” Da haka Mukhtar ya ji zuciyarsa ta dake ya yi shiru shi kaxai yasan abinda yake ji xacin mutuwa kenan Allahu Akbar Allah gwanin mai iyawa babu ya Allah rayaye mai kashewa mai rayawa a cikin abinda bai kai qiftawar ido ba.

Allahu ya ji qan malam ya sa mu cika da imani ya xauri ranmu a cikin sauqi mutuwar malam mutuwa ce wanda ba za a mance da ita ba, domin ta bar tarihi mai yawa domin da an tuno ranar xaurin auren Rashida dole za a tuna da shi.

           

Fauziyya tana lafe a can qurya xakin Hajiya hawaye ne wani yake bin wani duk kuwa da ruguntsumin da hayaniyar ‘yan biki hakan bai hana zuciyarta cunkushewa da xinbin baqin ciki da Abdul ya stomata ita da iyayenta ba musamman tozarcin da ya yiwa malam da gayyata kome malam zai cewa mutane ya fita kunyarsu? Shi yasa a lokacin da dama tun sanda Abdul ya xauke qafarsa zuciyarta ta shiga dawurwura da mummuna zargin kar Abdul ya yaudareta, ashe tana shirin ganin wulaqanci gaskiya ita kam bat a da sa’a sam-sam akan lamarin soyayya ta sake fashewa da kuka.

Sai da ta gaji ta shiga toilet ta wanke fuskarta ta sulale ta tafi gida tana isa gida babu kowa ta shiga xakin Umma bata ganta ba sai ta tsammaci ta kewaya makewayi ne don haka taja kujera ‘yar tsuguno ta zauna ta rafka tagumi hannu biyu, qwaqwalwarta ta cunkushe ta hargitse da tunanin barkatai me ta yiwa Abdul ne haka har zai ci amanar qauna? Ashe dama duk qaunar da yake nuna mata ta qarya ce yaudara ce? Me ya sa Abdul zai yi mata haka? Bayan ta sakankance ta yarda da shi ta yi amana ta aure shi? Wannan wance irin masifa ce Allah yake jarrabarta da afkawa cikinta? Ta yi ajiyar zuciya qwalla ta sake ciko mata to a daidai lokacin ne taga Umma ta shigo daga waje a hargitse fuskarta a yamutse alamun damuwa da baqin ciki hakan ya sat a miqewa a tsorace ga mamakinta sai ga Mukhtar fuskarsa cike fal da tsananin baqin ciki idanunshi sun yi ja kamaninsa sun birkita bakinta a buxe zuciyarta ta cika da tsoro da fargaba me yake shirin faruwa haka? To a daidai lokacin ne taga wasu datijjan unguwa sun shigo da gawar malam an lulluveshi da fara babbar rigarshi ko shakka babu gawa ce! Babu tantama malam ne ya mutu bata san sanda jikinta ya xau wata irin rawa da vari bakinta ya soma karkarwa kamar mai jin zazzavi cikin tsananin sanyi hunturu bata san sanda ta xora hannu akanta ba ta qwalla wata irin qara mai razanarwa lokaci xaya ta ji kanta kamar an buga mata qatuwar guduma a tsakiyar kan ta nan take wani jiri ya xebeta yuuu! Wani abu ya tsirga a qwaqwalwarta duhu ya gifta idanunta a haka ta tafi sululu a sume zata faxi qasa cikin zafin nama Mukhtar ya taro ta ta zube a jikinshi sharaf sumFauziyyaya a ximauce ya dinga kiran sunanta duk ya birkice umma ta saka salati a gigice tace.

“Ta mutu! Ta mutu! Shi kenan itama ta mutu wayyo ubangijia ka taimakeni Mukhtar ka taimake ni zata mutu itama” Mukhtar ya sureta a gigice suka nufi asibiti tashin hankali anan Umma ta zube zaune a qasa ta rafe fuskarta da zani tana sambatu cikin gigita da magagin irin wanda xacin mutuwa ya ximauta da zuciyarshi wannan ne mummuna tashin hankali a cikin wannan baqar rana.

         **

Fauziyya sai da ta kwana uku sannan ta fara farfaxowa hakan yana da nasaba ne da allurar bacci data sha saboda likita ya bada tabbacin dole ne ta samu isashen bacci kwanaki uku sa’o’i saba’in da biyu ta samu bed rest saboda qwaqwalwarta ta samu hutu da nutsuwa tunaninta ya daidaita ta dawo hayyacinta saboda firgita data yi ya kusa effecting xin qwaqwalwarta gaba xaya bayan ta dawo hayyacinta sai da likita ya qara mata kwana huxu saboda yawan damuwa da yawan zubar da hawaye da take yi Mukhtar baya rabuwa da kusa da ita yana rarrashinta jama’a da yawa sun yi ta tururuwar zuwa duba ta ciki har da Alhaji Usman Mahaifin Abdul.

A ranar da ta cika bakwai cin aka sallamota bugu da qari a rana ne aka xaurawa Abdul aure da Husna Aliyu an yi ta talla auren da yayata shi a kafofin yaxa labarai an sheqe aya sosai an shashance an yi bushasha da almubazzaranci da naira saura da me?

Musamman Mukhtar ya xauki hutu domin kula da rarrashin Fauziyya har ta haqura ta yi tawakkali ta maida lamuranta ga Allah Mukhtar ya zama abokin hirarta basu rabuwa yana nan jikinta yana xeve mata kewa da qoqarin mantar da ita abubuwan da suka faru a baya duk da haka xan xacin mutuwar ya motsa sai ta zubda hawaye ta ji duk duniyar ta yi mata qunci da quntata har ta dulmiya a cikin kogin magagin baqin ciki.

Rashin malam babban wawakeken givi ne wanda za a daxe ba a samu wanda zai cike shi ba domin mutum ne da yake da amfani ba ma a cikin family ba har society jama’a da yawa suna amfanarshi ta vangarori da dama kamar xaukar karatu da jama’ar unguwar suke yi a wajenshi da haxa kan ‘yan unguwa domin shi ne ja gaba uban tafiya wajen xaurin auren raxin suna ziyarar maqabarta dubo mara lafiya da son zumunci da sauran abubuwa da dama.

A rana da malam ya cika kwanaki arba’in da xoriya Fauziyya ta je ta buxe xakinshi ta shiga ta tsaya ta na jiyo kamar amsa kuwwa muryashi cikin nasihar day a dinga yi mata har yanzu xakin yana manned a irin qamshin daxaxan turarenshi.

Bata tava ganin mutum mai son turare da qamshi irin malam bah aka ya sa take koyi da wasu al’amuran na shi yakan ce “Annabi mai qamshi ne kuma ma’abocin qamshi ne sosai a rayuwarshi dalilin kenan nake koyi da sunarshi” Haka yasa baya rabo da turaruka har sautu yake bayarwa zuwa saudiya da Dubai shi yasa Mukhtar yak an yi masa guzuri da su, Fauziyya ta nemi gefen gado ta zauna har yanzu xakin yana nan fes-fes da shi da yake malam mutum ne mai tsaftar gaske ta kwanta akan gadon tana tunano rayuwar da suka yi da malam hawaye ya riqa zubo mata tasa hannu ta zame filon zata xora akan cikinta yadda takan yi ako yaushe sai taga emvelop ta xaga sai taga kati da takardu sun zubo jikinta yana rawa ta xauka gabanta ya faxi katin xaurin auren Abdul ne cikin sauri ta warware takardar ta karanta kafin ta gama baqin ciki da takaici sun daxa mamayar zuciyarta sai hawaye ne yake daxa ballewa ko shakka babu wannan takarda ita ta yi sanadiyar tashin hawan jinin Malam wanda ya yi sanadiyar mutuwar shi har lahira da sauri Fauziyya ta miqe ta fice daga xakin zuciyarta kamar zata yi bindiga ta fashe ta tarwatse don bala’in baqin ciki ta shixa xakinta ta jawo qaton enlargement xin Abdul da yake qarqashin gadonta ta xaga da qarfi ta tarwatsa a qasa gilashin ya tarwatse da hanzari ta tattaro duk wasu takardu da Katina da hotuna da duk wani abu mallakin Abdul ta tattara tana hawaye ta tattara ta kai kicin ta zuba a murhu ta haxa da kanazir ta kunna ashana suka kama da wuta. Tana tsaye tana kallonsu cikin hawaye har suka qone sannan cikin kuka tace.

“Har abada b azan yafe maka ba Abdul insha Allahu sai mun yi shari’a da kai a gaban Allah ba zan yafe maka ba! Ba zan yafe maka ba!! Ba zan yafe maka ba!! Har abada!! Har abada!!.


Jarrabawarsu ta fito resul kam ya yi mata kyau sosai don haka ta godewa Allah ta je ta sayo form na school of Nursing & midwife ta cike daman burinta kenan. A yanzu ba wani tunanin namiji a gabanta bayan sun yi interview babu daxewa sunayen xalibai da aka xauka ya fito sunanta ne on top(na farko) Alhaji mahaifin Mukhtar yaje ya biya mata registration da yi mata duk sauran hidimomin makaranta tare da qarfafa mata gwiwa domin yana son qwarai a cikin yaran wani ya yi aikin lafiya yana da sha’awar haka.

Fauziyya ta shiga da qafar dama domin tana jin daxin karatun nata sosai hakan yasa ta saki ranta ta mance da komai, saboda shiga jama’a da ta yi, shiga jama’a yakan mantar da mutum wani baqin ciki don jama’a rahama ne.

A cikin qarshen shekarar ne suka yi jarrabawa introduction wanda akan tantance da kuma yin tankaxe da rairayar wanda suke da hazaqa da ra’ayin karatu (orientation) jarrabawa tana fitowa Fauziyya Abdul Xanbatta on list wanda suka yi passing tayi wa Allah godiya sosai don haka sun shiga cikin shekara ta biyu shekarun zagewa da karatu dealing da rayuwar xan adam.

Ranar lahadi da yake yanzu komai ya canza hatta tsarin rayuwarta ta fannin gogewa da wayewa ilimi ya sake wanketa ta qara sabon kyau da qwarjini na musamman ta xaukarwa kanta tsaftace muhalli a duk ranar lahadi sai ta wanke ko ina a gidan ta cicire yana ta goge ko ina da yake ma dai ba wani datti sosai don Umma bata da qazanta ko kaxan sai ta gama sai ta kwashi kayansu ta wanke ta goge musu tsaf.

Da yammacin ranar tana kicin tana aikin dare kwatsam sai ga baqin ‘yan matan Hajiya Maryam ‘yan Kaduna sun zo gidan Umma ta fito tana musu lale marhabin Fauziyya ta leqo daga kicin tana ganinsu ta fito da gudu suka rungume juna cikin murna dariya da xokin ganinsu ta karvi jakar hannunsu ta kai xakin Umma sannan suka shiga xakin Umma ta je ta kawo musu ruwan sanyi da sovo sannan aka shiga gaishe-gaishe cikin fara’a da jin daxi ganin juna.

Can dai Fauziyya suka shige Hassana ta xan doki kafaxar Fauziyya tace “Mutuniyata kin qara kyau sosai wallahi” Suka yi dariya gaba xayan su Usaina tace “Yaya qarin haqurin malam wallahi sanda muka zo gaisuwa kina asibiti, mun so muje mu ganki Allah bai yi ba sai Ummi ce kawai ta zauna” Aminutace “Wai yaushe rabonki da Kaduna tun muna yara, gaskiya baki da zumunci tunda ko da can muka zo jifa-jifa” Fauziyya tace “Yi haquri ‘yar uwa kinsa sha’anin zumunci yanzu sai an daure, bare kuma kinsa babu wadataccen lokaci saboda karatu” Aminutace ‘Ai na ji haushin tafiyarmu lokacin ina ta jin kewar ganin Fauziyya amma Abba yayi mana yawa fir ya hana mu zama wani makaranta” Suka yi dariya.

Fauziyya ta ji wani abu ya tsirga zuciyarta don ta gane wanda suke magana a kansa Hassana ta ja xan tsaki tace “Ni wallahi ban tava ganin mutum mai tsananin takura tsiya kamar shi ba, Allah wani lokacin har so nake yi Mukhtar ya zo yana jan mu da wasa da barkwanci har bana son ya baro Kaduna in dinga cewa ina ma haka babban yaya yake ai da mun ji daxin amma kullum mutum baya fara’a kullum cikin cin xaci…” Aminuta katse su tace “Mhm Aunty” Suka kwashe da dariya.

Suna cikin hira suka jiyo maganar Mukhtar a tsakar gidan suna gaisawa da Umma da gudu suka fito suna murnar ganinsa ya taho wajensu yace “Yaushe kuka zo garinan ‘yan zariya” Suka yi dariya Aminu ta riqe hannunsa tace “Mu fushi muke yi da kai yaushe rabonka da Kaduna?” Ya shafa kai yana dariya yace “Tuba nake yi ‘yan zariya” Suka yi dariya suka ci gaba da cewa.

“Nima dirata kenan ko gida ban je ba” Hassana da Usaina suka riqa yi masa tsiya wai ko dai akwai magana a qasa, sabida yadda yak eta qarewa Fauziyya kallo har ta wayence ta gudu can kicin ta bar su nan dai ya barsu ya zame don ya gaji da tsiyar da suke yi masa.

Da daddare wajen qarfe tara suna xaki suna hira da Fauziyya ta bayyana musu duk irin cin amanar da Abdul ya yi mata, Aminuda Hassana har said a suka yi qwalla, Usaina ta dinga tsine masa “Wai ina ma zan ganshi, wallahi da sai na ci zarafinsa sosai, shi yasa bana ganin laifin Abba da baya son ganin muna kula irin waxan nan samarin,yakance ku maida kai kuyi karatu ku qyale duk wata harka samari randa Allah ya kawo mazan ku sai ku yi aurenku amma kar ku zubar da darajar ku a banza gashi ya vata miki lokaci a iska shi bai bari wani ya fito ba shi kuma bai aure ki ba, don ma Allah yasa kina da manufa a rayuwarki, gashi Allah ya taimake ki kin faxa karatun ki ai kya huce takaicin shi” Haka suka yi ta hira sai sha biyu suka yi shirin kwanciyar barci.



Qarfe goma sun gama gyaran gida tsaf da ganin yadda suke yi ka san sun saba da hakan. Suna kammalawa suka yi wanka kowacce ta shiga ta wayayyu, gogaggun matan zamani biyu ce ta haxu ga kyau ga wayewa Hassana Atiku farace tsaka-tsaki a tsaho, tana da hanci da ido madaidaici tana da kyan diri akwai tad a fara’a ga gashi mai yawa Allah ya bata don haka ba ta rabo da qananan kitso kuma yana mata kyau sosai, kana ganinta kaga mai qananan kyau tana karanta mass comm. a ABU Zaria.

Usaina Atiku itama dai fara ce amma ita gajeriya ce ba daf ba, tana da ‘yar qiba wanda ta fitar mata da fasalin kyan diri mai tsari fuskarta faffaxa kewayayya mai qunshe da dara-daran idanu farare hancinta qarami madaidaici bakinta xan tsuwet bata da tsahon gashi sosai amma gashinta baqi ne mai yawan gaske bata rabo da gyara shi a saloon ita kuma tana karantar community health office(C.H.O) anan Health Teachonology Kaduna.

Aminu Atiku koda yake sunanta na gaskiya Asma’u amma dai Aminuta bita launinta irin chokulate ne jikinta mai kyau daidai misali haka tsaho daidai misali akwai ta da structure(qira) mai kyau wato qirar kwalba coca-coka fuskarta ‘yar faffaxa mai xauke da dogon hanci da idanuwa dara-dara farare, gata da gashi mai yawa da tsawo baqi sosai, a rayuwarta bata son yin kitso sai dai ta tufkeshi a bayanta tana karatun Diploma a English(Harshen turanci) anan Kaduna poly.

Fauziyya Abdul Xanbatta kuwa yanayin jikinta da tsaho irin na Aminumadaidaita domin irin jikinsu Umma ne itama chokulate ce kalarta, idanunta dara-dara hanci madaidaici bakinta madaidaici mai tsari fuskarta mai xan faxi kamar ta Aminu kumatunta smooth(mai santsi) masu taushi da sulvi. Tana da gashin gira mai yawa kuma tana yawan gyarawa tana da gashi baqi mai yawan gaske kuma mai cika har gaban goshinta gata da xan saje a gefen fuskarta don haka a gefen kumatunta akwai qananan gashi sun kwanta tana son yin qananun kalba a kanta, vangaren diri akwai structure mai tsari da xaukar hankali sosai, hakan ne yasa kullum suka haxu da Aminusunyi ta faman yin musu kenan ita Fauziyya tana Aminuta fita ita kuma Aminutana cea Fauziyya ta fita amman Hassana tace ta yi bincike akan su ta tantance bambancinsu qalilan ne amma yanayin halitarsu duk iri xaya ne. ita Aminu tafi Fauziyya tsahon gashi da dogon hanci domin ta xebo irin hancin babansu ita kuma Fauziyya ta xarata tsarin diri kaxan amma dukansu Allah ya xiga musu baiwar kyau gami da kwarjini.

Koda yake masana sirrin kyan halitar xan adam sun tabbatar babu munana yanzu a wannan zamani domin kuwa ilimi da wayewa sun fatattaki muni kowa da irin baiwar da Allah ya yi masa wani kyau fuska wani kyau halaye wani kyau diri wani kwarjini wani ilimi baiwoyin Allah da dama wasu kuwa an haxe musu duka ne kamar su Fauziyya da ‘yan uwanta.

Suka zubawa juna idanu ba qiftawa Fauziyya ta yi bala’in tafiya into deep shock(tsananin tsorata) shu’uman idanunshi da suka sha firgitata a wani lokaci can da ya gabata sanda tana cikin halin quruciyarta idanuwanshi suna tsaye tsaf a cikin tsakiyar qwayoyin idanunta abinda ya taso mata da tsohon miki dake can danfare a qasan zuciyarta, wani abvu ya dinga yi mata yawo yana mamaye ruhinta gaba xaya jikinta ya yi bala’in sanyi ya xauki tsima, yanayin fuskarta ya nuna qarara halin data shiga na yanayin rauninta, yanayin fuskarta ya juya tamkar zata yi kuka.

Duk abubuwan da suka faru sun zama tarihi a garesu tarihi ma wanda take tunanin shafeshi kwata-kwata daga zuciyarta domin ta tabbatar ubangiji ya qara sanya wani babban hijabin a tsakaninsu a hankali ta ga fuskarshi ta canza ta yi duhu ta daxa xaurewa, yanayin kallon da yake mata ya canza salo zuwa wani mugun kallo mai cike da ximbin nuni da tsanarta a fili, hakan ya saka bugun zuciyarta ya qara tsananta ta shiga raxaxi da xacin baqin ciki a take ta xauke idonta daga kallonsa sannan cikin vacin rai itama ta maida masa martanin kallonshi ta fice daga xakin cikin sauri, tana fita kanta yana sarawa jiri yana neman tafiya da ita har yanzu zuciyarta tana harbawa da qarfi wanda ya sa ta ji numfashinta yana fita da qyar ta yi qarfin hali ra rava jikinta a jikin bango kusa da wasu shuke-shuken fulawa ta jingina bayanta a hankali ta rufe idanunta tana qoqarin sassaita numfashinta da yake fita sama-sama Innalillahi wa inna ilaihir raju’un yaya aka yi haka? Bata tava tsammanin Musbahuxin da Mukhtar yake yawan faxi Abba bane koda yake tsabar taka-tsantsan irin nata da qoqarin a kullum na ganin ta shafe babinsa a zuciyarta shi ne dalilin day a sa ko sunan Abba ta ji ana ambata sai ta tashi tabar wajen, kwata-kwata ma ko tunaninsa ta tsani ta yi bare ta ji ana zancenshi ko wani abu na harkokinsa hakan yana da nasaba ne da qoqarinta na ganin ta daxa ninsata zuciyarta daga kanshi, hakan ne zai baiwa zuciyarta dama nutsuwa da mantawa da shi kwata-kwata da sanya qaunar Abdul da qarfi da ya ji a wannan lokacin.

A yanzu komai ya zo qarshe domin ta tabbatar Allah ya yi mata iyaka da shi kwata-kwata kuma irin kallon qarshe da ya yi mata yana nuna rashin ko inkula da rashin fahimtar mema take yi? Wacce ita? Da kuma nuni da tsanarta qarara a qwayar idonshi don haka itama ta tsane shi! Domin bai san darajar mai qaunarsa bas aura me? Tayi qoqarin cusa qaunar mijinta ko ta halin qaqa ta kuma qoqarin jan xamarar yaqi da neman maganin mummunan dafin daya watsa mata yake kuma cin gaba da tasirin daxa naci a zuciyarta.

“Allah ka rabani da wannan jarraba da ke yi min, ka sanya min qaunar mijina kamar yadda ka sanya mishi qaunarta, ni kuma ka cusa min qaunar abokinshi shi kuma ka yi min iyaka da shi a tare da haramta min shi ubangiji ka sanya min qaunar Mukhtar a cikin ruhina” a hankali ta furta sai ta ji ance.

“Masanin qaunar da ruhina yake miki don shi ya halitta gareni” Da firgita ta buxe idonta sai ta ga Mukhtar a daf da ita yana kallon kwayoyin idanunta kuma ya gano zahirin akwai tsabar rikicewa da damuwa a cikinsu ta sunkuyar da kanta a sanyaye zuciyarta na daxa tsima da tausayawa Mukhtar ya sa yatsanshi yana share mata hawaye sannan yace a cikin tattausan murya.

“Fauziyya har yanzu bakya qaunata ko?” Gabanta ya faxi ras! Da sauri ta xago idanunta masu cike da qwalla tana dubanshi a cikin idonshi take ta ji zuciyarta ta daxa tsimewa da narkewa da tsananin tausayinshi wanda ya yi tasirin raunana zuciyarta bata san sanda ta kifa kanta a jikinshi ba cikin murya kuka tace.

“Ina qaunarka Mukhtar! Wallahi ina qaunarka! Ina qaunarka har abada! I realy love you…” ta qarashe da kukanta Mukhtar ya rungumeta zuciyarsa tana daxa tsuma da tsananin ruwan wutar qaunarta da tausaya mata. Don ya tabbatar har yanzu akwai abinda yake cinta a ranta, amman insha Allahu zai yi qoqarin ganin ya mantar da ita wancan tsohon tunanin nata a haka Musbahuya cimmasu ganinsu a wannan halin sai ya juya a hankali da niyyar komawa ciki. Mukhtar ya xago kansa a hankali yace.

“See mu best friend you regard him! I known he is your brother(kinga aminina nasan yayanki ne ya kamata ki girmamashi) Fauziyya ta sunkuyar da kanta ba ta ce komai bas hi kuma Mukhtar sai ya yi wani xan siririn fito da bakinsa, hakan ya saka Musbahuya tsaya a bakin qofar sannan ya juyo a daidai sanda Fauziyya ta janye jikinta ta juya zata tafi sai Mukhtar ya riqo hannunta ta juyo sai suka sake yin ido huxu da Musbahua cikin hasken flurecent har yanzu fuskarshi xaure take haka zalika har yanzu akwai yanayin kallon tsanar da yake mata a qwayar idanunshi ta xauke kanta ta hanzarta ta kalli Mukhtar tana jiran me zaice mata, Mukhtar ya yi murmushi yace mata.

“Muje ku gaisa da Babban yaya” Ta mayar masa da murmushi cikin qarfin hali tace masa “Ai mun gaisa da shi” Sannan ta juya da sauri ta fice Mukhtar ya yi ‘yar dariya jin daxi da ximbin farin cikin da yake mamayarshi a yau yana juya juyawa ba Musbahuba dalilinshi ya sake yin murmushi ya rasa meye dalilin mata suke tsoron Musbahusannan ya bishi cikin xakin.


    Qarfe tara da rabi aka kaita gidanta, ita kanta gidan ya burgeta hawa xaya ne flat, komai ya yi tsari ya yi mata kyau da kowa ya watse daga ita sai Rashida da take ta faman yi mata tsiya da tsinkalinta kala-kala. Fauziyya tace “Ni yunwa ma nake ji” Rashida ta riqe baki tace “Iyeh! Lallai ke irin damuwar nan ma irinta sababbin amare ba kya yi?” Fauziyya ta yi dariya tace.

“Haba damuwar me zan yi ina son mijina yana sona, kuma ma meye abin damuwa yayana ne fa dama can mun saba da shi damuwata xaya rabuwa da Ummata abinda yake karya min zuciya ji nake yi kamar na yi tsintsuwa na koma gida Allah sarki Umma” Qwalla ta ciko idonta Rashida ta yi dariya tace.

“To na gane wato kun saba shi yasa xazu ya yi kiranki kuka fito ko?”Fauziyya tace.

“A’uzubillahi” Ta jefa mata pillow tace “Yar nema sharri za ki yi mana nib a manufata kenan ba, aniyarki ta biki tari ma kiga naje na xan tava abinci, inje na rufe qofata ni babu ruwana da wannan harkar taki” Rashida ta dinga dariya hard a faxuwa Fauziyya ta miqe ta jefar da gyalenta ta fice zuwa kicin Rashida ta xaga murya ta ce.

“Allah sarki ‘yar qwaila yau za a rantsar da ke yarinya ta kusa girma” Fauziyya dai tayi mata banza ta je ta duba fridge ta xauko tuffa da rani ta xebo meatpie a flat ta dawo xakin ha yanzu Rashida tsokanarta take yi Fauziyya ta soma cin abinci tace “Kya yi kya gama yanzu nan Mukhtar zai zo ya koreki can wajen Mustapha” Rashida tace.

“Mhm har kin tuna min sahibi bari na leqa ta baranda na gani ko ya zo” Ta fice can sai ga ta da gudu ta xau Jakarta da gyale tace “Wai ga Mukhtar nan ya dawo” Da sauri Fauziyya ta ajiye gwangwanin lemo tace.

“Haba?” A tsorace Rashida ta sheqe da dariya.

“Ashe dai duk kuri kike yi?” Fauziyya tayi tsaki tace “Wai ke mene yake damunki ne, don Allah ki tafi ki qyale ni na huta” Rashida tace.

“Ba sai kin koreni ba yanzu zan tafi ga Mustapha yana jirana a mota” Fauziyya ta yi ‘yar dariya tace.

“Waya faxa miki amarya tana cin abinci mai nauyi baki ga snacks na ci bad a tuffa da juice da madara sun wadatar ni, light food kenan masu qara abubuwa da dama a jikin mace” Rashida tace.

“Eh lallai na yadda tunda ke ‘yar Health ce ai ba wanda ya fiku sanin komai sai an jima” Fauziyya ta xebe kayan ta xauki gyalenta ta bi bayanta sai da ta bita har waje suka tsaya suna ‘yan gulmace-gulmacen su cikin raxa, sannan suka kwashe da dariya ta rakata har mota suka tafi gidansa Mustapha ya dinga yi mata tsiya kala-kala da qyar suka qyaleta suka tafi ta dawo xaki ta zauna. Ta yi jugum data gaji da kaxaici sai ta miqe zata shige can xaki anan ta ji sallamar Mukhtar ta waiwayo tana kallonshi ya sake wasu fararen shadda mirrow har ya fi xazun yin kyau sai qamshi yake yi.

Ya zo ya zauna a kan doguwar kujera sannan ya jawo hannunta ta zauna kusa da shi ya yi murmushi haxe da xaga mata gira yace.

“Yaya bebena me ya faru?” Ta girgiza kanta “Ba komai”.

“I am very sorry na vata lokaci da yawa na je nakai Musbahumasaukinshi can prince Hotel don ya fasa tafiya baya jin daxi sosai” Gabanta ya faxi ras! Ta yi shiru bata ce komai ba amman fuskarta bata nuna wani yanayi ba yace.

“Allah na ji tausayinsa ciwon kai ne ya fiya damunsa migraine headath don shi likitane yana kiyayewa sosai” Nan ma shiru tayi yace “Oh ga take-away na kawo miki don ni na kammala cin nawa a can” Ta dube shi tayi dariya tace “Bash my man ni ma I am satisfy(na qoshi)” Ya riqo hannunta cikin jin daxi abinda tace yana mata wani mayen kallon qasa-qasa da idanunsa hakan ya saka taji wani irin kunya ta kamata ta wayance ta miqe cikin sauri zata gudu hakan ya bashi dariya yace “Fauziyya tawa uwar jin kunya, kin manta yanzu ni mijinki ne” Tayi shiru qasa-qasa ya miqe tsaye yace.

“Okey we should go for the most important thing prayer” Bata yi musu ba ta bishi a can xakin suka gabatar da sallah a nutse sun daxe suna addu’o’i sanan Fauziyya ta zame bai sani ba ta nufi xaki zuciyarta wasai ba sauran baqin ciki domin addu’o’in da suka yi sai taji kamar an cire mata wani qaton dutsen wutar bala’i da baqin ciki da yake neman halakar da ita a banza, ta tuve kayanta ta je ta yi wankanta da ta yi brush ta zo ta shafa mai tsananin qamshi da laushi ta gyara gashin kanta ta tufkeshi a can qarshe ta goggoga turaren moon coin da duk gavovinta ta je ta xau rigar baccinta baqa mai laushi amma ba shara-shara ba ce ta sanya ta je ta kashe bright light ta zo ta kwanta haxe da kunna dim light ta je sanyin xakin da qamshin xakin ya yi mata daxi sosai a ranta sai ta gyara kwanciya ta xauko pillow xaya ta rungume haxe da yin addu’o’inta ta tottofa sannan ta rufe idonta zuciyarta fari tas sanyi a.c yana ratsata a hankali ta ji yanayin lokacin ya dinga yi mata daxi da nishaxi ko meye dalili oho?

Sai da barci ya soma xibanta sai ta ji Mukhtar a jikinta hakan ya sata saki ajiyar zuciya a tsorace ta buxe idonta har tana dubanshi Mukhtar yana kallonta da idanunshi da suka canja salo da bata gane kanshi bat a tsorata sosai.

Da qyar take fiddo numfashi don fargaba Mukhtar ya yi dariya sannan ya rungumeta sosai yana shafa gashinta a haka cikin sanyi murya yace.

“Ki yi barcinki Fauziyya na ba abinda zan yi miki kin ji” Sai ta ji ya yi shiru ya rufe idonshi hakan ya sa ta saki ranta, bacci ya xauketa mai daxin gaske.

          


BABI NA BIYAR