p-9
_*🍇SILAR AURENA🍇*_
TAKU NA 1
Book 1📖
*NA*
Rabiatu Bashir Abdullahi
*_UMMU MAHER(MRS GREEN)_*🍃
_*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*_
*KOYON MAYAFI DA HULUNA DA RIBOM*
Kiyi shiga wannan grp ɗin domin dogaro da kai.👇👇👇👇👇👇👇👇
***
D6g00p1DxttAtHH1vmh54i
*ku sauke apps na palmpay domin ƙaruwa, kuyi joining ɗin link ɗinnan domin ku ƙaru👇👇👇👇* >>***
SHAFI NA 9
________________ ko da suka shigo garin Zaria wani irin sanyi da daɗi yaji, yayi shiru yana jin sanyi da daɗin garinsu wanda ya shafe shekaru har kusan biyu da rabi ba tare daya je ba.
Mubarak ya juyo ya kalli ogansa ya ce" yallaɓai mun fa shigo gari? kana ganin bazamu kira Hajiya mu faɗa mata ba saboda ta shirya zuwanka?".
Ya yi shiru ya ɗan kalli Mubarak sannan ya ce" ba sai na sanar da ita ba Mubarak, idan na faɗa mata zata iya barin gidan ma baki ɗaya saboda gudunta da nayi, amman kaga idan naje xai zo mata abazata".
Mk ya ɗaga kansa da gamsuwa sannan ya hau tuƙi cike da murna saboda yau ogansa zai haɗu da iyayensa, yana ɗaya daga cikin mutanen da suke cike da haushin abinda yake faruwa tsakanin AD da kuma mahaifansa.
suna zuwa dai dai ƙwanar gidansu AD yaji wasu hawayen farin ciki sun cika masa zuciya, ya ce" Mubarak ina cike da farin ciki yau ɗinnan, saboda ganin iyaye na da zanyi Familin me ƙamshi". Mk yayi ɗan murmushi cike da murna ya ce" ƙwarai kuwa uban ɗakina, nima ina tayaka murna sai dai ni murna biyu nake, na farko ni dai ban yada su Hajiya kamar yadda kayi dasu ba, duk bayan wata ina zuwa don ɗiban tabarakin Hajiya da Baba Me ƙamshi".
AD ya ɗan fito fa idanuwansa sannan ya ce" are sure? kana zuwa? shi ne ni baka janyoni munzo ba"?.
Mk ya ɗanyi murmushi sannan ya ce" to ai oga awannan lokacin kamar baka cikin hayyacinka, shiyasa na barka ka ɗan huta sannan sai in faɗa maka, amman ka gafarce ni idan na faɗi abinda ya ƙona ranka".
kasa ce wa uffan yayi, duk sai yaji babu daɗi abinda ya aikatawa iyayen na sa waɗanda suke matuƙar so da ƙaunarsa, basa son ko da ƙuda ya taɓa sa shi ne namiji ɗaya tilo agidansu wanda har yau ba'a samu wata ta haifi namiji ba sai shi kaɗai Shattima sunan da mahaifinsa ya raɗa masa kenan, tun daga ranar da yayi kukan farko acikin gidan duniya, saboda sunan Babansa yaci wato Me ƙamshi wanda ake ce masa Shattima, da yake su ƴan asalin ƴan meduguri ne Borno.
tun daga kan ƙwanar gidansu ya fara hango jama'ah, sosai gabansa yayi wani mummunan bugawa, yaji kansa na sara masa sai dai ya daure ne saboda shi namiji ne, kuma dukkanin namiji an sanshi da jarumta da miƙa kai balle shida yake soja mazan fama ga wuta ga harbi.
Har suka iso ƙofar gidan jama'a ne tamƙam, tuni yaji ya yar da jarumtar tun kafin ma Mubarak ya buɗe masa ya kama murfin zai buɗe.
da sauri Mubarak ya yi fakin ya fito da fitinannen sauri ya buɗe yana ƙamewa tamkar asalin soja, ko da yake shi sabo ai turken wawa ne tunda dai masu yiwa uban gidan nasa hidima duk sojoji ne.
sosai aka bi motar da kallo tun kafin ma ya fito, kamar sun san shi ne acikin motar yana fitowa kuwa kowa ya tsura masa ido, wasu har murza idanunsu suke saboda suna son su ƙara tabbatarwa ce war shi ɗinne ko kuwa ba shi bane?.
ya ƙarasa gabansa yana faɗuwa, mutane aka tattaso ana gaishesa da yake unguwar tasu ta jama'ace sosai, nan da nan aka baibayesa yana ɗaukar gaisuwa wasu kuwa ce wa suke shikkenan yau miyar gidansu zatayi zaƙi, don mutum ne shi me matuƙar bautatawa al'umma ko dama can idan yazo kuɗi yake basu bana wasa ba, don duk mutum ɗaya zai iya samun dubu hamsin na kansa, samari kuma dubu ashirin matan dake gidajen aurensu na layin suma dubu hamsin.
bai samu damar amsa musu wannan gaisuwar tasu ba, ji yake tamkar ƙafafuwansa ba zasu iya ɗaukarsa ba, kar dai ace wanine ya mutu agidan? ras gabansa ya faɗi tuno da yayarsa wacce ya bari ahalin jinya, dukkanin jikinta kuwa babu inda yake motsawa don tunda aka yi mata kishiyasa sai ya zamana kullum tana gidansu babu lafiya, zato zunubine ko da ya kasance gaskiya, amman yana jin mutane suna faɗar albarkatun bakinsu kan cewa wannan kishiyartata itace tayi mata asiri, duk dashi bai yarda alokacin nan ba sai da ciwon yayi nisa don ko dubata bata zo ba, shima mijin baya zuwa gashi suna da yara har baƙwai da mijin na ta.
Tunowa da Anti Badi'a sai yaji zuciyarsa ta tsinke, da dama ma kuka yake buƙatar yi sai dai kafin kaga yayi kuka to ba abune na wasa ba domin shi yanada zuciya me taurij gaske.
makara yaga an fito da ita daga cikin gidansu me masifar girma, don gidansu irin gidan yawan nanne kusan part ashirin ne agidan nasu kuma pary huɗu na mahaifinsa ne, sauran na ƙannensa da kuma yayyinsa sai ɓangaren tsohuwa me ran ƙarfe wato Jadda, wato kakarsu tsohuwa me tarin ni'ima da ƙwarjini yaranta 15 ne aduniya kuma dukkaninsu suna nan da ransu, kuma bazaka taɓa cewa ita ce ta haifesu ba saboda yadda Allah yayi mata jiki me kyau jikin Fulanin usul.
Ganin wannan makara bai san lokacin da ya kusa subewa awajen ba, har sai da Mubarak yayi sauri riƙe hannunsa don kada ya kai ƙasa, Mubarak ma tsoro da firgici ya kusa sanyasa daskarewa awajen, yaji wani tsoro ya ɗarsu aransa Allah dai yasa ba wanine ya rasu ba? sai kumq gashi yaga Makara wato ta tabbata rasuwa akayi kenan? indai kuwa haka ne wani babba ne ya rasu agidan, biyo bayan tarin al'ummar daya gani waɗanda idan ƙirgasu za'ayi sun kai dubu koma fin hakan.
~~~~~~~
Har nayi ƙwana uku Baba hari bata leƙo inda nake ba, amman don takaici Sulaiman ya sanyawa ƴata sunanta? duk da nasan sunan mahaifiyarsa ne kuma kowani ɗa daya taso da soyayyar iyayensa musamman ma mahaifiya yana da burin sanya sunanta, to sai akayi katari ita wannan mahaifiyar bata damu da damuwar ɗanta ba, balle ma har ta damu da damuwar wani? Baba hari irin mutanen nanne da babu abinda suke so suka kuma damu dashi irin kuɗi, tana da masifar son kuɗi wanda ko aƙwatance ban taɓa ji ko labarin me irin ƙwatan ƙwacin irin nata kalar son kuɗin ba.
ni har mamaki ma take bani, ba kunya ba tsoron Allah ta buɗe bakinta tace wai ita bata san Sulaiman saboda ba shida ƙashin arziƙi ya auro me farar ƙafa. abin ya girgizani sosai to ta cewa ɗanta wannan balle kuma kai.
Ina cikin wannan tunanin naji muryar Sulaiman, tamkar dai yana kaɗamin muguwar algaita ya ce" kiyi haƙuri Maryam, nasan ban shawarce ki wajen sanyawa yaran nan suna ba, kiyi haƙuri idan na ɓata miki nan gaba zan baki dama ki sanyawa yaranki duk irin sunan da kike so".
na kasa ce masa komi, sai dai haryanzu ina jin zafin sunan daya laƙabawa ƴata, ko da yake da ɗa da mahaifi sai Allah na manta komi na ce" ba komai mijina, abinda kayi ɗin ai shi ne dai dai duk namiji wanda ya isa da gidansa ai ba sai ya nemi shawar matarsa ba, don zaiyi wani abu wannan ai shi ne mazantakar ko"?.
murmushi yayi, azuciyarsa kuwa cewa yake Allah sarki maryam, ita kullum bana laifi sai dai ita tayi lallai Allah ya bani mace tagari.
Halima ta ce" gaskiya nima yaya banso ka sanya sunan Baba ba, ka duba fa ka gani yau ƙwana uku fa bata zo ba sannan kuma sai asanya sunanta? jiya fa har Saddiƙa na zugata wai ko ta dawo kada tayi mata barka".
na lura Halima irin mutananne masu faɗar gaskiya, kuma marasa rufi idan da nice ko mahaifiyata tayi ba dai dai ba bazan iya koda ɗaga kaina wajen kallonta ba, saboda bansan abinda zataji ba idan na faɗa mata gaskiyar.
Sau tari muna samun matsalane da mahaifanmu idan har muka zamo masu faɗa musu gaskiya, sai kiga koda su suka haifeka sun sanya maka karan tsana, ta yadda koda magana suke sai suce ga munafukar nan, kalmar da Innata take yawaita faɗa kenan idan ta ganni ni kuma ban zamo me wannan halin ba, amman ban san me yasa tunda na kawo Sulaiman amatsayin miji ta tsaneni ba, tamkar dai ba yarda ta haifa acikin cikinta ba wai don duk na kawo talaka amatsayin mijina, abinsa taso shi ne in kawo mata me kuɗi kamar yadda yayyina suke kawowa.
Sulaiman ya kasa magana, sai dai na lura maganar tayi masa zafi amman bai ce komi ba na lura Sulaiman irin mutanan nanne masu masifar ƙulafucin uwa, ko unguwa Baba taje sai kiga Sulaiman cikin damuwa sosai, ko fara'a baya yi indai ba Baba ce ta dawo ba.
muna haka Ummu jafar ta shigo, maƙociyarmu ita da mijinta Abu jafar wanda ya biya mini kuɗin asibiti har dubu hamsin, sosai nake ganin girman mutanen, don suna sona sosai mijin ya ɗaukeni ƙanwarsa, matar ma hakance daga ɓangarenta domin ni nakewa Jafar lesson na karatun turanci, don Allah ya horemin karatu na arabi dana boko ina da ilimin boko sosai duk da iya makarantar secondary na tsaya amman ilimina har malamai nakewa gyara idan suka faɗi wani abun, jin turanci kuwa tamkar ni na ɗinkewa bature cibiya, saboda tunda na taso ina son turanci sosai shiyasa na dinga siyan littafin koyon turanci har nazo nima na iya sosai na zama ƙwararriya.
Jafar yayo kaina da sauri, Mamansa tayi saurin riƙesa tana dariya ta ce" to Jafar baka ga babies ahannunta ba? da girmanka ka faɗa kansu".?
Jafar ɗan shekara tara ya kyalkyale da dariya yana ƙarasowa kusa dani ya dinga taɓa yaran yana dariya, ya ce" yauwa Ammi zaki kai mana yaran gida ko? kada ki bawa Anti mimi ki tafi dasu gidanmu tunda nima kinƙi kiyimin ƙannai, kisha wake kema ki haifosu tunda kince sai ansha wake ne ake haihuwa"?.
sosai aka sanya dariya, Halima ta ce" ai kuwa bazamu baku ba wallahi, ka matsawa Ammin ka tasha wake itama".
dariya akayi ta masa Sulaiman da Abu jafar suka fita suna hira, ni kuma muka cigaba da hirarmu da Ummu jafar.
Halima tayi mana sallama ta tafi gida.
Ummh jafar ta matso kusa dani ta ce" uhm ni kuwa wani abin al'ajabi na gani ɗazu?".
gabana ne ya faɗi na ce" me kuma kika gani"?...............
*MRS GREEN CE🫵*
Atayani sharing ƴan uwa.
*AMMEY LAYLERH DETA SERVICES*
*Azo asai DATA kan farashi mai sauqi, cikin rahusa👌🏻🤗*
*MTN*
500MB-180
1GB -280
2GB - 550
3GB - 750
5GB - 1250
10GB -2500
*AIRTEL*
300MB - 170
500MB - 200
1GB - 300
2GB - 550
5GB - 1350
10GB - 2600
*GLO*
200MB - 120
500MB - 180
1GB - 300
2GB - 550
3GB - 850
5GB - 1350
10GB - 2600
*9MOBILE*
500 - 180
1GB -280
2GB - 550
5GB - 1300
10GB - 2500
Account number: 3206656358
Account name: Maryam Nasiru first Bank
*MORE Information ****