BA茦IN HAURE..........

Chapter 23

by @maidambu41

*BA茦IN HAURE....馃惥馃惥*


{Greed for Money is the roots of all evils馃珋}

Arewabooks:maidambu41

Wattpad:Mai_Dambu

Mallakar:Mai_Dambu

*023*

Ko don na taso a tsakar gidanmu ne, ban tashi gaban Uwa ba, ban san yadda Uwa take handling yara kmr Babyna ba, akwai wani abu da na fahimta da zarar gari ya waye zata wuni barci, sai dare garinta zai waye duk da haka bai hana da zarar na saka abinci a gabana zata bude idanunta ta fara rigima ba, sannan baki daya a girman dakin da muke babu me iya tunanin ya taimaka min, Ummi da Addah kowa harkar gabanshi yake, sannan basu da lokacin da zasu tsaya lallai sai sun taya ni kula da yarinyar.

Bakidaya sai na kasa sabawa, da zarar dare yayi zan goyata ina yawo da ita har daren yayi nisa tayi barci. Na kwanta da ita a bayana, sannan zamu yi barci idan kuma sanyi ya dame ta hana kowa barci take, haka zasu yi ta tsaki suna mita. Gari na wayewa kowa zai kama gabanshi. Suna tafiya suna mita, ban tab'a fushi akan hakan ba.


Yazeed Hamir.

Asalinshi dan kasar aljeria ne, mahaifinshi babban attajiri ne sannan Basarake ne a babba a kasar , kuma Balaraben aljeria. Suna da kudi sosai sai dai shi Yazid ya lalata rayuwarshi ta hanyar shaye-shaye. Mutum ne da bai da yawan magana ko hayaniya, sannan akan abinda ya shafi sayar da kwayoyi baya da wasa. Domin ya bar 茩asarshi ta haihuwa ne yazo wannan wurin ya kafa inda zai na fitar da shu'uman kayan maye yana rabawa tsakanin kasashen Afrika. Shaidani ne na gayawa Sarkin gari, yana da wani irin sirrin da duk inda ya shiga sai ya fitar da kaya, zai yi wuya ya shiga wuri bai fitar da kayanshi ba, sai dai yana da rauni sosai matarsa da Yaran shi, biyu dukkansu mata ne yana matukar kaunarsu. Yazid ya bar gidansu ne tun yana shekaru ashirin da biyar a duniya, domin yana da matukar kiyayya da sarauta, domin a sanadin mulkin da za'abawa Babanshi Mahaifiyarshi ta rasa rayuwarta kuma dama ana ta fa蓷an cewa ya sadaukar da ita ne ga mulkin shi, shi yasa ranar da ya fara jin labarin ya sami mahaifinshi da maganar, 茩aryatawa yayi shi kuma ya ce matu茩ar ya tabbatar da haka sai ya bar mishi kasar da kome yaje yayi rayuwarshi,. Dake akwai mutanen da basu son Babanshi, sai suka yi amfani da haka suka tabbatar da cewa sadaukar da Amiratul Aminat aka yi, duk yadda Uban yaso mishi bayani amma ya茩i fahimta. Don haka ya saka kafa ya bar kasar da dukiyarshi a lokacin ya gama karatunshi a bangaren had'a magunguna.


Wannan abin yayi matukar yiwa mahaifinshi ciwo, har kwanan gobe yana zuba idon ganin shi, Yazid yana matukar tausayin mata da Yara, akan mahaifiyarshi ya kara jin tausayin Yaya mata, kuma wani abin da yake kara saka shi tausayinta, ita sikila ce. Sai akayi dace shi bai da shi, haka yasa yake son Reshmah kamar zai haukace da ta fara haihuwa ma bai tab'a ce mata ga zab'in shi ba, sunan da takeso take sakawa. Tozali da yayi da Zahrah yaji duniya bai tab'a tausayi da son wata Y'a mace ba kamar ta, sannan baki daya sansanin da suka zauna mutanen Yazid ne, hatta Uwar mugu dalilin da yasa Nawwas yazo nimanshi wurinta kenan, sai gashi kuma Nawwas din jin kamar Yazid din yana zuwa yasa shi guduwa da yan matan.

Matarshi itama balarabiya ce, Reshmah mace ce mai tsananin kishi da saurin fushi, sannan shima Yazid yana matukar kiyayye abinda zai saka kishinta ya fito har ayi tunanin wani abu. A wannan dajin idan kana son ka fita sai ka je an saka maka wasu kwayoyin da zaka masa safara da shi idan ka sha zaka je a cire maka, sannan kayi tafiyarka daga nan ka samu yanci, ba kuma zai barka ba domin abin shi kamar da siddabaru domin ko ka bar dajin ka manta kenan. Ba zaka kara tunawa ba, da haka Yazid yafi karfin abokan gabanshi, domin yana fito da kayanshi ta kowace fuskar ya sayar a waje.

Lokacin da muka zo garin ina cikin wa蓷anda aka rabawa aikin shara da goge gogen gidanshi, idan har Matarshi ta rigashi tashi hatta bango sai na goge, sannan babu ruwanta da ina da baby ko bani da Babyn, matar nan yar bala'i ce. Kafin Yazid ya fito na gama kome na bar gidan. Sai yamma kuma na koma.

Ban san me yasa ba ko yana sane da yadda matarshi take saka ni a gaba da fitinar aiki, ranar ina zaune a kofar gidan da muke sai gashi ya zo ina jijjiga Baby. "Babyn Zahran bata yi barci ba ne?" Juyawa nayi zan yi magana domin ban zata shi ba ne. Sunkuyar da kai nayi na ce mishi. "Yallabai kai ne?" Na fada ina jijjiga ta, ajiye wata jakar takarda yayi ya ce min. "Kawo min ita." A hankali na mika mishi ita har hannunmu yana gogan juna. Da sauri na janye nawa hannun, shi kuma ya cigaba da kallona. Yana me kallon inda kwanon abincina yake, na bude zan ci ta fara rigima. "Ki ajiye abincin anjima sai ki ci ga wannan ki ci." Ya nuna min jakar da idanunshi. Sai gashi na rikice baki daya, domin ina jin yadda yake bina da idanu, ban saba ba sai nake ganin kamar ba zan iya tsayawa da kafata ba. Jingina nayi na dauki jakar na bude, madara ce a kwalba sai gassashen nama, hadiye yawu nayi duk da ba laifi tunda muka zo ba laifi abincin mu yana da kyau, sannan a wadace muke samu. A hanya muka fuskanci matsala amma tunda muka zo abincinmu babu laifi. A hankali na fara bude takardar da ya nad'e namar, kamshinsa kawai yasa na hadiye yawu yafi sau goma. Na d'ago kai naga yana hidimar baby da sauri na fara ci, ban sani ba ko yana kallona domin ganin nama yasa ni jin duk wata yunwar da nake ji na tsawon watanni bakwai ta dawo min sabo fil, "ki ci a hankali." D'ago kai nayi naga Babyn yake wasa da ita, goge bakina nayi na cigaba da cin namar, har na koshi. "Zan tafi!" "Allah ya saka da alkhairi." Na fa蓷a ina sunkuyar da kai, koda su Addah suka dawo a gajiye, idanunta ya sauka akan jakar takardan, dauka tayi zata bu蓷e Ummi ta fauce. "Dalla bani." Dama kuma na rage musu ne, ganin kowannensu ya samu ba zai bawa dan uwanshi ba. Yasa na amsa. "Idan kuka yi hakuri na ku ne, idan kun yi fa蓷a ma naku ne." Na fada ina ciro musu na mika musu, faucewa suka yi suna jan tsaki.

"Wani dan iskan kika samu ya kawo miki?" Inji Addah, ban bata amsa ba na gyara mana kwanciyarmu da Baby. Washi gari da na shiga gidan aiki naga Matarshi sai hawa da sauka take, har na gama aiki zan fita ya fito dauke da Yarshi. Murmushi yayi min na sunkuyar da kaina, na fita da sauri.


A harabar gidan naga alamar zasu fita ne, haka yasa na bar gidan domin yau bata min kakale-kakale ba, asalima kamar sauri suke. Ina dawowa nayiwa baby wanka. Sannan muka kwanta bayan mun karya.


12:30pm,

Ji nayi kamar ana tsaye a kaina a hankali na bude idona, ya sauka akanshi yana bakin gadon Ummi yana latsa wayarshi, da dan sauri na tashi zaune ina kallonshi. "Yau Baby bata yi rikici ba kenan?" Ya ajiye min irin jakar jiya.

"Wai ya sunan Babyn?" Tiririn da nake ji na kamshi yasa ni rikicewa domin yunwa nake ji, kuma sai karfe biyu za a kawo mana abinci. "Ban mata suna ba, baby muke kiranta."

"Ya sunan Mamanta?" D'ago kai nayi ina kallon shi, kawai sai ya cika min idanu. Sunkuyar da kai nayi ina fa蓷in. " Zulaiha!" Na zabi na fadi haka ne domin ya min kwarjini. "Ok bani ita!" A hankali na mika mishi ita, kamar mai tunani sai kuma ya ce min. "Hmmm! Ba zan saka mata sunan Uwarta ba, domin zata iya gadon halinta."

"Ka saka mata sunan Addah." "Ita criminal ce zata tashi da shaidancinta."

"Tow ka saka mata sunan Mamana!" "Ya sunan yake?" "Aminatu!" Murmushi yayi ya ce "sunan Kakata ce da tasoni sama da kanta." Ya fada yana shafa kan Babyn yana me mata huduba. "Maman Aminatu!" Murmushi nayi, tare da Mikewa zan karbeta ya ce min. "Ci abinci" ba musu na zauna na ci grill fish da chips a gefenshi. Sai da na gama ci ya mike, ya ajiye min yarinyar.

Ya tafi, lokacin sallah yayi na mike na wuce ban daki nayi alola sannan.na dawo nayi sallah, sannan muka kara kwanciyarmu, domin kifin akwai maiko. A hankali wata irin shakuwa da bansan daga inda ya samo asali ba, ta shiga tskanina da Yallabai Yazid, da farko sau daya yake zuwa, daga baya ya koma yana zuwa sau biyu. Da rana da kuma Yamma, a hankali idan yazo shirya Baby Aminatu, Addah kamar zata rufe ni da duka da taji sunan har da Min Allah ya isa, bata yafe ba don na saka sunan Mamana.


Da yamma idan ya zo 蓷aukarmu yake muna zaga cikin garin, gonarshi da lambun shi har da gidan dabbobin shi. Yau ma haka ya saka ni a gaba, bayan ya kawo min wata doguwar riga da mayafinta. Muka shiga wani yanki ta Cikin gonar, mun yi dogon tafiya kafin ya kawo mu wani wuri a 茩ar茩ashin 茩asa, ya ce min. "Kin ga wannan wuraren? Akwai kofar da xasu fitar da ke har wani kauye, daga nan zaki wuce bodar Nijeriya da nijar ne da yake dole kaina, mu nan muna yankin River Benin ne.

"Ban gane ba?" Zama yayi yana kara murmushi ya bu蓷e kofar ya shiga shi da Babyn sannan ya mika min hannu na rike shi na sauko. "Kina da saurayi?" "Na'am?" Na ce mishi, ina kallon shi. Murmushi yayi min sannan muka cigaba da tafiya.


"Nace kina da saurayi?" Ya juyo yana kallona." Zare idanuwa na fara, da wasa da ya bakin mayafina. A hankali yake takowa na juya bayana naga ko wani abu yasa yake biyo ni, sai naga haka kawai koda na juya ya matso kusa dani sosai. "Baki da saurayin ne?" Hadiye yawu nayi na gyada kai na, a hankali ya sunkuyo da kanshi a tunanina sumbatar bakina zai yi, da sauri na kawar da kaina. A hankali ya kai hannunshi gefen wuyata ta wurin mayafina ya kad'e min gizo-gizon da yake kaina.

"Ki kula." Ya fada yana kallon kwaron. Hadiye yawun bakina nayi ina kara jin kamar zan saki fitsari.

---

Cikin larabcin da bai gama rike bakinta ba, Addah ta kara gyara zamanta ta ce mata. "Idan nayi miki karya, ki saka a kashe ni a binne gawata, amma yarinyar da Yallabai yake fita da ita yata ce, kuma zaki iya zuwa gidan mu, ki ga irin kyawawan kyaututtukar da yake kawo mata." Mikewa tayi tana fa蓷in. "Muje!" Haka Addah ta mike jikinta yana rawa ta ce mata. "Tow!" Suka tawo har gidan, wato ita Yazid zai ci amanarta. Ita zai tsallaka yana bin karuwa da ta gama yawon karuwancin kafin ta fado hannunshi, bata kara sarewa namiji ba dan goyo da zani ba ne, sai da ta ga katon akwatin kayan da ya kawowa uwar da yar, ciwon bakinta tayi sannan ta juya ta fita cikin nutsuwa Addah kuwa murna kamar zata daka tsalle.

Haka Reshmah ta koma gida, ta zauna tana tunanin me zai faru, me zata aikata da zai bawa Yazid tsoro ita ba kalar Matar da zai ci amana bane . Bai isa ya ci amanarta ba.

---Sai dare muka dawo tun a hanya aka tare shi, ana gaya mishi abin da ya faru cikin wani irin yare, murmushi yayi ya ce musu. "Suwa laula!" (Shi kenan naji) kallonshi nayi domin ban tab'a zatan yana jin wani harshe bayan Hausa da larabci ba.

"Wani yare ne haka?" Murmushi yayi ya ce min. "Harshen darsa, yana da saukin amfani.". "zan koya!" "Zaki iya kuwa?" "Hmm!" Haka ya rako ni gidan sai da na shiga ya ce min. " Za a kawo miki abinci." "Tow na gode!" Daura yatsar hannunshi yayi a baki ya ce min. "Shiiii" hadiye yawu nayi. "Kada ki b'ata min alakata da godiya." "Shi kenan!" Haka ya bani Babyn muka shiga cikin gidan, yana fita yayi waya aka kawo min abinci, muna kwance aka buga kofar kallona Addah tayi na mike na bude kofar na amso abincin na fara ci, tashi tayi zata saka hannu Ummi da take gefen gadona ta doke hannun da wani sanda, sai da kashin hannun yayi 茩ara. "Kika sake wani abu ya shiga bakinki sai na shakeki har lahira munafukar banza." Daga haka bata ci ba na kalli ummi ta dauke kai. "Me yasa kika hanata!" "Ba zata ci ba wallahi." Shiru nayi ina kallon Addah da ta koma ta kwanta. Ban kuma musu magana ba, sai da zan fita Addah ta ce min. "Bani Aminatu na taya ki goyanta." "Ba zata baki ba, duk abinda zai faru sai dai ya faru!" Inji Ummi. Fita muka yi, nima na nufi gidan Yallabai. A falon kasa na same ta a hankali naji jikina ya bani akwai matsala. Haka na wuce na fara aiki har na gama. Tana zaune sai da na gama zan fita ta ce min. "Ke jira ni!" Daidai shima yana saukowa daga sama, kenan ta shiga kitchen, kamar ya san nufinta, tana fitowa kawai ta watsa min soyayyen mangyad'a da ta dauko a fry pan.

Rumfa yayi min ta zuba mishi a bayanshi, bata san lokacin da ta saki fry pan din ba, "Yazid!" Ta kwalla mishi kira, bude idanu yayi a kaina."Yallabai!" Na kira sunanshi. "Jeki gida lafiya ta lau." "Yallabai bayanka fa?" "Ba kome, jeki"


Ya fada min da wata irin murya, da sauri na fita tana rufe da fuskarta tsoro ya kamata, hadiye yawu tayi tana kallonshi. "Me kike nufi?" Jikinta ne ya fara rawa, "don Allah kayi hakuri." Jan iskar bakinshi yayi ya yaga rigar tare da zama a bakin kujerar falon, da gudu ta fita ta kira Aseem ta gaya mishi, shi ya tafi har wurin likitan ya tawo dashi, suna shiga suka same shi a falon. "Garin yaya?" "Nice na zuba mishi ba da gangan ba." Bai ce uffan ba har likitan da Aseem suka yi ta cire mishi rigar da ya hadu da fatar bayanshi, ya zuba mata idanu. Cikin wani irin Imagining da Zahrah zata zubawa man gyadar nan a fuska. Sai lokacin ya iya bude baki ya ce Mata. "Nufinki Zeehra zaki zubawa?" Zubewa tayi tare da rufe fuskarta ta fashe da kuka. "Kayi hakuri sharrin iblis ne." Ta fada tana shasshekar kuka, haka ya cigaba da kallonta tana kuka. Yana wondering yadda zuciyarta ta mutu da tunanin ta nakasa mace yar uwarta, murmushi ya saki a hankali yana kallonta. "Sultan kayi hakuri don Allah!" Ta fada tana waiwayen bayanta. "Aseem!" Da rarrafe ta kama kafarshi. "Don Allah ka rufa min asiri Sultan kishinka ne ya saka na aikata haka, Sultan ba zan kara ba." " A bata abinci dare da rana, ta zauna a wurin sai na warke." Fashewa tayi da kuka kamar ranta zai fita,

"Sultan afuwa!" "Aseem!!" Zubewa yayi akan gwiwarshi. "Uwar Yaranka ce, kuma mace mai daraja a gare ka, kasan haka kuma kai da kanka ka gaya mana babu mace mai darajasama da Reshmah."

"Zeehrah tana da daraja, darajarta me girma ne!" Ya fada yana kauda kai. "Matar da nake aure idan bata ji magana ta ba nawa zata ji? Idan wani abu ne ya had'ata da yarinyar waye zata tinkara? Dole sai ni, wato shine aka gaya mata xata kona musu yar mutane. Idan ta lalata mata fuska fa? Fisabilillahi ace mangyad'a zata zuba a fuskar Zeehrah...

#Mai_Dambu