p-11
_*🍇SILAR AURENA🍇*_
TAKU NA 1
Book 1📖
*NA*
Rabiatu Bashir Abdullahi
*_UMMU MAHER(MRS GREEN)_*🍃
_*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*_
*KOYON MAYAFI DA HULUNA DA RIBOM*
Kiyi shiga wannan grp ɗin domin dogaro da kai.👇👇👇👇👇👇👇👇
***
/D6g00p1DxttAtHH1vmh54i
*_KARANTA SILAR AURENA TA AREWABOOKS HANKALI ƘWANCE👇🏽_*
https://arewabooks.com/
book?id=65bd172f88cb015808e5fc25
*_KARANTA SILAR AURENA TA WATTPAD HANKALI ƘWANCE_👇🏽*
***
1420716493?utm_source=android&utm_
medium=link&utm_content=share_
published&wp_page=create_on_
publish&wp_uname=Rabiatu333
SHAFI NA 11
________________Andi tayi saurin kallonta, kasan cewarta mace me haƙuri sai ta gyaɗa kanta kawai ba tare da ta ce mata komi ba.
Alti ƙanwarta tayi ƙwafa kasan cewarta macece me matuƙar zafi ta ce" yo ai gwara mu da daman kurciya akayi masa su o'o fa? yawon banza ne fa aka tafi babu alamun dawowa kuma to har ayi mana wani batu".
Tuni ɗakin ya fara rikicewa, masu goyon bayan Alti na yi masu goyon bayan uwar gida na yi, ita kuwa Andi dakawa ƙanwarta tsawa tayi cike da jin haushi ta ce" haba Alti menene haka kuma? dukkaninmu fa muna da hankali da tunani, bai kamata fa mu zama jahilai ba zaman makoki mukeyi ba zaman faɗa ko gaba ba".
haba wannan maganar da ta faɗa sai ta ƙara rura wutar masifa, har sai dai Andi taja ƙanwarta suka wuce ɓangarensu.
Safna tayi ƙwafa ta wuce, gamida murguɗa bakinta ta ce" uhm ai ni dai babu abinda zance sai dai mu yiwa Allah godiya, kuma sannan ƴan baƙin ciki ai sai dai su mutu".
wannan maganar da ta faɗa sai Hajiya Nanne ta fara kuka wato uwar gida, tana kiran wayar Alhaji wai ƴar tatsiyar yarinyar nan Safnah ta samu bakin yi mata rashin kunya.
Alhaji kuwa bai ma san tana kiransa ba, yana can shima cike da alhinin abinda yake ganewa idonsa na dawowar ɗansa ɗaya tilo namiji, abin tinƙahonsa kuma abin sonsa tabbas Allah ne ya amshi roƙon da suka daɗe sunayi.
Hajiya Nanne ta janyo mama Amarya kusa da ita, ta ce" haba Shukra wannan kuma wani irin rashin mutunci ne? ta yaya zaki munafurce ni? ban kin faɗamin boka ya ce ba zai taɓa waiwayar gida ba? sai kuma gashi ya dawo yanzu? to me zan kira da hakan? cin amana ko me"?.
wata dariyar ciki tayi, tana ɓoye fuskarta don ma suna daga can ƙarshen babban falon ne ba lallai a jita ba, ta ce" ni fa duk abinda zanyi bana zurfafa mugunta ni na rasa me yasa kika tsani yaron nan haka, ni dai wallahi na yarda makamai na ahalin yanzu saboda wa'azin dana ke ji ba abanza nake jinsa ba, ance duk mutumin da yake zuwa wajen boka ba za'a amshi sallarsa har ta ƙwana arba'in, to ina dalili? da zan ɓata waɗannan sallolin nawa"?.
cike da masifa ta ce" oh to ina kuɗina dana baki ki kaiwa bokan"?.
da sauri ta ce" indai kuɗinki ne yana ɗaki, ni daman ban ma je wajen bokan ba saboda haka zan baki kuɗinki an jima, saboda haka ni na koma ɓangarena Allah ya bamu alheri, dama ance zaman makoki duk munafurci ne , ni da za'a gane ma da an daina sa da masu asiri da kuma masu munafurci duk ba a rasasu agidan zaman makoki".
Sosai maganar ta tunzura Hajiya Nanne ta hau faɗa, ai kuwa sai aka hau mata dariya ana nuna ta, matan wanda ya rasu su uku ɗaya ce kawai ta bata ƙwarin gwiwa akan cewa ta cigaba dayi ai ita aka ɓatawa.
bayan an gama karɓar gaisuwa ya shigo gidansu, duk jikinsa asanyaye ya rasa ma da wani irin ido zai dubi Andi da kuma Jadda kakarsa?.
ɓangaren Jadda ya fara shiga, shi da Saminu ƙaninsa ɗan gidan ƙanin babansa wanda ya rasu.
Tun daga nesa ta ƙura masa ido, daya zo gab da ita kuma sai ta juya tamkar ma bata gansa ba saboda tana son nuna masa kuskurensa ne.
babban falo ne, falon an tsarasa kamar ɗakin amaryar da aka kawo yau falon yasha kayan alatu masu matuƙar kyau, fentin kuma irin wanda akeyi agidan sarakai ne irinsa ne a falonta sai haske yake yana walƙiya, ga kujerunta na alfarma masu kyau da tsada kujerun kusan guda goma a falon.
sunkuyar da kansa yayi, domin yasan yayi mata gagarumin laifi, ko iyayensa ba zasu nunawa Jadda sonsa sa ba tana matuƙar ji dashi agidan, sanda yana yaro kuwa idan taji kukansa ko iyayensa ne suka dake sa ta dinga haƙilo kenan tana faɗa, lokacin da yayi aure har kuka tayi saboda zata rabu dashi sai dai yazo ya ganta ya koma, duk da dama can yana tafiya daga ƙasa zuwa ƙasa gari zuwa gari amman duk da haka ba kamar aure ba, alokacin nan har tsokanar ta akeyi ana cewa kishi take hatta lefan daya haɗa na ƴan gata ne domin ya haɗa set ɗaya dozin na aƙwati, Jadda kuma ta haɗa masa guda ɗaya wato dozin ai kuwa lokacin nan sai da aka dinga ƴan ƙananan maganganu agidan akan cewar wai ita Jadda tafi son Shattima shiyasa ma take banbantasa da sauran yara.
ganin ya kasa magana, ita kuma ta juya gefe tana lazimo tamkar ma bata san yana wajen ba yasa Saminu ya ce" haba Jadda, ya kina ganinmu mun shigo kuma sai ki juua mana fuska? Shattima ne fa naki wanda kike banbantamu saboda shi na gaban goshinki ne".
ta wani harare sa, gamida kawo masa duka da casbaharta sannan ta nuna sa da yatsanta, ta ce" to naji munafuki an gungumi, Samuha kake ko Saminu? daman matam gida da yara na kawomin tsaiguminka, ashe ƙasurmin munafuki ne kai? sai yau na gane hakan kuma da kake ce wa ban ganku ba ai na ganku, tsufan nawa bai kai duk haka ba dama dai Faltama ce uwarka to da nace ɗimuwa ce ta kama ta, tunda na ga ta mayar da kanta mahaukaciya ƙarfi da yaji saboda mijinta ya mutu yo duk son da za tayi masa Allah na tuba ai baya nane, tunda ni ce nayi naƙudarsa na shayar dashi har ya rayu ta gansa ta aura da haƙoransa talatin da biyu, to kuwa kaga ai ni hauka ya kama inyi amman ba ita ba, saboda haka ka kai mata saƙon dana faɗa maka eh nayi ne domin taji, tunda kai sarkin munafukai ne".
da sauri ya sunkuyar da kansa, yana me nadamar yin maganar da yayi ya manta wacece Jadda sam bata yarda da maganar banza, balle har tayi wani wasan jika da kaka, da mutum ɗaya take wannan shi ne ɗan gidanta na gaban goshi wato Shattima.
magana ya farayi ahankali cike da kalaman daya san zai sanyaya zuciyarta, ya ce" Jadda nasan ni me laifi ne awajenku amman ina neman alfarma ayafemin don Allah, domin ni kai ma ban ma san me ya sanyani ƙim zuwa inda kuka ba, ban san me yasa ba naji na tsani zuwa inda kuke kuma babu abinda kuka yimin amman wallahi ayanzu nayi nadamae yin hakan, ina me neman afuwarku don Allah".
hawayen da bai samu yayi ɗazu ba su yayi yanzu, sai dai hannu ya sana da farin handkacif ɗinsa me kyau da tsada.
sosai Jadda taji ta sakko, sai kuma ta kula da wani irin lamari da yake shirin faruwa wato ita macece wadda Allah ya horewa gane abu da sauri, da yake daman fushin ba ko ina yaje ba sai ta hau jansa ajiki kamar dai ba itace me fushi ɗazu ba.
kuma da wannan jansa ajikin za tayi amfani domin ta bugi cikinsa don ko ba'a faɗa maka ba kasan aƙwai abinda ya ke samunsa, domin hatta jikinsa ya ragu sosai ya koma abin tausayi.
suna hira basu farga ba kawai sai suka nemi Saminu suka rasa, Shattima ya ce" banga Saminu ba? ashe ya fita tun ɗazu".
Jadda ta ce" uhm bar ɗan nema, ina sane nayi masa haka yaro ne ɗan ƙarami amman sai munafircin jaraba yayo halin Baburawa ƴan uwar babarsa".
sai daya ɗan dara sannan ya ce" haba Jadda ki daina zagar musu iyaye fa, babu daɗi wallahi".
Sai kuwa ta ce" to ai kaima ina zagin taka uwar idan ta haɗo mu, abinda yake haɗani da ita haƙurinta yayi yawa matan gidan nan sun raina ta sosai wallahi, amman duk abinda zasu yi mata bata iya magana ana cewa Buzaye suna da tashin hankali amman ni banga alamar haka ba, domin Andi ba haka take ba wallahi".
ɗan murmusawa yayi sannan ya ce" Andi fa da kike ganinta ko ni da kaina ina jin jinawa lamuranta, domin ko nj bazanyi irin haƙurin da take dashi ba".
haka dai sukayi ta hirarsu, har Mubarak ya shigo suka gaisa sannan suka fita tare gab da zasu fita ne yayi wani gamo.
da sauri ya dawo wajen Jadda wacce ke shirin tashi ta koma can wajen masu zaman makoki, domin wannan babban falon nata ba kowa ne yake zama ciki ba domin macece me matuƙar tsafta.
ɗan sosa kansa ya farayi yana ɗan sunne kai, ya ce" Jadda wannan yarinyar ƴar waye kuma"?.
ya nuna Adawiyya wacce ke gaidasu babu kunya.
ta ƙunshe dariyarta tana ce wa" to ikon Allah, yau kuma ƙanwar taka ka manta"?.
Mubarak ya ƙunshe dariyarsa, domin yasan ogansa ya gama harbuwa ne.
~~~~~
kukan dana ke shi yasa Sulaiman jin tausayina, domin yasan ba zan taɓa faɗawa ƴan uwana duk abinda yake faruwa ba sai dai idan sune suka fuskanci aƙwai matsala.
Sulaiman ya ce" ni dai kuyi haƙuri, kubar Maryam tayi wanka aɗakinta wallahi sai inji kamar za'a rabani da ita ne".
Anti fainusa ta ce" Sulaiman ba rabaku zamuyi ba, tunda kuna son junanku amman gaskiyar magana indai har haka ta cigaba da faruwa komi zai iya faruwa domin mu dai ba zamu zuba ido ana cutar mana da ƴar uwa ba."
nayi shiru, yaran suna kuka aka miƙomin su na fara shayar dasu sai dai babu ruwan mama sosai, nan da nan suka siyomin su madara da kayan shayi birjik, jin sunce ba zasu tafi dani ba sai naji zuciyata tayi min sanyi.
sai dai na lura duk jikinsu yayi sanyi matuƙa...............
Anti Safiya ta ce" daman idan munzo zamu kira miki Innarmu sai tayi miki barka, amman tace zata zo itama nan da ƙwana biyu".
sai naji zuciyata tayi min daɗi.
kiran farko ta ɗaga, Yaya Safiya ta ce" gamu ga Maryamanki Innarmu sai kiyi mata barka kafin kixo".
ai kuwa sai ta ce"yanzu ke safiya tsabar munafurci da gulma ban hanaku zuwa inda take ba? amman shi ne kuka munafurceni kuka tafi ba tare da sanina ba"?.....
wayar tana amsa kuwwa, saboda haka kowa na ɗakin yana jin abinda take faɗa........
*MRS GREEN CE🫵*
atayani share my fans👏🏻😘💃🏼
MAMAN AMEER DILKA SOAP*
*muna siyar da kayan gyaran jiki, jikinki ya yi silɓi da kuma shining ki zama tauraruwa acikin mata*.
muna siyar da dilka
soap
mulato soap
white scrub
da dai sauran kayan gyaran jiki har ma dana ƙamshi kamar👉🏽
Gab gab
Layal
Hawi
Cus cus
Coucounot sandal,
Marshoosh,
Frami
Kajiji,
Sandal.flask
Qalbul oud,
Noor hayaty,
Kindikaye,
Sultana,
Kajiji,
Sandal asly
Malika
Night queen
Misk humra,
White humra
Dufur khumura,
Khumura mukabassiya.
ga lambar wayata, don siyan ɗaya ko sari MAMAN AMIR GIDAN GYARA ƘAMSHI.
***