HAKEEM

Chapter 2

by @alkhair

Tun tana yarinyar ta take son hutawa a lokacin da ko wani yaro a wannan age din illimi iyayen shi ke iya ƙoƙarin bashi ita Mommynta yanda zata auri mai kudi ta rayu cikin kudi kawai take koya mata 


Shi yasa a lokacin da Hakeem din ya dawo nigeria tasan duk yanda tayi ta karkata hankalin sabeenar gunshi


Anata tunanin idan ta aure shi sun riga da sun gama warkewa saboda HAKEEM shine ne kudin tafeeda's gaba daya


Mommy ne tai saurin cewa "daddy naga sabeenar duka duka nawa take da zaace tazauna tayi jinyar mai lalurar ƙwaƙwalwa sabeenar ai yarinya ce bazata iyaba gaskiya"


Abba qarami ne ya katse ta da fadin "yanzu Raliya dan Allah Sabeenar ce yarinya na lura duk abunda yarinyar nan takeyi kece kike daure mata shekaru 35 take ne ma ki daina yaudarar ta saboda Allah bai hada rabo tsakanin su bane da yanzu tayi haihuwa hudu zuwa biyar a auren shekaru bakwai"


Hajiya Fatimace tayi wuff tace" Abban su ai da ka rabuda su idan ba rashin alqawari ba ai raliya bazatace komai ba, ina yaron nan baya kaunar auren nan hakan suka shiga suka fita saida aka cuce shi aka aura masa, ai gayinan sun haukata shi ni wallahi Ammin cema ke bani tausayi bata iya ki katabus duk an raba ta danta ƙwaya" daya sai kuma ta fashe da kukar munafurci.


Ita dai Ammi ji takeyi dama daddyH din zai ce tabar wajen ta huta da zafin da zuciyar ta take mata gaba daya ta tsani tafeeda's din idan banda san zuciya da san kai babu abunda suka iya Allah sarki hakeem tun yana yaro yake cikin jarabawa Allah ya bashi juriyar cinyewa.


#HAKEEM#