HAKEEM

Chapter 3

by @alkhair

ABDUL-HAKEEM IDRIS ABDULHAKEEM TAFEEDA shine cikakken sunan shi babanshi Alhaji Idris Abdulhakeem Tafeeda ɗa ne a wajen Abdulhakeem Tafeeda su asalin fulanin dukku ne dake jahar gombe.

Iyayen shi shi kadai suka haifa sunan TAFEEDA ya samo asaline saboda shine sunan da mahaifiyar shi take kiransa dashi.


Suna zaune lafian Allah har Allah ya haɗa soyayya tsakanin Tafeeda da Asma'u yarinya mai hankali da natsuwa diyar abokin baban shin, nanda nan maganar aure ta kankama.

Bayan shekara daya da auren sune Allah Yayiwa iyayen tafeeda rasuwa a lokacin Asma'u nada tsohon ciki, bayan wata biyu da rasuwar su ta haifi danta namiji akasa mishi suna IDRIS.


Kwanci tashi babu wuya a wajen Allah Idris nada wata biyu tafeeda ya samu aikin driver a gidan wani Alhaji a garin ABUJA cikin ikon Allah da zuwan su ko shekara basuyi bazawar yarinyar alhaji tai tsalle tace tafeeda takeso.

Yace ma Alhaji yayi haƙuri shi yana san matanshi kuma bayi da halin ƙara aure, jin haka yasa hankalin ADAMA tashi da taimakon ƙwarta suka shiga suka fita har sai da aka daura suka tare shida matanan sa guda biyu a gidan da Alhaji ya gina mishi.

Zaman da daɗi da babu da har yanzu Allah ya azurta shi da ya'ya harda jikoki Asma'u tunda ga kan IDRIS(ABBI) bata sake haihuwa ba suna kiranta da HAJIA MAMA ita kuma ADAMA(HAJI BABBA) tanada ABUBAKAR( sunan baban tafeeda wato kakanshi) suna kiran shi da ABBA QARAMI sai FATIMA dakuma RABIU suna kiranshi da BABA..


ABBI duk ya fisu arziki saboda shi businessman ne a harkar kasuwanci shi suka hadu AMMI Yar qasar QATAR har Allah ya haɗa su aure sukayi zaman su acan saboda bashi da abun da zai dawo NAIJA yayi tun bayan da Hajiya mama ta rasu wanda babu wanda yasan dalin mutuwar har yanzu sun dai tashi kawai sun ga gawanta, ranar daddyh yayi kukan rashin matar arzikin sa. Ko da DaddyH ya fada ma hajia mama abbi a Qatar zai zauna hauka ne kaɗai batayi ba dama tana baƙin cikin fin ƴaƴanta arziki da yayi duk da yanzu dawainiyar gidan shi yakeyi.

Saida suka shekara biyar da aure Allah ya basu ABDUL-HAKEEM wani irin kyakkyawan yaro daya biyo kamannin Ammin na larabawa sak harya fita kyau.


Bayan haihuwar HAKEEM da shekara goma suka dawo NAIJA a mansion din family house din da abbin ya gina musu kowa da flat dinshi a cewan babansu(DADDY HAKEEM) yafi so ya gansu guri daya dukkan su