SILAR AURE NA

p-13

by @rabiattu0444

_*🍇SILAR AURENA🍇*_

      

TAKU NA 1

Book 1📖




*NA*

Rabiatu Bashir Abdullahi

*_UMMU MAHER(MRS GREEN)_*🍃


_*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*_



*UMMU MAHER COLLECTION👜👜*

_Domin siyan kaya masu sauƙi da

rahusa danna wannan link ɗin na ƙasa_👇🏽

***

3tsX4CqiEp939DhYvJ3SZ


 *_KARANTA SILAR AURENA TA

AREWABOOKS HANKALI ƘWANCE👇🏽_*

https://arewabooks.com/book?id=

65bd172f88cb015808e5fc25


*_KARANTA SILAR AURENA TA

WATTPAD HANKALI ƘWANCE_👇🏽*

***

link&utm_content=share_published&wp

_page=create_on_publish&wp_uname=

Rabiatu333


SHAFI NA 13

_______________ ya ce" Jadda, inason yarinyar nan idan zaku bani"?. 

 

 Jadda ta ce" to me zai hana shalele na, indai har kana sonta ai babu matsala zan baka ita tunda daman ita nan waje na take".

Ya ɗan sosa ƙeyarsa sannan ya ce" amman bana son abin ya daɗe domin da matata nake son komawa".

Jadda ta ce" ƴartsana ce jikar tawa? da zaka ce wai da ita zaka koma? ko fahimtar juna ma bakuyi ba".

ya ɗan sosa ƙeyarsa sannan ya ce"Jadda bazan ɓoye miki komi ba, wallahi ina cikin matsala ne da matata Hajara, yanzu haka ma na kore ta daga gidan taje can tayi rayuwarta tunda abinda ta zaɓa kenan".


 jij wannan zancan yasa Mubarak tashi daga wajen, domin baya son jin sirrin wani duk da yasan ogansa ya zama jinin jikinsa, kuma rabin sirrin rayuwarsa yasan wasu amman duk da haka bai kai lokacin da zai zauna yana jin abinda yake faɗa na sirrin rayuwarsa.



yana tashi AD ya ce" dawo kayi zamanka Mubarak, matsalar Hajara ce baka sani ba? ko kuwa wani abu sabo zan faɗa? dawo ka zauna muyi maganar duka agabanka kaji".


 dawowa yayi ya zauna, ammanfa ba don yaso ba don sam baya son shiga sharru ba shano.


 Jadda ta ɗan gyangyaɗa kanta, alamar anzo wajen sannan ta ce" shalele dama wannan lokacin nake jiye maka, alokacin da kaso yarinyar nan idon ka rufewa yayi kaƙi saurarar kowa kaje kayi abinda gashi yanzu kana jin abin ba daɗi".


 ya ce" Jadda na yarda ayanzu, saboda Hajara sam ba tada hali me kyau wallahi Jadda tunda na aure ta kullum gidanmu tarin ƙawaye ne, da tarin ƙartin maza sai tace min ƴan uwanta ne duk na haƙura na jure amman duk ba tasan zuru ba, saboda kuwa ahalin yanzu rawar tiktok ta koma yi shiyasa ni ayanzu nake ganin gwara in haƙura da ita baki ɗaya, duk da har yanzu ina sonta to amman dole in haƙura da ita domin ni Allah ya halicce ni da kishi musamman ma akan abinda nakeso".


Jadda ta riƙe baki gamida ce wa" ikon Allah, rawar tiktok dai da yara naga sunayi yanzu? shi matar taka takeyi? idan kuwa haka ne ta cika taƙadararriya".


 AD ya ce" to kinje matsalar dana ke ciki, shiyasa nake son ƙara aure domin bazan iya zaɓa haka ba, kuma Allah ya bani lafiya da komi zamana hakan ba zai yiwu ba".


 Jadda ta ce" eh gaskiya ne Shalele saboda haka zamuyi magana da iyayen naku, sai muga yadda zamu ɓillowa abin ko? sannan maganar matar ka inason ka ɗan barta taɗan sha gidan nasu ko kaɗan ne, kada kayi saurin dawo da ita har ta gane kurenta sannan ni gani ma nake ko bata son haihuwa da kai ne"?.


  ya ce" Jadda wannan maganar zato ne, saboda haka ni aganina meye ribar Hajara na yin hakan? haihuwa kuma nufi ne na Allah idan har lokacin yinta yayi sai kika yazo, addu'ata ɗaya ce Allah yasa wannan auren da zanyi ya zamo samun ƙwanciyar hankalina, sannan itama Allah ya shiryar da ita".


 dukkansu suka amsa da amin.


 ya tashi ya wuce wajen Andi, gabansa sai faɗuwa yake domin bai san ta yadda Andi zata karɓi lamarin dawowarsa ba, zata yafe masa kamar yadda Jadda ta yafe masa ko kuwa? yasan macece me matuƙar haƙuri xata iya yafe masa cikin ƙanƙanin lokaci, sai dai ahalin yanzu kunyar haɗa ido yake da ita.




yana shiga ɓangaren ta ya dinga kallon gidan, yana aro dauriya da jarumta har ya ƙarasa ɓangaren nasu, babu wani sauyi atattare da gidan sai da yaji babu daɗi aransa duk kuɗin da yake dashi ace baya ko tunawa da iyayensa? adalilin me ya aikata hakan? haryanzu ya kasa tuna abinda yasa ya aikata hakan ganin babu mai basa amsa ya sanyashi shiga kansa tsaye.


 ba kowa afalon, sai Yaya Badi'a, wacce kanta yake kallon sama tana shimfiɗe kan doguwar kujera, hawaye wasu na bin wasu akuncinta tausayinta ya dabaibaye masa zuciyarsa ya ƙarasa har kusa da ita ya riƙe hannunta, yana ɗan murza mata ya kasa hawaye sai haɗiyar zuciya yake Allah sarki ɗan uwa me daɗi sai yaga ta dena kukan ta fara fara'a, kyawawan lotsa kumatunta suka ƙara fito da ainihin kyaunta, ya tuna lokacin da take da lafiyarta amman yanzu babu abinda yake amfani jikinta, hatta wuyanta bata iya juyashi kuma bata iya magana sai dai duk abinda ka faɗa tana iya jinsa, amsawar ce dai Allah bai nufe ta da yinta ba.



magana ya fara mata, cike da so da ƙaunar ƴar uwarsa ya ce" Yaya Badi'a ina neman afuwarki akan abinda na aikata muku, wallahi ina cike da dana sanin yin hakan don Allah ki yafemin ƴar uwata".


 sai yaji tana ɗan kyaɓe baki, alamar tana son yin magana kuma tana furtawa ne amman baya jin ta, saboda haka ya kawo kunnensa dai dai inda kunnenta yaji tana cewa" ba.....ba....ba... komi ɗ.....ɗ...ɗan uwa na".


 sosai yaji daɗin maganar da tayi.


Andi da Alti suna tsaye akansu, murna fal zuciyarsu suna kallon ɗansu cike da zaƙuwa Alti ta ƙaraso inda yake cike da hawaye ta ce", Shattima yau kai ne agidan namu? ashe dama zaka tuna damu"?.



~~~~~~

aranar da aka sallamoni muna taxi ɗin da Sulaiman ya tare, gabana sai faɗuwa yake shima kuma ya lura da hakan saboda haka ya amshi me sunan Babansa ahannuna ya haɗa da Harira duka ya rungumesa ajikinsa, sannan ya riƙe hannuna guda ɗaya tam ahannunsa sannan ya ce" Maryama, bana son wannan damuwar da kike yi in sha Allahu babu abinda zai faru, Baba zata dena yi miki abinda take yi ɗin saboda haka ki dena ma damuwa".


 duk abinda zai faɗa bazan yarda ba, saboda nasan wacece Baba hari macece me masifa ga kuma tsana ta da tayi, nasan babu abinda zai sanya ta dena duk abinda tayi niyya.

Amman don in nuna masa ba komi sai na shanye damuwa ta, har Allah ya kawo mu ƙofar gida ya fara fito mana da kayanmu, da kayan shayin da ƴan uwana suka siyo min ya kai gida sannan ya riƙe yaran ya bashi kuɗinsa muka shigo, gabana sai dukan uku uku yake ina tunanin halin da zan tsinci kaina awannan baƙin gidan dana sanyawa suna......


MRS GREEN CE🫵



*MAMAN AMEER DILKA SOAP*


*muna siyar da kayan gyaran jiki, jikinki ya yi silɓi da kuma shining ki zama tauraruwa acikin mata*.


muna siyar da dilka

 soap

mulato soap

 white scrub

 da dai sauran kayan gyaran jiki har ma dana ƙamshi kamar👉🏽


Gab gab

Layal

Hawi

Cus cus

Coucounot sandal,

Marshoosh,

Frami

Kajiji,

Sandal.flask

Qalbul oud,

Noor hayaty,

Kindikaye,

Sultana,

Kajiji,

Sandal asly 

Malika

Night queen

Misk humra,

White humra

Dufur khumura,

Khumura mukabassiya.


 ga lambar wayata, don siyan ɗaya ko sari MAMAN AMIR GIDAN GYARA ƘAMSHI.

***