Duniyar mata

Chapter 1

by @kwalisa



 KASHI NA DAYA

Y

ar uwa ana son mace ta zama mai tsafta a ko da yaushe ya zama komai nata a tsaftace yake. Kama daga gidonta da kuma ‘ya ‘yanta. Wannan zai taimaka qwarai wajen kawo soyayya da shaquwa a cikin zuciyar mai gidonta.

Ganin yadda wasu matan suke wufintar da aikin gida hakan yasa na xauki wannan matakin a matsayin mataki na farko da zan soma kira gareki uwar gida ko nace amarya. Shin ke ‘yar uwa kinsa cewar gyaran gida ya kasu kasha-kashi idon baki sani ba saurarra sosai ki ji :-

Kullum(Daly)

Sati (weekly)

Wata-wata (monthly)



Zamu fara da daily (kullum)

Ana son kina tashi ki soma buxa windo saboda a samu wadatacciyar iska.

Sannan ki share ko ina ciki da waje.

Sannan kiyi mopping (gugar xaki)

Sai kiyi wanke-wanke.

Ki yi gyaran banxaki.

Gyaran kicin.

Gyaran gado da gyara zanin gadon.

Saka turaren qamshi na wuta dona ruwa.

Weekly (sati-sati)

Cire yanar gizo.

Wanke firji

Gyaran wardrofe (sift)

Canza zanin gado/ wanke shi.

Gyaran risho a wanke a kuma gyara shi.

Goge kayan kallo.


Monthly cleaning (wata-wata)

Wanke carfet.

Wanke labulayen gidon.

Gogoge kujerun gidon.

Ita kanta mace idon ta kasance tana aikata haka wallahi sai taga gidon yana bata sha’awa kuma duk wanda ya shiga gidon nata zai zama yana sha’awar gidon.

Amman wasu matan za ka samu gidonsu kaca-kaca bola ta ko ina. Wasu idon ka samu gidonsu duk qazanta sai ka ji suna cewar ai yara ne basa barin gyara. Ni ban xauki wannan a matsayin hujja ba kawai dai kece ki ka zama daga cikin qazaman mata marasa son tsafta. Ya kamata dai ‘yan uwa mata a gyara domin a samu damar mallakar miji.

 Idon son samu ne bayan kin tashi da safe kin soma shara xaki kin gyara duk abinda kike da buqata sai ki kunawa xakin naki turaren wuta yanda oga yana tashi zai soma cin karo da qamshi yana tashi ko ta ina.





KULA DA MIJI.

 ‘Yar uwa idon kika tashi da asuba to bacci ba naki bane. Kina gama wannan za ki kama wannan aikin ba za ki samu hutu ba sai mai gidon naki ya fita.

Idon kin kammala komai sai ki haxa masa break fast ana son kafin ya tashi ki kuma xora masa ruwan wanka yadda yana tashi sai ya yi wanka. Ki xauko kayan da zai saka a rana ki ajiye masa an so ki zama ke kike da ikon zavar masa kayan da zai saka.

Idon ya kammala wanka ya fito ki taimaka masa wajen shiryawa kama daga shafa masa turaren shuwa na hamata dona jiki da kuma feshe masa sigilet xin da zai saka ki feshe ta da turare sannan ki saka masa ita a jikinsa ki xauko kayan da zai saka ki taimaka masa wajen sakawa.

Yana da kyau kuma a matsayinki na matar gida ki dunga kula da faratan mai gidon ki idon sun fito ki saka almakashi wajen yanke su. Haka kuma gashin baki ki gyara masa. Idon gashin hammata ya fito dona gaba shima duk ki saka abin aski ki aske masa shi wannan kulawar zata samar miki da soyayya a wajen mai gidonki.

Bayan kin kammala shirya shi sai ki kamo hannunsa zuwa wajen cin abinci. Idon kuka zauna kuka ci abinci da zara ya tashi fita kasuwa ko wajen aiki sai ki masa rakiya har bakin qofa kina mai yi masa addu’a ta fatan alheri akan Allah ya bashi nasara a fitar da zai yi.

Idon ya fita sai ki dawo ki qarasa ayyukan da suka yi miki saura baki qarasa ba.


WAJEN DA AKE SON AMARYA TA DUNGA KULA DA SHI SOSAI.

BAKI:- Shi baki da kike ganinsa waje ne da yake fitar da wari a ko wane lokaci ana son ko wane lokaci ya zama a cikin tsafta. Ana so kullum ya zama kina yin brush a qala sau biyu ko sau uku. Sannan ki yawaita amfani da abubuwa masu saka qamshin baki kamar su mouth fresh ko irin su cingam masu saka qamshin baki kamar irin su orbit idon kuma sun miki wuyar samu sai ki dunga amfani da kanunfari shima yana hana warin baki.

KUNE:- Shima kune da kike ganinsa yana fidda wari wanda ke ba za ki ji ba sai mai gidonki shi da zai kusance ki. Don haka shima ake so ki dunga goge shi akai-akai kuma sannan idon za ki kwanta ya zamanto kina shafa turare a bayan kunen naki da kuma gefensa.

HAMMATA:- Ai wannan ba sai na ma faxa miki ba ko wacce mace tasan hamata waje ne mai fitar da wari mai hamami. Don haka yake ‘yar uwa ya kamata ki kasance kina aske gashin hammata a ko wane lokaci domin wannan gashin shi ne yake haxuwa da gumi yana fitar da wani wari.

Kinga kuwa idon haka ne ya zama dole ki tashi tsaye domin ganin kin gyara ta yadda idon oga ya matso kusa dake ba zai ji wari ba. Idon son samu ne ki dunga shafa alimun a hammatar taki. Haka ma ki dunga goga turaren hammata idon za ki kwanta.

KASAN NONO:- Shima yana xauka dati sosai ana son duk lokacin da za ki yi wanka ki dunga wanke shi sosai da kyau.

MATSE-MATSI:-Shima waje ne da yake fitar da wari ana so a dunga wanke shi sosai. Domin rashin wankewa sosai shi zai saka kiga har wata nankarwa wajen yake yi dati yana taruwa a wajen wannan datin shi yake haifar da warin gaba ya kamata duk lokacin da kika zo wanka ki dunga wanke wajen sosai da sosai.

DOKIN WUYA:- Wuri ne da dati yake kwanciya shi yasa ake son a dunga wanke shi sosai kuma idon za ki kwanta shima ya zama kina kula da shi wajen shafa masa turare.

Waxan nan guraren sune suka fi fitar da wari a jikin mace. Don haka ya zama cewar kina kula da wurin sosai a ko wane lokaci.

‘Yar uwa sai kin tashi tsaye da gyara sannan za ki riqe mijinki sosai. Abin takaici sai kiga wasu matan wai ba za su yi kwalliya a cikin gidajen su ba sai idan za ki biki ko suna.

To abin tambaya a bikin wa kike yiwa kwalliyar? Ga wanda ya kamata ki yiwa ki xebe ladan da Allah yake bayarwa. Ko kin manta duk abinda kika yi domin mijinki Allah zai baki lada akan haka don haka ya kamata ‘yan uwa mata mu gyara sosai idon muna son samun damar mallakar mazanmu.


SIRIKAN ZAMA DA MIJI

Ki kasance mai tattalin mijinki.

Ki kasance mai ladabi da biyayya.

Ki kasance mai tsaftace jikinki da kuma gidanki.

Ki kasance mai lura da abinda mijinki yafi so da wanda baya so.

Ki kasance kina nunawa iyayensa da qanensa da sauran danginsa qauna.

Ki kasance mai tattalin abinda ya kawo gida kama daga kayan abinci.

Ki zama mai rashin nuna gajiya a lokacin da yake buqatarki.

Ki zama mai faranta masa rai a ko wane lokaci.



QISAR ZAMA DA MIJI

Kwaliya

Tafiya

Magana

Kallo

tsafta

Bara mu xauki xaya bayan xaya muyi bayani akai mu gani shin ‘yar uwa wane ne a ciki kike aikatawa wane ne kuma bakya aikatawa.

1-KWALIYA:-Hausawa sun ce idan kana da kyau ka qara da wanka. Wannan yana nuna cewar ya kamata ‘yar uwa ki dunga kula da kwalliya domin ita ce matakin farko da za ki kama linzamin zuciyar mijinki.

Kada ki zama a cikin sahun matan da sai za su gidan biki sannan suke yin kwaliya wannan zai saka a xauke ki kamar ba macen data waye ba. Ki dage wajen yiwa mijinki kwaliya a cikin gida domin ki burge shi ki bashi sha’awa kinsa a lokacin da zai dawo daga kasuwa zai dawo cike da gajiya gashi kuma ya ga ‘yan mata kala-kala sunyi kwalliya idon ya dawo gida ya same ki babu kwalliya sai yaji wani iri.

‘Yar uwa bayan kinyi wanka kin shafa mai ki shafa hoda ki saka kwali ki saka janbaki sannan ki xauko eye shadow ki saka..wayo Allah ina mai baki tabbacin za ki yi kyau sai ki xauko kayan da kike buqatar sawa ki saka nasan idan ya ganki hmmm abin ba’a cewa komai.

Don haka sai ki dage ki dunga kwalliya kada oga ya dunga gani a waje shi kuma matarsa ta gida bata masa komai.

2-TAFIYA:- Ita kanta tafiya iya wace kuma salo ce bawai ana son ganin mace tana tafiya bazar-bazar ko kuma kina tafiya zani yana kwance wa ko leven zanin naki xaya sama xaya qasa. Wata ma gani za ki gefen zanin naki ya yi dati ko ya yage sabida tsabar rashin iya tafiya.

Macen da ake so ita ce macen da take tafiya a hankali cikin nutsuwa kamar hawainiya kina tafiya xas-xas kina xan karkaxa jikin ki cikin salo mai jan hankali yadda duk wajen da kika motsa oga sai ya juya yana kallonki. Kina tafiya kina juya mazaunanki kina kaxa mamanki amma cikin salo yadda zai fahimci haka ya kuma shagala da kallonki.

3-MAGANA:-Abin haushi sai kaji wani lokacin ma maqociyarka tana jin muryaki wai sunan kina magana da mijinki. Ba za ki yi magana a hankali ba har sai kowa ya jiki. Ya kamata ko wane lokaci kina yin qasa da muryarki kada ki kuskura muryarki ta xara ta mijinki ki dunga magana qasa-qasa kina haxawa da shagwava.

Kina xan marairaicewa kamar za ki yi kuka kina matse muryarki haba wa ‘yar uwa nan da nan za ki ga duka hankalinsa ya dawo gareki domin sauraron abinda za ki ce masa.

Amma idan kika dunga buxa murya kamar ta gardi sai ya zama baya ma son jin kin zo masa da buqata.

4-KALLO:- ‘Yar uwa idan za ki kalli mijinki ana son kiyi qasa-qasa da qwayar idanunki sannan ki lumshe idanu kamar mai shirin yin bacci.

Bawai ya zama kina zare masa idanu ko ki kakkafe shi da idonu ba. Bara ki ji shin kinsa kallo da kike ganinshi iri-iri ne.

Kallon na yin kewarka.

Kallon ina ka tsaya.

Kallon soyayya.

Kallon matso kusa da ni masoyi.

5-TSAFTA:- Wannan fanin yana da muhimmaci sosai ga mace domin shi ne yake janyo mata samun daraja a wajen mijinta haka kuma rashin tsafta yana kawo savani mai yawa a tsakaninku.

Ana son ki dunga kula da duk wani abu daya shafi jikinki kamar yadda muka faxa a baya su kune da baki da kuma matse-matsinki wannan shi zai saka mijinki ya ji baya gajiya da son matsowa kusa dake a ko wane lokaci.


ZAMA DA KISHIYA

Idan Allah ya haxa zamanku da kishiya dole sai kinyi haquri domin sai kin zama mace mai done kishinki sannan za ki samu ikon mallakar mijinki. Ana son mace tana yin kishi irin na addini kamar yadda shari’a ta tanada hakan shi zai saka ki zama mai nasara a ko wane lokaci.

Ana son a zamanku ya zama da haquri yadda hankalin ki zai kwanta shima na mijin ki ya kwanta. Don haka ku zama masu haquri domin a samu kwanciyar hankali da zama mai xorewa. Kuma dole sai kin kula da abubuwan da muka lisafa a baya hakan shi ne zai baki damar mallakar mijinki yaji ya matsu rana xakin ki ta zo ya shiga domin yana samun farin ciki da nishaxi.

Haka kuma qissa zata zamar miki cin ribar zama da mijinki ki kuma xara kishiya a wajensa. Na kawo qissar mallakar miji yanzu bara mu garzaya ga gyaran dukiyarmu abin alfaharin mu wajen da muke mallakar maza.

Yanzu zamu yi bayani akan abinda suke qara mana ni’ima don haka ‘yar uwa sai ki matso kusa domin ki samu bayanin.