Chapter 29
by @maidambu41
*BAƘIN HAURE....🐾🐾*
{Greed for Money is the roots of all evils🫀}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu
*029*
Bahaushe yayi gaskiya da ya ce d'an uwa rigar k'aya, kabarshi a jikinka ya soke ka. Ka cire shi duniya ta zage ka. Ban fadi haka don kome ba, sai yadda nake cike da kewar Addah da Ummi, musamman Zuzu da ban san wata duniya take ba, ina matuƙar son ganin Zuzu ta gaya min meye nayi mata haka? Me yasa tayi min haka? Me yasa ta ha'ince ni? Kowacce rayuwa tafe take da kalubale. Sai dai a wannan lokacin na fahimci girma da muhimmancin nisantar su Addah. Sannan akwai wani abu daya da na kasa sabawa shi, wato tunanin Yazid, na kasa yarda ya mutu domin zuciya ta bata bani damar amsar labarin Mutuwarshi ba, sannan haka su Addah bana fatan ace suma sun mutu domin ciwon zai min yawwa.
Yau ya kamata na fara zuwa makaranta, amma bani da karsashi da nutsuwar zuwa, zuciya ta a rufe take wani irin yanayi nake ji mara daɗi, haka yasa na cigaba da kwanciyar da nake har zuwa wani lokaci. Karfe tara na fada ban daki, na dad'e sosai sannan na fito daure da towel, a hankali idanuna ya sauka kan Baby da ta farka, gadon na nufa ina faɗin. "Kin tashi ne?" Na d'auketa a kafadata, zuwa banɗaki na mata wanka sannan na daurata akan karamin poo mikewa tayi tana ihu, "yi hakuri zauna kiyi " ai kamar na zage ta, haka yasa dole na.hakura muka fito na shirya ta cikin wata riga da wando, pink da purple. Sai farin hular Amnas, da nasaka mata, na shafe ta da turare mai daɗi da sanyi, Yallabai Yazid ya koya min amfani da turare dan zaman da nayi da shi, ko wannan gidan haka ne domin gaban mirror akwai turaruka kala kala wasu ma ban taba jin sunansu ba. Hadiye yawu nayi ina jin kwalla na cika min idanu. Mikewa nayi na nufi sip dinmu na bude, karamin drowe din jikin siff din,bra ne da pants ɗinsu, a hankali na cire wasu farare kalkal, na saka a saman gadon na koma na bude asalin wurin kayana. Wata doguwar riga na ciro, da mayafinshi da hular da zata dace da shi.
A hankali na saka bra din da pant, sannan na saka wani gajeran wando, iya gwiwa kafin na saka gown din. Wanda aka rubuta Amnas collection, na saka a hankali, kallon kaina nayi a madubi fuskata tayi kyau, ba laifi sai dai kana kallon kwayar idanuna zaka fahimci ina cike da damuwa. Murmushi nayi na tattara gashin kaina,.na saka bam na daure shi tsaf, sannan na nufi inda mayafinshi yake na lullube, bugun kofar dakin aka yi na ce. "Shigo." Ina gyara jakar da zan fita da shi, ta shigo. "Tante!" Cikin kulawa na amsa mata. "Na'am Barakatu?" "InJi Babanmu wai na gaya miki, mai kaiki makaranta ya jima da zuwa."
"Ok gani nan zuwa!" Na mike ina.gyara zaman mayafina, tare da saka jaka a kafadar, na nufi wurin turare na shafa, sannan na fito ina dauke da baby, dake bata da rikici, mikawa Barakatu ita nayi na koma daki na d'aga towel din na shanya sannaan na dauki kudi a cikin drower gadon, na zuba a jakar ko da zan bukaci nayi wani abu, ina gamawa na dauko flat shoe na saka, sannan na fito bayan na rufe dakin, na dauki kayan abincin baby na kai musu, da wasu kayanta kala biyu da Pampers. "Maman Barakatu zan tafi ga Baby Amirah sugrah!"
"Allah ya dawo dake lafiya, sai kin dawo." "Yawwa, Barakatu idan ban dawo ba, ki dafa mana shinkafa akwai sauran miyar nan ki zuba muku ku bar min sauran."
"Tow Tante!" Ta fada, da sauri na fito daga wurinsu na nufi hanyar waje. Tun kafin na isa driver ya fito ya bude min kofar baya, na shiga na zauna. "na gode! Nace mashi" Sannan ya shigo muka bar gidan, kwantar da kaina nayi a jikin kujerar, ina ji na kamar wata sabuwar halitta, wacce aka sauya mata duniyarta, tabbas an sauya min duniyata amma kuma ina dangina da zuri'ata suke? Buɗe idanu nayi, ina shaƙar kamshin turaren motar, kafin na dan zubawa gefen hanya idanu. Bani da kowa bani da kome, daga ni sai Baby haka zan rayu cikin kaɗaici, cizon fatar bakina nayi ina mai da kwallar da ke shirin zubo min. Haka muka isa makarantar, na kasa barin zuciyata ta huta, muna isa ya Fito ya bude min kofar, sannan ya amshi jakar hannuna. Har Office din Dean na Mariama Abacha University marad'i ya kai ni.
Koda muka shiga office din, Dean din bata nan, don haka muka zauna har ta dawo. Cikin girmamawa mutumin ya gaishe ta cikin harshen French, ya mata bayani. "Tow shi kenan, zan duba bari na kira shugaban tsangayarsu." Ta fada da hausa, jin tana hausa sai naji kamar ina cikin dangina ne. Domin wani lokaci idan kana jin wani harshe aka zo ana yin irin shi, zaka ji kamar dangi kuke da mutum,haka yasa na zuba mata idanu ita kanta hausar da take cikin gayu da kwarewa, kamar irin ban ma san yadda zan yi bayani ba, amma tabbas na tsinci dami a kala. "Muje Madame!" "Ok!" Na furta a hankali, haka muka fito daga cikin office din zuwa department ɗinmu na Yan economic, duk wasu abubuwan da ya dace duk muka kammala a yau, sannan ya kalle ni cikin girmamawa ya ce min. "Madame daga yau bani zan kara zuwa ba, akwai wanda xai rika zuwa yana kawo ki, sannan asabar da lahadi zai zo ya kaiki wurin koyon tukin motar, wannan shine inda zan tsaya. Idan na tafi da motar wanda zai cigaba zai dawo da ita."
"Da gaske Yazid ya mutu?" Bai kalle ni ba, kuma nasan ba lallai ba ne ya kalle ni tunda iya kan aikinshi yake, ina ji ina gani ya ja motar ya bar makarantar. Hawaye ne ya zubo min, tabbas ba mutuwa akewa kuka ba, sabo ita ce akewa kuka kuma yanzu da na saba da shi, ya tafi ya barni da ciwo a rayuwata. Haka na share hawayen da ya zubo min, sannan na nufi hall din da zamu na daukar lecture na zauna, bamu da yawa a cikin hall din haka ya tabbatar min da cewa course ɗin mu bai da farinjini. Eh bai da farinjini domin ba kowa yake yin shi ba, ko ni naso da accounting dina da nafara tun farko na karanta da na samu damar cigaba daga inda na tsaya, amma wancan takardun ma Yazid cewa yayi basu dace dani ba. Ina zaune malami ya shigo ya gama bayaninshi, masu maida hankali suna maida hankali mu kuma, muna ta baza idanu, sai bayan fitar shi na sauke ajiyar zuciya. Wunin ranar ban da Masallaci ban je ko ina ba, asalima ni yanzu ban son sakewa da mutane, gudun kada wani abu ya taso a san Asalina ayi min gori ko cin mutuncin. Haka yasa ana tashi na tafi inda aka ajiye motar dazun naga motar, tun kafin na isa ya taso da sauri kamar zai kwanta na bi ta kanshi, ya amshi jakar hannuna, ya bude min baya na shiga, sannan ya ajiye jakar a kujerar gaba, sannan muka bar makarantar. Koda muka isa a matukar gajiye na isa, na samu Baby Amirah sugrah tana ta ihu, amsarta nayi ina faɗin. "Me ya same ta?" "Faduwa tayi dan zaki dawo nan!" A hankali idanuna ya sauka kan hannunta da yayi jajjur, "toh ba kome." Na wuce da ita falo, ina rungume da ita. Sai kuka take kamar zata tsaga gidan, na rasa me ke min dad'i. Haka na bata ruwa tasha, ta faɗa kirjina tana sauke ajiyar zuciya. "Mirah me aka miki?" Sake k'amk'ame ni tayi, tana sauke ajiyar zuciya. Dakyar na samu damar shiga kitchen na duba Barakatu ta gama abinci, na zauna naci na bata amma taki ci, kafin ayi Magariba jikinta yadau zafi kamar wuta rau. Haka na daure nayi sallah, sannan na fito ina gayawa Baban Barakatu zan kaita asibiti. "A'a da dai kin koma, za azo a dauke ki." Haka na dawo can kuwa sai ga drivern da ya dawo da ni, yazo muka je asibiti aka duba hannun ashe tsagewar kashi ne, domin ta fadi akan hannun ne. Haka aka daure hannun muka dawo gida da lodin magunguna muna dawowa Mamansu Barakatu tazo tayi ta bani hakuri. Ni na rasa hakurin na meye? Naga dai tsautsayi yana kan kowa, don haka na fahimci wani abu, babu yadda zaka yi ka daurawa wani nauyinka, don kawai wani dalili. Haka yasa da muka kwana washe gari da kaina nayi abin karyawa, da duk wani abin da ya dace, sannan na ajiye na mata wanka, na shiryata. Bayan na gama shiri cikin nutsuwa da cikar kamala, na fito ina rungume da ita. "Hajiya zaki tafi da ita ne?" "Eh idan ta warke zan barta domin ko na tafi ba xan samu nutsuwar karatu ba." "Shi kenan a dawo Lafiya, Allah ya bata lafiya."
"Amin Ya Allah."
Daga haka na wuce mota, muka bar gidan. "Madame ko za a akaita gidan renon yara ne, kada ta raba miki hankali." "Ba kome zan iya." Haka muka isa har makarantar, wani abin mamaki shine tana ganin baƙin fuska ta ware, kowa ta gani Ba, wai ita Baba. Haka muka shiga aji, tayi ta yawo dake tana tafiya, ganin bandeji a hannunta yasa kowa ya ganta sai ya tambayeta. Ita kuma tayi mishi gwaranci. Lokacin da malama ta shigo nan ta ɗauke ta. Ta fara mana darasi, kafin wani lokaci tayi barci. "Ina Mamanta?" Mikewa nayi na je na amsheta. "Jikinta kamar da zazzaɓi, ki bata magani."
"Tow na gode!" Na wuce da ita, na zauna muka cigaba da darasi, ta fara goma ta gama sha biyu, sai karfe biyu zuwa biyar haka muka wuni. Koda ta farka magani na bata da abincinta, wasa ta cigaba da yi, har muka taso.
Haka na cigaba da tafiya da ita har aka warware hannun, na sakata a daycare. Ba lallai kowa ya fahimce ni ba, amma nasan har ga Allah shi daycare makaranta ne, su kuma Barakatu, ba zan daura musu dawainiyyar bari-bari ba, haka yasa na yanke shawarar sakata, amma nasan ran Mamansu ya b'aci,. Sai dai ban wani damu ba. Domin yanzu ba da bane da damuwar wani zai hana ni nutsuwa, sannan a gefe guda ina tsoron kada wata rana Uwarta ta bayyana taga yarta ta nakasa ta ce ban rike amanar da ta bani ba, gashi na nakas ta mata yarta.
Watana biyu da fara karatu aka fara shirin azumi, nayi farinciki sosai amma kuma sai nake ganin kamar ba wani farinciki da karsashi, dake ina koyon tukin mota kuma mutumin ya gaya min bayan sallah ba xai cigaba da ajiye ni a school ba, iya wa'adin shi ya ƙare, na takura kaina sai na koyi mota. Domin ni sai abin yazo min banbanrakwai. Haka na cigaba da zuwa koda aka fara azumi ina makarantar aka kawo min duk wani abin bukata, "baban Barakatu basu gaya maka daga ina suke ba?"
"Gaskiya basu fada ba, kawai ajiye min kayan suka yi suka tafi."
"Shi kenan!" Na bude kofar ya shigar min da shi store, sannan na wuce daki ina nazarin waye da wannan dawainiyyar.
*In sha Allah, ba zaki sake kuka don yunwa ko wurin kwana ba, duk wani abu sai dai ki bawa wani. Nayi alƙawarin ko bayan raina ba zaki wulakanta ba, zan tsaya miki idan ina raye. Haka koda na mutu sunana zai cigaba da baki duk wani abin da zaki roka, a tab'a kimarki ba, ba zan tab'a barin ki rasa shi ba.* Zubewa nayi akan gwiwata na fashe da kuka, wata irin rayuwa nake yi ne? Da farko mutumin da ya taimaka min ya kubutar dani a hannun wancan azzalumin, babu shi babu labarinshi, na ganshi ma nayi mishi godiya babu dama, Aunty Umaimah ma, ban san inda zan same ta ba. Shima wanda nake farin cikin na same shi, baya nan baya nan ya tafi "innalillahi'wa'inna'ilaihi'raji'un, me yasa mutanen kirki suke fita a rayuwata lokacin da nake tsannanin bukatarsu????????????
#Mai_Dambu
```Hajiya ga kaya nan Masha Allah, Available price
Huluna da Mayafai, da na yara sai Wanda ranko yakeso gasunan kala kala, Hajiya muna dasu ba iya hulana da Mayafai ba, har da shadodin na fitar sallah, Hajiya domin hutar dake da fitar dake kunya na tanadi yadda ba zaku sha wahalar yawo kasuwa a cikin azumi ba, don haka kafin kishiyarki tazo ta sata au 🤣😹😂 kafin kishiyarki tazo ta saya na tayiwa mijinku shakara gara kizo ki sata au 😔🤣😹 baki ya saba gara kizo ki saya, barauniyar gida, kai Sarauniyar gida 😂😹 atow kayana na Uwaren gida da na Amare ne```
*TUNTUBE WANNAN NUMBER ****
Laces
ATAMFOFI
SHADODDI
Materials
Kayan yara
Veils
Huluna....etc