Chapter 30
by @maidambu41
*BAƘIN HAURE....🐾🐾*
{Greed for Money is the roots of all evils🫀}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu
*030*
Haka nayi ta kuka ina jin kamar bani da sa'a shi yasa mutanen kirki suke barina, nayi kukana na godewa Allah. "Ma....ma!" Naji Muryar Baby Amirah sugrah, bude idanuna nayi a kan fuskarta, da sauri ta tako zuwa wurina, bude mata hannu nayi ina jin sabon kaunarta. "Ta kira ni Mama!" Na fada da karfi wanda yasa na kara k'ank'ame ta a jikina. "Amirah sugrah, nice Mama?" Sai ga hawaye ashe haka uwa take ji? Ranar da d'anta ya kirata Mama, ashe haka abin yake da dad'i,. Sai ga hawaye shar da duminsu, wannan irin bazatar da Amirah tayi min da tab'a zuciya yake, sai na rasa kukan farinciki nake ko na bakinciki, bakiɗaya rayuwata ta kuma sake samun wani nauyin daga wanda na amsa, domin amsa sunan uwa ba karamin al'amari bane, balle irina da nasan dayawa suna son sanin wacece ni, kuma na fahimci haka a makaranta musamman idan aka ga yadda nake makale da ita, a cikin aji. Sai ya kasance kowa son sanin wacece ni yake meye alakata da Yarinyar da nake dauke da ita. Sai dai na barwa zuciyata wannan aikin ba zan fara buɗe cikina da zuciya ta ga kowa ba, komai alakata da kai balle kuma na fahimci idan har mutane suka ji ina turanci, sai na zama kamar wata criminal domin yadda yan Nigeria muka b'ata kanmu ba mazan ba matan.
Mikewa nayi na nufi store na ware kayan cikin kitchen din na fito da shi, sannan na nufi hanyar waje, na kira baraka ta dauka musu, ina shiga na samu suna aikin
abincin buda baki. "Tante baki bar aikin da za ayi miki ba."
"Assalamu alaikum! Amma ai na fara sallama ko?" Murmushi tayi tana sosa kai. "Wa'alaikis salam, Amirah tunda kika fadi tante ta raba mu dake!" Inji Zainab mai bin Baraka tana amsar Amirah. Murmushi nayi nace mata. "ba haka bane, kawai idan na barta ba zan iya nutsuwa ba, amma ai yanzu ma gamu a gida."
"Sannu Maman Amirah!" Murmushi nayi, ina mai rusunawa na gaida ta. "Yawwa Maman baraka, ya zafin nan ya niyya kuma?" "Alhamdulillahi, ya makaranta."
"Masha Allah, sai godiyar Allah." Na fada ina zama, "Nace baki bar abin da za'ayi miki ba?"
Murmushi nayi nace mata, "Maman baraka, jiya aka fara azumi yau biyu babu wani abin tashin hankali, yanzu aka fara kuma ina ji ba zamu cigaba da zuwa makaranta ba, domin nan da sati biyu zamu dawo gida hutu sai bayan sallah."
"Ayya amma da kina barin aikin, domin a rage miki kafin ki dawo." Murmushi nayi ina kallon yadda suke ta shirin buɗa baki, "yawwa Baraka, ke da Zainab ko zaku dauko kayan abinci yana kofar kitchen." Kallon Mamansu tai, kafin ta kalle ni. "Maman Amirah!!!" "Kuje ku dauko." Hadiye yawu tayi tana son magana amma naki mata magana, sai kallon garin kunun da zasu yi. Ina zaune bayan fitarsu sai ga Babansu. "Wai ayi haka?" Murmushi nayi, a karon farko na kara samun wasu ahalin me ya kai haka dad'i. Haka suka fito da kayan abincin, muna da shinkafa da na bude tun zuwa na, sannan na basu buhu guda, taliya, makaroni, na dibar musu sugar sai madara da na ware musu da Ovaltine. An karo min nama da kifi, na basu daga cikin wanda nake da shi.
A hankali naga hawaye a idanun bayin Allahn nan, yana zuba sai naji kamar an sauya ni, domin ban basu don su min kuka ba, na basu ne don niman lada. Haka suka yi ta min Addu'a. Tashi nayi na bar musu Amirah don taki biyo ni , haka na dawo na shiga aiki, dankali na fere sannan na zuba mishi ruwa, na koma daki nayi sallar la'asar don nayi azahar a makaranta. Ina idarwa na shiga soya tare da gyara kaza nayi mana farfesu mai dankaren kamshi, na koya ne a wurin Zuzu, sannan na daura jallof din taliya, dake gas ce cikin lokaci ƙalilan na gama, na wuce ban daki nayi wanka na sauya zuwa doguwar rigar material me laushi da taushi na Amnas collection da hula me kyau, body mist na shafa oil ɗinshi. Na nufi hanyar falon na zauna ina kallon agogo karfe shida da minti uku, ina zaune a wurin har da minti ashirin, na mike na fito da kome falon na jera, sannan na wuce dakina na dauro alwala, na fito ina azkar da salatin Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama, ina zaune har aka kira sallah, a lokacin Baraka da Zainab suka kawo min kunun tsamiya da kosai, ba karamin dad'i naji ba, haka na nuna musu abincin da na zuba suka ɗauka suna godiya. Kunun da kosai naci, na koma daki da Amirah nayi sallah, ban fito ba sai da nayi sallar Isha da tarawee, sannan na fito na saka hand out a gabana, ina karatu ga Abincin wurin, ina ci ina karatun.
Daga nan ina jin Radion Baban baraka, da yake sauraren Malam Jafar Mahmoud Adam, haka kawai naji ina son rike waya, ina tow tawa take? Sai lokacin na tuna na bar kome a can garin. "Gobe in sha Allah, idan na fita zan nime waya domin na gaji da shirun nan, ni ba Ma'abociyar kallo ba, balle nace zan yi kallo kawai dai nasan ina son jin Radio kasancewar Baffa'm yana ji, sannan Alhajijo shima yana yawan sauraren Radio. Haka na tashi abincin da na zuba, tare da farfesu. Har wurin karfe sha biyu, na mike zuwa daki na sauya kaya, tare da alola na fara sallah, sai wurin karfe biyu na idar na kwanta. Akwai wata dabi'ar da nasan na koya a bayan zuwana garin nan shine kuka kafin nayi barci, haka na ci kuka na koshi, sannan barci yayi gaba da ni.
***
South Africa.
Tunda aka fara azumi yau biyu ga wata, lumshe luhu-luhun idanunshi yayi yana kara bude su, jin wayarshi tana kara. Bai bude ido ba, ya dauka Sannan ya saka a kunne. "Yes.!" "Ubangiji ya shirye ka." A hankali ya tashi zaune yana kallon gefen gadonshi, ya kunna wutar dakin yana jin wani yanayi don bai saba ganin haske a dakinshi ba. Tattaro nutsuwarshi yayi ya ce mata. "Hajiya Barka da shan ruwa." "Hmmm Barka dai Alhaji, ya Ibada?"
"Alhamdulillahi!" "Ina rokon arzikin kazo kayi hutu a gida." "Hajiya!" Ya kirata, "Na gama magana na baka nan da kwana biyu, idan ka sake aka yi azumi biyar baka zo ba, Abdul Majid na barwa sojoji kai. Kai ka saka ni a damuwa dan uwanka ya saka ni a kunci gaya min ya zanyi? Na maka uzuri tunda baka da lafiya, ina son farinciki da nutsuwa na zaɓe ku sama da farinciki na, idan na isa ka taho idan ban isa ba, ka sha zamanka Allah ya baka sa'a!" Kit ta kashe wayar, kut da wani tsalle ya dira a gadon, ya nufi inda kayanshi suke,. Ya shiga zubawa a wata Kyakyawar Luggage, yana gamawa. Ya koma ya zauna tare da kiran Aryan. Sai da wayar ta kusan katsewa sannan ya dauka, Muryar shi a shake ya ce mishi. "Hammayo lafiya?" Yarrrrr yaji kamar wani abu yana yawo a tsakiyar kanshi. "Sorry zamu yi magana gobe, ina hanya."
"Haba? Ubangiji ya kawo ka."
"Amin Ya Allah!" Ya katse kiran, domin shi ba yaro ba ne, yana jin Muryar Nabeeha. A hankali ya ajiye wayar bakiɗaya yana jin shi kamar bai cancanci rayuwa ba, kowa na cikin farinciki da iyalinsa, amma banda shi. Rufe fuska yayi da tafukan hannunshi yana jin wani abu yana tsaya mishi a rai.
Kusan shekara daya da rabi kenan, Umaimah ta kasa samo yarinyar da ya yanketa, yana tsoron kada sanadin wannan yankar ta mutu, domin yasan yadda irin wannan yanka yake, bakiɗaya jin shi yake sama-sama da zaran ya tuno da abinda ya faru. Sai yaji kamar yana da hannu a cikin abin da ya samu yarinyar tunda Umaima ta gaya mishi sun koma garinsu har anyi faɗa sun tashi amma taji labarin kamar faɗar da aka yi ya shafe ta, ko mutuwa tayi shi bai ma iya tuna abin ba, amma tabbas yaji Umaimah tana faɗin anyi faɗa a garinsu ga abinda ya faru, wani takurarren numfashi ya fesar, yana jin kamar bai kyautawa kanshi ba, na rashin ganin fuskar yarinyar amma ya rike muryarta, har a kwanan gobe ba zai manta da sassanyar murya mara amo da kwaramniya ba, shi fatan ma ya ga fuskarta ko sau daya ne, amma ina sai yanzu ne ma yake danasanin domin Umaima da ta gaya mishi, ita ce suka yi barci da ita a gado daya, a ranar da suka zo aikin ceto rayuwar sojojinsu, shafa kanshi yayi cikin tsananin damuwa da takaicin halin ko in kular shi, amma kuma a gefe guda sai yake ganin bai ga dalilin tunawa da ita ba. Meye hadinshi da ita? Meye matsalarshi da ita? Sam baya jin yana da wata alaƙa da zai saka shi tuaninta.
***
Yahunde. Cameroon,
Shashekar kuka take tana jin kamar zuciyarta zata buga, domin wani irin tukikin tashin hankali take ji a ranta, tana jin wani azazzben zafi da ciwo a ranta, ita kanta bata san iya adadin lokacin da ta dauka a gaban Mahaifinsu ba, kukan yayi yawa da yasa Yafendo tashi zuwa ɗakinta Sumee ce ta kasa hakuri ta ce mishi. "Ayya Ayya Datti haka zaka cigaba da kallonta, tana kuka abu biyu ta rasa fa, ta rasa miji da Yarta ai ba zaka zuba mata idanu har haka ba."
Yalwataccen murmushi ya saki, yana faɗin. "Bilkisu idan har Nafisah bata fahimce ni ba, ai ke ya dace ki fahimce ni. Iya su biyu mata Allah ya bani a tsakanin Ya'ya maza, Allah sai ya albarkaci rayuwarsu da jarabawa, idan ban gode mishi ba, me zan iya yi ? Alhamdulillahi Allah ya basu ikon cinye jarabawarsu."
Ya fada yana murmushin karfin hali, domin izuwa yanzu yasan yayi kuskure, ahalinshi sun yi kuskure da ya shafi bayansu. Kuskuren da yayi ba karamin kuskure ba ne, yayi watsi da Amanar da Allah ya bashi, ya watsar da Yaran dan uwanshi sannan ya rungume kashi.
A ina zai ga Isma'il da Aminatu? Ta haka zai gyara kuskuren da yake bibiyar Yaranshi mata da jikokinshi. Ace Yaranshi mata biyu, a wulakance ake aurar dasu, sannan mazajen su azabtar dasu da Yaransu. "Tashi ki tafi Allah ya kara miki hakuri da dangana, Ubangiji ya mata rahama, sannan ki rungumi Zaytoonah domin tana jin zafin hanata ganin mahaifinta, wannan ma wani jan aiki ne da dole sai kin yi da gaske. Allah ya kara miki hakuri."
"Baffayo." Sai kuma tayi shiru kafin ta fashe da wani irin kuka, "Sai hakuri idan har ka yi hakuri, akwai riba da fa'ida." Mikewa tai ta nufi cikin gidan, tana kuka har dakin Yafendo. D'ago kai Zaytoonah tayi tana kallon yadda take rusur kuka. Kauda kai tayi bata jin tausayinta ko kad'an, ta roke ta ta bata hakuri ta ce ta yanke mata kome, ita dai ta barta taje ta ga mahaifinta da Yayarta, amma taki sai yanzu zata yi wani kuka. Ita kuma da bata san shi ba fa? Ita da bata ji duminshi ba fa? Hmmm ita kukan dadi take tunda gata da nata iyayen ita kuma tayi mata asarar rashin ganin Ubanta. Ita yanzu ta tsani kowa ma banda Babynta, domin ba zata iya tsanar Babynta ba, tana son abinta kuma ba zata rabata da mahaifinta ba, domin ita nata rayuwar ta zama incomplete, tunda ta rasa inuwar uba, hatta zaman aure ya haramta a gare ta, domin abinda ya kashe mata aure har da gorin rashin uba. Haka kawai ta ja...
"Zaytoonah!" Mikewa tayi tare da ɗaukar yarta zata bar dakin. "Ki tsane ni babu laifi amma, idan kika nisance ni mutuwa zan yi. Da kewar shi xan ji ko da rashin yar Uwarki? Zaytoonah ina cikin wani yanayi da ban san mafarinsa ba, balle karshensa.....
#Mai_Dambu