p-15
_*🍇SILAR AURENA🍇*_
TAKU NA 1
Book 1📖
*NA*
Rabiatu Bashir Abdullahi
*_UMMU MAHER(MRS GREEN)_*🍃
_*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*_
*KOYON MAYAFI DA HULUNA DA RIBOM*
Kiyi shiga wannan grp ɗin domin dogaro da kai.👇👇👇👇👇👇👇👇
***
FHgAO8onZ0LHIRTHPG2qY4
*_KARANTA SILAR AURENA TA
AREWABOOKS HANKALI ƘWANCE👇🏽_*
https://arewabooks.com/book?id
=65bd172f88cb015808e5fc25
*_KARANTA SILAR AURENA TA
WATTPAD HANKALI ƘWANCE_👇🏽*
***
?utm_source=android&utm_medium
=link&utm_content=share_publishe
d&wp_page=create_on_publish
&wp_uname=Rabiatu333
SHAFI NA 15
_______________Boka ya bushe da dariyar hauka sannan ya gimtse fuskarsa ya ce" ai wannan duk ba abune me wahala ba, ƙafar kiyashi zata samo mana da ƙafar tattabara sai kaza da zakara sai haƙorin ɓera, da kuma gashin ita wacce zai aura ɗin shi za'a haɗa ayi mata asiri idan akayi wannan shi ne kenan an lalata rayuwarta, mutuwa ma zatayi daga ƙarshe".
sosai gaban Hajara ya faɗi, ganin hakan yasa Sady riƙe hannunta gam gamida ce wa bokan" ba komi boka za'ayi yadda kace to amman za'a iya baka kuɗin sai ka haɗa mana komi, ko kuwa?".
ya bushe da dariya gamida ce wa" ku bani kuɗin to amman gashin ne dai zaku nemo nata duk yadda za'ayi ku nemo gashinta ko kawo nan".
Sosai gabanta ya faɗi ta gaza haƙuri ta ce" boka gashij nata ma wahala zai mana, tunda kace ƴar uwarsa ce kuma ni kaga ban ma taɓa zuwa garinsu ba balle har inje yanzu in nemo gashinta, da dai zai yiwu shima anemo mana gashin nata sai in ƙara maka kuɗi".
Boka ya ce" banza gafalalliya asararriya ke kina ganin kina da kuɗin da zaki iya biyanmu, to masu kuɗi waɗanda ko tattaɓa kunnensu zasu ci mun ce sai sun samo balle ke? saboda haka ki gaggauta nemo gashinta, idan kuma ba haka ba abin ya dawo kanki".
sosai abin ya sanyata damuwa, amman saboda zuciyarta ta bushe babu ko ɗigon imani sai ta ce" to boka ayafeni zamu kawo amman zai ɗan ɗauki lokaci".
Boka ya bushe da dariya ya ce"muguwar halitta, to sai kin kawo ko yaushe ina nan ina jiranki ki tabbatar dai nata ne".
Suka sallamesa sukayo hanyar gida.
Suna shigowa ta faɗa kan kujerar Sady, ta ce"wash! gaskiya na gaji Sady wai a ina kika samo wannan mutumin"?.
Sady tayi murmushin mugunta sannan ta ce" a mugunta mana, ai ni kinsan duk inda ƴan tsibbu suke ina wajen badon su ba ai da ban ma san yadda zanyi da rayuwata ba, kinga kuwa idan kanason a gama maka da mutum sai ka fidda kuɗi kuma ka iya mugunta".
Hajara ta ce" to amman fa aikinsa da wahala gaskiya, ni yanzu a ina zan samo wannan gashin ko hauka nayi ai yanzu bazan shiga cikin ƴan uwansa ba, domin nasan ba sona suke ba tun ma kafin muyi aure, balle yanzu dana zamar musu ƙadangaren kan tulu sannan ƙiris suke jira su fyato ni ahanyacinsu ai kinga dole in yi protecting ɗin kai na, saboda kada su babbakamin wuta".
Suka tuntsire da dariya, Sady ta ce" oh mudai aƙwai mugunta kamar fulanin daji, muga mutum da ƴan uwansa kuma mu rabasu anya kuwa muna adalci? kada fa wataran ayi mana muma"?.
Hajara ta ce" uhm ke wannan yake gabanki, ai ni ko tunanin wata haihuwa ma bana yi, balle har in haifa ayimin tunda na samu duniya da kuɗi ai shikkenan, ni dai yanzu hanyar da zan samu wannan gashin kawai nake tunani kuma ban ma san hanyar da zanbi domin samunsa ba".
Sady ta ce" to yanzu dai so nake ki tuna dawa sukaje cikin masu aikinsa, domin dai nasan ba zai yafi siƙau ba yana babban mutum, saboda haka ki bibiya kinga sai muyi amfani da wannan wajen samun wannan gashin".
"yes besty kin kawo shawara, to amman kina ganin ba matsala"?.
ta ce" matsalar me kuma, tunda da kuɗi zasuyi duk abinda bakya zato".
sai kuwa Hajara ta ce" ni dai nasan tabbas da Mubarak sukaje, sai dai yaron ɗan aƙida ne ta yadda zan biyo masa ne kawai dabarar da ta rage mini, kuɗi bazai sa ya sauya ba sai dai ayi masa wata barazanar ko ta ƴan uwansa ko na mahaifansa na ƙauye, ina ganin shi ne shawarar daya kamata muyi".
sady ta ce" yo ke da kina da wannan shawarar ma kika hau, kame kamen jarababbun ƴan uwansa? ai tun yanzu ma aikinmu zai fara ɗakko wayarki mu haɗa wani bom".
~~~~~~~~
Ina cikin barci da rana sai naji ihun Baba ƙarami, agigice na tashi na duba gefe na naga ban gansa ba sai Harira me sunan Baba, shi kuma baya nan bai dawo da daddare ba na tashi da sauri domin haryanzu ina jiyo ihun gunjin kukansa.
wajen ta ɗakin Baba naji ƙararsa, na buɗe labule da saurin gaske sosai gabana yayi masifar faɗuwar na ƙarasa gamida saurin ɗaukar yarona, wanda aka sanyashi cikin wata ƙatuwar ƙwarya, ga jini duk ya ɓata masa jiki sai dana duba jikinsa na tabbatar ba jinin jikinsa bane, jinin jikin wanine aka ɗebo amatuƙar gigice na rasa ma me zanyi, kai tsaye na ɗauki Harira na fice da mugun sauri na fice daga gidan babu ko mayafi ina ihu.
gidan Abu jafar na shiga, duk suna zaune afalo suka ga shigowata atsorace sukayo kaina domin ina son zubar da yaran yadda jikina yake kakkarwa.
suka amshe yaran suna tambayata abinda ya faru, cikin kuka na sanar musu da komi.
Tuni Abu jafar ya ɗakko ruwan addu'a da yake yi suna sha agidansu ya hau shafawa duka yaran ajikinsu, sannan nima ya bawa Ummu jafar ta shafamin tun daga kaina har ƙafafuna, sai ga wani wahalallam barci ya ɗaukeni daga ni har yaran.
Abu jafar ya saki ajiyar zuciya, ya juya ya kalli matarsa sannan ya ce"baki fuskanci wani abu ba"?.
da sauri ta ce" ni kuwa na fuskanta wallahi babu ko makawa Baba hari ce ke son shanye jininsu ai daman tun dana ganta da wannan gurguwar matar wato Dillaliya nasan za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya".
Abu jafar ya ce" zato zunubi ko da ya kasance gaskiya mu kyautata musu zato sannan duk yadda za'ayi ayi bincike sosai ganin gano wanda yake da sa hannu, sannan yanzu zan duƙufa da addu'ah zanyi sallar nafila in faɗawa Allah kukanmu, ke kuma ki lulluɓesu saboda sanyi bari inje inyi sallar".
ta amsa da to, sannan ta wuce da sauri domin aikata umarnin mijinta.
***ana cikin yiwa Baba hari wankan tsafi randar ta fashe, ji kake tas tas ros ros jikin kowa na wajen ya tumbatsa ya fara fitar da jini ita kuwa Dilalliya ta kusan sakin fitsari, domin tun da har hakan ta faru babu makawa sai dodon tsafi ya ɗauki mummunan mataki kan Baba hari, domin duk yadda akayi ta bari wani ya gani ya ɓata musu aiki.
ogansu ta fusata ta fara magana kamar an buga dodo ta ce" tunda muka fara aikinmu babu wacce ta taɓa tona mana asiri sai ke saboda haka ko kina so ko bakya so dodon tsafi sai ya ɗauki mummunan mataki akanki".
Saboda tsoro da firgici sai ga Baba hari na sakin fitsari tsuuuu da gudawa.........😅
~~~~~~
tashinsa daga barci kenan yaji shigowar tsako ta wayar salularsa, ya ɗauka ya buɗe ya fara karantawa.
_ASSALAMU ALAIKUM MUBARAK NASAN BAKASAN WACECE NI AYANXU BA SAI DAI INASON FAƊA MAKA WATA MAGANA, WACCE NASAN ZATA TSORATA KA SOSAI AMMAN BA ABIN KA TSORATA BANE INDAI HAR KAYI ABINDA MUKE SON KAYI ƊIN SAI DAI AƘWAI SHARUƊƊAN DA ZAMU GINDIYA MAKA.NA FARKO KADA KA SANAR DA KOWA IDAN KUMA BA HAKA BA DUK FAMILINKA SUNA CIKIN TASHIN HANKALI DA KAI KANKA IDAN HAR KA MATSU KASAN MU SUWAYE AN JIMA KA BIYO LAMBAR NAN………………_
*kash anan labarin zai tsaya wato takun farko, taku na biyu dana uku kuma zai zama na kuɗi ne amman farashin kaɗanne naira ɗari uku ne kacal ki biya kici gaba da karatunki babu tsayawa, zaki biya kuɗinki ta wannan account ɗin na ƙasa sai ki turo da shaidar biyanki ta wannan lambar wayar ****
MY ACC👇🏽
2212328303
RABIATU BASHIR
ZENITH BANK.
MRS GREEN CE🫵
please share👏🏻