52
by @azizat
*MUTUM.....Mugu ne*
52
Kiran da Alhaji Idris ya yi wa SY da asubahi ya tada shi daga baccin da ya ke yi. Ya ɗau wayar tareda sallama.
" Shabbir ka na ina yanzu?" Ya tambaya muryar shi ɗauke da damuwa
" ina Kaduna, Alhaji lafiya?"
"Dan Allah ka wuce Jos yau yau ɗin nan, akwai matsala. Mijin Raudha zai ƙara aure bata sani ba sai jiya, kasan ta da kishin hauka, ta je gidan su yarinyar ta kama ta da faɗa ta ji mata ciwo sosai. Iyayen yarinyar sun sa an kama Raudha kuma sun ce sai an shigar da ƙara kotu"
"Hasbunallah, wai yaushe Raudha za ta dena wannan shirmen ne"
" dan Allah ka je a daidaita maganar ba sai an kai kotu ba, akwai tafiyar gaggawa da zan yi yau shi yasa ba zan samu isa Jos ɗin ba"
" ba komai Alhaji, Insha Allah komai zai daidaita"...
A gurguje ya yi sallah ya yi wanka ya shirya ya fito.
" antashi lafiya?" AY ya gaishe shi
SY yai murmushi ya ce " lafiya, kai ma da alama ka makara"
"Ai wayar Ummu Bashar ne ya tashe ni ƙarfe shida. Na leƙa ka na ga kana Sallah"
"Ni ma ɗin kira ne ya tada ni"
"Ya na ganka da jaka?"
SY ya duba agogon hannunsa sannan ya sanar da shi abin da ya faru.
" mata sai a hankali ai, Allah ya rufa asiri"
SY ya amsa da " Amin"
AY bai barshi ya tafi ba sai da ya karya tukun.
A mota ya tura wa Nazira text kamar haka " ina hanyar Jos" bai fi minti uku ba ta tura masa da reply tana ma sa addu'ar Allah ya tsare shi ya sauke shi lafiya.
.....JOS.....
Ba ƙaramin kai ruwa rana aka yi ba da iyayen Fadila, sun dage sai an shigar da ƙara kotu. Duk yadda SY ya yi ta bada haƙuri ba su yarda ba. Daga ƙarshe dole sai da ya kira wasu dattawa 'yanuwansu su ka zo daga Kirfi. Bayan dattawa sun shiga zancen shine suka haƙura su ka janye ƙaran bayan an rubuta shaida cewa ko bayan aure Raudha ta daki Fadilah hukuma za ta kama ta.
"Yanzu dan Allah kin yiwa kanki adalci, ke kenan akan namiji an dinga kulle ki kenan kamar marar gata. Haba Raudha, ina Ilimin ki ya ke, ina wayewar ki?, kwanan baya akan irin haka kika fasawa wata yarinya kai aka kulle ki, amma ba ki daddara ba still kika sake" SY yana magana kamar zai buge ta.
" haba Shabbir, Muhammad ya munafirceni, wani irin gata ne ban masa ba, kyautatawa ko wani iri ina masa amma still ban ishe shi ba sai ya duba waje. The painful part shine lokacin da na ji zancen a wajen ƙawata na ma sa maganar ƙaryata zancen ya yi tsabar munafirci"
"to yanzu ke Raudha idan ma za ki nuna ɓacin ranki ai iya Muhammad za ki yiwa tunda shi ya ga yarinya ya ce zai aura, ba ita ta kawo kanta wajensa ba"
"Shabbir haka ma za ka ce" ta girgiza kai ta wuce ɗaki ta fara haɗa kayanta. Duk yadda SY ya yi da ita ba ta ko kula shi ba ta haɗa kayanta da na yara ta ɗau hanyar Kirfi, dole sai bin bayanta shima ya yi.
***
ABUJA
Bayan kwana uku......
Jiya Shabbir ya shigo Abuja amma gidan ba lafiya, Shahida ce aka kwantar a asibiti wai hawan jini gareta. Shi gaba ɗaya yanzu ba a nitse ya ke ba. Ga Raudha itama can ta tuɓure sai dai Muhammad ya sake ta dan ba za ta koma gidansa ba, ga tunanin ceton Nana Khadija da zai yi.
Ya fito zai tafi office sai ya haɗu da Alhaji Idris bai san ma ya dawo ba. Bayan sun gaisa Alhaji yace "Shabbir akwai maganar da na ke son mu yi idan ba ka sauri"
"ba matsala Alhaji"
Ya bi bayan Alhajin har suka isa ɗakinsa.
" wato Shabbir ina neman alfarma a wajen ka ne"
"Alhaji, alfarma kuma?"
Alhaji ya gyara murya ya ce " tun shekara huɗu da suka wuce na san Shahidah na sonka, tun tana ɓoyewa har ta fito fili ta gaya min. Na share zancen saboda a tunani na kai ya kamata ka min magana ba ita ba, ƙarshe na gane ba ka da ra'ayinta. Dan Allah ka taimaka mata, kaga duk wannan ciwon da ta ke yi, dalilin son ka ne ba komai ba. Ka taimaka ka aure ta ko da a ta biyu ce"
Gaba ɗaya sai kunya ya rufe shi , ya daɗe da sanin Shahidah na son shi, tun tana ɓoyewa har ta fito fili ta gaya masa gaba da gaba. Ga shi abin ya kai har mahaifin Shahidah wanda ya ke Uba a gare shi yana roƙonsa.
Ya sunkuyar da kai ya ce " Alhaji zan yi tunani zuwa dare Insha Allah kowani hukunci na yanke za ka ji"....
Kafin ya wuce office sai da ya biya asibiti ya duba Shahidar, ya samu tana bacci, ba ƙaramin tausayi ta bashi ba, dan gaba ɗaya ta rame ta fige. Ya ba da saƙo idan ta tashi a ce ma ta ya zo kuma zai dawo da yamma.
Lokacin da ta tashi, tunda aka ce mata Shabbir ya zo duba ta ta ke ta farin ciki, tana jiran dawowar shi.
Ƙarfe biyar da minti arba'in Shabbir ya shigo ɗakin. Su ka gaisa da Zulaiha ƙanwar ta sannan ya ce ta basu waje.
"Ya jikin?" Ya tambaya yana zama kan kujeran da Zulaiha ta tashi
"Da sauƙi, Yaya"
" Shahidah ina so na mi ki wasu tambayoyi ne kuma ina so ki amsa tsakanin ki da Allah"
" ina ji Yaya"
" kin san aikin da na ke yi aiki ne mai hatsari kuma ba ni da lokacin zama sosai, kin amince zaki zauna da ni a haka?"
" na amince"
" akwai mata biyu da na ke son aura nan ba da daɗewa ba, kina ganin za ki zauna da ni a matsayin matata ta uku?"
" yaya ko a ta huɗu ne zan aure ka banda matsala da wannan"
Tausayi ta bashi dan ba kowace mace ba ce za ta amince da wannan.
" kin san soyayyar da na ke mi ki ta matsayin ya da ƙanwa ne kina ganin ba za ki cutu ba knowing I married you saboda ƙarfafa zumunci?"
" son da na ke ma ka ya ishe ni matuƙar za ka kwatanta adalci tsakanina da sauran matanka"
Ya ja numfashi ya ce zan aure ki Shahidah.
Shahidah ta ɗaga hannu tana faɗin "Alhamdulillah, ya Allah na gode da ka amshi addu'ata".....
***
*Gidan Sajid*
Dawowar shi kenan ƙarfe tara na dare ta ɗan wuce, he was very exhausted ya zauna kujera kusa da Yamin da Yassar da ke kallo a falon yana faɗin " Yassar kawo min ruwa dan Allah"
Bayan ya sha ruwa, da farin ciki Yassar ya ce " Uncle, ɗazu aka turo mana admission ta email"
Sajid ya i Murmushi ya ce "Masha Allah, so my boys are leaving me kenan"
" Uncle kar ka damu kafin mu dawo za ka samu set of two boys ma su ɗebe maka kewa, kasan amarya ma 'yan biyu ce, so Insha Allah za ta ba mu 'yan biyu a gidan nan"
Sajid ya ja kunnensa ɗaya yana faɗin "ka cika surutu "
" Uncle Saj gaskiya na faɗa fah, ko ba haka bane, Yamin?"
Yamin ya ce " Uncle Saj ni ban san zancen ba"
"Yamin haka za ka ce ko"
Sajid ya ja kunnen Yamin da ɗaya hannun ba tare da ya sake na Yassar ɗin ba ya ce "na san tare ku ka shirya wannan maganan"
Dukkansu sai suka sa dariya.
Ya jima a falon ƙasa suna hira kafin ya tashi ya haura sama. A falon sa ya taradda Zaytunah na kallo.
Ko gaishe shi ba ta yi ba tace "dama ina jiran ka dawo ne, dan gobe zan je siyayya Lagos"
" yaushe za ki dawo?" Ya tambaya ba tare da ya kalle ta ba.
" kwana biyar zan yi"
"Na baki kwana uku" ya faɗa sannan ya wuce ɗakinsa.
Washegari kafin ya ƙarisa shiryawa ya fito tuni driver ya wuce da ita airport, Ko sallama ba ta masa ba. Ya girgiza kai kawai lokacin da Saratu ta ce mi shi "Hajiya ta ce in ce ma ka ta wuce airport".
Ya san duk cikin kishi ya sa ta ke wannan shirmen, amma ba zai biye mata ba.
A ranar da Zaytunah ta tafi Lagos da Yamma Nadia ta shigo ƙasar dan fara shirye-shiryen biki. Koda ta zo Sajid bai dawo ba ta tambayi Saratu ina matar gidan?. Saratu ta sanar da ita Zaytunah ta yi tafiya yau da safen nan. Nadia ta taɓe ba ki ta ce " Zaytunah dai ba za ta chanja ba da shegen yawon gantali".
Da Sajid ya dawo bayan sun taɓa hira sannan ya kai ta ɗakin da Ziha za ta zauna. Gaskiya an kashe kuɗi kam dan kaya ne aka zuba ma su tsada.
" yanzu Ya Saj ya za ayi ka bar Zaytunah ta yi tafiya ana saura kwana kaɗan biki"
"Auta, idan ban bar ta ba wani tashin hankalin za ta fara. A halin yanzu kuma I need peace"
" ba wani, kai dai tun asali ka sakaltata, shi ya sa ta ke abinda ta ga dama ba tareda tsoro ba"
"Kwantar da hankalin ki Auta, ba daɗewa za ta yi ba"
" ko za ta mutu ma dai, aure kam sai an yi"
Sajid ya yi dariya ya ce " Auta ki tausaya mata ma na, she's your cousin fah"
" cousin my foot" ta faɗa tana buɗe ƙofar banɗakin da ke cikin ɗakin, ta ce masa " Yaya ɗaki ya yi Masha Allah "
***
......LAGOS....
Kai tsaye gidan Saudah Zaytunah ta wuce hankalin ta kwance, dan zuciyar ta na ba ta akwai nasara acikin abinda ta sa gaba.
Koda ta isa dama Saudar ita ta ke jira ko zama ba ta yi ba su ka wuce wajen Malam (kamar yadda Saudah ke kiransa).
Zaytunah ta yi mamakin ganin gidan da su ka tsaya, ita da take jira ta ga sun kutsa daji, sun isa gidan bukka.
"Saudah nan ne kuwa?"
" nan ne mana, Malam ai ɗan zamani ne ba irin ƙananun masu maganin ƙauye ba "
" I'm just surprise" Zaytunah ta ce yayinda Saudah ta buɗe ƙofa ta fita, itama ta fito.
Sai da aka musu iso sannan suka shiga falon Malam.
Sai da su ka gaisa sannan Saudah ta ce "Malam ga ƙawata Zaytunah da na maka maganarta jiya"
Malam, Bahaushe ne sarai sai dai jimawa da ya yi a Lagos yana jin yarabanci sosai. So walau hausa ko yoruba, kai ko turanci ka iya Malam da shi zai ma ka magana.
Malam ya ɗan kalli Zaytunah na wasu seconds sannan ya ce " an riga an ɗaura auren su, sai dai ki yi ƙoƙarin raba auren"
Zaytunah cikin rashin fahimta ta ce " ban gane ba, auren fah saura kwana goma ko tara ne ma. Amma ba a ɗaura auren ba"
Malam ya yi ƙaramar dariya sannan ya ce " auren su tabbatacciya ce, babu wani mahaluki da zai sa a fasa auren nan, sai dai idan an ɗaura ayi ƙoƙarin rabawa"
Zaytunah a firgita ta ce " Malam what are you saying? This is gibberish, ta ya za a yi kace auren My Sajid da yarinyar nan tabbatacciya ce, it will never happen, i will never allow it to happen"
Malam ya kalli Saudah ya ce " kin san aiki na ba zamba a ciki, kuma ba yau na fara mi ki aiki ba. Ki fahimtar da ita haka idan ta ƙi kuma ku tashi ku bar waje na"
Saudah tace " a'a Malam ba za ayi haka ba, yanzu tunda ka ce za ayi auren ni na yarda za ayi. Amma mi ye mafita? Ma'ana ta ya za mu koreta a gidan?"
" Saudah ki tashi mu tafi wannan bai san aikinsa ba, he's just beating around the bush"
Saudah ta harareta sannan ta ce "Malam bari mu je zuwa gobe zamu dawo bayan ta nitsu"
Malam ya ce " ya kamata kam"
Tunda suka fita Zaytunah ke ta kwarwa wai ita sam wannan malamin bai san aikinsa ba. Saudah na ƙoƙarin fahimtar da ita wannan mutumin harta 'yan siyasa yana yiwa aiki amma ta ka sa fahimta. Ƙarshe Saudah ta ji haushi ta ce "to ke kika sani, ni dai na yarda Malam gaskiya ya faɗa".
Lokacin da suka koma gida Saudah share Zaytunah ta yi.
Ƙarshe Zaytunah da kanta ta zo ta sameta a kitchen.
"Saudah ba wani malamin da kika sani sai wannan kawai?"
" Zaytunah ki yarda da maganar shi dan gaskiya ya faɗa, ni ɗin nan zuwa na garin nan sai da na jarraba waje biyu ban samu biyan buƙata ba sai akan wannan mutumin. Kuma tunda ya min aiki na kawo mutane sun fi goma da yai wa aiki kuma suka ji daɗin aikinsa, dan haka ke ma idan kika kwantar da hankalin ki za ki ga kin yi nasara"
" haba Saudah mi ye amfanin zuwa na idan har Malam zai ce min auren My Sajid ya tabbata da wata. Kenan ni Zaytunah dole sai na zauna da kishiya. Allah ya tsare, ni kishiya ko ta 30 seconds ne bana so "
" tsaya ki ji Zaytunah, ba fa ni ce matar Hassan ta farko ba, shekararsa shida da uwargidansa ya auro ni, na shigo na fara neman hanyar da zan fitar da ita daga gidan. Sau biyu ina zuwa ana min aiki amma duk shiru ne, su ka ci kuɗina a banza. Wannan Malamin da kika raina shi ne ya min aiki a kanta. Ba shiri Hassan ya ma ta saki uku, kin ga har yau an min katanga da ita ba za ta sake zuwa ko ƙofar gidan nan ba balle ta nemi dawowa. Bayan nan ya min padlock na sa a gidana as long as that padlock is there Hassan ba zai taɓa ƙara aure ba har abada. So relax ke ma zai mi ki aikin da za ki jinjina ma sa"
" Saudah i'm counting on you, kin san just the thought of my Sajid sleeping with that witch is killing me, idan auren bai rabu ba zan iya mutuwa, Saudah"
"Ba dai ke ki mutu ba Zaytunah sai dai ita ta mutu".....
din dish din dish.....
©AzizatHamza2019