54
by @azizat
*MUTUM.....Mugu ne*
54
Tun daren Jumu'ah Zaytunah ta ɓarke da gudawa ba wai dan ta ci wani abu da ya birgita mata ciki bane a'a. Tsoro da fargaba ne ya sa haka. Mommy da wasu 'yanuwan Sajid mata da ba su je Ilorin ba su ke tare da ita a gidan, da gidan zai fi haka zafi.
Mommy da Zaytunah suna zaune a ɗaki Faridah 'yar ƙanwar Sajid ta shigo ɗauke da waya a hannunta tana faɗin "Mommy ki ga Anty Nadia ta turo clip ɗin wajen biki they look adorable"
Mommy ta ce "Faridah je ki zan zo in kalla anjima".
Zaytunah da ke kwance ta ce " ke! kawo na gani, ai Nadia ta turo ne dan na gani" ta faɗa tana tashi zaune.
" Zaytunah you don't have to see it, kar ki ɗagawa kanki hankali" Mommy ta faɗa tana ƙeftawa Faridah ido akan ta fita da wayar. Sai dai Faridah yarinya ce, ba za ta wuce 11yrs ba, ga shi irin ajebon nan ne, ba ta gane nufin eye gesture da Mommy ke ma ta ba.
Zaytunah ta ƙarɓi wayar ta kunna video'n. Wajen da Sajid ya ɗaga gyalen Ziha da kuma signing ɗin certificate da su ka yi ta gani
Faridah ta ce "Anty akwai wasu video ɗin barin kunna miki"
Zaytunah ta yi wurgi da wayar " dan karuwanci da kafirci da suke ji da shi, agaban ta aka ɗaura auren kaman auren church. This girl is really shameless"
Faridah ta yi kan wayanta tana kuka.
Mommy ta ce " ai gashi kin ga abinda ya dame ki"
" Mommy ki duba abin nan fah, ta ya Sajid zai yi wannan rashin kunyar kamar ba jinin fulani ba. I'm sure magani suka masa"
Mommy ta girgiza kai ta ce " ke kika san wannan, ki tashi ki sha magani ki yi wanka ki shirya kafin a kawo Amarya" ba ta jira mi za ta ce ba ta wuce wajen faridah da ke faman haɗa waya, ta ja ta su ka fita daga ɗakin.
Gaba ɗaya haushin Mommy ta ji wai ta tashi ta shirya kafin a kawo Amarya. "Mommy kenan, wannan Amarya ba ta zama ba ce, In Allah ya yarda"...
Dai-dai ana kiran Maghrib masu kawo Amarya suka iso gidan. Tun da su ka shiga compound na gidan 'yanuwan Ziha ke mamakin girman gidan.
Nadia ce ta buɗe wa Amarya ƙofa ta fito da ƙafafuwanta a hankali. Sanye ta ke da lifaya fiskarta a rufe. Nadia ke riƙe da ita har zuwa ƙofar gidan sauran matan da suka fito tarban Amarya sai guɗa suke. Sai da aka zo gab da shiga Alaja Kudirat ta ce a kawo buta da Amarya za ta yi alwala da kuma silifas.
Wata cousin ɗin Nadia ta shiga gidan da sauri. Tare su ka fito da Saratu, Saratu ta ajiyewa Amarya stool aka zaunar da ita, aka ajiye mata buta a gabanta.
Naziha ta zauna a stool ta fara alwala, da ta gama Nadia ta miƙo sabuwar flat room slippers da aka kawo, Ziha ta saka su. Alaja ta ce "Masha Allah, yanzu ta shiga sabuwar rayuwa, daga wannan lokaci ta zama haƙƙin ku"
Da Bismillah Ziha ta shiga cikin gidan Sajid a karo na biyu a rayuwarta, sai dai yanzu ta shigo ne a matsayin matarsa ba 'yar riƙo ba.
Tun da suka shiga falon gidan ake ta guɗa. Nadia ta kai Ziha gaban Ummi ta ce " Ummi ga Amarya mun kawo miki amana"
Ummi ta riƙe hannun Amarya tana ma ta addu'a. Nadia ta shiga yi wa sauran 'yan kawo Amarya bayanin matan da ke wajen. Ta nuna mu su Ummi ta ce ita ke matsayin Mahaifiyar Sajid. Ta nuna Mommyn Zaytunah a matsayin ƙanwar Baban Sajid kuma uwa ga uwargidan Sajid. Aka shiga musayar gaisuwa ana yi ana raha, duk cikinsu Alaja Kudirat ce ke jin Hausa, itama Hausan nata sai a hankali.
Tsinin takalman Zaytunah da ke gugan stair case ya ke ba da wani sauti 'ƙas ƙas ƙas' shi ya janyo hankalin mutanen da ke zaune a falon, hatta su Mommy sai da su ka juyo. Ba ƙaramin shiga Zaytunah ta yi ba, ka ce wa ta amarya ce da ke shirin zuwa dinner. Ta yi kwalliya sosai wanda ya ƙara fidda kyaunta. Abu ɗaya ne za ka lura da shi kasan tana cikin damuwa, yanayin yadda idonta ya yi ciki-ciki fatar ƙasan idon kuma sun kumbura. Hannunta ɗaya na wasa da jelar gashinta da ya sauko zuwa rabin cikinta ɗayan kuma tana shafa sarƙan diamond da Sajid ya ba ta lokacin 10yrs anniversary ɗinsu. Sai da ta ƙarewa kowa kallo sannan ta ƙarasa saukowa cikin taku na ji da kai.
"Waɗannan ne awakin da suka rako bunsuru gidana?" Ta faɗa tana yiwa su Alaja kallon ƙasƙanci.
Gaba ɗaya falon ya yi tsit dan wanda su ka ji me ta ce mamakin maganarta su ke yi. Allah dai ya sa cikin 'yan uwan Ziha Alaja Kudirat ce kaɗai ke jin Hausa.
"Banga bunsurun da aka kawo gidan nan ba, amma kuma ina jin warinta, dan Allah tana ina?"
Ta sa hannu ta fara toshe hanci alamar wari ta ke ji.
" kin san Allah, Zaytunah ki ja bakin ki ki yi shiru, dan Wallahi zan mi ki rashin mutunci a nan wajen" Nadia ta faɗa tana nuna Zaytunah da yatsa.
Mommy ta yi saurin cewa da fillanci "Nadia dan Allah ki yi wa Amarya jagora zuwa ɗakinta"
Nadia ta kama hannun Ziha da tun maganar Zaytunah na farko ta fara hawaye, suka haura sama, sauran 'yan rakiya na bin su a baya.
Har kan gado ta zaunar da Amarya sannan ta ce mu su tana zuwa.
Fitanta ke da wuya Alaja ta fara ƙorafin gaskiya Zaytunah ba ta da mutunci wai su ta ke kira awakai.
Mama ta ce ai ita tun ɗan zaman da Zaytunah ta yi da su a Lagos ta gane halin ta na rashin daraja talaka. Sauran kam hankalin su ya tafi kan kyaun ɗaki da irin kayan da aka zuba a ciki. Sai taɓe-taɓe suke na ƙauyanci.
Nadia ta koma ƙasa ta samu Mommy na yiwa Zaytunah faɗa ta ce " Lah mommy ki bar ta, duk abinda za ta yi yanzu ihu ne a bayan hari. Naziha dai matsayi ɗaya gare su a gidan nan. Idan ta kasa haƙurin zama da ita sai ta bar mata gidan gaba ɗaya"
Zaytunah ta hayayyaƙota da masifah ita kuwa ta shige wani ɗaki da ke kusa da na Saratu...
*
Ƙarfe takwas saura na dare mai kwalliya ta gama tsarawa Ziha kwalliya, ba ƙaramin kyau ta yi ba. Nadia ta shigo ɗauke da kayan da za ta saka acikin ledarsa. Tun kafin a warware kayan sauran cousins ɗin Ziha ke yaba kyaun gown ɗin.
"This gown is designed by the famous Indian designer Sabyasachi Mukerji, it is design specially for you Naziha" 'yanmatan suka sa tafi suna yaba kyaun gown ɗin. Nadia ce ta taimaka mata ta sa gown ɗin dan idan aka bar ta ba iya sa shi za ta yi ba.
Yadda suka fito kowa ya sha kwalliya abin gwanin sha'awa. Duk da 'yanuwan Ziha kaɗan ne a wajen amma kana ganin 'yan uwan Sajid ka san suna murna da wannan biki. Dama Nadia ta ce ƙanne da cousins ɗin Sajid ne suka haɗa wannan Dinner ɗin.
Nadia ce ta sa ta a motar da zai kaisu wajen dinner. ta leƙa cikin motar ta ce "Ya Saj a yi a hankali dan Allah kar a ɓata kwalliyar kafin a isa" ɗan dariya ya yi yace mata kar ta damu.
Ziha na shiga motar ƙanshin jikinta ya buge shi. Ya jima ya na kallonta bai ce komai ba. He can't believe Ziharsa ce wannan, she looked more matured and more beautiful. Gaba ɗaya ta tafi da shi. Sai da motar su ta tashi sannan ya yi firgigit ya kamo hannunta ɗaya ya kissing ya ce " I love you Naziha" sai a lokacin ta ɗago ta kalle shi ta yi murmushi lokaci guda kuma kunyarsa ya sauka mata.......
Dinner ya yi, dan ya samu halartar manyan mutane da dama. Cikin 'yanuwan Ziha maza da su ka zo har da AbdulBasiɗ, Daddy, Gbenga da Timothy da sauran 'yan ganin ƙwaƙwaf.
AbdulBar bai zo ba saboda shi dama Ustaz ne. An ci an sha kuma an kashe naira abin sai wanda ya gani kawai. Ba a tashi daga wajen Dinner ba sai ƙarfe shaɗaya na dare.
Ƙarfe sha biyu da minti arba'in na dare Nadia ta fito daga ɗakin Ziha ta wuce falon Sajid. A zaune ta same shi yana danna waya. " Yaya na shirya maka ita, duk da ma dai yau kam sai kwanan haƙuri"
"na gode Auta, you make this wedding a memorable one. Allah ya biya ki da Aljannah"
"everything for you babban Yaya, sai da safe"....
Wutan falon ya kashe ya fito, ɗakin Zaytunah ya fara zuwa ya ƙwanƙwasa amma ba a buɗe ba ya haƙura ya wuce ɗakin Amarya.
A kan gado ta ke zaune an lulluɓe ta. Da sallama ya shigo ta amsa masa ciki-ciki. Ya zauna kusa da ita ya sa hannu ya ɗaga lulluɓin. " na san kin gaji ko, yi haƙuri ban ma san an shirya dinner ba sai yau da safe"
" its Ok" ta faɗa a hankali still bata ɗago ta kalle shi ba.
"Kin ci abin ci?"
Ta gyaɗa ma sa kai.
" na san kin gaji, kwanta na mi ki tausa" da farko ta noƙe daga baya kuma ta kwanta ruf da ciki. A hankali ya fara mata tausa kaɗan-kaɗan. Bai fi minti goma ba bacci ya sace ta dama a gajiye ta ke. Sai da ya gyara mata kwanciyar ta sannan ya shiga banɗaki ya yi alwala ya zo ya yi nafila yana godiya ga ubangijin da ya bashi auren Ziha. Ya roƙi Allah ya ba shi ikon aiwatar da adalci tsakanin matansa biyu ya kuma sa wa gidan shi zaman lafiya. Da ya gama addu'o'i sai ya hau gadon ya jawo Ziha jikinsa ya tofa mata addu'a sannan ya kashe wuta. Yana shafa gashin Ziha a hankali har shima baccin gajiya ya tafi da shi.
**
Washegari kasancewar ya san bata sallah shi yasa da ya tashi da asuba bai tashe ta ba, ya yi alwala ya wuce masallaci, har ya dawo kuwa ba ta tashi ba. Yana zaune kan sallaya yana karatun ƙur'ani ta tashi.
A hankali ta sauko daga kan gado tana tafiya a hankali dan kar ya lura da ita. Ta shiga banɗaki ta yi fitsari sannan ta haɗawa kanta ruwan zafi ta fara wanka. Daga bakin ƙofa ta ji ya ce "Ife, barin je na shirya saboda akwai baƙi ma su tafiya yau, zan je mu yi sallama"
Murya ƙasa-ƙasa ta ce "to"
Tana fitowa daga wanka ta shirya a gurguje, cikin akwatin kayan da ta zo da su ta ɗauko abaya kalar light blue ta saka. Tana ƙoƙarin gyara gado Nadia ta shigo.
Har ƙasa ta tsugunna ta gaishe ta. Nadia ta ɗaga ta ta ce " ni bana son gaisuwan ki na yarabawan nan, I'm now your sister and your friend, we should be free with each other"
Ziha ta yi murmushi ta ce " na gode Anty"
" mutanen Ilorin sun ce yanzu da safe za su tafi, suna kan shiryawa kenan, a kawo mi ki breakfast nan ko za ki sauka ku yi tare?"
" zan yi da su" ta amsa a taƙaice....
Tare su ka karya da 'yanuwanta, su na ci ana hira. daga gidansu Zaytunah ma aka kawo abincin. Kuma abinci ne na gani na faɗa dan farfesun kan rago ne, da jollof rice da pepper chicken, sai masa da miyar taushe da ya ji kayan ciki. Sai kayan tea da aka ajiye musu.
Bayan sun karya Alaja ta sake mata nasiha musamman akan haƙurin zama da Zaytunah.
Hijab ta je ɗauka a ɗaki Nadia ta biyo ta, ta miƙa mata kuɗi a envelop ta ce "ga shi Yaya ya ce a ba wa baƙi su sha ruwa a hanya"
Ta amsa tana zuba godiya.
Sun raka su har bakin mota bayan an haɗa su da kayan biki da souveniers da aka raba wajen dinner. Ziha ta ƙanƙame Alaja tana kuka lokacin da za su tafi, ta san yanzu kam ita da 'yanuwanta sai an ɗau lokaci.
Bayan sun tafi sai ta ga gidan ya yi shiru ban da masu aiki da ke ta ƙoƙarin gyare- gyare bata ga alamar akwai wasu mutane a gidan ba. Ta tambayi Saratu ina sauran baƙi. Saratu ta ce ai 'yanuwanta kaɗai suka kwana a gidan, 'yanuwan Sajid gidan su Zaytunah suka kwana wasu kuma a hotel....
Da dare Sajid ya ɗauke ta suka je gidan su Zaytunah gaisuwa, saboda washe gari Alhaji da Ummi za su wuce Jalingo. Anan Alhaji ya haɗa ta da Zaytunah ya musu nasiha.
Da suka gama gaisuwa sai suka wuce gidansu. Ranar ma tare suka kwana hankali kwance cikin shauƙin junansu. Ziha ta rasa dalilin da ya sa Zaytunah ba ta kwana a gidan ba, ba ta kuma tambaya ba saboda ba ta son shiga tsakaninsu.
Ranar litinin da yamma Zaytunah ta dawo gidan. Ziha na ɗaki ta jiyo muryan ta su na magana da Nadia.
" na ɗauka ai kin ba su hutun honeymoon na wata uku ne, kafin ki dawo"
Zaytunah ta yi tsaki ta ce " ashsha, kin san dai albarkacin Daddy da Alhaji kika ci da wallahi sai na hargitsa wajen dinner nan, su kan su wanda su ka kawo Amaryar da sai sun ƙwammaci ba su zo Abuja ba"
Nadia ta ce " ke kika san wannan, anyi kuma an gama lafiya, 'yan baƙin ciki sai su mutu"
Zaytunah ta yi ƙaramar dariya ta ce "Nadia kenan, za ki sha mamaki".
"Ke dai za ki ga abin mamaki matuƙar ba ki chanja halin ki ba"
***
Duk wasu haɗe-haɗen kayan gyara da Nadia ta ba wa Ziha sai da ta yi mata bayanin yadda za ta yi amfani da su. Ziha kam ba abinda za ta iya biyan Nadia da shi sai godiya kawai, dan Nadia ƙanwar miji ce ta ƙwarai.
Safiyar Talata Sajid ya kai Nadia airport ta wuce nata gidan mijin.
Naziha na zaune a ɗaki tana duba kayan da Nadia ta bata, ta ji an buɗe ƙofa. Ta bi ƙofan da ido. Ganin Zaytunah ke shigowa sai jikinta ya fara rawa.
Zaytunah ta ƙarewa ɗakin kallo sannan ta kalleta a walaƙance ta ce " I pity you Naziha, domin duk wannan daula da kike gani ba ɗaurewa zai yi ba. Your days are numbered in this house. Ki ci, ki sha kafin ki rasa ci da shan ki nan ba da jimawa ba"
Tana gama faɗin haka ta fita. Ziha ƙwaƙwƙwaran numfashi ba ta yi ba sai da Zaytunah ta bar ɗakin.
Har lokacin da Sajid ya dawo hankalin ta bai kwanta ba domin maganganun Zaytunah sun bata tsoro.
Da dare Sajid ya haɗata da Zaytunah ya musu nasiha, ba Sajid kaɗai ba har Ziha sun yi mamaki da Zaytunah ba ta nuna gardama ko ta tankawa Sajid ba a maganar da ya ke yi. Shiru ta yi har ya gama sannan ta tashi ta ce "sai da safen ku" ta wuce nata ɗakin.
Yau kan hutu ya ƙare ta riga ta yi wankan sallah tun da safe. Dan haka tun da ta yi wanka ta yi sallar Isha, ta sa rigar baccin da Sajid ya taɓa kawo ma ta lokacin tana Ilorin. Ta sa babban hijab a kai ta zauna akan sallaya tana azkar.
Ƙarfe tara da rabi na dare Sajid ya shigo ɗauke da manyan ledodi biyu a hannunsa. Ya ajiye su kan stool da ke wajen dressing mirrow.
Sanye ya ke da farar jallabiya, jikinsa na fitar da ƙanshi mai sanyaya zuciya.
Ya kissing goshin Ziha ya ce " mu yi nafila ko"
Ziha ta miƙe tsaye tana raurau da ido. Dan ta san yau kan ba wani uzuri.
Sai da suka yi sallah sannan ya kawo mu su kazar suka fara ci, da hannunsa yai ta feeding ɗinta har ta ƙoshi. Da suka gama ya tattara wajen, suka shiga banɗaki su ka yi brush.
Tuni ya yi cilli da hijab ɗin da ta saka, a hankali ya ke kallon ko wani saƙo na jikinta. Ya jawota jikinsa, a hankali yana shafa bayanta zuwa hips ɗinta. Daga nan ya ɗauke ta cak sai kan gado. Ziha ta yi lamo jikinsa tana amsa saƙonnin da Uncle Saj ke tura mata. A hankali ya fara kissing ɗinta tun daga ƙafa har ya kai goshinta. Ya haɗe bakinsu while he stylishly turn off the light. Deep kiss ɗin da su ka jima suna yi sai da numfashinta ya kusa ɗaukewa, daga nan ya fara kissing wuyanta zuwa saman nononta.
Yau ta zama cikakkiyar mace, Uncle Saj bai sarara mata ba duk da kukan da ta rinƙa yi. Tun tana jin sorry da ya ke ta maimata mata har ta daina gane mi ya ke faɗa. Yau dai rana ce da ba za ta taɓa mantawa ba a rayuwarta.
Da asuba shi ya taimaka mata, ta gasa jikinta dan tafiyar kirki ta kasa. Sallar Asuba ma a zaune ta yi. Bayan sun yi azkar sun gama ya damƙa mata tukuicin makullin mota. Ka sa cewa komai ta yi, ta shige jikinsa tana hawayen farin ciki.
Zaytunah kam zazzaɓi mai zafi ne ya rufeta tun da daddare, tunanin Sajid na chan tareda Ziha ya sa ta cikin tashin hankali daga ƙarshe zazzaɓi ya rufeta. Ƙarfe bakwai Sajid ya shigo dubata bayan ya bar Ziha a ɗaki tana baccin gajiya. Yadda ta ke rawan sanyi har da kakkarwa a kan gado ya sa yai kanta da sauri yana kiran sunanta.
©AzizatHamza2019