🌍 DUNIYA MAKARANTA!!🥀

Eight

by @nanabmb

🌍DUNIYA MAKARANTA!!🥀


Arewabook

https://arewabooks.com/u/nanabmb

My novels


RABON KWADO...!!


JARABTAR MU!!


RABO!!


AND NOW


DUNIYA MAKARANTA!!


Page Eight


Kano


Ta kware a makirci Meenal shiyasa na soma yashe baki ta tari Mamee din tata tana cewa. " Mamee! Har kun gama shirya abincin ne? Nima na kasa zaban kayan da zansa Mamee duk na rasa kayan sawa ma yau din?" Kallon tuhuma sosai auntie Lubna keyi mata don duk duniya tafi kowa sanin diyar tata amma ta banga ren makircin ta kam batada ko labari, " dawa kike waya ne Meenal? Ina jiyo maganar ki kafin na shigo banason rigima Meenal! Se yaushe zaki dena daukar magana ne? Sam bakyajin magana kina girma amma lamarin ki sake tabar barewa yake! Kalla wai duka uban wan nan suturun da kika tasa a gaba amma kina cemin kin rasa kayan sawa! Meye yake damun kine?" " Allah mummy muje ki gani kayan nawa da gaske nake miki duka wasu ba guga ma!" Yadda tayi maganar ne a shagwar gwabe yasa auntie Lubna wucewa gaban wardrobe din tana cewa. " Kawai kice kin har gitse kayan ki sunyi sequencing malama amma ba wai kin rasa na sawaba, kuma sekin fada min dawa kike rigima a waya!" Duk kayan da auntie Lubna ta dauko Meenal taki su karshe seta sa mata kuka ma ita setaje ta siyo wasu kayan, ay kuwa rai a bace ta soma cewa. " Meenal halin nan nakifa shine yake hadani dake Koh! Kalli yadda nazo na sami wardrobe dinki! Idan an Shekara gyara miki kaya sekin lalata! Kuma abin bakin ciki keba karama ba amma bakisan ya kamata ba! To ni banida lokacin cigaba da duba miki kaya! Babu time enough daza kije yo wani siyayya tunda safe bakisan da siyayya ba se yanzu da kikaga zamu tagi airport! To babu inda zaki! Kuma ki tabbatar kafin na dawo kin gyara wardrobe din nan daga yau na dena miki gyaran ta tunda baki da nutsuwa dazaki killata suturan ki, kika bata lokaci kuma wlh tafiya zamuyi mu barki a gidan nan Allah kuma yasa na dawo naga baki abinda na sakiba kiga abinda zan miki yau a gidan nan!" Cikin fushi auntie Lubna ta fita tana jiyo fadawar ta kan bed tasa kuka bayan ta gama hararar kayan tana tura baki, birgima take a bed din saboda an mata fada Mamee ta bata mamaki! Yadda take kukan ne yasa auntie Lubna yin murmushi ta karasa ficewa taname cewa. " Allah ya shirya minke auta!"


Uku saura su Bilal suka sauka a birnin tarayya Abuja, sede auntie Lubna da Mahmoud ne kadai suka taro su daga airport, Meenal kofan tama rufe shi tayi saboda sun bata da Mamee din tata Bilal da Mahmoud tamkar zas hadiye junan su dan farin ciki na ganin juna shekara 5 ayba wasaba, Mahmoud da Bilal suna matukar yanayi Sosai don kana ganin su ma ko ba a gayama ba zaka san su yan uwane, yaji dadi sosai Bilal da a ba taho da Meenal ba shiyasa ya saki jiki sukai ta shargallen su da Mahmoud wasa da dariya kamar bashiba, don in tana gu ko dariyar sa bayason Meenal ta gani bare ta sake raina shi!, Koda suka isa gidan, again Daddy bega Meenal ba shiyasa ya kasa hakuri yace.


" Yaya waini kam banga uwar gida naba! Nayi kawai cin harna kasa hakuri!"


Mummy jitai kamar taje ta rufe Daddy da duka don bakin cikin tambayar Meenal da yay, ita kam auntie Lubna murmushi tayi tace.


"Uwar gidan ka tana nan lpy! Yau tsiya taku takeji ne tunda ta tashi dama! Ko shirya wama takiyi saboda rigima dakin ma rufeshi tayi danaje!"


" OH wan nan yarinya! Har mamaki take bani wlh! Meenal hali na nan bazata sauya shiba, na zaci idan ta girma abin ze ragu ashe ba haka bane sema dai ya karu!"


Cikin mamaki Mahmoud yay maganar yana murmushi shima, shi kuwa Bilal tabe baki yay yace. " Kaji ka bro! Ina girma yake a gun waccan? Ayni bangan shiba gaskiya!" Mummy kuwa shiru tayi da Sara tasan Daddy seyay magana ilai kuwa yayi dariyar su ta manya yace. " Aww watakam ka raina kan wallin taka kenan Bilal yayi! Sannu rikakke! Meenal kuruciya ce kawai take damun ta kodan ku naku lokacin ya wuce!"


" Ah!! To Wazece! Banten uwar sarki ya jirge! Ay Bilal baya tuna baya ga dukkan alamu shiyasa yake addabar rayuwar autata yanzu!"


Auntie Lubna tayi maganar ne da biyu shiyasa Bilal yay murmushin haka Mahmoud yace. " Haba Mamee! Ay halin wan nan rigimam man diyar taki se de ita wlh kaf cikin mu bame hali irin nata!"



" Ahhhhhhhhh!! Yeeeeassssssss! OH my sweet elder!!!!" Meenal ce ta soma ihu tana yowa dawnstairs daga ita se t-shirt da monkey jacket tama gashin ta tufkar two babies, cikin matukar farin ciki ta isa gaban Mahmoud din tana cewa. " Ya Mahmoud yaushe ka siya motan ashe surprise dina kakeso kayi! Jiyafa na tambaye ka yaushe zaka siya mota kace ba yanzu ba! Wayyo Allah na, ya Mahmoud ta sumar dani motar gaskiya gaskiya ya Mahmoud nice zan fara danawa!"


Sam Mahmoud besan ina maganar ta ta dosaba, haka duka mutanen dakin shiyasa auntie Lubna tace. " Wai auta akan waca motar kika rude hakane?" " Mummy ba jiya ya Mahmoud yace min ba yanzu ze siya motaba! Ashe surprise dinmu zeyi ina gani ta window aka kawo motar naga me gadi ya amsa key wlh ya Mahmoud nasan takace motar! Duk tafi motar gidan nan kyau!" Sosai auntie Lubna tasoma yiwa Mahmoud kallon tuhuma, koda yaga kallon da take masa seya tabe baki yana daga kafadun sa alamun besan komai bah, seta jin jina masa kai, ta mike tana cewa. " To muje de na gani wai Meenal waca mota kika ganine? Kode baki akayi a gidan kar kisa muje muji kunya fah!" Su duka yuuu suka fita don ganin mota, mota kuwa ta keru black se sheki take tana daukar ido Daddy ne yay murmushi ya jawo Bilal saitin sa yana cewa. " Bilal kode wan ne surprise dinne dazaka ma Mahmoud ne? Cikin jin dadi Bilal ya daga Kai ya wuce gurin gate man ya amso key din motar ya kawowa Mahmoud din yana cewa.


" Fatan alkhairi masoyi na! Wan nan karamar kyauta ce daga gareni, ina tayaka murnar dawowa kasar ka ta gado, ka dawo cikin family dinka me cike da tarin albarkatu da kuma rayuwar farin ciki da jin dadi!"


Ay gaba dayan su baki suka saki kowa yana kallon Bilal haka Mahmoud din ko key din ya kasa amsa, shiyasa ya kamo hannun sa Bilal din ya samai key din tukunna yay hugging dinsa yadan bubbuga bayan sa tukunna ya sakeshi yana cewa. " Oya Bismillah a fara warning dinta tun daga yanzu!" Saboda tsananin farin ciki Mahmoud ya kasa magana smiles kuwa ya kasa tsaida shi juya key din kawai yake a hannun sa yana kallo, Bilal ya matsa kusa da auntie Lubna yana cewa. " Kalla kiga auntie! Irin wan nan murmushi shine abinda kullum nakeso gani a fuskan masoyi na! Farin ciki da soyayya shine rayuwa auntie! Ku din nan duka akan wan nan kuka gina rayuwar mu kuma kuka haifo mu! Shiyasa muke daraja soyayya da farin ciki da kuma kwanciyan hankali!" Hawayen farin ciki auntie Lubna ta fara ta jawoshi ta rungume shi cikin farin ciki tana sa masa albarka haka Daddy ba karamin jin dadi yay ba da abinda Bilal din yay, yana kuma sake musu Addu'ah Allah ya kara dankon zumunci a tsakanin su da kaunar juna, itama mummy sosai tayi Addu'ah ta nuna farin cikin ta akan hakan, Meenal kuwa tunda taga wanda ya siya motan salin alin ta silale ta koma daki batare da kowa ya kula da ita bama, haushi jitake kamar ta dinga dukan kanta saboda ta bada kanta a gurin Bilal wai 😂 se cije baki take kamar ta hadiye zuciya don takaici, sedaga baya kuma kome ta tuna, aiseta buga wani uban tsalle ta fada kan bed tana dariya, to daga part din su Nadiya ma suna ganin yadda Mahmoud ke zan zana motan a parking space sunata nasu tsurkun har su Mahmoud suka gama shagalin su suka koma ciki, Mahmoud nata santin mota yana cewa yama nayi zasu shiga gari gurin abokan sa dama tunda ya dawo be fitaba, yaukam akwai shagali yace, Dady kuwa da bega Meenal bane yace.

" Wai ina auta ne! Itada tafi kowa santin mota ko shiga ma batayi ba" " am here Daddy!" Se suka juya suna kallon ta taga dama ta shirya tayi light makeup Masha Allah kawai za ce, Daddy yana ta zolayan ta har suka isa dining room don yin lunching Meenal seda ta bari Bilal ya zauna ne tayi maza taje ta zauna a kujeran dake gefen sa, Sara ta sake kuluwa don tahowa tayi da niyyar zama kusa da shidin Meenal ta rigata, zatayi magana ne mummy ta nuna mata kusa da ita inda ta zauna dole ta hadiya bakin ciki ta taje kusa da mummy ta zauna Mahmoud ya kula da komai, shiyasa tun daga nan yasan Sara nada kishi dukda yau ya fara ganin ta sede yaji labarin ta gurin Bilal, ita kuwa Meenal dama da biyu ta zauna duk dan ta kona masa rai ta zauna kusa dashi kuma be tanka taba bare yasan ma da ita a gurin sede wani azabab ben kamshi ma daya ziyar ci hancin sa ya wuce ta heart dinsa har seda ya lumshe eyes dinsa ba tareda yasan yay hakan bama, duk duniya kamshi shine abinda yake saurin daga masa hankali, haka suka gama cin abincin su suna fira sama sama.


Wajan 6 na yamma Bilal da Mahmoud suka shiga gari, wanda basu suka dawoba se wajan 10 yadan Gota ma, kuma da suka dawo aka bude sabon dandalin fira, atakaice dai se wajan 12 kowa ya nemi makwanci dake Daddy su Meenal ma anan gurin auntie Lubna yake harda shi akasha fira kafin suje su kwanta abinsu, hankali kwance Bilal ya shiga room dinsa ya soma cire kaya seda ya rage daga shi se boxes ya wuce bathroom yana dan lumshe idanun sa saboda dan ciwon da kansa ya masa ka idane dama idan ya fiya surutu se kansa yay ciwo, be kawo komai a ransa bare ya lura da wani abu ba ya kunna shower ya zame boxes din yaje ya tsaya ruwan na zuba a tsakiyan kansa zuwa jikin sa kusan mintu 4 tukunna ya bude idanun sa zeyi wanka ya bar bayin ne yaji wani irin matsiyacin yaji ya shiga a cikin eyes dinsa a matukar kideme ya maida eyes din ya rufe amma ina ya kasa jurewa kokari bude idon yay amma azaba ya hanashi shiyasa ya soma laluben bango haryaje gun sink ya kunna fanfo, ya tara hannun sa seda ya cika da ruwa tukunna ya cije ya bude eyes din ya watsa ruwan ya ilahil alamin!! Wani irin zabura Bilal yay saboda masifan dayaji tafi ta farko jikin sa nan danan ya soma bari na azaba Addu'ah kuwa duk wadda ya kama baya iya karasa ta saboda firgice da kuma wani irin tirirn masifa dayake ji a jikin sa kasance wa yana iya fahimta dakin shiyasa ya soma laluba hannun sa a wall din dakin harya isa gurin fridge ya sunkuya ya bude ya dauko gora besan ta ruwa bace kota lemu, shidai koma meye sauki yakeson samu a idanun sa, hannu ya sake cikawa da ruwan ya bude idanun sa ya watsa ruwan ya kuwa saki karar masifa yay wurgi da goran don itama yajin ne a cikin ta, ya soma sosa jiki ta ko ina yana shirin yin kuka hawaye kuwa babu control a fuskan sa ya rasa ina ze tsoma rayuwar sa yaji dadi gashi bashi da kaya....✍️