🌍 DUNIYA MAKARANTA!!πŸ₯€Free

ArewaPen original

FantasyFreeOngoing

🌍 DUNIYA MAKARANTA!!πŸ₯€

  • 1views
  • 17chapters
  • 0audios
  • words
  • 0likes
Start reading

Share:

The story

Synopsis

ongoing

No synopsis yet.

About the author

Jarabtar mu

More from @nanabmb

Sample Β· Episode One

🌍DUNIYA MAKARANTA!!πŸ₯€ BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM Assalm Alaikum my fan's barkan mu da sake saduwa a cikin wani sabon novel din nawa, me suna duniya makaranta! Yana kunshe da abubuwan ban mamaki ban tausayi da kuma ban al ajabi, gami da kauna ta hakika, akan zaman take war rayuwa, kamar yadda kuka saba a wan nan time din ma ina son ku cigaba da bibiya ta har karshen labarin domin mu amfana da darrusa dake ciki mu kuma nisha dantu, ina kuma matukar jin dadin Addu'ah an ku a gareni, da kuma yadda kuke kaunar novels dina na gode sosai Allah ya bar kauna πŸ€— Wan nan novel din nawa, is free nayi shine domin masoyi na masu nuna min kauna akoda yaushe, Warning❌ Ban yarda kowa ya juya min book dina a yadda na rubuta ba, ko a maida min shi document bada izini naba gaskiya banaso kowa yayi min ba dai dai ba shida Allah Arewabookhttps://arewabooks.com/u/nanabmb ( MY NOVELS ) RABON KWADO...!! JARABTAR MU!! RABO!! AND NOWDUNIYA MAKARANTA!! PAGE ONEKotu tayi shiru jama ar dake cikin ta sun zubawa alkali ido suna sauraren hukun ci da ze zartar akan wadda ake kara, wanda itama tayi tsuru ne tana jiran taji makoman rayuwar ta kyawawan eyes dinta sunyi matukar yin ja sun kumbure da gani taci kuka harta gode Allah, Seda alkali ya gama duba shedun da suka bayyana akan wadda ake kara tukunna ya dago yana me gyara farin tabarau din dake manne a idanun sa ya soma zartar da hukun ci kamar haka, " Bisa kwakkwaran hujjoji da suka gabata, sun tabbatar da Fatima Abdullahi ta aikata laifin da ake tuhuma ta dashi na yunkurin kashe babbar aminiyar ta kiran Abdul ahad, saboda haka kotu ta yanke mata hukun cin shekara 7 a gidan kaso!" Al kali ya kammala shari a gami da buga guduma, " INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI UN!! shine kawai abinda iyayen Fatima suke nana tawa mahaifiyar ta kuka take riris kamar za a zare mata rai tana cewa. " Kaicon ki Bintu!! Bamuda gata daya rage mana yanzu a duniya Allah ne kadai gatan mu! Ka dubemu da rahama ya Allah!! Ka fidda diyata a cikin tsaka me wuya!" Fatima da aka yankewa hukunci kuwa, hannu biyu tasa ta rufe fuskan ta tana wani irin kuka me tsuma zuciya, Daga ban garen masu karar Fatima din kuwa, hamsha kiyar dattijuwan matace a zaune daga kallo daya zakasan tana wulakan ci da nera, tayi hani an da kudi da hutu harta tada Kai, duba da irin shigan dake jikin tama ya wadatar ba wani karin bayani, hutu da jin dadin kuma ya boye tsufan ta, fata luwai kuwai kamar za a tsungula jini ya fito, daga gefen ta kuwa wata hadaddiyar matashiya budurwa ce fara tar da ita taci uban ado kamar zata gasar kyau, a sanda idanuna kuma yay tozali da guy din dake gefen budurwar se naga kyawun budurwar ya dishashe da duk abinda take takama dashi seda naga ta dena haskawa duba da irin cikar zati da Allah y...

Continue reading free chapter

Contents

Table of contents

Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.

chapters17
premium0

Continue in the ArewaPen app

Unlock offline reading, audio mode, and sync your bookmarks instantly.

Download on the App StoreGet it on Google Play