Nine
by @nanabmb
🌍DUNIYA MAKARANTA!!🥀
Arewabook
https://arewabooks.com/u/nanabmb
My novels
RABON KWADO...!!
JARABTAR MU!!
RABO!!
AND NOW
DUNIYA MAKARANTA!!
Page Nine
A matukar rikice Bilal ya soma tafiya don ya samu koma miye ya suturta al aurar sa ya fice neman agaji soshe soshe yake kamar mahaukaci yana tafiya seji yay yay tuntube da dining table duk yadda yaso ya tsaya Allah be nufaba seda ya fada kan dining table din goshin sa yay mugun buguwa akan dining din dake bana glass bane shiyasa be fashe ba se goshin sa daya tasa saboda buguwa dayay a gurin hannayen sa ji yake kamar yay targade tunda yake be tabajin azaba irin wan nan ba, ko baki ya kasa budewa se dakyar ya iya yazame wa kasa ya kwanta yana jawo numfashi dakyar besan iya adadin time din daya bata a hakaba kamar matacce shi kadai yasan azaban dayake ji a jikin sa to hawayen daketa ambaliya a idanun sane yasashi kokarin bude idanun dakyar amma ina ya kasa bari seda ya sake rufe idanun yay karfin halin mikewa ya nufi bathroom din abinda yakeyi kuwa shine daya dan kyalla idon yaga hanya seya maida idanun ya rufe haka ya karasa bayin ya dauki boxes dinsa daya cire ya maida ya fito a daddafe ya dauki rigar shadda dinsa daya cire ya bude kofar ya fice kamar dan maye haka yake hada hanya jijiyoyin kansa sunyi wani irin rada rada sun fito jikin sa ko ina ciwo yake saboda buguwa dayay da dining goshi ya sintime, makarin benen daze sauko ya rike kam a hannun sa da lalube da lalube harya iso parlour matsanan ciyar azaba yakeji inya bude idanun sa shiyasa yake dan kyalla idon duk da ba ganima yake sosai bah, duka duniyar jiyay ta masa duhu komai jiyay ya tsane shi a rayuwa Meenal ce kawai ke masa zarya a zuciya saboda ya tabbatar da duka itace ta sakashi a cikin wan nan masifan, shiru gidan ya dauka shiyasa ba gun wanda ya nufa don babu ma wanda yakeda kaunar gani a wan nan lokacin shiyasa yaje ya bude kofan daze sadashi da compound, yana budewa wata irin san sanyar iska ta soma kadashi azaba seta karu a skin dinsa kamar masifa ake sake hura masa a jikin sa shiyasa ya saki kofan seda ya gama soshe soshen sa tukunna ya jawo kofan ya rufe ya karasa fita wajen kamar tabbabbe se soshe soshen yakeyi to motsin sa da gate man yajine yasashi fitowa yana waige waige da wani katuwar gora a hannun sa ta bayan wandon sa kuwa pistol ya boye sede yana hangen Bilal yay Turus a tsaye ganin abinda yake kamar mahaukaci se mamaki ya isheshi ya tsaya yana hagen sa kawai, inda ya sake tabbatar da ba lafiya ba gadan gadan Bilal gurin flowers ya nufa zeje ya rufta cikin su shiyasa gate man ya soma rafka salati ya nufi gurin sa yana me ajiye sandar dake hannun sa ay koda yaji muryan sa seya tsaya Bilal yaname hamdala da godewa Allah yana kara sowa ya soma cewa.
" Yallabai lafiya kuwa? Subhanallah! INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI UN!! Menene ya faru dakai haka?"
Cikin kaguwa Bilal ya mika masa hannun sa alamun yanason rikosa muryan sa kamar zeyi kuka ya soma cewa. Don Allah bawan Allah ka temake ni kajee! Ina bukata ruwa me kyau na wanke ido na don Allah!" " Tom shikenan yallabai an gama!" Hannun Bilal din yaja har suka isa bakin fanfo yace masa. " To yallabai Bismillah!" Saurin girgiza masa kai yay yana cewa. " Ka fara duba ruwan tukunna kaga lafiyan sa!" Mamaki ya sake kama me gadi be yana tunanin abinda ya sameshi haka, hannuwan sa biyu yasa ya tari ruwan yasha ya koshi san nan ya matsa yana cewa. " Babu matsala yallabai zaka iya amfani dashi" cikin sauri yaje ya tara kansa a fanfo din ahankali a hankali ya soma bude idanun sa ruwa na shiga dayaga ma tsuguno baze masaba, seyay zaman dirshan a gurin ruwan yana ratsa shi tako ina yana sakin ajiyan zuciya, koda me gadi yaga haka, se tausayin Bilal ya matukar kama sa shiyasa yace. " Yallabai bari na kira Alhaji na sanar dasu halin da kake ciki!" Girgiza masa kai Bilal yay alamun a ah, san nan yace. " Kaje dai ka kira min Mahmoud ai kasan inda yake Koh?" Cikin gamsuwa ya daga masa kai san nan ya nufi hanyar cikin gidan dama mukullayen gidan suna aljihun sa koda ya karasa bakin kofar seya tarar da Meenal tsaye a gaban kofan ta harde hannayen ta cikin rashin mutum ci da rashin kunya take kallon sa a wulakan ce, tunkan ua furta wani abu ta saita mai hanya da hannun ta tana cewa. " Kaga malam iliya!! Ka rufawa kanka asiri kabar kofar gidan nan inba hakaba wlh kasan Halina ko a waya ka kira Daddy ko Mamee sena maka tuggun dase an koreka a gidan nan, korama ta wulakan ci don haka ka tafi ka bani guri wan nan abinda ya shafeni ne da shi, ba abinda ya dameka ka wuce ka tafi dakin ka bance ka kuma temakon saba inba hakaba kuma zakasha mamaki wlh!"
Sarai yasan halin ta donko yan uwanta ma bata kyale ba Meenal bare shi karan kada miya a tsotse a wurgar kala bata subuce masaba ya juya sim sim yabar gurin cikin zuciyan sa kuwa yaname kara tsine mata albarka, yana shirin komawa gurin Bilal dinne ya juya yaga still dai tana tsaye tana kallon sa taga ina zashi, beda zabi dole ya saita hanya ya koma dakin sa don be shirya barin aikin saba yana samun na abinci shida iyalan sa, Bilal tun yana saran jin me gadi da Mahmoud amma shiru yakeji yaci wahala ba kadan ba kafin ya samu abazan dayake ji a idanun sa ya ragu har yana iya bude idanun nashi amma sam baya gani dakyau ya daddafa ya mike tsaye ya zura rigar shadda din nashi dagowa da zeyi yaga an maida kofa an rufe daga cikin gida, shiyasa yadan yi kasake na wasu sakanni tukunna wuce direct ya nufi bakin gate yanaso ya bude, koda me gadi yaji haka seya, fito jiki a sanyaye yana cewa. " Kayi hakuri yallabai! Meenal ce ta hanani shiga ciki!" Batare dayabi takan maganar ba Bilal ya kalle shi yace. " Bude min gate!" Me gadi firgita yay dayaga yadda Idanun Bilal suka koma, kamar jini ai kuwa jikin sa har rawa yake yaje ya bude masa kofar gate din, yana cewa. " Amma yallabai da kayi hakuri gari ya waje yanzu dare ya soma nisa yallabai!" " Bani takalmi!" Shine abinda ya sake gaya masa be sake masa musu ba seya cire sidaddun silifa dinsa ya mika masa jiki a gajiye ya zira takalmin ya fice daga gidan kansa nata digan ruwa,
Meenal kuwa koda ta koma cikin gidan saman da Bilal din yake ta nufa taje gaba daya ta kwashe goran data zubawa ruwan kayan miya da barkono ta maida normal drinks maida fridge din ta rufe san nan taje ta tarar har time din shower na zubda ruwa da kuma fanfo don zuwa lokacin ma ruwan yajin ya gama fita se normal ruwa daketa shatata cikin farin ciki taje ta kashe komai ta fito ta jawo bayin ta rufe, goran dayay cilli da itama taje ta dauke ta gyara gurin tsaf kamar babu abinda ya faru ta fito ta jawo masa dakin ta koma dakin ta rai fess ta hau kan bed tanata tsallen murna tana cewa.
Kai Allah na gode maka plans dina sun tafi yadda nakeso ya Bilal kaima kaji irin azabar daka gana min a gidan ku! Kuma yanzu ma aka fara wasan indai nice Meenalyn Daddy ba a taba ni a zauna lpy!" Seda ta gama tsallen murna dinta tukunna ta kwanta tana maida numfashi cikin dariya take cewa. " Yau ya Bilal ya zama makaho!! Yaji aikin barkono da kayan miya!!" Dariya kamar tababba haka ta dinga mutan gidan kuwa babu wanda yasan abinda yake faruwa.
Bilal yana tafe yadan danna goshin sa a hankali don zafi yakeji sosai Idanun sa har yanzu hawaye yake zubarwa ga sanyin dake kada jikin sa yana shirin sa masa zazzabi, akan titi yake tafiya babu kowa shiru tako ina, kafin yaga mota ya wuce yana jumawa yana tafiyan yadda zuciyan sa yake zafi ne yaji baze iya komawa cikin gidan ba saboda wani irin tukukin bakin ciki dayake ji kamar ze kasheshi koda da wasu mugaye ze hadu gara ya hadu da sudin shiyasa tafiya kawai yake besan inama ze dosaba, Saboda azabab ben zuciyan dayake cinsa ko gidan bayajin zema iya komawa, sede duka wan nan bakar zuciyan bata kai ko inaba ya soma nadamar fitowan sakamakon wata irin halitta dayaga tana tafiya akan titi nan da nan wani irin tsoro ya kama zuciyan sa ya waiga ko ina bega kowa ba se shi kadai, aiseya soma jero Addu'ah gashi baze iya gudu ba, kuma yaga kamar gunsama take niyyar isowa, yade soma fahimtar kamar macen aljanna yay gamo da ita yau, saboda yadda ya hango ta da wasu irin matsatstsun kaya riga da wando kai bako kallabi gashi kanta a sunkuye yake tana tafiya tana layi da tangadi kamar zata kifa, ga hill din dake kafar ta me shegen tsine shine ya sake sawa tai zan gangan a tsaye, Bilal ya rasa dalilin dayasa ya kasa barin gurin dukda tsananin tsoron dayake ji, ko kadan be taba kawo mutum ke tunkaro saba face aljana dayake tunani, sanni a hankali tana tafiya tana hardewa kamar zata fadi ta iso kusa dashi Bilal hankalin sa yana kan kafafun ta daya kafe da idanun sa shiyasa besan ta karaso kusa dashi ba don hankalin sa baya kanta, hannun data rike masa sane ya dawo dashi cikin hayyacin sa ya fisge hannun sa yaja baya yana mata wani irin kallo a tsorace, koda taga haka seta kuma matsoshi kamar zata fada kansa seya yaja baya da sauri yana sake karanto Addu'ah a zuciyan sa yana tunanin wan nan a aljanun ma bugaggace saboda yagan ta a make idanu sun hargitse ya rasa abinda ya hanashi guduwa ya kuma kasa dena kallon ta duba da yadda tana masa wani irin kallo daya kasa tantance na menene, gashi yaga tana shirin bude baki zatayi magana tana kasawa seda tayi yunkuri har sau uku san nan ta iya furta.
" Ridwan!!"
Se kuma tayi shiru nan danan hawaye ya soma zubowa a idanun ta gashi tsaiwama ta gagare ta ta sake fusgo magana dakyar tace. " Ka tsane ni Koh? Ni har yanzu ina matukar kaunar ka! A yanzu ya kamata ka yadda da soyayyar da nake maka tunda Allah ya sake hadani dakai anan! Kuma nasan ba abinda ya kawoka nan sedon ka kashe nine Koh! Ay dama nafiso na mutu a gurin ka ba a son raina na tahoba, nima farkawa nayi naga Daddy ya kawo ni nan bazan iya rayuwar rashin jin dadin nan ba gara ka kashe ni kowama ya huta....tarine ya sarke ta kamar zata mutu dama tunda ta fara maganar tayi kusan minti 15 tana gutsin tsinata gashi hausar tata wani iri baya fahimta sosai gashi tanayi kamar zata rufto masa, kallon ta kawai yake yana yatsina fuska sosai ya fahimta yanzu mutum ce amma mara hankali shiyasa yake kallon ta a kyankyami, yadda ta soma tarin ne a yanzu se idanun ta sukayo waje kamar zasu fito, ay Bilal be ankara ba sejiyay ta feshi masa fuska da wani irin tsinan nan amai me doyin masifa, ta silale kasa ta cigaba dayin aman kamar zata mutu sega jini ya soma fitowa daga baya, idanun Bilal a rintse don bakin ciki ya isheshi ya tabbatar yauba ranar sa arsa bace a duniya, fuskan sa bata taba ganin banu irinna yauba fuskan kamar zeyi kuka ga wani irin amai dake taso masa, cikin tsanar kansa da yakene ya tattaro kasan rigar sa ya goge fuskan nasa san nan ya sake bude eyes dinsa da har a yanzu yana zubar da hawaye, yagan ta a yashe a kasa kamar matatta ko motsi batayi ga jini dukya bata mata baki da fuska harda gaban rigar ta kyam ya tsaya yana kare mata kallo sam batayi kala da mahauka ciyaba buguwa ne kawai tayi da yawa ya bata lokaci sosai a tsaye akan ta yana kallon ta yana tunanin kodaga ina take, yadai tabe baki ya juya ze koma gida don se a yanzu ne yake tunanin inyay gaba besan waze kuma ganiba, tafiya yake amma hankalin sa yana kanta tunanin maganar ta kawai yake magan ganun nata sunata masa yawo a brain dinsa zuciyan sa nata azalzalan sa ya koma kodan yasan wacece ita wai yarasa wan nan masifa yarinya besan taba amma heart dinsa ta isheshi akanta jiyay baze iya jure waba ya sake juyawa ya koma yana jin haushin kansa ma don takaici har koma inda take tana nan a kwance tana cikin wani hali na rai da mutuwa, shiyasa Bilal harya sunkuya ze ciccibe ta se kuma ya fasa har sau uku yay yunkurin yana fasawa se ana hudu dai tukunna ya dauko ta ya sabota a kafadan sa yaji ina baze iya hakan ba tana shirin rinjayar sama su fadi, se kawai ya maida yadan dagota dakyar ya ciccibe ta kamar ya dauko buhun cement seyaji abu ya fadi seya duba ya kalli kasan yaga ashe wayar tace ta fado daga aljihu dole haka ya sake kwantar da ita, ya dauki wayar yasa a tashi aljihun San nan ya ciccibe ta ya soma tafiya yana tunanin mafitar daze samu a cikin wan nan dare ko alamun dan adam babu bare ya nemi temako a kaita asibiti yayi matukar gajiya har yana shirin ajiye ta ya huta ya hango wata mota a gaban su, seyaji karfi ya sake zuwa masa ya hanzar ta ya kara sauri donyaje gun motar dukda yaga alamun babu kowama a motar kuma hakan ne ya kasance murfin motar gashi dai a bude amma babu kowa a ciki ga kuma key din motar again a jiki to saboda tsananin gajiyan dayay ne yasa be iya dogon tunani ba yasata a gaban motar ya jinginar da ita, ya fito yanata waige waige babu alamun kowa sede hasken fitilu seya koma cikin motar ya rufe ya tada motar a zuciyan sa yanata mamakin kansa ya biyewa zuciyan sa zeyi temakon da baida tabbacin waye itaba mutum ce ko a a ko muguwa ce mussam dayaji ta ambaci kisa, shidai kawai yana bin umarnin zuciyan sa da kuma kwadayin sonjin wacece ita din? Meya fito da ita tsakar dare, seda ya karewa motar kallo yaga kayan maye iri iri the same irin doyin motar irin doyin aman datayi masa kuma itama take warin wan nan yasashi tabbatar da motar ma tatace kenan, seda ya ciro wayar tata a aljihun sa yaga 2 saura mitina kalilan, san nan ya sake maida ta aljihun yaja motan ya tafi laluban asibiti....✍️