🌍 DUNIYA MAKARANTA!!🥀

Ten

by @nanabmb

🌍DUNIYA MAKARANTA!!🥀


Arewabook

https://arewabooks.com/u/nanabmb

My novels


RABON KWADO...!!


JARABTAR MU!!


RABO!!


AND NOW


DUNIYA MAKARANTA!!


Page Ten


Inda Allah ya temake shi beyi wani dogon tafiya ba ya iso wani karamin clinic hospital yaje yay wa masu gadi magana sukazo suka bude masa gate ya shiga da motan ya sake ciccibo ta a motan ya fito da ita to ganin hakan ne yasa masu gadi zuwa suka kira ma aikata asibitin dake duty na dare akazo aka sata a gado aka shiga da ita ciki aka soma bata temakon gaggawa shi kuma wata nurse ce guda daya tazo da kayan aiki inda yake zaune ta soma treatment din face dinsa dayay jajir ga idanu har yanzu basu dawo dai dai ba goshi a kumbure, yana bukatar temakon shiyasa be hanata aikin nataba duk da yanajin azaban zafi abinda take masa a fuska yay hakuri ya daure zuciyan sa fall da tunanin wan nan daya kawo hospital din se ganin abin yake kamar a almara, nurse din kamar tasan me yake tunani yaji tace.


" Nasan ba kanwar ka bace! Kuma ba matar kaba duba da yadda ta mayar ma da fuskan ka haka! Sabani kuka samu da itane? Amma na tayaka jimami! Abinda ya daure min kai shine! Nagan ka lpy kalau amma ita kuma karewar maye ma akwai kwayun da suka riga suka ma rayuwar ta illah! Garin ya kabari hakan ta kasance? Yadda kake kyakkyawa din nan dai! Nasan bazata iya jurewa ba idan kukayi fada! Koka nemi ku rabu! Jikina gaba daya bani yake saboda kaine tama rayuwar ta haka! Allah sarki mu muta! Rayuwar su a wasu lokuta akan maza take lalacewa!" Duka wan nan uban suturun da takeyi tana ta aikin danna masa goshi tana shafa masa wani cream a gurin Bilal beko kalli fuskan tataba, saboda haushin ta daya kamashi shiyasa yaji baida lokacin tama bare ya bata amsa, to abinda ta fesa masa a idone tasa shi ya rufe idanun nashi na wasu lokuta, tana shirin tafiya ne don taga beda niyyar bata amsa sega Dr ya fito yana tambayar ina wanda sukazo tare nurse din ta bashi amsa da gashi, tom halin daya gansa a ciki ne yasa bece ya bishi office ba yazo ya zauna kusa da shi yana cewa.


" What is your relationship with the patient?" idanun Bilal still suna a rufen ne ya yamutse fuska yace.I don't know who she! Temakon ta kawai nayi because she need!" Cikin dariyar rainin hankali nurse din tace. " What! You don't know her! But how did you seen her and help her in this night? Hey Mr Man! We are not a children fah!" Dakatar da ita Dr din yay san nan yace. " What ever is not our problem oh you have a secret relationship with her, is not my problem! abinda zan sanar maka shine, indai kana son ta sami rayuwa a gaba se anyi mata operation! Tana cikin mawuyacin hali, Sakamakon ciwon datake dauke dashi, yanzu ga wani matsalan za ayi mata wankin kayan ciki san nan a kara mata jini kwayoyin datake sha gaba daya sun riga sun illata mata ko ina, jini isashe bata dashi don haka kasan abinda zakayi inma ka santa ne inma temakon nata zakayi oho, kawai dai tunda kaine ka kawota kaine zamu gayawa matsalan ta!"


" Ko nawane zan iya kashewa indai zata sami lpy!"

" San nan kuma kace mana baka santa ba? Ko nawa zaka iya kashe wa akan ta kuma bakada wani alaka da ita?"


" I don't need your trust ok!!" Cikin hassala Bilal ya mata maganar yana me bude idanun sa yana watsa mata wani kallo rai bace ya juya ya kalli Dr din yace. " Muje na dauko ma kudin nayi sign koma miye ayi mata inasone ta sami lpy, badon komai ba sedon inaso nasan ko wacece ita! Senasan su waye sakar karun iyayen ta da suka barta ta lalace haka! Har ta saka rayuwar ta a cikin matsala!" Yana gama maganar yasa kai ya fice ya barsu da sakakken baki seda ya kusan ficewa ne nurse din tabi bayan sa taname cewa.


" These ajebotas Koh!! Hmm!" Inda Allah temaki Bilal aljihun sa akwai kudi a ciki kuma yaga wasu a motan shiyasa yace direct ya debo na cikin motan don sunma fi dubu 50 gana aljihun sa besan ko nawa bane, ya ciro ya hada ya bata ta masa jagora yaje yay payment yasa hannu za ayi mata aiki, bayan an sa mata ledan jini guda biyu, jinin shine daga baya ya bata lokaci kafin aka samu akasa mata jinin har kusan asuba Bilal be zauna ba yana matukar mamakin kansa yadda ya zage yana temakon yar maye! Ko tunanin gida bayayi, seda jinin da akasa mata na farko ya kare ansa na biyun ne Dr ya bashi damar shiga dakin da take! yaga yadda akasa mata roba harda ta hanci mamaki sosai yake kamashi na wan nan yarinya ita kuwa miye yake damun rayuwar ta haka, dayaga babu me bashi amsane, ya wuce bathroom ya wanke fuskan sa sosai ya fito ya nemi kan sofa ya zauna ya matso kusa da ita yana kallon ta zuciyan sa fall da tunani iri iri yana al ajabi abun daya faru bacci ya soma fisgan sa, sannu sannu harya kwantar da kansa akan kujeran se bacci,


Karfe 6 da kusan rabi gidan su Meenal kowa ya hallara a parlour kowa yana cikin tashin hankali bare Mahmoud daya kasa zaune ya kasa tsaye cikin wani hali auntie Lubna tace.


" Gaskiya dai abin da mamaki! Bilal inane ya tafi haka? Koba muba ko Mahmoud ayya kamata yasanar wa idan zashi wani guri! Amma kuma cikin dare inane zeje? OH ya Allah ka kawo mana dauki Bilal kana inane haka kana ina?"


Dakatawa daga zaryar da Mahmoud yake, ya soma cewa." Mamee wlh ni nasan duk inda Bilal yake baya lpy dole akwai abinda ya faru hankali nah yaki kwanciya su Daddy kawai nake jira su dawo don nasan akwai wani abu dole! Ga wayar sa ya bari a gida bata yadda za ayi a sameshi don dai kin hanani naje na kai ilu gurin hukuma, don babu me laifi a wan nan abun sama dashi! Taya ze raina mana hankali kuma mu kyale shi!"


" Mahmoud ka kwantar da hankalin ka, ni bana tunanin wani abu babbane ya samu Bilal! Hasali jikina yana banima shine ya hana me gadi a gaya mana inda yake! Zefa dawo duka inda yaje iname tabbatar maka Bilal ze dawo!" Cikin karfafa gwiwa mummy take maganar shiyasa hankalin Mahmoud ya soma kwanciya ya fara tunanin to ina ya tafine, kasa hakuri dai yay still yace. " Bari dai na kira su Daddy naji miye labari!" Ita kuwa hakima Meenal tana can luntsume a gado batasan abinda yake wakana ba baccin ta kawai take hankali kwance, ta tsula tsiyan ta tabar Sara da matsar kwalla.


Hospital


A hankali ta soma bude idanun ta harta budesu garau tana karema dakin kallo kafin ta maida hankalin ta kan Bilal dayake zaune har yanzu yana sharbar baccin sa ganin hakan ne yasata murmushi ta zare roban dake hancin ta tayi kokarin tashi sede ta kasa mikewa saboda jikin ta ba kwari har yanzu kwayan idanun ta bata dawo daidai ba a hargitse yake tabi tayi wani iri da ita abin tausayi kallon datake masane yasata soma zubar da hawaye se kuma kuka wanda kukan ne yasa tarin ya dawo mata tasoma kuwa harda kaki tana tara hannun ta taga jini firgigit cikin mafarkin da yake Bilal ya bude idanu saboda tarin da yakeyi ne ya tashe shi, to ganin halin da take ciki ne ya tashi ya zauna a gefen ta ya tayar da ita daga kwancen a yanzu numfashin ta ne yake shirin daukewa saboda tarin ya tsanan ta, shiyasa Bilal ya mike a rude yana cewa. " Bari naje na kira Dr" koda ya mike yaji ta riko masa hannu ya juyo cikin tausaya wa halin da take ciki yace. " Dr zan kira yanzu zan dawo! Kinjee!" Girgiza masa kai takeyi tana sake rike hannun sa ga matagugu da take tarin masifa yaki barin ta, hakan daya ganine, yasashi ban bare hannun ta a nashi ya tafi don kiran Dr harya kai kofa yaji ta fisgo magana dakyar tace.


" Ridwan!!!"


A yanzu seya soma mamakin sunan data ke kiransa dashi tun a jiya, shiyasa ya girgiza mata kai yace. " Bani bane Ridwan! Baki gani bane? Ki kalleni dakyau! Bari nayi maza na kira Dr kina bukatar temako!" " Ridwan kayimin Addu'ah!! Don Allah..... maganar ta gagara karasawa shiyasa yasa kai ze fita amma still ya kasa haryasa kai waje seya waigo yana kallon ta yaga ta miko masa hannu tana juya masa kai alamun karya tafi, shikuwa saboda yanason temakon ta sebe dawoba a rikice ya fita yaje ya sami Dr yana shirin zuwa yi mata aiki, don aikin nata shine aikin sa na karshe dazeyi ya tafi gida kuma, rikice Bilal ya masa bayanin halin da take ciki, batare da bata lokaci ba kuwa ya biyeshi zuwa dakin yana tunanin meye matsalan ne bayan koda asuba yaje dakin ya cire mata robar karin jinin data kare yaga Bilal nata sharar bacci haka ya fita ya barsu, to koda isowan su dakin dai yanayin da suka sameta ba lpy ba, tayi wani irin kwanciya kamar zata wuntsila kasa idanun ta a kafe, Dr ya gama dubata ya tabbatar da ta mutu, kawai seya saka hannun sa ya shafo saman fuskan ta ya rufe mata Idanun ta yana girgiza kai, ay Bilal cikin wani irin hali yay baya yana cewa.


" No!! No!! Dr karka ce min ta mutune! Ya subhanallah! Wai meye yake faruwa dani hakane?" Dafashi Dr din yay yace. " Sede fa hakuri wan nan ta riga ta mutu, koda bakasan dangin taba a yanzu ya kamata kayi kokari ka nemo dangin ta don susan halin da diyar su ke ciki!" Wani irin shiru Bilal yaji duniyar tayi masa daga tsaye yay wani irin zubewa a kasa yana furta. " Inna lillahi wa inna ilahi raji un! Gaba daya Bilal se yake ganin wan nan abun kamar a mafarki, yama rasa meye zeyi tunani ne a wan nan lokacin shi kuwa yanzu ina ze sami dangin wan nan yarinya! Yayi tunanin yayi tunanin haryama rasa yazeyi, daga karshe dai ya yanke shawaran zuwa cikin motar ta koze sami wani sheda kamar ze kifa haka yake sauri harya isa bakin motar ya ya bude ya shiga, yanata dube duben sa, can wani tunani yazo masa kamar wanda aka mara ya zabura ya zauna a kujeran motan yasa hannu cikin aljihun sa ya ciro wayar tata, har seda yay murmushi saboda dadin dayaji, kuma babban abin farin cikin yaga wayar babu password ko daya, direct gurin contact ya shiga ga mamakin sa yaga wayar contact din se number daya anyi saving da( mon père) ma ana my father, be tsaya dogon tunani ba ya soma kiran number din ringin daya aka daga ba a jira komai ba aka soma magana cikin french.


" Jawaheer!! Hankali na ya tashi rashin jinki danayi jiya, meya hanaki kiran mu! Gaba daya hankalin maman ki ya sake tashi kullum mafarki take akan ki mara dadi, gaba daya mun rasa kwanciyan hankali Jawaheer saboda rashinki a kusa damu, nasan kin fimu shiga damuwa kiyi hakuri kinji nadan lokaci ne komai ze wuce! Kinyi Shiru kice min wani abu diyata!"


Dukda Bilal be tantance mema yake cewaba yadai dan tsinci maganar kadan da dan guntun french dinsa tun wanda suka koya a primary shiyasa ya danyi gyaran murya yace. " I'm sorry for what I'm going to tell you, are you speaking with Bilal Osman! Your daughter had an accident,we are in the hospital, if possible you can come now!" Shiru ne nadan wasu ya wakana kafin mahaifin nata san nan cikin damuwa ya soma masa magana da turanci yana cewa. " Menene ya sami Jawaheer? Ya subhanallah! Jawaheer menene ya sameki? Bazan taba ganin nisan Nijer da Nigeria ba yanzun nan zan taso zuwa Nigeria temako daya zakayi min ka zauna min tare da ita kafin na karaso, karka bari wani abu ya sameta ko nawane zan baka kayi min temako ka kula min da ita kafin na karaso!"


Bilal cikin mamaki ya cire wayar daga kunnen sa ya soma kallon number din ya tabbatar da bata kasar bace se jikin sa ya sake yin sanyi jiki a sanyaye ya amsa masa daze jirashi seya karaso din, cikin mutum tawa sukayi sallama ya sanar masa suna cikin Abuja din ya tura masa address din da suke na hospital din, seya fito cikin motar yaje sukai magana da Dr ya shaida masa mahaifin nata yana hanya, ze taso daga Nijer Dr yay mamaki dayaji haka ya shaida masa ay tana canma mutuware an kaita, Bilal kamar abin azziki ya zauna jiran sa shiru, awa daya ta shude shiru awa biyu uku ayse hankalin Bilal kuma yay gida ya tabbatar da iyayen sa suna cikin wani hali yanzu shiyasa yawa Dr bayani zeje gida ya kuma bashi number din Jawaheer yace idan mahaifin nata ya karaso ya kirashi, a wayar dukda ya tabbatar ma mahaifin nata ze nemeshi idan yazo, cikin gamsuwa Dr yay saving number din Jawaheer a wayar sa Bilal ya tafi, seda yaje shiga motar ne yagamu da nurse din nan me

surutu se wani kwarkwasa take masa tana mai gaisuwa mutuwar Jawaheer, kamar abin azziki ya amsa ta har suka gaisa,seta soma masa magana ya rage mata hanya, ko kulata be kuma yiba ya shiga motar Jawaheer din yaja yatafi don bashida time din shiri rita a wan nan lokaci....✍️