Twelve
by @nanabmb
🌍DUNIYA MAKARANTA!!🥀
Arewabook
https://arewabooks.com/u/nanabmb
My novels
RABON KWADO...!!
JARABTAR MU!!
RABO!!
AND NOW
DUNIYA MAKARANTA!!
Page twelve
Seda ya gama karewa hoton kallo san nan ya jin jina masa kai cike da mamaki yace. " Tabbas shine! Amma yanayin sa beyi kama da dan Nijer ba babu alamun daya nuna shi dan canne! Tabbas shine! Karya yay min kenan ya santa! To amma yallabai kwayoyin maye wanda sukafi karfin ta takesha babu alamun daya nuna yayi mata wani abu!"
Wani shu umin smiles mahaifin Jawaheer yay cikin hausa irin tasu yace. " Ay dama bazaka taba ganin alamun shi dan Nijer bane! Ya iya takun sa fiye da yadda kake tunani, koma meye yarinya ta tasha shine sila kuma shine ya kawo ta hospital Allah ne kadai yasan abinda yay mata, amma kuma Ridwan kayi kuskure zan tabbatar maka da kayi kuskure, burin ka ya cika ka kashe ta, wlh zakaga yadda rayuwar ka zata wulakan ta! Yadda nakejin wan nan radadin a zuciya ta kai idan kaji naka seyay ajalin ka kaima!" Magana Dr ze sakeyi ya dakatar dashi, shima mamaki ya ishi Dr din sosai yake mamakin Bilal kuma still yana ta kiran number din Jawaheer a kashe, seda suka gama komai tukunna ya dauki Jawaheer shida mutanen sa suka tafi, shima Dr hada inashi inashi yay ya tafi gida zuciyan sa fall da tunanin abubuwan da suka faru daga jiya zuwa yau.
Koda su Daddy suka karaso a matukar kaguwa Bilal yay kansu yana cewa. " Daddy please nasan kai zaka fahimce ni, ina cikin hankali nah babu abinda ya sameni, banaso su ci gaba da karya tani Daddy muje hospital din domin ku tabbatar da abinda nake fada, bani da enough time Daddy banaso mahaifin nata yazo bana nan!" Dafashi Doctor yay gami da ce masa. " you will give me only ten minutes okay!!" " No doctor! Let's go to hospital!! in the hospital you can also treat me!! you should understand I don't have time" Ya karashe maganar kamar zeyi kuka, su mummy kuwa duka sakin baki sukayi suna kallon ikon Allah gurin Bilal basu taba ganin ana musu dashi irin na wan nan rana ba, " am Bilal ya kamata kayi hakuri ka tsaya ya duba mana lafiyan ka! Hakan shine kadai abinda zesa hankalin mu ya kwanta! Duk duniya lafiyan ka yafiye mana komai akan wasu can daka tashi hankalin ka haka! Koma menene daga baya za a iyayinsa ka kwantar da hankalin ka Bilal gaba daya ka birkice dole bazasu aminta cewa lafiyan ka kalau ba! Anya kaga yadda ka koma kuwa harda kake kokarin fita again! Wai menene ya faru dakai waye ya maka wan aika aikan?"
Saboda kuluwa Bilal kasa magana ma yay yaje ya zauna, ko doctor din baya son gani nadama kuwa sosai yake yinta akan dawowa din dayay daya sani yayi ta ba yar kadan ba, zuciyan sa nata gaya masa daya sani ma seda mahaifin nata yazo tukunna ya dawo gida, rufe Idanun sa yay da Dr ya soma tabashi saboda kuluwa yakai karshe gurin kuluwa, yana cikin yanayin ne yaji ya masa allura a damtsen hannun sa takaici ne ya hanashi responding ko motsi beba, sam be taba kawo allura bacci Dr ya masaba daga wan nan lumshe idanun be kara sanin inda kansa yake ba, har seda doctor ya gama aikin sa ya shaida musu lafiyan sa kalau kawai buguwa ne yayi, a fuskan sa, se skin dinsa data samu reaction daga wani abun me cutar wa, ya kuma shaida musu zekai 5 hours be farka bama, ya bada magani wanda zesha idan ya farka, sukai masa godiya Daddy su Meenal ya rakashi ya mai sallama me tsoka tukunna ya tafi, cikin mamaki Sara tace. " Daddy anya ba gaskiya Bilal yake fada ba kuwa? Doctor yace lafiyan sa kalau!" Cikin wani irin kallo da mummy takeyi mata tace. " Koda gaskiya ya fada dai ay mutuwa bata buya, kuma ga waya a hannu na indai gaskiya ne abinda ya fada to mahaifin nata ze kira wayar, koda be farka ba aka kira wayan nan se Mahmoud suje hospital din, ayba wani abu bane! Mu ta lafiyan sa mukeyi yanzu!" kuma babu wanda yasan mummy ta kashe wayar tana dai rike da ita a hannun ta amma ta riga ta kashe ta tun sanda ta amshe ta sanine Bilal beba,Cikin gamsuwa auntie Lubna tace. " Gaskiya ne kuwa, indai aka kira wayar sesu Mahmoud suje!" Sara bata kuma cewa komai ba ita kuwa Meenal tayo tsamo sede tabi wan nan da ido ta kalli wan nan ba bakin magana, auntie tasa su Aseem suka gyara ma Bilal din kwanciya sunata kare masa kallo kamar sabuwan halitta a garesu.
******** *********
Nijer
Ridwan ne yake sauko wa downstairs na gurin aikin su, fuskan sa karara ta nuna zallan tashin hankali dayake ciki, tafiyan yake amma sam baya cikin hankalin sa, to yana cikin tafiyan ya gama saukowa kasa yana shirin fita ne yaji an dafa masa kafada an rike, shiyasa ya dakata gamida da dagowa a sanyaye yana kallon wan da ya dafashin, yaga ashe Rafeeq ne abokin aikin sa kuma aminin sa, cikin damuwa da halin dayaga Ridwan din a ciki ne yasashi cewa.
" what is happening again?"
Batare daya tanka shiba Ridwan ya mika masa takadda dake hannun sa, tun kan ya amsa jikin sa ya kuma yin sanyi, ya amsa takaddar ya karanta yaga abinda ta kunsa ko karasa wa be iyayi ba ya linke takaddar cikin wani irin yanayi dayakejin kamar zema aminin nashi kuka cikin french ya soma cewa. " An dakatar dakai daga aiki? For what reason? Wai meyake shirin faruwa dakai ne Ridwan? Kama san kuwa abinda yake faruwa? Ya Allah!! gaskiya da akwai matsala Ridwan dole muje mu samawa kanmu mafita rike hannun sa yayi suka fita daga gun aikin nasu, suna tafe cikin mota Rafeeq yanata kokarin kwantar masa da hankali duba da irin labari daze gaya masa again, seda suka isa wani Mall hadadde tukunna suka shiga sukai parking, shidai Ridwan nashi idone, saboda tsananin halin da yake ciki na mamaki da kuma al ajabi na mahaifin sa, guri Rafeeq ya sama musu Ridwan ya zauna san nan yaje amso musu dan abin sha Rafeeq din, tom kafin ya dawo ne, Ridwan yasoma jin wani mummu nan labari ta news a TV din dake manne a saman Wall din da ake sarving din mutane, daga kan da Ridwan zeyi yay arba da hoton sa dana Jawaheer ana jawabi kan cewar shine ya dauke ta a cikin cell yaje ya kaita wani gurin daban ya kashe saboda bayaso masoyiyar tashi tayi mutuwar wulakan ci, saboda wan nan dalilin ne yasa aka dakatar dashi daga aiki sede saka makon dakatar dashi din da akayi mutane gari sun soma suka akan abinda akaiwa Ridwan bazeyi aiki ba tunani ba akwai dai wani abu dole a tsanan ta bincike. Anata kokarin jin ta bakin Ridwan amma hakan ya gagara, kasa ci gaba yayi da saurare Ridwan yay ya dafe kansa da yake gani dishi dishi ya mike daga kan kujeran dayake zaune gaba daya tunanin sa ya dauke cak yama rasa abinda ze aikata gashi gaba daya mutanen dake gurin sun koma kallon sa ana kus kus kawai seyay waje gaba daya ya fita a gurin, time din kuma Rafeeq ya dawo hannun sa rike da juice sede yana ganin wayam ba Ridwan annurin face din sa ya dauke yanata waige waige harya iso gurin ya aje juice din tunda be ganshi ba ya tabbatar fita yay saboda yanzu yaga abinda ake haskawa a TV shiya sa ya fita shima ai kuwa yana fitowa ya hange shi ze shiga 🚕 batare daya jira komai ba ya shiga nashi motar ya bisu.
********* *********
Se bayan Isha Bilal ya farka, yana bude idanun sa yaga mummy kusa dashi babu kowa a parlour din cikin jin dadi ta riko masa hannu tana hamdala da farkawa tashi cikin jin dadi tace. " Sannu yarona kajee! Mahmoud yanzu ya tafi ciki donyin wanka bari na kirashi yazo ku shiga ya fara hadama ruwa kayi wankan tukunna se kaci abinci ga magun gunan ka Dr ya bada! Ko kanajin wani ciwon ne yanzu?" Girgiza mata kai Bilal yay yana me mikewa zaune gaba daya yayi weak yana jin kansa yay masa wani irin saka yau, koda ya daga kai yay arba da agogon parlour yaga har 8 ya gota, se hankalin sa ya tashi ya soma rafka salati ya mike ze fita mummy ta riko masa hannu tana cewa.
" Ina zakaje wai?"
" Mummy hospital zan tafi don Allah yanzu dai karki hanani tafiya ki barni naje na gani"
Jawo hannun sa tayi ya dawo ya zauna tana cewa. " Kaga Bilal! Ka kwantar da hankalin ka, magana a yanzu ta riga ta kare, mun riga mun gama magana da mahaifin nata ya kirawo a wayar na daga, ka kwantar da hankalin ka kajeee yarona yace ayi maka godiya sosai ba amfanin ka sake yin wani magana akan su ya riga yanzu ya koma!"
" Mummy meyasa baki tashe niba? Inaso fah naje gurin sa seda fa na gaya miki mummy meyasa zakiyi min haka? Akwai magana dana ke so muyi da mahaifin nan nata abinda nayi ta gudu kenan! Gashi seda kuka sa nayi wani irin asarar ren bacci har dare yayi ina kwance!"
" Kaga yarona ka kwantar da hankalin ka, mahaifin nata ya bani number dinda zaka same shi ta can Nijer din, don haka ka kwantar da hankalin ka!"
" Mummy bani wayar to na kirashi! Hankali na baze kwanta ba mummy ki fahimta yadda nakeji don Allah "
" Wai kai Bilal! Meyasa kake da taurin kaine! Wayar tana guri na ba kuma zan baka ba se sanda kaji sauki gaba daya ko maganar banaso naji ka sake yinta inba hakaba ba to bazan baka wayar bah, ka riga ka sani babu inda zamu bari ka tafi a haka ba tare dakaji sauki ba, gobe goben nan ma zamu tafi gida!"
Shiru Bilal yay don baze iya musu da mummy din tashi ba, kamar bazeyi magana ba dai ya kalle ta yace. " Inasu Daddy din mummy?" Murmushi tayi masa tace. " Suna masallaci yaron kirki ba jumawa zasu dawo, yanzu kaje kayi wanka domin ayi abinci tare dakai, zan sanar wa kowa ka farka maza kaje kajee! Kona kira Mahmoud din ya temaka maka!"
" A ah mummy ki barshi may be ya shiga wankan yanzu bari kawai naje dakai nah!"
Mikewa yay Bilal ya soma tafiya slowly yana dan mika, abinsa, kamar daga sama sega Meenal ta fito daga kitchen zata koma dakin ta hannun ta dauke da kayan marmari tana tafiya cikin yaukin ta daya bi mata jiki, cakk Bilal ya kame yana kallon ta zuciyan sa nata raya masa abubuwa da dama akan ta, tana tafe tana latsa waya dayan hannun an riko bowl, cikin rashin tsamma ni a dagowa da zatayi ta ganta daf da Bilal yana mata wani irin kafirin kallo, saboda firgitar da tayi ne yasata sakin wayar da bowl din ya kuwa tarwatse a kan tiles, ta kuma kasa guduwa kuma tana kallon sa da fuskan ta kamar wadda akace wa za a zare mata rai yanzu, bata lokacin dataga yayi yawa ne yasa mummy cewa.
" Bilal!! Me kake kallo ne haka? Ka wuce ka tafi mana!"
Koda yaji hakane Bilal ya dan lumshe eyes dinsa san nan yama Meenal wani irin bangaje wa da seda taji kafadan ta ya amsa, ya wuce abinsa, yabar ta anan tsaye tana zara idanu, koda ya wuce mummy se tayi murmushin da ita kadai tasan ma anar sa tace. " Yarinya man kaza! Da sannu zakiyi bayani!" Koda Meenal taji tama bata ko kalli inda take ba ta sunkuya ta dauki wayar ta data tabbatar ta tashi aiki, ta wuce saman itama.
******** ********
Me taxi be sauke Ridwan a ko inaba se a gidan su Jawaheer tun da yaga yadda al umma ta cika a gidan ya tabbatar da gaskiya ne Jawaheer ta rasu, shiyasa jikin sa ya karayin sanyi, direct ya shige cikin gidan mutane kuwa kallo kamar ze kifa yadda Idanun jama a yake a kansa yan jaridu kuwa dama kamar jira suke kamar sunsan da zuwan sa sukayo kansa da tambaya, to halin da yake cikine, yasa ko kallon suma be iyayi yiba, a lokacin kuma Rafeeq shima ya iso gidan, jikin Ridwan a sanyaye ya isa gurin dasu Daddy din suke zaune, ya tsugunna a gaban su amma babu wanda ya kalle shi cikin su Daddy din sede duk da haka beyi kasa a gwiwa ba ya soma cewa.
" Papa!! na kasa fahimtar abubuwan da suke faruwa! Bayan abinda kuka sa akayi min, meyasa yanzu za a dora min laifin kashe Jawaheer? Koda wasa bazan iya kashe Jawaheer da hannu naba Papa kaima ka sani amma me yasa zakuyi min haka? Da wan nan abun Papa da sawa kukayi aka kashe harda ni! Zuciya ta ta kasa yarda da da abinda nake gani yanzu, papa meyasa?"
Murmushin dayafi kuka ciwo papa din nashi yayi san nan yace.
" Ridwan ashe bakasan ma duka abinda yake faruwa ba Koh!" Cikin french yay maganar nashi,
Mahaifin Jawaheer kuwa cewa yay" hmmm Ridwan kenan! Ka iya yaudara! Burin ka ya cika ay yanzu ko! Ka kashe min farin cikin rayuwa ta hankalin ka ya kwanta, yanzu kuma ka dawo mana da mayaudarin fuskan ka zaka ce baka san komai bah! Sam bazan kashe kaba, amma daga yau zamuyi maka abinda seka gwammace meyasa kazo duniya!"
" Ay zesan abinda yake faruwa yanzu tunda be saniba!"
Papa ne yay maganar yaname mikewa tsaye, kai kana ganin sa base an gaya maka cewa rashin mutum ci ze aikata bah, Ridwan kuwa kasa cewa kala yayi a yanzu saboda abubuwa da suka soma shamai kansa, Manma tana cikin gidan suna zaman makoki labari ya isar mata ga Ridwan yazo, shiyasa ta bazamo a guje ta fito dama tayi kuka harta fita a hayyacin ta saboda Papa ya gaya mata hukunci daze yanke akan Ridwan din, a lokacin da ta fitone, ta tarar harya kama hannun Ridwan din ya nufi inda yan jarida suke cikin tashin hankali ta ruga jiki na bari, ta tafi gurin nasu kobi takan Ridwan batayi ba ta riko hannun Papa dana Ridwan wanda suke guri daya duka biyun hannun nasu ta rike cikin zubar hawaye ta soma cewa.
" Iname rokon ka mijina a matsayi na matar ka, ina neman alfarma kayi hakuri kada ka tozar tamin Dana! Ina tsananin kaunar sa idan kayi min haka nima bazan iya rayuwa ba karka wulakan tamu a idon duniya na rokeka mijina, idan kayi min haka ka gama min komai a duniyar nan kayi hakuri komene ne kakeso zamuyi maka amma kar kayi mana haka!"
Shidai Ridwan ikon Allah kawai yake kallo a yanzu tun kan yaji meze faru zuciyan sa na tsananin bugawa, cikin wulakan tattacen kallon da Papa yake mata ne yace. " Hadizatou kenan! Ay dama na gaya miki ki cigaba da sawa zuciyan ki bakida Da a duniya, inba haka ba kam tabbas kamar yadda kika fada hakan shine zeyi ajalin ki!" A fusace ya fisge hannun nasu ya karasa gaban yan jaridar da a yanzu sun musu cin cirin do kowa hankalin sa yayo kansu, cikin hucin bala i ya daga hannun sa, dana Ridwan sama ze soma magana ne, Manma ta sake rike Papa cikin kuka me tsanani take cewa.
" Na rokeka mijina karka tona min asiri,wlh Ridwan bashida laifi wani irin rashin imani ne wan nan? Sam bakada imani baka da tausayi indai kayi mana haka" Hadizatou idan baki wuce cikiba wlh wlh sena hada dake na sallama ki kinji ma na gaya miki!"
" Eh na yarda ka sallame mu daga yau, amma don Allah karka tozarta mu a idon duniya na rokeka!"
Ridwan yadda yaga yan jarida nata yi musune ya kalle ta murya na rawa yace.
" Mama koda abinda zanji yanzu ze iya yin ajali na Papa baze fasa abinda yayi niyya ba don Allah kiyi hakuri ki koma ciki ki kyale shi komene ne zeyi baze fasaba ki tafi ciki manma!" Duka cikin french suke magana sosai jikin ta ya kara yin sanyi, kawai seta rungume shi ta cigaba da kuka meban tausayi duk da haka kuma Papa be fasa yin abinda yay niyya bah cikin daga murya ya soma magana da yaren Hausa. " Jama ar duniya gaba ki daya daga yau inaso su shaida hukunci da zan yanke, zasu san kuma wani sirri da duniya bata taba sani ba amma ayau zan bayya nashi, wan nan sirri kuwa shine, kamar yadda duniya ta sanni a baya ban taba samun haihu ba, haka yanzu ma nakeso ta cigaba da dauka banida Da ko jika, wanda duniya takewa kallon dana wato Ridwan sam ba dana bane bani na haife Shiba bani da wani alaka dashi, matata Hadizatou itace ta kawo shi cikin rayuwar mu....✍️