Sixteen
by @nanabmb
🌍DUNIYA MAKARANTA!!🥀
Arewabook
https://arewabooks.com/u/nanabmb
My novels
RABON KWADO...!!
JARABTAR MU!!
RABO!!
AND NOW
DUNIYA MAKARANTA!!
Page Sixteen
lokacin da Sara tashiga daki nta fadawa tayi kan gado tana sharbar kukanta har mummy ta shigo hankalin ta a tashe tace. " Sara meya faru me Bilal din yay miki hakane? Gaba daya kin daga min hankali na Sara?" Sam kin tanka ta tayi seda tazau na gefenta ta dagota sannan ta fada jikinta cikin kuka tace." Auntie ashe Bilal dan iska ne muna furtata yakeyi seyau Allah ya toni asirin sa na kamashi yana kallon mace tsirara ashe har wayace dashi aboye wacca yake iskancin shi da ita bamu saniba kuma akan nayi magana yakama marina ashe mugune shi!" mummy baki shanye take kallonta harta kare zancen ta sannan tace " Sara yana kallon mace tsirara fa kikace!" "Eh wlh auntie kinsan dai bazan iya yimasa karya va saboda nace zan kawo muku wayar yamur de ni yakwaci wayar ya kusan karya min hannu!" kasa tanka mata mummy tayi kallon Sara din kawai take tana kuka, seda tagama tunanin ta ranta abace tace " Tashi muje gurin nashi inji meyake so ya zama kuma yanzu!" mikewa sukayi Sara a zuciye ta fita ita kuwa mummy dakin ta ta wuce ta dauko handbang dinta da suka je Abuja sede ga mamakin ta taga babu wayar data ajiye a ciki, cikin takaici kuwa ta cije bakin ta tana me girgiza kai ta ajiye jakar ta fito tana zuwa parlour din ta samu Dr nama Bilal tambayoyi shiyasa ta zauna gefen Sara harta na kada kafa saboda rai ya baci fuskar ta a daure ita kuwa Sara se zubar hawaye su Daddy basu ko kallesu bah har Dr yagama abinda zeyi yatafi, ba bata lokaci Bilal ya mike ze haye sama mummy tace " Zonan Bilal!" Ta kalli Daddy tace ina fata dai Daddy ya sanar maka abinda ya aikata wa Sara dai koh!" Daddy ya kalleta yace be fadamin ba Maryam wani laifin yayi ne?" kallon Sara tayi tace " Fadi abinda yayi miki da bakinki" dagowa tayi tana sharbar kuka tace " Duk duniya nayar da Bilal Daddy ban taba tunanin ze aikata hakaba sega shi yau na kamashi yana kallon vidion wata yar iska tsirara abin ya girgizani meyasa zeyi min haka bayan na amin ta dashi" Bilal yanada ga zaune yadago yana kallonta saboda kalaman datayi yanzu beyi mamaki bah sabida yanzu kusan yasoma sabawa ma da sharrin mace duba da irin abinda Meenal ke aita masa kallon shi Daddy yayi yace "Bilal kajee abinda tace meye gaskiyar lammarin?" Bilal yakai karshe gun kuluwa kasa cewa komai yayi seda yarin ga sauke ajiyan zcy sannan yace " Daddy ina kallon wani abune ta net vidion ya shiga sam ban saniba ma ina tunani bansan meyayi playing bah ita kuma data gani shine zatayi min banzan fahimta kamar batasan wanene nibah harda zata fara yimin rashin kunya" Kallon Sara Daddy yayi yace " Sara kin taba kama shi da laifi makaman cin wannan ne ko aka baki labari?" kanta akasa tace " a ah bantaba gani bah!" "To Alhmdlh abinda nakeso dake Sara wannan dalilan sukara miki tasiri azcyn ki har indai kinason abu to koda yaushe kikasan ce me masa kyakkya wan zato kada kiyadda shedan yay miki hudu ba tunda baki taba ganin shi dawani mugun haliba wannan shizesa kiyi masa hakuri yanzu tsautsa yine,sedai in hakan takara faruwa kuma to kome yafaru dashi shine yajawa kansa dukda bama fata hakan takara faruwa INSHA ALLAH Kai kuma Bilal seka kara kiyaye wa kasan yakama ta duk abinda ze bata mata rai ka gujeshi fushi ai banaka bane ina laifi don masoyin ka yanuna kishi akanka?" mummy tace "Aini Bilal kabani mamaki harda zakayi fushi akan wannan abun bayan ka aikata kabar ta taji da daya mana a ah kazo harda marin ta wlh kabani mamaki wani irin haline haka zaka daukar wa kanka dukan mace matar ma wadda zaka aura wannan ai ba dacewa bace!" katseta Daddy yayi ya ce " Ya isa komai ya wuce ai daga yanzu shi dama zama ance zomu zauna zomu saba haka rayuwar take se hakuri kai kuma koda wasa karka kuma kai hannu da niyyar dukan ta babu kyau hakan kuma kasani sarai don haka karna kuma ji!" cikin ladabi Bilal yace " Insha Allah bazan kuma bah Daddy yan zunma tsautsayi ne!" Daddy yace " To Allah yasa kaje kahuta kasan bakajin dadin jikin ka kema Sarah ina fata komai ze wuce agurin ki!" kanta a sunkuye tace " komai ya wuce Daddy!" mikewa Bilal yayi yay sama shima Daddy betsa ya wata hiraba ya shige part dinshi mummy taraka shi da idanu wadda ita kadai tasan tunanin datakeyi a zuciyan ta.
Washe Gari
Nijer
6:40am Ridwan da Rafeeq suna hospital dinda aka kwantar da Manma cikin kunci Ridwan yake magana da french" kai Alhaji Hamraz baka hadu bah harwani samma ko yayi ya tafi da Manma haka! ban taba zaton zeyi wannan samma konba duka saboda ni kuma yake haka yanzu ta ina zan fara neman su kenan?" ina son insan wanene ni Rafeeq abin yayi min yawa!!" dafashi Rafeeq yayi yace "Daddyn Jawaheer yana nan bazamu sha wahala bah gurin sanin inda yatafi kai koshi nasan yasan ko wanene kai dole semun zage damtse akan lamarin nan semun karya doka kome zefaru yafaru kada kawani damu Ridwan yau zamuje gidan sa kobaya kaunar Allah seyayi bayani!" kallonsa ridwan yayi yana murmushin da yafi kuka ciwo yace" Nikuma bana tunanin ko su Manma sunsan wani abu kaina bare Abban Jawaheer!" da mamaki Rafeeq yace " Meyasa kace haka?" dage kafadun sa yayi yace kawai haka jikina yake bani duba da yadda al umaran rayuwar mu suka kasance a shekarun da suka shude!"
" Yallabai kozan iya sanin sunan ka?"
Kallon juna sukayi sanan suka juya bayan su da sukaji amon muryar macen da tayi magana tozali sukayi da nurse a tsaye fuskar ta dauke da fara ah take kallon su shirun da sukayi matane yasata sanin basusan watake nufi bah cikin su seta ce. "Shin ko akwai Ridwan a cikin ku?" Ridwan yayi shiru nadan lokaci sannan yace "kwarai kina magana dashi yanzu haka!" sauke ajiyan zcy tayi sannan tace Hajiya Hadizatou ce ta bada sako abaka shin kozan iya sanin yadda kake da ita?"shiru Ridwan yayi shikan shi yasan baze iya dena kiran Manma matsayin mahaifiyar saba shiyasa jikin sa a sanyaye yace " Mahaifiya tace!" murmushin ta ta fadada ta kuma cewa " Inason ganin shedar da zata tabbatar min da haka!" Magana Rafeeq zeyi Ridwan ya dakatar dashi gamida ciro wallet dinsa ya nuna mata huton su da suke su uku shida Papa da Manma, hakan ne yasa ta yin murmushi cikin gamsuwa da abinda ta gani ta ciro envelop a aljihun ta ta mika masa tace " Ga wannan Hajiya tace a baka sannan ta amshi number na da address tace zata kirani ta tabbatar zaka zo nan dama so tana son in hada ta dakai wannan dalilin ne zesa kabani number dinka yanzu da naka address din!" Ansar envelope din Ridwan yay yana me cewa " Banada address din dazan baki yanzu ina ganin kibani nakima ze wadatar!" saurin ciro wani card Rafeeq yayi yace " No gashi ma bari nabaki kawai koda zata kira zaki iya ne manmu akwai number da address a jiki!" kallon shi Ridwan kawai yake yana shirin cewa wani abu yay saurin katse shi yana me cewa. " Shikenan fah nurse mun gode sosai mu zamu tafi yanzu domin ki samu ki koma bakin aikin ki, but naga ke kamman sabuwan ma aikaciya ce anan koh?" Kallon shi take harya ida maganar sa san nan tace. " Sunana Rafeeah! ba nurse bah nima na gode sosai!" ansar card din tayi tana murmushin daya gama zauna wa akan innocent face dinta " Fatan alheri" shine abinda kawai ta furta musu ta juya abin ta ta tafi shi kuwa Rafeeq sakin baki yayi ya bita da kallo harta shige Emergency tun daga cikin zuciyan sa saboda shaukin daya dibe sa ya furta " Kai wani irin smiles ne wan nan me tada hatsaniya a zuciyan raunanan ne iri na! Gaskiya ta iya murmushi yarinyar nan!" Dukda halin da Ridwan yake ciki seda yasa shi murmushi don be taba ganin aminin nashi ya rikice irin na yauba akan mace, shiyasa a mamakan ce ya furta " Me kace?" kanshi yadan shafa da hannun sa Rafeeq san nan ya kallesa yace " Daman nayi magana ne yanzu?" Cikin basarwa Ridwan yay maganar shiyasa Ridwan be kuma tanka masaba yay gaba yabar sa anan hankalin shi nakkan envelope shiyasa yana shiga mota ya bude ta da farar pepper yaci karo aikuwa cikin kaguwa ya zarota ya bude yaga rubutun maman shine be tsumayi komai ba ya soma karan tawa karantawa.
“ Dana Ridwan! harna mutu bazan dena kaunar kaba abin alfahari na, ina matukar kewan ka lokaci daya Hamraz ya tarwatsa mana farin cikin mu! Nida kai gaba daya bamusan cewa muna rayuwa bane da azzalumi! Duk hallaccin da nayi masa amma karshe ga abinda yayi min, na tsani rayuwa ta dani kaina saboda yardar da nayi na aure shi! Mun zagaya hospital babu iyaka akan haihuwa karshe ko wani Dr yana cewa matsalan daga gurin shi take shine baze iya haihuwa ba, amma saboda yadda nake matukar kaunar sa alokacin nace naji na gani zan zauna dashi a haka! Duk da ina matukar son ganin yaya na a duniya haka na hakura na jure bakin ciki na shekaru da dama, kada ka cika damuwa kajee Allah yana tare damu shine ze saka mana abinda yayi mana ya rabani dakai yanzu kuma ze rabani da yan uwana ina cikin matsanancin kunci Ridwan ina kuma yin kuka a yanzu saboda bazan iya cema ga asalin kaba sam bamu san wanene kai ba ban taba tsamma nin irin wannan ranar zatazo ba ta tonan asiri na gama shaida wa duniya kai dan mune koda mahaifiya ta bata saniba don banason koda gangan agoran tama akan iyaye se mummunan kaddara yanzu tariga fata nasan zakaji ciwo sosai idan na sheda maka wata kalma yanzu ammah kayi hakuri yarona!! 😭 nida Hamraz mun siye kane a gurin auntie bashariya!! sam bama da dan gantaka da ita in banda kai daka hadamu! mun hadune da ita wata rana munje ganin likita damu keyi kan rashin haihuwar mu kai kuma tazo dakai kana rashin lpy me tsanani kanata kuka kallo daya namata nasan ba itace mahaifiyar kabah kukan ka har cikin bargo na nake jinshi koda natam bayeta ina mahaifiyar kah tashai da min cewa iyayen ka basa raye kuma 3 weeks kenan da haihuwar ka! ka matukar bani tausayi na kumaji ina matukar sonka sosai koda na dauke ka ka dena kukan yadda nakejin ka a zuciya ta hawaye na ya kasa tsaya wa a idanuna, dakyar na iya maida wa auntie bashariya Kai, kuma na amshi address din gidan ta, da muka dawo gida na shaida wa Hamraz nide zuciya ta ta kamu da kaunar ka ina ganin ka kamar danda na haifa, na rokeshi alfarma muje gurin ta musan yadda zamuyi da ita ta bani kai na zame maka mahaifiya, Hamraz beki ta tawaba saboda yaga yadda gaba daya bani da kwanciyan hankali aka haihuwar nan, kuma shima yana son yaga da ace nashi ne duk kudin shi bashida magaji abin yadame mu sosai da daddare bayan ya amince mukaje gidan ta muka isar mata da bukatar mu koda ya shaida mata kowaye shi rudewa tayi saboda kowa yasan shi yasan kudin shi bata musa manaba saboda yace ko nawane ta fada ze bata kudin da duk take bukata domin ta bar mana kai, sam bata musaba auntie bashariya tayan ka million dari biyu tace indai muka bata to zata sallama mana kai yan uwanka ma zata shaida musu cewar ka rasu, kariga da kazama mallakin mu baki daya Ridwan son Da yarufe mana ido alokacin shiyasa da murna muka bata kudin da ta bukata tabamu kai ta gaya mana sunan ka, muka kuma shaida mata indai wannan maganar tafita to seta biyamu kudin, mu tadauki alkawarin babu wanda zesani takuma nemi alfarmar zata ringa zuwa tana ganinka bamuyi mata musu bah washe garin ranar muka tafi dubai saboda gujewar tsurkun mutane seda mukayi shakara biyar muka dawo Nigeria lokacin kuma muka shedawa duniya kai danmune damuka haifa, koda wasa ban taba tambayar auntie bashariya suwaye iyayen ka waye kai sam bamu saniba ban taba tsamma nin haka zata kasan ce bah kayi hkr Ridwan da boye maka asali da mukayi ka yafemin kayi hanzarin zuwa gurin auntie bashariya kuma don Hamraz ya shaida mata ta hada komay nata tabar garin ya danka mata kudi masu yawa yace ta nisanta damu, zanta binka da Addu'ah akoda yaushe Allah yabaka nasara har kazo ka rabani da Hamraz don yanzu rayuwa dashi bakin cikine dakuma tashin hankali a gareni sam ko ganin shi bana sonyi kate maka kazo ka rabani dashi Ridwan harna mutu bazan dena ganinka a matsayin dana ba ina tare dakai akoda yaushe kada ka dagawa kanka hankali kada wani abu yasa meka Allah yana tare dakai shine ze kareka daga cikin damuwa da zaka shiga yanzu dangin ka bazaka wahala ba zaka samesu indai ka hadu da auntie bashariya shikenan, ina maka fatan alkhairi akoda yaushe farin ciki na kada kum ka taba sawa zuciyan ka cewan kai maraya ne! Indai kasa wan nan aranka to hakika kaci amanata yarona! Kahuta lpy, zanta tsumayin ka daga yau har zuwa ranar da zaka zo ka rabani da azzalumin nan!!"
Wasu irin hawaye ne masu zafi suke sauko wa daga idanun Ridwan cukwikuye paper din yayi hannun sa na wani irin bari na tashin hankali yanajin duniyar tana wani irin juya masa Rafeeq yana gefen shi a cikin motar shima ya shigo tare suka gama karanta abinda takaddar ta kunsa fuskarsa kamar zeyi kuka haka yake kallon Ridwan da a yanzu ya kasa jurewa yasaka kuka!"
Mahmoud da Meenal 11: 12am a gidan su Bilal ta musu saboda jirgi na safe suka biyo domin tafiya daura da wuri fuskar Meenal babu walwala ko kadan bata da sukuni saboda batasan tafiyan sam wan nan dalilinne yasa bata gallabi kowaba a gidan Mahmoud lokaci daya ya fahimci gidan akwai abinda yafaru don shima Bilal baya wata walwala suna parlour azaune Daddy ya sauko da fara arsa suka gaisa yace "Meenal kodai kiyi zaman ki anan tunda bakyasan tafiyan nan ko kadan naga alama!" Mahmoud ta kalla ta tuna gargadin daya mata da suna jirgi wani yawu ta hadiye tace " a ah zanje Daddy kai nane kawai yake ciwo Daddy" "ashsha Allah ya sawake zede na tafiyan safen da kukayi ne" mummy ya kalla yace " Maryam yaudin zaki tafi kose goben in Allah ya kaimu?" Sara ta kalla wanda tana cikin damuwa sosai na rashin kulata da Bilal yayi yamaki saurarar ta tace " yau zan raka Sara gida ne sedai gobe InshaAllah nima da wuri zan tafi!" Daddy yace " To Allah ya nuna mana bari muma yanzu muzo mu dau hanya Janan tana can harda kukan murnar ta nace ga munan muna hanya mussamman dataji da kawar ta Meenal za azo!" da mamaki Mahmoud yace " lallai tayi kokari! har yanzu bata manta kawancen su da meenal bah kuma na tabbatar Meenal ta watsar da ita yanzu, yarinya me hakuri Meenal taci zalin yarinyar nan itama nasan ta girma kamar meenal koh Daddy?"
Dariya Daddy yayi yace " bakada dama Mahmoud ta ina taci zalin ta Meenal, ay Janan itace sakarai har yanzu janan bata raina abin kuka tana da hakuri sosai kamar maman ta marigayiya Allah ya jikanki Hadiza!" suduka sukace ameen, har suka tafi Bilal beko kalli Sara ba infact ma maganar ma bayin ta yake da kowaba, mummy kadai yay wa sallama suka tafi aikuwa kamar zatayi kuka har abin ya ishi mummy cikin fushi tace " Haba Sara? kada kibani kunya mana! don yaki kulaki seme!! ke kamar bama cebah! duk ina class din naki yake? karewa ma ina aure zakuyi kitattara shi kikyale da kanshi ze nemiki shi ko ajikin shi ke kuwa kin hana kanki sukuni banna son irin hakafa!" hawaye taf a idanun Sara tace "Wlh auntie nasan halin Bilal sosai idan yayi fushi yanada wuyan sha ani zafin kishine ya debeni nagaya masa magana meyasa baze yimin uziribah?" hararar ta mummy tayi tace " Tabbas kuwa Sara kika bida Bilal ahaka to wlh rayuwar ki akunci zata kare! akan mace namiji bashi da tabbas karki kuskura ki saurara masa akan mata!! ki mallaki abinki ke kadai in kuma kika masa lakwa lakwa zakisha mamaki da idon kidai kinga yadda mata ke binshi seki zauna ko auren kukayi ya sake auro wata wadda zatazo tana miki mulki da gida!! Ay indai kanason kwanciyan hankali a gidan ka ka zauna kai kadai da mijin ka seka tashi tsaye wayace miki haka ake sake jiki a zauna?" kallon ta Sara tayi tace "Wlh dana sani nabisu mun tafi tare duk tsiya nasan zan shawo kan abina kafin mudawo ban san meyasa kika hanani zuwa bah kika ce naje gida!" wani kallo mummy tayi mata awulakan ce tace " kekuma kin zama jela bakida aiki duk inda zasu kibi su ke uwar soyayya! ke bazakija girman kiba! Ko kunya babu ko ina se a tafi dake kafin ayi auren! koni haka kikaga inayi koni abinda yasa nakawo tafiya ta yanzu saboda banason shiga familyn daddyn shi ko kadan saboda irin kallon da suke min sam basa kauna ta Sara basa sona dole bazan kauna ci zuwa inda sukeba bare kena bari kije! don haka kema kija girman ki!" Sara tace " wai wani kallo suke miki ne da kullum kike fada kinyi wani abune da bakyason zuwa can ne?" hararar ta mummy tayi tace " bansani ba! inkina ganin zama acikin su dadine wataran ki gwada kiga yadda zasu wulakan taki! Mara tunani da lissafi kawai! Koke yanzu akayo miki kishiya ta mutu dangin ta ba tsanar ki zasuyi bah, kuma da dangin Amina danashi Alhaji duka kusan sun zama abu daya shiyasa tun daga mutuwar Amina suka doramin karan tsana, so bazan sake hanaki zuwa daura bah Sara zan bari kisha kallo da idanun ki!" harta tafi tajuyo tace " ki tashi kuma kishir ya don bazan zauna jiran ki bah!" sama ta haye abinta takyaleta nan zaune tana hawaye....✍️