Mutum Mugu Ne

55

by @azizat

*MUTUM.....Mugu ne*


                     55


Wasa- wasa duk kwanakin da Sajid ya yi a ɗakin Ziha, Zaytunah cikin rashin lafiya ta yi su. Da dare kasa bacci ta ke yi. Daga ta kwanta sai ta dinga imagining Sajid da Ziha, and it drives her nuts.

"Wallahi Saudah zan yi hauka, I can't take it anymore. Kin ga fiskar Sajid a 'yan kwanakin nan kamar wanda aka yiwa albishir da Aljannah, he looks happy"

Daga ɓangaren Saudah ta ce " Zaytunah ki kwantar da hankalin ki, ki nuna kamar ba ki damu da su ba, nan zuwa wata ɗaya sai mu koma wajen Malam a san yadda za'a yi"

"Wata ɗaya!" Zaytunah ta faɗa da ƙarfi. Saudah ba zan iya haƙurin wata ɗaya ba, nan da wata sati zan zo kawai ayi ta ta ƙare"

" kin ga mutane za su zarge ki"

"I don't care, as long as zan raba auren Sajid da Naziha, ba ruwana da maganar mutane"

Tun da ta ajiye wayar ta ke ta tsaki 'lallai ma Saudah wai na bari su zauna na wata ɗaya, a'a shekara ɗaya ne ba wata ɗaya ba'...

Wasa-wasa yau kwana goma sha biyu da zuwan Ziha gidan. Tsakaninta da Zaytunah sai harara dan ko ta gaisheta ba ta amsa wa. Sajid kam kullum ƙara gode wa Ubangiji ya ke da ya bashi Ziha sannan ya sa wa Zaytunah haƙuri. Dan tun da ya fara rabon kwana ba ta taɓa nuna tashin hankali ba. Ya ga ƙoƙarin danne kishinta da ta yi. Duk da ya san ba sa magana da Ziha, yana fatan a hankali komai zai daidaita.

Yau kwanan Zaytunah ne, suna zaune a dining ta na serving ɗinsu abinci aka kira wayanta. Ganin Saudah ne ya sa ta katse kiran.

" Mom that's rude" inji Nurain da ya ga abinda ta yi.

Zaytunah ta ƙaƙaro murmushi ta ce " Zan kirata idan muka gama cin abinci. By the way where is my princess?"

Aamir ya ce " she's with Nazzy"

Yassar ya ɗan mangare bakin shi ya ce " Anty Nazzy not Nazzy"

Aamir ya fashe da kuka

"Haba Yassar kuma sai ka dake shi. ka san sai a hankali za su saba da kiranta Anty"

" idan Yaya ya ƙwaɓi ƙaninsa ba laifi ba ne" Sajid ya faɗa yana kai abinci bakinsa.

"yi haƙuri adalin Shugaba" ta shafa kumatun Aamir tana rarrashinsa har yai shiru. A takure ta ke cin abincin dan rabin hankalin ta na kan wayar ta. Tunanin abinda Saudah za ta gaya ma ta ta ke, dama sun yi jiya za ta kira Malam su ji abin yi.

Bayan sun gama cin abinci sai ta kwashe kwanukan ta kai kitchen. Ta fito da waya ta kira Saudah. A hankali ta ke magana kamar wata sabuwar munafuka " Saudah mi Malam ya ce?"

Shigowar Saratu kitchen ɗin ya sa ta yi saurin cewa "zan kira ki anjima"

Ta dubi Saratu ta ce " ke kuma tun ɗazu mi ya hana ki fito ki yi wanke-wanke?"

Saratu ta ce " ina Sallah ne"

Zaytunah ta fice daga kitchen ɗin ba tareda ta ce komai ba...

Ɗakin Azra ya shiga jin dariyar su a ciki. A kan gadon Azra su ke suna game ɗin chess. Ya shigo a hankali ba tare da sun ji shigowarsa ba har sai da ya zo gab da gadon sannan Ziha ta ɗaga ido ta kalle shi, Ta wani sake masa murmushi. Ya sa hannu ya rufe idon Azra

"Dad" Azra ta faɗa tana dariya.

Shima dariyar ya yi ya cire hannunsa sannan ya kissing goshinta ya ce " my princess" ya zauna kusa da ita ya riƙe hannun Ziha ɗaya ya kissing. Kunyarsa ta ji dan Azra ta gan shi.

" You should kiss her forehead just like you did for me" Azra ta faɗa hankali kwance.

"Azra!" Ziha ta faɗa da ɗan ƙarfi.

Sajid ya ce " you are Absolutely right my princess, I will do just that"

Ziha ta sa hannu ta rufe fiskarta.

Azra sai dariya ta ke ya matso dai dai fiskarta ya sa hannu ɗaya ya cire hannayenta biyu ya kai bakinsa dai dai lips ɗinta, Ta gimtse su, ya yi murmushi sannan ya kissing goshinta da hancinta. Ya raɗa mata magana a kunne " ina bin ki bashi".....

Zaytunah na shiga ɗaki ta kira Saudah. Maganar da Saudah ta mata ya sa ta ƙyalƙyalewa da dariya ta ce " Saudah bar min komai ina nan zuwa nan ba da daɗewa ba"

Da dare Sajid ya yiwa Zaytuna maganar tafiya Taraba da zasu yi jibi, zai raka 'yanbiyu da za su je yiwa 'yanuwa bankwana.

" Ban san ya tafiyar za ta kasance ba, kin ga su Azra na school ko za a kai su gidan su Mommy ne?"

Zaytunah ta ce " ba ka ce tare za ku je da su USA ɗin ba saboda akwai aikin da za ka yi a can, just go with her, sai ku yi honeymoon ɗinku a can kawai. Ni zan zauna da yara"

Ya yi mamakin kalaman ta, he can't believe wai Zaytunah ce ta yi wannan maganar. Ya kissing hannunta ya ce "Thank you Zayty"

Sajid, Ziha da 'yanbiyu suka wuce Taraba da safiyar ranar Litinin.

Ita kuwa Zaytunah daga kai su Azra makaranta ta wuce airport sai Lagos. Saƙo ta bar wa Saratu akan idan yaran sun dawo ta kai su gidan su Mommy.

Daga gidan Saudah direct gidan Malam suka wuce.

" Malam ba ka san irin dauriyar da na ke yi ba 'yan kwanakin nan da mu ke sharing Sajid."

" wani irin abu ne ke ɗagawa Mijin ki hankali?"

Malam ya tambayi Zaytunah

"Ban gane ba Malam, be more specific"

" miye mijin ki ba ya so, wanda zai iya shiga tashin hankali idan yana kusa da abin?"

Zaytunah ta yi shiru tana tunani chan ta ce "ƙwai, Sajid is allergic to egg"

"Kin tabbata ƙwai zai ɗaga ma sa hankali har ya kasa samun nitsuwa"

"Idan akwai abin da zai iya kashe miji na cikin sauƙi to ƙwai ne. He has a deadly allergy to egg. Wata rana farkon auren mu na manta baya son ƙwai na yi home made bread na sa ƙwai a ciki, kaɗan ya ci amma idan kaga halin da ya shiga kamar wanda ya ci poison sai da ya kwana biyu a asibiti. Likita ya ce da ya ci da yawa da zai iya mutuwa. System ɗinsa is very sensitive to egg, duk min kaɗan ɗin ƙwai idan ya cu sai ya dame shi. Idan ya ji ƙarnin ƙwai ya dinga amai kenan ranar ba zaman lafiya"

"Tunda kin tabbata ƙwai ce ba ya so to aikin ki da sauƙi. Yanzu za ki kawo min tsillin gashin kishiyar ki guda ɗaya, ki tabbatar ke ki ka cire gashin da kanki. Idan kin kawo wannan sai a haɗa sauran aikin"

"Dole sai ni zan cire gashin?"

"Kar ki kawo wanda ya faɗi ko wanda ta cire da hannunta, wanda kika sa hannu kika cire da kanki za ki kawo"

Zaytunah ba ta dawo Abuja ba sai kusan ƙarfe shaɗaya na dare saboda jirgin su bai tashi da wuri ba. Tunanin yanda za ayi ta tsinke gashin Ziha ya hanata samun bacci. Ƙarshe ta barwa ranta akan komai zai zo da sauƙi.

Ranar Talata da yamma su Sajid suka dawo, tafiyar su sai Alhamis. Da safiyar ranar Laraba Sajid ya kai Ziha makaranta dan ta ƙarasa registration. Dama ya sa Yassar ya biya registration fee da wasu minor things da ake biya.

Sajid bai samu daman zuwa ya ɗauke ta ba sai driver ya turo mata. A falo ta samu Zaytunah tana hira da wata ƙawar ta, ta gaishe su amma ƙawar ce kawai ta amsa tareda cewa" Amarya har kin fara fita ne?"

Ziha ta ce "na je registration ne"

"Ayya, Amarya Allah ya sanya alkhairi ko" Ziha ta amsa da Amin.

Lokacin da Ziha ta haura sama Zaytunah ta yi tsaki ta ce " Haba Rahima, miye na amsa gaisuwarta, salon ta raina ki"

"Uwargida Zaytunah kenan, yarinyar tana da hankali. Idan kika kwantar da hankalin ki za ku yi zaman lafiya da ita. Ba ki ga zaman da mu ke da Anty ba, Anty ta riƙe ni tamƙar ƙanwarta"

" ke dai kawai kishiyar ki dan ba ta haihuwa ne ke kuma kin haihu shi yasa ta ke kwantar mi ki da kai dan ta san ke ce da gida yanzu"

" Allah Zaytunah tun ina amarya ta ke ja na a jiki kuma har yau, su Mahmud duk sun fi sabawa da ita da ni ma"

"Whatever, ni dai yarinyar nan zaman ta temporary ne a gidan nan. Ba za ta haihu bama balle har su Azra su samu step siblings"

"Hmmm Zaytunah ki bi duniya a hankali. Ni ya labarin ƙawar ki ne. Na ji wai ana ƙaran ta ko?"

Cikin rashin fahimta Zaytunah ta ce "wace ƙawa ta?"

"Sadiya mana"

" as in Sady ƙawata da na sani"

" e , aka ce ta ci kuɗin wani Alhaji, wata fitinanniyar matarsa ta maka ta kotu, kai akwai many rumors akanta abin ba daɗin ji"

"This is unbelievable, wai a ina ne haka?"

"Kaduna"

"Well, ba ni da lokacin ta yanzu, sai na gama magance nawa matsalar na bi ta kanta"

.....

Naziha na shirya kayanta cikin jaka aka buɗe ɗakinta, ba ta ɗago ba dan ta ɗauka Azra ce. Ƙanshin turaren Zaytunah da ya tunkaro ta ya sa ta waigo. A ɗan tsorace ta ce " barka da dare Anty"

" ki ɗau kaya ma su nauyi, saboda yanzu lokacin ƙanƙara ne"

"Ok Anty"

Zaytunah ta matsa kusa da ita tana ƙare mata kallo. Guntuwar bath robe ne a jikinta fari ƙal, ya tsaya iya rabin cinyarta. Da alama ba ta jima da wanka ba. Gashinta a tsefe ne ta ɗaure shi da ribbon ya yi high puff saboda cikar gashinta.

Ta yi Murmushi ta matso daf da ita ta raɗa mata magana a kunne " enjoy this 9 days to the fullest, duk abin da kike so My Sajid ya mi ki, ki ce ya mi ki tun yanzu, cause after this 9 days bana tunanin za ki sake amsa sunan matar Sajid"

" Tawakkaltu Alallah Anty"

Zaytunah ta yi murmushi ta ce " we'll see"

Zaytunah na fita Naziha ta zauna kan gado tana ajiyar zuciya " Allah please protect me from this woman" maganganun Zaytunah da actions ɗinta na rashin nuna damuwa its suspicious. Ta san zafin kishin Zaytunah da wuya ta bar ta haka nan su yi zaman lafiya. Ta jima a zaune kafin ta cigaba da haɗa kayan.

Zaytunah na shiga ɗaki ta buɗe tafin hannun ta sai ga tsillin gashin Ziha a hannunta. Ta yi murmushi ta ce " very soon Ziha za ki ƙwammace ba ki shigo gonar Zaytunah ba"

Ta saka gashin a leda, ta ɗaure shi sannan ta je ta buɗe drawer ta jefa ciki.

Da safiyar Alhamis suka wuce airport wanda Zaytunah ce ma ta mu su rakiyar.

Zaytunah na komawa gida ta kira Saudah ta gaya mata ta samu tsillin gashin Ziha. Saudah ta ce ta bari sai Monday ta zo dan za ta je Jigawa bikin ƙanwarta. Zaytunah ba haka ta so ba amma ta haƙura a haka.

Tun da suka sauka ƙasar ta kasa gane kanta. Duk da ana sanyi amma ba sanyi ne matsalar ta ba. Ga shi Sajid idan ya fita sai dare ya ke dawo wa. 'Yanbiyu ma suna fita school" sai gidan ya ke mata wani iri.

Ranar Talata da yamma Irene ta kawo musu ziyara.  Tun da suka bar Nigeria ita ma ta fara shirye-shiryen yin Msc ɗinta. 'yanbiyu suka takura wai sai sun fita zaga gari, wannan ya sa ta kira Sajid ta faɗaa masa, ya ce mata ba komai su je.

Dukkan su huɗu suka fita. Ba su dawo ba sai chan dare. Da su ka dawo har lokacin Sajid baya nan. A gajiye Ziha ta shirya cikin kayan bacci ta kwanta. Cikin zuciyar ta ta ke lissafi ya kamata ace ta ga period ɗinta kwana uku da suka wuce amma shiru. Da sauri ta tashi ta zauna tana sake lissafin. " could I be pregnant?" Ta tambayi kanta. Ta girgiza kai " no, its too early"

Ta jingina kanta da pillow " but what if I'm pregnant. I have to confirm"

Tana cikin tunani Sajid ya shigo " I'm sorry Ife mi, daga yau komai ya dai-dai ta. The deal is closed." Ya kissing goshinta ya ce "barin yi wanka"...

Washegari Laraba suka wuce Paris su biyun su. Anan suka ƙarisa cin amarcin su. Ba su dawo America ba sai safiyar litinin.

Da asubahi Naziha ta tashi ta shiga banɗaki ta fito da PT strip da ta siya wani fitar su shopping da suka yi. Ta sa fitsarin ta tana bin strip ɗin da kallo. Ganin reading ɗin ya sa layi biyu sai ta zaro ido. " Ya Allah, positive" ta yi ajiyar zuciya sannan ta yi hamdala ta tattara strip ɗin ta jefa a dust bin. Sai da ta tsarkake jikinta sannan ta yi alwala ta fito. Sajid da ke kwance ta kalla ta yi murmushi ta ƙaraso wajensa ta kissing goshinsa ta fara murza kunnensa a hankali. Ya buɗe ido ya sake rufewa

"we have a plane to catch, Ade mi" ta faɗa tana cigaba da shafa kunnensa. Ya yi murmushi ya ce " mu bari sai ranar Jumu'ah mu koma"

"Ade mi an fara lectures a school fah" ta faɗa a shagwaɓe.

Ya buɗe ido ya kalleta cike da shauƙinta ya ce " anya ba za ki haƙura da school ɗin nan ba"

"Noooooo" ta faɗa da ɗan ƙarfi.

Ya jawota ta faɗa jikinsa ya ce " then you have to work to get my permission" kafin ta amsa ya haɗe bakin su....

' yanbiyu ne suka raka su airport bayan ya musu nasiha akan su ji tsoron Allah, su kama mutuncinsu.

Hankali kwance Zaytunah ta tarbe su lokacin da suka dawo har da tsokala "Naziha daga kwana tara sai da kuka kai kwana goma sha uku. Ko dai na bar mi ki shi ne ku yi kamar wata uku kuna amarci " Naziha dai murmushi ta yi dan ba ta san mi za ta ce mata ba.

Sajid ya ce "that would be so sweet of you Zayty, but then I need you too"

Zaytunah ta yi murmushi ta ce " My Sajid ai na tsufa"

Sajid ya ce "Ni dai ban faɗa ba, my Zayty ever green ce, bata tsufa"....

*

Hankali kwance Zaytunah ta fasa saman ƙwan ta jefa 'yar ƙaramar layar da ke ɗauke da tsillin gashin Ziha a ciki. A hankali ta saka shi cikin ramin da ta tona, ta sa ƙasa ta rufe shi. Ta tashi ta sake smoothening wajen kamar ba ta tona ba.

Ta yi sauri ta bar garden ɗin kafin wani ya gan ta. Ta san yau kam komai zai tafi yadda ta ke so.

Ƙarfe biyar Naziha ta dawo daga class, yau ne ta fara zuwa lectures bayan kwana biyu da dawowar su daga ƙasar America. Kasancewa yau Sajid a ɗakin ta ya ke ya sa a gurguje ta shige kitchen ta fara shirya abincin dare ita da Saratu.

Ƙarfe takwas saura na dare Sajid ya dawo. Kai tsaye ɗakin shi ya shiga. Ya rasa dalili tun da ya shigo gidan yanayinsa ya chanza.

Ta ji shigowarsa gidan dan haka ta yi saurin gyara jikinta ta fito ta shiga shashinsa. Fiskarta ɗauke da murmushi dan a yau ta ke son sanar da shi tana ɗauke da ciki.

Ya fito daga wanka yana shafa mai ta shigo. Shigowar ta ɗakin ya tsinci kansa cikin wani hali. Ya rasa wani irin wari haɗe da ƙarni ya ke ji. Da murmushi ta kalle shi tana ƙarasowa wajensa ya fara toshe hancinsa.

"Ade mi, mi ya faru?"

Yana son mata magana sai amai, ya dinga kwarara amai. Ta dafa shi tana son tallafoshi amma ina kamar ƙara aman ta ke yi. Hankalinta ya tashi ganin yadda idonsa ya yi ja yana jan numfashi da ƙyar. "Anty, Anty, Anty Zaytunah" ta fara kira da ƙarfi" ganin Sajid a ƙasa ya na riƙe da wuyan sa kamar wanda aka shaƙeshi ya sa ta fita daga ɗakin da gudu tana kiran Zaytunah.

Zaytunah dama tun shigar Sajid ɗaki ta baza kunne ta ji mi zai faru. Malam ya ce in dai ta bisine abin nan to duk inda Naziha ta ke Sajid ba zai iya zama ba.

Jin kiran Ziha ya sa ta taso da sauri a bakin ƙofa ta tare ta " mi ya ke faruwa?" Ta tambaya kamar bata san komai ba.

"Anty, Ade mi...Daddyn Azra, he's sick..." Zaytunah ba ta tsaya jin ƙarshen ba ta yi ɗakinsa da gudu, Ziha ma ta bi bayanta.

Tun fitar Ziha a ɗakin nitsuwa ya fara zuwa ma sa. Duk abinda ya ke ji ɗazu ya dena ji. Ya dafe kan sa yana mamakin abin da ya faru. Shigowar Zaytunah ya ɗaga ido ya kalle ta yana so yai magana tsikar jikinsa ya tashi. Shigowar Ziha ya sa shi fara jin warin da ya ji ɗazu. Ya fara toshe hancinsa amma ina warin wani irin shigarsa ta ke yi. Jikin sa na kakkarwa numfashinsa na shirin ɗaukewa.

Da ƙarfi Zaytunah ta ture Ziha da ke shirin taɓa Sajid da ke kwance ƙasa " ki fita daga nan, ba kya ganin ke kika sa shi cikin wannan halin. Call the doctor" Ziha ta fita daga ɗakin da sauri tana hawaye.

Ziha na fita daga ɗakin jikin Sajid ya fara dawowa normal. Zaytunah ta yi murmushi ganin maganin Malam ya fara aiki.....

©AzizatHamza2019