58
by @azizat
*MUTUM.....Mugu ne*
58
ABUJA
"Naziha, ko za ki je gida ki nemi taimako, kafin wannan abin ya fi haka girma. Ko kuma ki kira Iyayen Alhaji ki sanar da su abin da ke faruwa"
" Baaba Saratu ba zan iya ba, yaushe aka yi aure na har da zan fara kiran gida ina kawo complain. Ki dai cigaba da min addu'a, i'm sure tunda ban taɓa danne hakkin wani ba Allah zai kawo min mafita"
Saratu ba haka ta so ba amma babu yadda ta iya haka ta haƙura da maganan ta taimaka ta share wajen da plate ɗin ya tarwatse. Ziha ta haura sama dan ta gyara jikinta. Tana haurowa ta ga Zaytunah ta shiga falon Sajid da sauri yadda ta buga ƙofar ka san tana cikin tashin hankali. Ta girgiza kanta ta shige nata ɗakin. Wanka ta yi ta sa kaya ta zo ta zauna a sallaya tana karanta Alƙur'ani. Kusan minti talatin sai ga Azra ta shigo ɗakin tana kuka, kai tsaye ta faɗa jikinta ta cigaba da kuka.
"Baby na mi ya faru, what happened?"
Cikin kuka ta ce "Mom is crazy today, she yelled at me and slapped me"
Ziha ta ajiye ƙur'ani gefe ta gyara mata zama a cinyarta ta ce "stop calling your Mom crazy, it's very bad to do so. Good girls don't do that, kin ji"
Azra ta gyaɗa kai.
Zaytunah ta bankaɗo ƙofa ta shigo, Azra na ganinta ta challa ihu ta ƙanƙame Ziha. Ita kanta Ziha yanzu kam ba ta ga laifin Azra da ta kira Zaytunah Crazy ba domin wata ƙaramar rigar bacci ne a jikinta har yanzu, gashinta a barbaje kamar wata sabuwar kamu. Ɗazu da ta same ta a kitchen akwai bonnet a kanta kuma da alama gashin a ɗaure ya ke to yanzu kam yadda ka san ta yi wata uku bata taje ba.
Ta dakawa Azra tsawa akan ta bar jikin Ziha, yarinya ta cigaba da kuka tana ƙanƙame Ziha.
Da ƙarfi Zaytunah ta zo ta finciketa ta fita da ita. Sai ihu ta ke tana kiran "Nazzy, help me"
Duk labarin cikin Ziha ne ya birkita Zaytunah, yaran na ta ma yau bata bar su ba, tun ɗazu ta ke ta musu faɗa.
Ziha ta cigaba da jin kukan Azra na wani lokaci daga baya kuma ta ji shiru. Cigaba da karatun Ƙur'ani ta yi dan ta samu sanyi a ranta.
Tun da safen kuma bata sake jin ɗuriyar Zaytunah ba. Yaran sun dawo daga school Saratu ta shirya su su ka wuce Islamiyya bayan sun ci abinci. Sajid ma sai dare ya dawo. Shi kansa bai san inda Zaytunah ta ke ba, dan tana ji yana tambayar Saratu ko ina Zaytunah ta ke tace masa bata sani ba. Sai da ta ga ya haura sama sannan ta bi bayansa, lokacin da ya shigo dama tana kitchen tana shan kankana.
Ta shiga falonsa baya nan, ta wuce ɗaki, ta murɗa sai ta ji a kulle. Ta ƙwanƙwasa. "Azra i'm coming" ya faɗa daga ciki da alama ya ɗauka Azra ce. Minti ɗaya sai gashi ya buɗe ƙofar, yana ɗaure da towel da alama wanka zai yi. Yana ganin ta yai saurin rufe ƙofa kamar wanda ya ga abin tsoro.
"Ade mi, please open the door, please talk to me" ta cigaba da buga ƙofar tana kuka amma ya ƙi buɗewa, ta fi minti talatin a wajen tana buga masa ƙofa. Ganin ya ƙi buɗewa ya sa ta haƙura ta koma nata ɗakin ta kwanta ta cigaba da kuka.
Shi kam bayan ya maida ƙofa ya rufe zama yai a bakin gado ya rasa mi ya ke ma sa daɗi. A office ya yi ta tunanin Ziha amma da ya dawo sai ya ji ko sunanta baya son tunawa. Gashi da ya ganta yanzu wani shock ya ji a jikin shi, kamar akwai wani force da ke hana shi raɓanta. Ya jima zaune yana jin bugun ƙofar ta kafin da ya ji shiru ya shiga banɗaki dan ya yi wanka.
Zaytunah kuwa Lagos ta wuce, bisa shawaran Saudah suka wuce wajen Malam. Anan ta zayyane ma sa Ziha na da ciki.
"Yanzu mi ki ke so ayi mi ki" ya tambaye ta
" a hallaka cikin na ke so, kuma ya sake ta"
"Na riga na gaya miki rabuwar su mai wuya ce sai dai kamar yadda abin nan ke ruɓewa a cikin ƙasa haka soyayyar da ke tsakanin su zai cigaba da lalacewa, ki yi haƙuri zuwa lokaci kaɗan komai zai zama yadda kike so"
"Malam, is like you don't get it, Naziha ciki ta ke da shi, Cikin Sajid. Ko da sun rabu za a samu ɗa ko 'ya tsakaninsu, ka ga sun haɗa zuri'a tare kenan"
"Idan haka ne, da ba ki yi wahalar tahowa ba, akwai maganin zubar da ciki ai na zamani, ki zuba mata a abinci ta ci, cikin ya zibe tinda shine matsalar ki yanzu"
Saudah tace "mi zai hana a ma ta kurciya, ta bi duniya kawai"
"Saudah, what's kurciya?"
Malam ya ce " ƙaramin aiki ne wannan ai idan kin amince"
Saudah ta ma ta bayanin kurciya ba tareda wani tunani ba ta ce " perfect, Malam ayi shi kawai"
***
Tana kwance tana kuka, kaman an tsikare ta sai kawai ta tashi ta ɗau hijab ta sa, ta haɗa wasu kayanta cikin ƙaramar jaka ta fita daga ɗakin. Tana saukowa ta tarar yaran na kallo a falo basu ankara da ita ba har ta fita daga gidan. Da taje wajen mai gadi ce ma sa ta yi za ta je ta siyo abu ne. Haka kawai ya kasa yi mata musu ya buɗe mata ƙofa ta fita.
Da safe hankali kwance Zaytunah ta dawo gidan tana murna, daga yanzu ta rabu da Ziha har abada. Dan ta tabbatar da aikin da aka mata, sai ta shiga ɗakin Ziha amma ba ta nan. Ta kira Saratu ta tambaye ta ko ta ga Naziha. Sai a lokacin Saratu ta ankara tun jiya da dare rabon da ta ga Zihan ma.
"Ina ga tana ɗaki"
" ina ga ba ta gidan" Zaytunah ta faɗa tana murmushi.
Saratu ta je ɗakin Ziha amma ba alamar ta. Mamaki ya kama ta, to yaushe Ziha ta fita bata sani ba?.
Ta dai share, ƙila lokacin ta na shirya su Azra ne ta fice.
Wasa-wasa har dare ba Ziha ba dalilin ta.
Saratu ta damu dan ga wayar Zihan a ɗaki ba ta fita da ita ba. Da farko ta ɗauka school ta je amma da ta ga har dare ba ta dawo ba sai ta yi tunanin ba school bane. Har washe gari ba labarin Ziha. Lokacin Sajid zai fita aiki ne ma Saratu ta tare shi "Alhaji, ni kam Amarya ta yi tafiya ne?, na ga tun jiya ba ta gidan nan"
Zaytunah ta dafa kafaɗarsa "My one, Ziha tafiya ta yi garinsu, kar ka damu kanka, ba nan kusa za ta dawo ba"
kamar wani wawa haka ya yadda da maganar Zaytunah ya ce wa Saratu "to kin ji abinda ta faɗa" ya wuce ya bar ta tsaye tana salati.
Zaytunah ta raka shi waje.
Saratu na tattare wajen dining Zaytunah ta shigo " ina ga kin gaji da aiki a gidan nan, na ga sabon salon haɗa guri kika fara"
" ki yi haƙuri Hajiya" ta faɗa tana jimamin abin a ranta.
"Ki san matsayin ki anan gidan, ba na son munafirci, shi da ya kawota gidan bai neme ta ba sai ke za ki fara jajenta saboda gulma"
" Allah ya huci zuciyar ki, Hajiya"
Zaytunah ta haura sama tana takunta cikin jin daɗi da kwanciyar hankali.
Abu kamar wasa har sati babu Ziha ba dalilinta, Azra har kuka ta yiwa Sajid akan ya kaita wajen Ziha amma shi kansa bai san inda ta ke ba. Alamu ma sun nuna bai damu da ɓacewarta ba.
Tun ɓacewar Ziha maimakon Zaytunah ta samu farin ciki kamar yadda ta yi hashashe sai kuma ya zamana ba ta samu yadda ta ke so ba. Yaranta sun dena sake jiki da ita musamman Azra. Ga uwa uba ta rasa gane kan Sajid, kullum idan ya dawo sai dai ya zauna ya yi ta tunani.
Ta yi tambayar duniyar nan kan mi ke daminsa sai ya ce mata ba komai. Duk wani kayan jan hankali idan ta sa shi ba ya gani. Idan kuwa ta fara ƙoƙarin takalo shi da wasa sai ya tashi ya bar wajen ya ce ba shi da lafiya. Ga shi dai Ziha ba ta gidan amma gidan maimakon ya mata daɗi sai ya zamana gara ma lokacin da Zihar ta ke gidan.
Yau Mommy ta zo gidan, tun bayan bikin Ziha. Ba ta samu Zaytunah a gida ba dan haka ta ce wa Saratu za ta wuce tunda yaran ba sa nan gashi numbar Zaytunah ba ya shiga. Har ta juya za ta tafi sai ta ce " dan Allah kira Amarya mu gaisa kafin na wuce"
Saratu ta ce "ba ta nan"
Mommy ta yi murmushi tace " hala bata dawo daga makaranta ba"
Saratu ta yi shiru. Tunani ta ke a ranta ko ta faɗa wa Mommy ko kuma ta yi shiru. Har Mommy ta fara tafiya sai ta ce "Hajiya, dan Allah ki ɗan tsaya akwai abinda zan faɗa miki"
Mommy ta juyo da mamaki tana kallon ta " Bismillah mi nene?"
Saratu ta yi ajiyar zuciya ta ce " Hajiya, Naziha ta ɓata fa, babu wanda ya san inda ta ke"
" Hasbunallahu wa ni'imal Wakil, ki faɗa min ya aka yi haka"
Saratu ta zayyane ma ta iya abinda ta sani game da ɓacewar Ziha da kuma irin abubuwan da suka faru kafin ɓacewar ta.
Mommy ta dafa kai tana salati....
***
Satin Shabbir biyu a Maiduguri su ka dawo Abuja shi da Nana, ya warke sarai sai dai kuma har yanzu ba ya magana. Saura sati ɗaya bikin sa da Shahidah da Nazira sai dai abin da ya faru ya sa Alhaji Idris ya ce a bar auren sai ya warke gaba ɗaya. Da aka gayawa Shahidah cewa ta yi yanzu ne Yaya Shabbir ya fi buƙatanta dan haka ita ta amince ayi auren nan da sati ɗayan. Tunda yarinya ta amince dole Alhaji shi ma ya amince. Sai dai kamar yadda Shabbir ya buƙata a faɗawa Nazira abinda ya same shi saboda idan za ta iya zama da shi a haka to sai a ɗaura auren tareda Shahidah idan kuma ba za ta iya zama da shi yanzu da ya kurmance ba shikenan ya janye neman.
Har Bauchi aka zo aka sanar da Abba, tun kafin Abba ya gayawa Nazira ma ya riga ya yanke hukunci akan kurumta ba dalilin da zai sa a fasa aure bane, dan haka aure na nan a lokacin da aka sa.
Da ya samu Nazira da zancen kuka ta dinga yi tana tausayin masoyinta. Ta ƙara tabbatar wa Abba za ta auri Shabbir ko da matsalarsa tafi ta kurumta...
©AzizatHamza2019.