Mutum Mugu Ne

59

by @azizat

*MUTUM.....Mugu ne*


                     59


Mommy na fita daga gidan ta kira Sajid ta tambaye shi ina Ziha, da mamaki sai ta ji ya ce bai sani ba. Salati ta yi ta kashe wayar. Ta sake gwada numbar Zaytunah ta ci sa'a ya shiga.

"Hello Mommy ina wuni"

" ki na ina? Na zo gidanki ba kya nan"

"Sorry Mommy, na fita ne amma yanzu haka ina hanyar dawowa"

" ki same ni a gida akwai maganan da za mu yi" daga haka ta kashe wayar ta je ta shiga mota zuciyarta cike da tunani kala-kala...

***

Tunda aka sauke su a park ta fito tana tafiya ba tareda ta san inda za ta je ba. Da yunwa ya addabeta sai ta tsaya a wani shago ta sayi bread da fanta ta sha. Haka ta dinga yawo a garin Kano ba tareda ta san takamaimai ga inda za ta je ba. Dai dai ana kiraye-kirayen Sallan maghrib ta zo wucewa ta wani gida da mata ke ta fitowa da alama walima aka yi a gidan. Ta ji an riƙe ta, ta juyo a fusace kamar za ta doki wacce ta riƙe tan.

"Naziha" matar ta kira sunanta ai kuwa tana jin haka ta wafce hannunta ta fara tafiya da sauri. Matar ta cigaba da kiran ta "Naziha, Naziha" amma Naziha ko juyowa ba tayi ba sai ma ƙara sauri da ta cigaba da yi. Wata mata ta ce "ko dai ba ita ɗin bace"

Matar da ta riƙe Ziha ɗazu tace "da za tace ai ba ita bace" ta fara sauri ta bi hanyar da Zihan ta yi.

Sauri Ziha ta ke yi kamar za ta tashi sama. Tana tafiyar ma kamar ingiza ta ake yi.

Wasu yara ta gani su uku da za su je sallah ta ce su tare ma ta matar da ke ta saurin chan. Su tunanin su ma sata ta yi dan haka suka sa gudu.

ɗaya daga cikinsu ya sha gabanta. "Malama ana mi ki magana"

" Ziha ta juya ta ga matar ɗazu ne nan jikin ta ya fara rawa, ta ture yaron gefe ta sa gudu. Su ma yaran suka bita, abinka da yara nan da nan su ka cin mata. wani tsoho ya daka mu su tsawa ya ce "ya za ku riƙe matar mutane haka kamar wanda ta yi sata"

Ɗaya daga cikin yaran ya ce "ƙila satan ta yi matar chan ce ta ce mu tareta" ya nuna matar da ke ta sauri tana son cin musu.

" ku bar ni na tafi, ni tafiya zan yi" Ziha ta faɗa tana hawaye.

Tsohon ya ce " baiwar Allah tsaya mu ji ta bakin waccar matar tukunna"

"Ban san ta ba, ku bar ni na tafi" ta cigaba da faɗa

"Wallahi Naziha ce" matar ta faɗa lokacin da ta ƙaraso wajen.

" Malama lafiya kika ce a tare mi ki ita?"

"Naziha ba ki gane ni ba ne? Mommy Aisha ce fa"

"Ni ban san ki ba" Naziha ta faɗa kai tsaye.

"Innalillahi, mi ya ke faruwa?"

" kin ga ba wannan za ki ce ba miye haɗin ki da ita?" Tsohon ya tambaya.

"Wallahi 'yata ce, 'yar ƙawa ta Marigayiya. Baifi wata biyu bama da mu ka yi bikinta"

" ƙarya ne, ban san ki ba" Naziha ta faɗa tana kici-kicin ƙwacewa daga hannun yaran

Matar ta ce " ina ga akwai matsala, barin fito da hotunan bikinta ku gani" ta fito da waya daga cikin jaka, ta fara duba hotunan wajen ɗaurin auren su Ziha. Allah ya taimake ta ta samu. Ta nuna wa tsohon hoton ya ƙarɓa yana gani. Duk da hoton ta sha kwalliya amma hakan bai ɓoye kamanninta ba. Wani saurayi da ya ƙaraso wajen ya ce Baba mu gani ya ƙarɓi wayar shi ma yana duba hotunan.

"Idan da za ku cigaba da kallo akwai wanda muka ɗauka tare ma"

"Ƙila an samu matsala ne ta gudo daga gida, kun san yaran yanzu"

Ziha ta yi kururuwa ta wafce daga wajen yaran ta yi Titi da gudu. Cikin rashin sa'a wani mai mota da shima ya taho da gudu ya bigeta, ta faɗi ƙasa ta suma.

Su Mommy Aisha suka ƙarasa wajen suna salati...

***

Zaytunah kuwa ta je tarar Saudah a airport, ta sa wayar a chaji a jikin mota, da ya ke wayar mutuwa ta yi shi ya sa sai da ta ɗan yi chaji ta kunnata.

Sauda biki za ta je Kano amma saboda azarɓaɓi irin na Zaytunah wai ta zo ta ga gidanta yanzu babu kishiya shi ne ta biya mata kuɗin jirgi akan ta fara zuwa Abuja ta yi kwana ɗaya kafin washe gari ta bi jirgi zuwa Kano.

"Kin ji Mommy wai tana son gani na, mu je tare ko na fara zuwa na sauke ki a gidana kafin na je na same ta?"

"Mu je mana, sai na gaishe su ma ai"

Zaytunah ta yi murmushi tana ƙoƙarin chanja hanya....

Tunda Mommy ta ga Zaytunah ta shigo da baƙuwa sai ta haɗiye duk maganar da ke ranta. Ta ce " ai da kin ce da baƙuwa ki ke sai na sa a fara haɗa mata girki kafin ku ƙaraso"

" Mommy kar ki damu dama gaishe ki ta zo yi. Kika ce akwai maganar da zamu yi, maganar bikin Auta ne ko?"

Mommy ta juya tambayar kan baƙuwar ta ce "Saudah mi za a girka miki?" Lokacin da mai aiki ta ajiye mata ruwan gora da kuma juice.

"Mommy wannan ma ya yi, na gode"

Hira kaɗan su ka yi sannan Zaytunah ta ce za su tafi saboda Saudah gobe za ta wuce Kano.

Mommy ta ce su bar maganan sai goben.

Lokacin da suka tafi sai Mommy ta kira Alaja Kudirat su ka gaisa. Ita tunaninta ko za ta ji ta mata maganar Ziha amma ba ta ce komai ba. Lokacin da ta ajiye wayan dai tunanin da ta ke ɗazu ne ya dawo mata. Zaytunah ta asirce Sajid ta kori Ziha shi ne abinda ke faruwa.

" na shiga uku idan hashashe na ya zamto gaskiya, yau ko Sajid ba ɗan yaya na ba ne ba zan ji daɗin abinda Zaytunah ta yi masa ba balle kuma. Allah ka sa ba abinda na ke tunani bane ya faru"...

Saudah gidan su Zaytunah ta gani ta ke santi sai da suka je gidanta ta riƙe baki dan ya ci uban inda suka baro a kyau. Ai dole Zaytunah ta ƙi kishiya, irin wannan daula haka.

Saudah ta taso ne a gidan Yayan Mamanta, yana da arziƙi dai dai gwargwado shi ya sa ta tashi da son masu kuɗi. Ita zuwanta turai karatu ma scholarship ne. Tun a can ta san Zaytunah 'yar ma su kuɗi ce shi yasa ma ta liƙe mata musamman da ta ga Zaytunan kamar wawuya ce.

Ɗakin Sajid da ko masu aiki basa shiga su gyara masa shine Zaytunah ta shiga da Saudah tana nuna mata fasalin ɗakin mijinta.

"Gaskiya gidan ki ya yi kyau, musamman ɗakin Sajid ya tafi da ni sosai. Idan ka na kwana a irin gadon shi ai ba za ka taɓa tunanin lahira ba"

Zaytunah ta faɗaɗa murmushinta a dole ta ji daɗin maganar Saudah.

"Kin san Architect ɗin bature ne, Engineers da su ka yi aikin gidan ma yawancin su turawa ne"

"Gaskiya kin daure da kika bari har Sajid ya ƙaro aure"

" to ya zan yi da mummunan ƙaddara, dan ma yanzu na rabu da ƙaya na huta"

Hatta ɗakin Ziha sai da Zaytunah ta nuna wa Saudah da shi ke ba a rufe ya ke ba.

(Allah ya raba mu da halin rashin hankali irin na Zaytunah. Wai duka asirin gidanka ka gama zayyana wa ƙawa, har da kai ƙawa ɗakin miji...)

Abinci kam kala-kala aka kawo wa Saudah, haka ta buɗe ciki ta yi ta ci.

Sajid tunda su ka yi waya da Mommy hankalinsa ya tashi amma yana shigowa gidan ya ji wasai ya manta ma damuwar me ya ke yi.

A falonsa ya tarar da Zaytunah da ƙawar ta suna cin fruits. Ran shi ya ɓaci amma bai ce komai ba ya wuce ɗakinsa. Yana ƙoƙarin cire kaya ta shigo " my love tun ɗazu na ke sauraron dawowar ka, yau ka jima" tana ƙoƙarin taya shi cire kayan ya riƙe hannunta idonsa ya yi ja "get her out of my parlour"

" but my one, yara na falon ƙasa suna wasa, za su damemu shi yasa na kawota nan"

"Idan ba za ki iya fitar da ita ba, zan fitar da ita, ba daga falo kaɗai ba, daga gidan gaba ɗaya"

Yanayin da ya ke magana ya bata tsoro ta fice daga ɗakin da sauri. A falo ta tarar da Saudah hankali kwance tana cin apple, "ƙawata zo muje ɗaki akwai wani sirrin da za mu yi" 

Saudah ba ta kawo komai a ranta ba ta tashi suka fita.

"Ina son maganin mallaka, irin wanda kika yiwa mijin ki"

Saudah ta kwashe da dariya " yanzu kika shigo gari Zaytunah, dama na zuba mi ki ido ne na ga yaushe za ki farfaɗo"

"Seriously Saudah I need it fast, duk da Ziha ta bar gidan nan amma ba na jin daɗin zaman mu da Sajid kamar da, It's like yarinyar nan da zuciyarsa ta tafi. I want Sajid to be completely mine"

"Kar ki damu barin dawo daga Kano za mu je wajen Malam ayi mi ki mai kankat irin wanda aka min, amma fa za ki kashe kuɗi"

"Kuɗi ba matsala bane a waje na Saudah"...

Saudah a ɗakin Zaytunah ta kwana ita kuwa Zaytunah da ta shirya ta je ɗakin Sajid a kulle ta tarar da ɗakinsa, ta buga ya ƙi buɗe ma ta. Ƙarshe borin kunya kar ta je ɗakin ta Saudah ta mata dariya sai ta kwana a ɗakin Azra zuciyarta na ƙuna saboda abinda Sajid ya mata...

Washe gari ƙarfe takwas Zaytunah ta kai Saudah airport saboda jirgin ƙarfe goma za ta shiga. Daga airport ta wuce gidansu saboda tun da sassafe Mommy ta kira ta ta tuna mata akan lallai idan Saudah ta tafi tazo gida ta sameta.

KANO..

Tana zaune da ita a ɗaki tana jiran su Malam su zo. Mutumin da ya kaɗe ta ya shigo " Hajiya na yi magana da likita ya ce zuwa anjima za ta farfaɗo sannan ba abinda ya samu cikinta. Idan kin bani dama ina so zan je na yi sallah"

Mommy Aisha da tayi hamdala saboda maganarsa ta ce " kaje mana bawan Allah, ai Sallah ya fi komai"

Ta fara tunanin idan Ziha ta farfaɗo ta ji mi ya faru ta taho Kano sai ta kira 'yanuwanta ta sanar da su, tun da Alhamdulillah ba wani ciwo ta ji sosai ba.

Lokacin da Malam ya shigo ma Ziha ba ta tashi ba. Mommy Aisha ta yi masa bayanin komai ta ce ma sa Naziha ce 'yar marigayi AbdulSamad da Fatima. Buɗe bakin Malam ya ce "Aisha akwai sihiri ajikin yarinyar nan"........

LAGOS

Hassan mijin Saudah yana son surprising ɗinta idan ta dawo daga Kano sai dai ta ga ya yi gyaran gida. Ya san za ta ji daɗi sosai shi ya sa daga tafiyar ta ya kira masu aiki suka fara renovating gidan.

Washe gari da aka cigaba da gyaran ana fenti wani daga cikin masu aikin ya ga wata 'yar ƙaramar padlock a ta jikin ƙofa, padlock ɗin an ɗaure da wani jan ƙyalle ga shi an ɗan tsikara tsinken kwakwa a jiki.

Mai fentin ya fara ihu "Haaaa! haaa, e' gba mi ooo" yana nu na abin da ya gani. Da ya ke duk yawancin ma'aikatan wajen Yarabawa ne suna gani sai suka koma gefe su na ta ihu. Kowa ya san wannan abin asiri ne. Wani da ake cewa Ifagbemi shi ne da ya zo ya ga abin ya yi dariya ya ke ce musu " an ɗaure maigidan nan ne fa, ni kuma sai na kunce shi yau" dama Ifagbemi ɗan Babalawo ne. Wasu sunbatu na surkulle ya farayi a wajen kafin ya cire ƙwaɗon ya buɗe shi. Ya ce a kawo ma sa petrol ko kerosene. Da aka kawo ya cilla wa kwaɗonta. Yin hakan ya yi daidai lokacin da Hassan ya ke office, sai ji ya yi kansa ya fara ciwo. Ya tashi zai fita daga office ɗin sai ya faɗi ƙasa. Ko minti ɗaya bai yi ba ya buɗe ido yana tunano abubuwa dayawa a rayuwar sa. Lokaci guda tsanar Saudah ya shige shi. Ya tattara kayansa ya yi gida, shi ya ma manta ta tafi Kano...

©AzizatHamza2019