61
by @azizat
*MUTUM.....Mugu ne*
61
Ba ƙaramin gyara ake wa Nazira ba musamman da ya ke ba budurwa ba ce. Sai da za ta yi aure ta ke ƙara jin haushin yadda Inna Laure ta sa suka rasa budurcinsu a walaƙance. Allah ya isa kam sun fi dubu ta turawa Inna Laure.
Abin mamaki ana saura kwana huɗu ɗaurin aure sai ga Shamsiyya ta zo gidan su. Gaba ɗaya ta chanja ta yi bleaching ta yi wani iri. Wai ta zo bikin 'yaruwarta. Har da mota ta zo wanda ko ba a gaya musu ba ta san wani cikin abokanan harkanta ne suka siya mata.
Zuwanta ya sa Nazira ta ƙara tsanar Inna Laure da irin rayuwar da ta yi a baya.
Da ya ke a Azare za a ɗaura auren ranan Alhamis dukkansu suka wuce chan domin a cigaba da shirye-shirye. A can Malam kakan su Nazira da ya ga Shamsiyya sai ya kirata ya mata nasiha mai shiga rai, ta yi kamar ta ji, amma har lokacin huɗubar sheɗan yana nan yana yawo a zuciyarta. Ita Allah-Allah ta ke a gama biki ta wuce inda ta fito dan wani ƙaton gida aka siya mata a Kaduna. Anan ta ke harkanta yadda ta ga dama.
Ranar Jumu'ah aka ɗaura auren Muhammad Shabbir Yunusa da Shahidah Idris a garin Kirfi wanda ya samu halartar mutane da dama. Da ya ke bikin na gida ne kusan Alhaji Idris ne ya yi komai musamman da ya ke Shabbir ɗin har yanzu ba ya magana.
Ranar Asabat kuma su ka wuce Azare aka ɗaura auren Muhammad Shabbir Yunusa da Nazira Sulaiman. Da aka ɗaura auren har hawaye Abba ya yi saboda farin ciki. Ko ba komai Allah ya rufa masa asiri, Nazira ta yi aure.
Tuni Alhaji Idris ya sa aka gyara gidan Shabbir duk da ba wani babba bane gidan, amma a hakan SY ya ce zai zauna da matansa.
Tun ranan Alhamis aka zo aka yi wa Nazira jere a ɗakinta, kuma gaskiya Abba ya mata ƙoƙari dan ba ƙaramin kuɗi ya kashe ba.
Shahidah ma da Nana an musu, dan Alhaji Idris ne ya musu kayan ɗaki.
A ranan Asabat aka kai Shahidah ɗakin ta. Yayin da aka kai Nazira ranan Lahdi.
Har da Anty Zahra a ka kai Amarya, ta sha nasiha kuma an bata sirrika da dabarun riƙe miji. Abba kam sanda aka zo tafiya da ita da ƙyar aka raba su dan tun farko Nazira ɗiyarsa ce da ya ke tsananin so.
Duk da ɗakin Shahidah ya kwana amma hankalin sa na kan Nana saboda ya lura kwana biyun nan bata da lafiya amma kuma sai ta dinga nuna ma sa babu komai.
Amarya Shahidah dai period ya ruining mata first night ɗinta. Yammacin Asabat da aka kaita ta ga baƙonta babu shiri. Har ɗan hawaye sai da ta yi da ta gani. Ta dai ci kazarta sannan koba komai ta kwana a ƙirjin mijinta kuma masoyinta wanda ta jima tana dakon son shi.
Kwana biyu ya yi a ɗakin ta ya koma ɗakin Amarya Nazira. Ya ga tarairaya da soyayya a wajen ta, domin kuwa da bai san ta taɓa yin harka a waje ba sai ya tambayi inda ta san dabarun gamsar da miji haka.
Zaman su gwanin sha'awa kowacce ranar girkin ta ƙoƙarin farantawa mijinta ta ke. Sai dai abu ɗaya, Nana bata da lafiya, dan tun ta na ɓoyewa har ya zama yanzu kam dukkansu sun sani shi yasa suke tausaya mata, ranar girkin ta ma Nazira ce ta ke ma ta girkin. Da aka kaita asibiti cewa su ka yi damuwa ne ya mata yawa da hawan jini. Kwana biyu aka sallamota.
Yau ma kwananta ne amma tana kwance saboda jiya ma da zazzaɓi ta kwana. Nazira ta shigo ɗauke da tray.
"Anty ki tashi ki ci abinci na gama" ta ajiye tray ɗin a ɗan ƙaramin table da ke ɗakin.
Daga inda ta ke kwance ta ce " dan Allah ki kira min Muhammad"
Ta ƙarasa bakin gado ta ce " Anty jikin ne?" Ta sa hannu a goshinta ta ji shi da zafi.
"Barin ɗauko wayata a ɗaki" ta fita da sauri.
Da shike yanzu saboda rashin magana Shabbir desk job aka mai dashi, shi yasa ma ya ke samun lokaci wa iyalinsa, ba kaman da da ya ke field work ba, ko yaushe suna aikin undercover.
Nazira ta kira shi ta sanar da shi, da ya ke yana ji amma ba ya iya maidawa ne sai ya kashe kiran ya tura ma ta text akan gashi nan zuwa.
Ba a fi minti arba'in ba sai ga shi ya zo. Nana ta kwanta jikinsa yana ɗan bubbuga mata baya, da ƙyar ta yadda ta ci abinci kaɗan. Da Nazira ta zo tattara kwanukan kamar daga sama ta ji Nana ta ce " ki yawaita addu'a Nazira, ba za ki haihu da yawa ba kuma ba za ki haihu da wuri ba"
Nazira ta ce "Na gode" ta yi saurin fita daga ɗakin saboda kar hawayen da ta ke maƙalewa su zubo.
Daren ranan da misalin ƙarfe shabiyu Nana ta rasu. Kukan Shabbir ne ma ya tashi sauran matan nasa. Kafin Asuba su ka mata wanka su ka mata sutura. Washegari ƙarfe bakwai a ka kaita. Ko da aka bugawa Malam Ibrahim aka sanar da shi ya ji abin a ransa sosai dan har kuka ya yi, ba dan shima yana fama da jiki ba da Abujan zai zo ya yiwa Shabbir ta'aziya.
Bayan kwana shabiyar da rasuwan Nana Shabbir ya tafi Maiduguri saboda jikin Malam Ibrahim da ya yi tsanani. Abunda Nazira da Shahidah ba su sani ba shine tun daren ranar da Nana ta rasu Shabbir ya fara magana sai dai ya ɓoyewa kowa sai Malam kawai ya sanarwa.
" mi yasa mugayen mutane su ka yi yawa a doron ƙasa? mi yasa son zuciya ya yi yawa? Mi yasa masu aikata laifuffuka Allah ba ya tona asirin su? sai ka ga wani lokaci su jima suna ɓarna kuma su ƙi mutuwa da wuri" Shabbir ya faɗa yana hawaye
Malam da ke kwance yana jin jiki ya ce " a koda yaushe ka ji tsoron Allah, sheɗan yana nan yana bin cikin jininmu domin ya ga mun kauce wa bautar Allah, mun kauce wa bin dokokin Allah. Mafitar shine mu yawaita neman tsari daga sharrin sheɗan la'ananne. Domin yanayin imaninka yanayin yadda zai zo domin ya ruguza ma ka ayyukanka. Ka duba Alƙasim mahaifin Nana Khadija, da karatunsa amma hakan bai hana sheɗan ya ingiza shi zuwa ga shirka da aikata manya manyan zunubai ba. Haka nan sauran mutane abu ƙanƙani sai ya kai mutum ga aikata shirka. Mace ba ta son kishiya sai wajen boka, ɗan kasuwa yana son kasuwar sa ta bunƙasa sai wajen masu tsibbu, kana son farin jini, kana son samun suna da ɗaukaka duk sai ido ya rufe, maimakon a roƙi Allah wanda shine Mabuwayi mai bayarwa a wanda ya so ya hana wanda ya so. Sai a koma neman taimako a wajen Aljanu da Sheɗanu. Allah ya daɗa shiryar da mu, Amin"
Shabbir ma ya amsa da Amin.
Shiru ne ya biyo bayan hakan na wani lokaci.
Kalmar Shahadar da Malam yai ne ya sa Shabbir saurin ɗagowa tareda sauran wanda suke ɗakin wanda itace kalmar ƙarshe da Malam ɗin ya yi a duniya.
Ɗaukakan da Allah ya baka daban ta ke da ta mutane ko Aljanu. Shabbir ya ga jama'a kam a wajen jana'izar Malam Ibrahim duk da Malam ɗin ba wani sananne ba ne ko na ce ba public figure ba ne. Sai a kwana na uku Sheikh Sidi Alƙasim ya zo ta'aziya, nan ma ya zo ne saboda kar mutane su zargi wani abu dan an san alaƙar Malam ɗin da shi Sheikh ɗin.
Dama ranar farkon rasuwar Aljanunsa ma su ma sa hidima ne suka ce masa kada ya je, dan idan ya je wajen gawar ko ƙabarin Malam duk wani aiki da su ke masa zai lalace shi yasa sai a ranan na uku ya je.
Shabbir da ya ga yadda mutane ke haɓa-haɓa da shi wani haushi ya ji a ransa. Mutum ƙusurgumin Mushriki amma mutane suna ta wani tararradin sa kamar wani Mumini, su a hakan kallon waliyyi su ke ma sa. Sai da aka yi bakwai ɗin Malam sannan ya koma Abuja. A ranan da ya dawo Nazira itama ta dawo daga Bauchi, sunan 'yar Anty Zahra ta je wadda Abba ya maidawa yarinyar sunan Waheedah...
Suna zaune a kitchen suna girki ana taɓa hira. Jollof ɗin shikafa ne Shahidah za ta yi amma ƙarnin kifin da ya sa ta amai ɗazu ya sa Nazira ƙarɓan kifin tana gyarawa.
"Assalamu Alaikum" ba dan dukkan su biyu sun san muryan Shabbir ba tun kafin ya kurmance da sai su rantse ba shi bane. Gaba ɗaya suka ɗaga ido suna kallon shi. Ya kashe mu su ido ya ce "tunda ko oyoyo ba zan samu ba gobe zan fita na nemo tsaleliyar budurwa....." ai bai ƙarasa ba gaba ɗayansu su ka je su ka rungume shi.
"Alhamdulillah! Yaya ashe ka fara magana" Nazira ta faɗa tana hawaye. Ita ma Shahidar hawaye ne a idanunta "yanzu dai ba kuka za ku min ba, domin abin farinciki ne gashi ko sujjadar godiya ba ku yi ba" gaba ɗaya su ka yi saurin yin sujjada a kitchen ɗin, abin har dariya ya bashi. Shi kam Alhamdulillah da ya bashi mata ma su hankali da haƙuri su ka zaɓi su zauna lafiya su faranta ma sa rai maimakon su yi ta yiwa juna kishin hauka kishin da babu lada. Irin kishin da su ke yi ma sa tsabtacacciya ce....
***
ABUJA
Awa biyar kenan da aka gama yiwa Sajid aiki ga shi jini leda biyu ya sha saboda ya zubar da jini sosai hakan ma ance washe gari za a ƙara masa ɗaya. Ya bugu a gefen kansa sosai sai kuma ƙafarsa wanda likita yace kafin Sajid ya yi tafiya normal sai an ɗau lokaci.
" please i'm sorry, ka ji My one, wallahi duk inda Naziha ta ke zan nemo ma ka ita. Please wake up, wallahi ba zan sake tada ma hankali ba, idan ma ba ka so na zauna tareda ku na yadda zan zauna a wani gida daban. Please don't die"
Zaytunah ne ke tsugunne gaban gadon da aka kwantar da Sajid tana magana tana kuka. Idan ka ganta abin tausayi.
Alhaji da su Daddy ne suka shigo ɗakin wanda isowar su Alhajin kenan.
Da ta kalli Alhaji ko iya gaishe shi ba ta yi ba saboda kunyarsa, ta san yanzu kam an gaya ma sa duk abinda ta aikata.
Daddy ne ya ce "tashi ki bamu waje" ba musu ta tashi ta fita ta haɗu da Mommy da su Ummi da wasu da ko tsayawa duba su waye bata yi ba. Wani waje da ba mutane ta samu ta zauna ta fito da wayarta ta fara kiran numbar Malam ta yi kira ya fi sau goma amma ba ya shiga dama tana so tace masa ya karya kurciyar da aka yiwa Naziha, domin yanzu so ta ke Naziha ta dawo gida. Ganin numbar ta ƙi shiga ya sa ta kira numbar Saudah itama dai ba a ɗauka ba sai a kira na uku. Da aka ɗauka ta ce "Hello Saudah numbar Malam ba ya shiga I want...."
"Umman Saudah ce, ke ma 'yaruwarta ce ma su bin Malaman tsibbu ko?"
Zaytunah ta yi shiru gaba ɗaya kunya ya cikata.
A hankali Umman Saudah ta fara ma ta nasiha tareda faɗa mata abin da ya samu Sauda.
Lokacin da ta katse kiran jikinta sai ɓari ya ke tsoro ya cikata. " Saudah ta ƙone" Shi ne abin da zuciyar ta ke ta maimaitawa...
©AzizatHamza2019