Chapter 35
by @maidambu41
*BAƘIN HAURE....🐾🐾*
{Greed for Money is the roots of all evils🫀}
Arewabooks:maidambu41
Wattpad:Mai_Dambu
Mallakar:Mai_Dambu
*Alhamdulillahi na gode sosai, marubuta da makaranta Allah ya saka da alkhairi, musamman yan grp din Fitilar hikayar Dambuje, Allah ya bada lada naga kira da sakonnin ku. Allah ya karo dubun zumunci, Ubangiji ya jikan dukkan yan uwa musulmai da suke faɗin duniya, tare da iyayenmu bakiɗaya... Allahumma Amin*
035
_Yau kan babu editing 🥰_
Nad'e hannunshi yayi a kirji, yana kallonta yadda take gurfane a gabanshi. "Ba xance kada ki hana shi ba, amma tabbas nayi ido biyu da shi, sai dai Uwarshi ta kara haifar wani koda yake ina zao ganta. Amma ki saka idanu akan shi domin." Sake hannunshi yayi ya nufi kofar fita yana faɗin. "Duk yadda kika so, kiyi amma inuwar Ba'are da al'ummar gidan kada na kuma ganinku." Daga haka ya bar mata dakin da gidan bakidaya. Wani irin zufa ke karyo mata, yana fita da gudu ta mike ta ɗauki goran ruwan da yake gefen gadonta, sai da ta shanye goran bakiɗaya, sannan ta ajiye. Zirga zirga ta fara a cikin dakin tana jin kamar tayi ta kurma ihu, Hajiya Sa'a ta gaya mata magana akan haka, yanzu ma Majid ya kara gaya mata, haka yaná nufin sun san kome akanta, ita ce dai bata san kome akansu ba, wanda ta sani ma na bogi ne domin sune suka san wacece ita.
Hannu ta saka a kai, kafin ta koma ta zauna tana jin kamar ta tattara yan abin da take da shi ta gudu, domin zuwa yanzu da Majid yasan Sajjid ba dan Mamman ba'are ba ne, zai fi mata kyau tayi ta gudun hijira. Ai na Majid wasa ne akan na Sajjid don binne ta zai yi da ranta, matukar yaji wani labari mara daɗi akan waye shi, cikinta ne yayi wani irin murdewa a daddafe ta shiga toilet. Bata san ya aka yi ba, sai g kashi shaaaa cikinta ya tsinke. Wato Majid bala'i ne, idan ta sake wani abu ya kara had'a su. Binne kanta zata yi da ranta kafin Majid ya zo gare ta, don na Majid me sauki.
Koda ta fito daga ban dakin, a daddafe ta nime wuri ta zauna. Can cikin ya kuma murdeta, da sauri ta shiga banɗakin ta zauna akan wurin kashin.
A lokacin da ya bar gidan Tani, a hankali yake jin wani irin abu yana yawo a kanshi, har wani nutsuwa yake ji, Hajiya Tani ba ita daya ba ce akwai wasu a bayanta. Bari ya ga iya gudun Tani domin idan akwai wani a bayanta dole zai fito, don haka ya tab'a spot point. Lokacin da ya isa asibitin Hajiya tana barci, zama yayi na wani lokaci kafin ya mike ya nufi Office ɗinshi, bude drowe office din yayi ya ciro abin sallah da jallabiya, murmushi yayi domin yasan aikin Jami'ah da Aryan ne, sune zasu nishi haka.
Ban daki ya shiga yayi alola, ya fito ya shimfida abin sallah, tun ya fara sallah nan karfe uku bai tsaya ba sai da Masallacin asibitin aka kusan shiga sallah, ya sallame ya nufi masallaci. Bayan an idar da sallah ya zauna yana addu'a, sai da rana ta fito sannan ya wuce asibitin. Anan ya samu Anisah da Salamatu sun shigo. "Hammayo!" Ta kira sunanshi, bude mata gefen hannunshi yayi ta isa wurin tana kuka kamar ranta zai fita. "Hamma kayi hakuri." "Shiiii!" "Duk laifina ne, da na fada maka haka da bai faru ba." "Ya isa haka, kin yi barci kuwa?" Ya tambaye ta cikin kulawa, "Nayi su'ad ya saka ni nayi barci." Murmushi yayi ya ce mata. "Good girl, muje ki bani abinci naci don naga basket a hannun Mama Salamatu." Ya faɗi haka don ya kwantar mata da hankali. Har dakin da Hajiya take suka shiga, "ina zuwa ko" ya faɗa yana nufar dakinsu Aryan a can ya samu Matarshi tana ta kuka. "Ya isa haka, ya farka fa bari na duba shi." Ya faɗa yana shiga dakin,duba shi yayi yaga lafiya lau barci yake, bai tashe shi ba ya nufi wurin Amaan, ya shafa kanshi tausayin shi ya masifar cika mishi zuciya, duk da rashin jituwa da yake tsakaninsu, haka bai tab'a damunshi ba, domin yasan wata rana zai gane gaskiya, duba karin wurin yayi yana me saka mishi wani ruwan. Sannan ya wuce kan Aryan da yake ta motsi. A hankali ya isa kanshi, ya cigaba da dube-dube har ya farka. "Welcome back Mr Mamman Ba'are." "Anisah fa?" Tab'e baki Majid yayi, sannan ya ce mishi."Na zata matarka da Yaranka zaka tambaya." "Wani hali kanwata take ciki?" "Ina zan sani tunda ina tsaye akanku." "Hamma kasan bala'in da na gani jiya." "Ina zan sani ragon maza." Ya faɗa yana murmushi, d'ago shi yayi ya zauna. "Hamma!" "Guduma!" Ya faɗa yana murmushi, don ya gaji da maganar Aryan. "Hamma Abdul Majid."
"Anisah tana lafiya, wurin Hajiya matarka tana waje bari ta shigo." Ajiyar zuciya ya sauke, "Manyan mota biyu suka tasamu a gaba, Hamma dole na firgita." "Allah ya kiyayye na gaba." Ya faɗa yana ƙara duba shi. "Ina ke maka ciwo yanzu?" Ya tambaye. "Hakarkarina ke ciwo." Matsawa yayi ya d'aga mishi hannunshi, da sauri ya riko hannun Majid, "Hamma bari kawai." Sake hannun yayi yana dauki wani littafi yayi rubutu, sannan ya ce mishi. "Motar ya doke ku ne?" "Tsakiyarsu suka saka mu, wallahi ban san yadda aka yi aka ciro mu a ciki ba."
"Anjima zaa zo a kaika x-ray, mu ga wurin " inji Majid, juyawa Aryan yayi yana kallon Amaan, "bai farka ba ko?" Ya tambaye shi idanunshi cike da kwalla. "Ba shi ne matsalata ba, Jamilah tana da ciki, kuma har yanzu bata farka ba." Shiru ne ya gifta a dakin, dukkansu babu me kuzarin magana, fita yayi ya nufi ICU, inda aka kwantar da Jamilah. Yana shiga yaga yadda kome yake tafiya a cikin na'urar da aka saka mata, amma ya kasa tabuka kome dake ya samu wasu drs akanta, sai ya zama kamar dan kallo, haka ya juyo daga dakin ya gagara yin kome, a bakin kofar ya samu Mijinta, dasu Nanah.
"Ya jikin nata?" Kallon kayan jikinshi yayi kafin ya ce mata. "Da sauki." "Kace anan kake zaune?" "Eh!" "Ayya to dama ina babu wanda ya mutu?" Banza ya bawa ajiyarta, ya cigaba da tafiya. "Kai kurma ne ina magana kayi banza dani." Uffan bai ce ba. " Yau ga lalacewar duniya, kai yanzu ina magana kayi banza dani don kaga na tako inda kake? Yanzu don."
"Me kika ce ne?" Ya juya yana me tambayarta da sigar renin hankali. "Uwarka Sa'adatu da ta haifi ɗan karuwi." Murmushi yayi tare da cigaba da tafiya, tana kuwa bin shi, tana zagin shi. Sai kallonsu ake shi kuwa ko a jikinshi. Yana isa kofar office din shi ya ce mata. "Idan kin gama jarabararki, na gode sai ko wuce gida domin na fito na same ki wallahi ni kaɗai nasan me zan dirka miki a asibitin nan." Ware idanu tayi tana faɗin "yanzu don baka da imani sai kayi min wani abu? Tambayarka nake sai kayi min wani abu!"
Hango wata nurse yayi ya ce mata. "Ki kawo min babban sirinjin allura tare da maganin nan, yanzu." "Ke dan uwarki kika kawo wani abu, sai na saka an kore ki a asibitin nan, kafira me kama da fatalwa. Kai kuma zamu gamu da juna, mara mutunci dan banza me kama da gwaggon biri "
Murmushi yayi ya rufe kofar shi, domin yasan Nana da dan banza tsoro, kuma bai zama dole ta kuma dawowa ba, murmushi yayi shi kaɗai, har ya gama sauya kaya. Ya fito dakin Hajiya, ya samu ta farka sai kuka Anisah take Nana sai surutu take ta musu da sababi. Safar hannu ya saka tare da haɗa kayan aikin ya cire ruwan daya kusan karewa, ya saka wani sannan ya zuba mata allura a ciki. Yana kallon yadda take kallonshi kamar irin ta farka daga cutar makanta, ya sani tana mamakin yadda aka yi babu abin da ya same shi. Sai da ya gama sannan ya dawo gabanta ya riko hannunta, ya saka a fuskarshi."Hajiyana nine Majid Mamman Ba'are gani nan lafiyana lau, ki kwantar da hankalinki." Murmushi me had'e da hawaye ta sake tana kallonshi har barci yayi nasarar gaba da ita. "Nana muje na kai ki gida kinji." Kallonshi tayi a kaikaice irin zata kafta mishi rashin mutunci. Yadda ya saka fuskar sojojin tuni hankalinta ya dawo jikinta, "hmmm muje!" Ta ce tana shirin mita. "Nisah kema idan ba da motarki kika zo ba, zo muje na ajiye ki kada na kuma ganinki tunda kuka zaki na mana asibitin. "
"Don Allah kayi hakuri ba zan kuma, na daina kukan." Ta fada tana k'amk'ame jikinta alamar ba zata fito ba, "ok muje ki ga jikin Aryan da Amaan." Mikewa tayi suka fita, har dakin a lokacin Aryan yana Sallah, yana idar da sallah. "Hamma Aryan?" Ajiyar zuciya ya sauke. "Ya jikinka?" Ta fada tana kuka, "Ya isa Auta, ba gashi naji sauki ba. Bar kuka ina fatan babu abinda ya same miki ko?" Girgixa mishi kai tayi tana share hawayen da yake zuba mata. "Bari na kai matar nan gida " "kaga matar nan a kofar dakinka, ni ba matar nan ba ce." Ta fada tana wani dauke kai, ita fa gara mata ma Majid da wannan me kalar zabiyar haushi yaƙe bata, balla mishi harara tayi. "Don kana gadara da Alhaji yana tsaye sai ka kashe min jikoki, dan banza me kama da mutanen boye." "Muje!" Majid ya faɗa mata, domin ya lura jaraba take nima. "Aikin banza kishiya da shashasha, da ka kafe ni da idanun kamar na mayu kurwana kur, idan ma ka kirkiro hatsarin ne don su mutu kaci kasonsu kayi karya, ina sane daku munafunkin banza munafikin wofi." Maganar Nana tayiwa Aryan tsauri amma kuma sai yayi murmushi ya ce mata. "Ai ke zan fara turawa lahira, domin na gaji wannan gwal din wuyarki." Wani dafe kirji tayi, tana nuna shi tare da kallon Majid. "Kaji ba, yana shirye shiryen turani lahira bayan ban ga matarka ba, dan bakin ciki wannan sarkan na matar Alhaji ne ko mutuwa nayi bata cikin gadona."
"Ai kuwa ki saka idanu sai kin garzaya barzahu bari a sallame ni, domin zan fara aikatar da aikina ne akanki."
"Wallahi baka isa ba, sai kotu da yan sanda sun shiga tsakaninmu, na rantse da Allah ba zan yarda ba, ko tuntube nayi Alhaji kai zaka nimo min lauya domin Ariyan ya shirya kisan kai, ya ga baya tow na rantse da Allah sai nayi fatalwa ko na mutu na kwaci hakkina."
"La fatalwa ma zaki zama?" "Kwarai don ba barin hakkin jinina zan yi ba." Ta fada tana hura hanci kamar ta doka mishi sandan hannunta. "Tsuhuwa lokacinki yayi, sai a fara shiri kafin na zo." "Alhaji kana jin shi ko." "Muje ki daina biye mishi, cinnaka Aryan ba zai kashe ba, balle dan mutum nayi mishi wannan shaidar tun daga duniya har lahira ba zai kashe wani ba."
"Au hatsarin da ya ja musu fa?"
"Muje a hankali zaki fahimci abin da yake faruwa." Haka ya fita da ita, " Nabeeha wai zan iya kashe ..." Hannu ta saka mishi a baki, "Tsakanin harshe da hakori ana samun sab'ani, haka tsakanin mutum da mutum ana samu, Aryan ban kowa a duniyarka ba, sai adalcinka har abada ba zaka b'ata hannunka da jinin kowa ba in sha Allah."
Ta fada tana kuka, tana son Mijinta kuma bata ji a ranta zata zarge shi ba. "Idan Hamma!" "Hamma Aryan, itama Nana gurbata mata tunani ake da zancen banza, muji da halin da Amaan da Jamilah suke ciki."
Shiru dakin ya dauka, babu wanda ya kuma magana, sannan Mijin Jamilah da dangin shi suna asibitin, hatsarinsu yasa videon Amaan ya mutu, sai aka koma labarin hatsarin domin abin ya faru ne da safen jiya, kuma kowa ya ga yadda abubuwan suka faru, sai aka shiga yayyata videon hatsarin da yadda abin ya faru, sama da labarin Hajiya da Amaan. Wannan al'amarin ya faru cikin kwana ɗaya, sai ya zama kome ya tafi kamar bai faru ba, don haka Majid shima yayi amfani da nashi kwarewar yasa aka binciko mishi wanda ya sake videon Amaan. Ai kuwa gayen yaci uban dokar sojoji.
* Tunda Majid ya bar Tani a ɗakinta har gari ya waye bata fito ba, koda Hajiya Fauziya tazo gidan a daki ta same ta, don ta kawo mata tsegumi ganin halin da take ciki yasa, bata iya bata labarin ba. Domin ta same ta ta birkita dakin tana niman abu.
"Tani lafiya?"
"Lafiyan kenan wayata nake nima." Kallonta Hajiya Fauziya tayi baki sake ta ce mata. "Ban gane wyaarki ba, wanene a gefen gadonki?" Juyawa tayi ta ganshi ta ce mata. "Ikon Allah, ban san yana wurin ba." Ta dauka da sauri har yana kokarin faɗuwa a hannunta, ta shiga kiran Sajjid..
"Dauka mana."
Katse kiran aka yi ta kuma kiranshi, sai da tayi bugu uku sannan aka ɗauka a make ya ce mata. "Dalla me zan miki?" "Idan kana cikin Niamey tow ka gaggauta barin garin nan, Majid na gaya maka Majid. Wallahi kafin wayewar gari nayi kashi ya kai sau goma maza ka bar garin nan ka kashe wayarka kada ka kunna sai nan da wata uku na gaya maka kada ka dawo Nijar "
"Babu inda zanje, ina garin nan wallahi."
"Na gaya maka kamar kare zai kashe ka, domin ko ya kashe ka babu abinda zai faru, ya fika gata ya fika kome ka kyale kome ka bar garin nan daga baya zamu yi magana don Allah." Ta fada a raunane, "Ni dai ban ji dadi ba, kawai zan tafi ne ba don ina da ra'ayi ba."
"Jeka don Allah da kuma ni." Kit ya kashe wayar yana mita. Itama zama tayi dabas da malmalan duwawunta tayi da kasa, a hankali ta sauke ajiyar zuciya me nauyi domin sai yanzu taji abu ya wuce mata, d'ago kai tayi a matuƙar gajiye ta kalli Hajiya Fauziya.
"Uwar me kika zo yi?"
"Hmmm! Hmm dama na gaya miki Aryan ya farfaɗo sannan an kama kama mutanen da suka yi ta."
"Je ki don Allah domin kin zama tauraruwa mai wutsiya, ganinki babu alkhairi domin nasan sharri ke tafe dake, don haka tafi wanda nake ciki ma ya ishe ni wallahi."
"Hmmm daga abin arziki, amma tunda bakya son na gaya miki shi kenan." Ta juya tana jin haushi kamar zata rufe Hajiya Tani da duka, don tazo da mugun labarin cewa an kama yaron da suka saka aiki. Don ba iya Sajjid yake mocking Amaan da yan uwanshi ba, har da taimakonsu....... *Kuyi hakuri babu yawa*
*₦300*
***
#Mai_Dambu ce....